Showing 228001 words to 231000 words out of 260401 words

Chapter 77 - Dare da Duhu complete

/>
ɗ

a masa gangi ya ce.

"Ƙarya yake Afra, ta ya ya zaki aure wanda ki ka girma yayanki ne shi bai dace ya zama mijinki ba, ni ne daidai da rayuwar ki" ya fa

ɗ

a yana jawota jikinsa sbd zafin da zuciyarsa ke masa.

"Don't try to hug the girl I'm going

to marry again, na fika hauka zafin kishina yafi naka, kuma ka kusa daina ganin ko fuskarta, ita

ɗ

in mallakina ce"

"Idan kai namiji ne sai ka hanani abin da na yi niyya" Adnan ya fa

ɗ

a cikin raunin murya tare da ƙoƙarin kama bakin Afra da niyyar kissing

. Cikin zafin zuciya Salman ya tattare hannun rigarsa farar fuskarsa ta yi jajir sbd abin da Adnan

ɗ

in yake ƙoƙarin yi

ɗ

in.

Saukar marin da Salman ya ji ne ya sanya ya tsaya da sauri baki bu

ɗ

e yake kallon Afra wacce ta fisge kanta da ƙyar daga hannun Ad

nan ta kuma sauke masa marin da ita kanta bata san tayi ba. Idanuna ya cika da hawaye sbd nauyin marin da tayi ya kalli Adnan ta ce.

"Wa kake da suna? Wallahi na tsaneka ba zan ta

ɓ

a son ka maye kawai"

"Koda zan fa

ɗ

a miki su waye iyayenki na gaskiya?

" Ta watsa masa harara ta ce "Ai ƙarya kake tun a garinmu kake yaudarata, babu wasu iyayena daka sani"

Adnan ya fara tari sosai idanunsa na rufewa tari yaci ƙarfin sa. Abbi da Mami da suke tsaye tun

ɗ

azo suka ji kuma suka kaga abin da ke faruwa suka shi

go cikin parlourn da sauri.

"Subuhanallah! Adnan lafiya me ya sameka? Na'ima kawo mini ruwa" Adnan yakai hannu bakinsa sai ka jini ya wanke masa tafin hannun da alama kamar aman jini yake. Bai damu da halin da yake ciki ba, tarin na sarƙafe masa numfashi

cikin mayuyacin hali ya kalli Afra da jikinta ya gama sanyi baki

ɗ

aya ya ce.

"Ko da zance maki Dr G.Y Bulama shi ne mahaifinki na gaskiya..." Cak numfashin sa ya tsaya jikinsa ya saki a jikin Abbi, a ki

ɗ

ime Abbi ya ce "Salman get the car"

A hankal

i cikin nutsuwa da kamala Abdullah ke driving motar daga Airport zuwa gida. Yana mamakin abin da ya hana Uncle

ɗ

in magana, girgiza kai ya yi yana mai da idanunsa kan titi yasan yau Ummi kwanan farin ciki za tayi speaking calmly ya ce.

"Uncle lafiya dai?"

Wanda aka kira da Uncle ya juya ya kalli Abdullah a hankali ya ce.

"Alhmd Abdullah" ba wanda ya sake magana a haka suka ƙarasa gida, Abdullah yai horn a gaban makaken gidan iya ha

ɗ

uwa ya yi gatekeeper ya bu

ɗ

e, a parking lot sukai parking kafin Abdullah

ya fita ya riga shi.

Ummi na zaune ta yi ado cikin wani dakakken lace sai

ɗ

aukan ido yake ga gwalalen dake zube a hannunta. Ƙamshin turaren shi yasa ta tabbatar da zuwan mijin nata bayan wasu watanni zuwa shekara. Tsaye ta gansa ya zuba mata idanu cike da

tunani a ransa da kuma son Ummi

ɗ

in saura ka

ɗ

an ya yi kuskure a rayuwarsa.

Ummi ta miƙe tsaye tare da ƙara sawa gabansa ta ce. "Wlcm Man" murmushi ya ƙirƙira kafin ya ce "I missing Maaah" girgiza kai kawai tayi suka ƙarasa parlour idanunsa a kanta ya ce

"Kiran gaggawa ina tsaka da bu

ɗ

e sabon company hope lafiya dai?" Tai murmushi cikin sanyin maganar ta ce.

"Ka fara yin wanka kaci abinci?"

"I can't dole na fara jin damuwarki a gigice na tahu" ta gyara zama cikin damuwa ta ce "Abubuwa ne suke ta fara

, gaba

ɗ

aya dukiyata na neman lalacewa kullum cikin asara da rasa ku

ɗ

a

ɗ

e nake, na rasa inda abin ya samu tushe ina son magance matsalar, wannan dalilin ya sanya na saka Abdullah ya rufe company ta kalman dana bu

ɗ

e" Ya runtse idanunsa domin abin ya zo masa

a bazata bai

ɗ

auka abin zai sauri har haka ba, shi bama wannan ce damuwar shi ba.

Yana ƙoƙarin magana wayar shi tayi ringing ganin wata number ya share, Ummi ta kafe shi da idanu can dai ya

ɗ

aga a fusace ya ce.

"Wai mene?" Tsaki kawai yaja ya ce.

"Allah

ya sawwaƙe" Ummi ta ce "Waye ba lafiya?" Yaja tsaki ya ce "No wani ma'aikacina ne" tana ƙoƙarin wata maganar aka sake kiran shi da sauri ya miƙe ganin number wanda yake ta jira. Jikinsa na rawa yama mance a gaban waye yake.

"Hello, Assalamu alaika" daga

can wayar aka ce "Muna magana da Dr Bulama" ya juya ya kalli Ummi ya ce "E, shi ne" aka ce "Mahaifin Adnan Aliyu Matawalle ke magana, ina son ganinka domin samun tabbaci shin da gaske Abra da Afra yaranka ne kai ne real father nasu?" Gaba

ɗ

aya jikin Uncle

ko nace Dr Bulama rawa yake ya ce "Oh!ok yanzu haka Ina Dubai, amma zuwa gobe zan sauka Nigeria I'll call you" Abba da Abbi suka kalli juna a tare suka ce "Dubai????" Ya ce "Eh, amma gobe zan zo Insha Allah" kashe wayar ya yi gaba

ɗ

aya jikinsa rawa yake ya

ce. "Rumaisa daman yaranmu ba mutuwa sukai ba???" Ummi da Abdullah suka ce "What???....

[11/22, 4:52 PM] Abk: Cikin gigicewa, da gur

ɓ

atacciyar hausarta, ta fara ha

ɗ

a larabci, turanci da kuma hausa, ta kalli Bulama ta ce "Wane irin zance ne kake mini haka

? Kamar yaya yaranmu ba mutuwa suka yi ba? Bayan ina labor room, aka ce mini na haifi yara tagwaye amma babu rai?".

Jiki a sanyaye Bulama ya ce "Nima abin da nake mamaki kenan, ta yaya za ce suna raye?".

Ummi ta ce "Wai wani irin zance ne wannan? Baka

tabattar ba kenan, ya kake son ka yi mini wasa da hankali Yusuf Bulama?".

Abdullah ya tattaro nutsuwarsa ya kalli Bulama, shi ya iya hausa sosai ba kamr rumaisa ba, ya ce "Ka sakamuna ru

ɗ

u ya kai Yusuf, ka sani cewa wannan maganganun naka barazana ne ga t

unaninmu, da kuma zukatanmu, amma kuma biri ya yi kama da mutum, zan iya gasgata ka akan abin da kake fa

ɗ

a, amma bamu labari, kafin ni in sanar da ku wani abu mai mahimmanci da Yakamata in fa

ɗ

a".

Bulama yayi jimm, sannan ya basu labari tiryan-tiryan yadda

abubuwa suka wakana, har zuwa lokacin da Abra ta rasu.

Gigicewa Rumai ta yi, yarana suna raye,

ɗ

aya ta mutu? Waye ya yi mini wannan zaluncin, na rayu shekaru Ashirin da hu

ɗ

u cikin

ɗ

acin rai da ƙunar zuciya, yarana na raye amma suk rayu nesa da ni, ya za

ayi ace na haifi yara aka ce mini sun mutu? Meyasa aka mini haka Ya kai Yusuf, ya a kai ka tabbatar da yarana na raye? Ka kaini in gansu a ina suke, ko da yake kace mini

ɗ

aya ta mutu, to ina

ɗ

ayar a ina take? Dan Allah kar ka gaya mini abin da ba zai yiwu

ba, in saka rai kuma in zo ba yarana ba ne".

Abdallah yayi ajiyar zuciya ya ce "A shekarun baya,  da naje Nigeria, a garin Kano, naje sayayya wani mall, na ha

ɗ

u da wata yarinya da sai da hantar cikina ta ka

ɗ

a saboda mamaki. Tana tsananin kama da shi Yus

uf, kuma akwai wasu kamanni da ta

ɗ

auko na ki, hatta wannan

ɗ

igon baƙin na gefen idonki ta na da shi, mamaki da rikicewa ya sanya na kai hannu fuskarta, wanda suke tare da shi ya mareni, ina tunanin mijinta ne a wannan lokacin, ita yarinyar ta tsorata, har

ta suma, ya

ɗ

auketa suka bar wurin. Still a watannin da suka shu

ɗ

e, na ha

ɗ

u da ita a nan Dubai, amma ita da wani daban n kuma ganinta, amma ban yi mata Magana ba saboda wanda suke tare ya mini kwarjini da yawa, kuma ina tsoron abin da ya faru wacan lokaci

n ya kuma faruwa, idan kuwa haka ne ina kyautata zaton ko da duk mutum

ɗ

aya na gani, ko kuma su biyun ne Amma sanin gaibu sai Allah".

Fashewa da kuka Ummi tayi, tana fitar da tulin damuwar da ke mamaye a ranta, saboda tun bayan haihuwar yaran nan ba ta

kuma samun wani rabon ba, kuma gashi Allah ya jarabce ta da son yara, yo ta ina ma zata samu rabo, miji ma wata ƙasar ita ma tana wata ƙasar daban, sai su shafe watanni hu

ɗ

u wani bai sa wani a idonsa ba.

Cikin kuka ta ce "Abdallah, a gaggauta neman mini v

isa Nigeria, muje ya nuna mini 'ya'yana, ni da da yadda za ayi, a yanzun nan zamu tafi, amma ni haryanzu na kasa gazgata hakan"

Bulama ya rungumeta a jikinsa yana rarrashinta, tare da bata tabbacin cewa zasu tafi Nigeria tare, dan tabattar da abin da ya

ke fa

ɗ

a mata.

Afra kuwa ta

ɗ

an fara tausayin Adnan, saboda yadda aka ce yana aman jini, gaba

ɗ

aya baya hayyacinsa, amma sam ita Adnan bai mata ba, kallon mugu take masa, saboda yanayinsa yadda yake wasu abubuwan da zafi, Salman ya fishi kirki da bin kom

ai a hankali, dan haka ita ba ta ga ta yadda zata za

ɓ

i Adnan ba, ga salihi mai lalla

ɓ

ata.

Adnan kuwa yana kwance a gadon asibiti, an

ɗ

aura masa drip, sai dai yadda yake numfashi kawai ya isa ya tabbatar maka da cewar, yana jin jiki, daga nesa ana iya ga

nin yadda ƙirjinsa ke fat-fat da sauri da sauri.

Abbi kam mamaki ya cigaba da yi, dama Adnan ya san mahaifin Abra, amma yayi shiru da bakinsa bai fa

ɗ

a ba? To yaya ma aka yi ya tabattar da Bulama ne mahaifinsu, ko dai zafin ciwo me ya sanya shi fa

ɗ

ar hak

an, suka biye masa suka kira bawan Allah.

Hajiya Saudat ta rasa in da zata saka kanta, abin duniya ya isheta, ga Meenal a kwance ba lafiya tun da aka yi aikin nan, ta ƙi lafiya, an cire mahaifa

ɗ

ungurun gum, ba ta ta

ɓ

a sanin Meenal na bin maza ba, g

a uwa ba, abin da Bulama ke shirin yi, idan bar tone tone yayi yawa, tabbas akwai Matsala, dan daga ita har shi suna cikin tsaka mai wuya, nan ta koma tunanin yadda zata shawo kan lamarin.

Wayarta ta

ɗ

auko, ta kira layin Bulama, ba ta damu da ku

ɗ

in da za

a ja ba a waya, saboda kiran lambar ƙasar waje.

Har ta fidda ran zai

ɗ

aga, ya

ɗ

aga wayar.

"Hello, kana ina ne?"

Haushi ne ya kama Bulama ya ce "Meye hak sai kace wani

ɗ

anki? Ya ma dace ki kirani a halin yanzu? Kin fi kowa sanin ina na tafi, ina tare da

Rumaisa, kuma sai ki kirani a waya?"

"Dan me ba zan kirak a waya ba, in ruwana da wata Rumaisa? Ka tafi ka bar ni da yarinya da larura, ko ka kira kaji ya jikin nata"

"Saudat, abin da ya samu Meenal, ke ta shafa da ke da ita, ni ban yiwa Meenal tarbiyyar

taje ta bi maza a waje ba, har ta zubar da ciki wanda ya kusa ajalinta ba, dan haka ki gaggauta rabata da gidana kan in dawo, i disowned her as my child, taje ta nemi wani uban".

"Wallahi ƙarya kake yi, Meenal jininka ce, 'ya

ɗ

aya tilo da Allah ya baka,

dan haka dole muyi haƙuri da ain daya sameta mu riƙeta".

"Dole kiyi haƙuri dai, amm banda ni ku san yadda zaku yi ke da ita" ya katse wayarsa.

Jifa tayi da wayar tare da taune lips

ɗ

inta na ƙasa 'Anya zancen nan bai tabatta ba na cewar yaran nan suna ray

e ba, tun da har ya iya nuna halin ko in kula ga 'yar da ya ƙallafa ransa a kanta kasancewar ita ka

ɗ

aice ba? To yaya aka yi yaran suka rayu, bayan tun a Asibiti aka ce ba su zo da rai ba? Wane al'amari ne haka mai ban mamaki? Anya ba ƙarya bace da rainin h

ankali kawai? To amma hotunan da aka aiko masa fa kika ƙona' wata zuciyar ta tambayeta. Tabbs yarinyar jikin wannan hoton duk in da ta fito tana da alaƙa da Bulama. To ko dai matan banza ya fara bi? Aka haifa masa ita? Haka ta dinga tunani barkatai, ba tar

e da ta samo amsoshin tambayoyin ta ba, sai dai ta san tasowar wannan lamari barazana ne a gareta da Bualaman kansa, mussaman a kan sirrin da suka yi shekaru suna binnewa.

Abba ne da Abbi tsaye a kan Adnan, da aka samu ya

ɗ

an farfa

ɗ

o daga fita hayyacin

da yayi, lokaci

ɗ

aya duk ya yi rama, yayi zuru-zuru, Mami da Hajiya Mama kuwa suna reception, suna wa Adnan Adduar samun lafiya, saboda ya sha wahala.

Abbi ya numfasa ya ce "Yanzu muna jiaran dawowar wannan mutumin, sannan shi Adnan ya ƙarasa warkewa, m

u ji yaya aka yi suka zama 'ya'yan mutumin?".

Abba ya ce "Ba zamu jira sai ya warke ba, dole ai wadda za ayi idan mutumin ya dawo gari, ko mu muje, ko shi ya zo ya same mu".

Abbi ya gyara tsayuwarsa, yana kallon Adnan, a lokacin da Adnan ya gyara kwa

nciyarsa, yana bin sun Abbi da ido.

Abbi ya ce "sannu Adnan, Allah ya baka lafiya, in dai a ka Afra ne, ka kwantar da hankalinka, ni zan rarrasheta, za a aura maka ita insha Allah, dan ita ya dace ta maye maka gurbin 'yar uwatta".

Abba ya ce "In ji w

a? Ai ida har ina raye Adnan ba zai auri Yarinyar nan ba, Salman shi ya dace ya auri Afra".

Abbi ya ce "Me yasa zaka ce haka?".

"Wa zai bawa Mutumin banza 'ya, ai shi ya san mai nake nufi"

Adnan ya ha

ɗ

a hannayensa biyu, alamar ban haƙuri, yana gir

giza kansa, hawaye na fita daga idonsa.

Abbi ya ce " Bai kamata ka fa

ɗ

i haka a gabansa ba, bayan ga halin da yake ciki".

Abba ya ce "Wannan yaron ba abin tausayi bane, gara a bari ya

ɗ

an

ɗ

ana ku

ɗ

arsa, kuma sati mai zuwa zan kar

ɓ

awa Salman Auren Afra a w

urinka, idan har zaka mini kara, Salman

ɗ

ana ne"

Cikin hanzari Abbi ya janyo hannun Abba, zuwa waje ya ce "Duk laifin da yayi bai cancanci wannan horon ba, magana fa ake ta rayuwarsa".

Abba ya ce "Amma dai ka san Aurensa da Afra ba abu ne mai yiwuwa ba

ko? Alhalin ga Salman".

"Na sani, amma sai a tausayawa halin da ya tsinci kansa a ciki, koma wani irin laifi ya aikata maka, bai kamata ace ka

ɗ

au wannan zafin ba, har ka nesanta shi da tausayawarka ba, haba Alhaji Aliyu, ka zafafa da yawa, akwai buƙatar

ka sassauta masa haka"

Abba ya girgiza kai ya ce "Ba zaka gane bane Major, halin da Adnan yake ciki, dai-dai da shi ne, shiya janyowa kansa".

Abbi ya ce "Ba ina son jin laifin da ya aikata maka bane, ina nema masa alfarma ne, dan Allah dan Annabi, a

sassauta masa a duba halin da yake ciki, ka rage wannan fushin da ka ke da shi".

Abba ya ce "Na ji, amma ni yanzu babbar damuwata shi ne, ba zan bar garin ba, sai Mutumin nan ya dawo, mun cinma matsaya, na tabattar da abin da Adnan yake fa

ɗ

a, gaske ne k

o kuma ƙarya yake yi".

"Haba Alhaji Matawalle, ga gidana mai zai sa kaje ka kama hotel ka zauna, idan ma ba zaka zauna a gida na ba, akwai guest house

ɗ

ina, sai kaje can ku zauna, mu jira zuwan mutumin, Allah dai ya sanya mu ji alkhairi".

Afra sai ko

ke koke take yi, gaba ta ma rasa kukan me take yi ne? Damuwa da halin da Adnan yake ciki? Ko kuma farincikin an san waye mahaifinta? Bana wannan ba, ai haryanzu lalube ake a cikin duhu, ba tare da an tabattar da sahihancin cewar wanda Adnan

ɗ

in ya ambata s

hi ne mahaifinta ba, wataƙila ma ƙarya yake mata, kamar yadda ya yi mata ƙarya a ƙauye.

Kwanakin Adnan uku a Asibiti, ya

ɗ

an farfa

ɗ

o jikinsa da sauƙi, Afra taje duba shi sau

ɗ

aya yana bacci, ya yin da Salman kuwa, sai da Mami ta ha

ɗ

a masa da zagi, sanna

n ya yadda yaje duba Adnan, duk da a ƙule yake da Adnan, amma ya tausaywa yadda ya ga Adnan

ɗ

in ya koma.

Akwa abubuwa da yawa da Salman ba zai ta

ɓ

a mantawa da su ba a rayuwarsa, daga shigowar Adnan rayuwarsu, ya rusa musu farinciki, zuwa ga mutuwar Abra,

ba zai ta

ɓ

a manta lokacin da a gaban idonsa, Adnan ya mari Abra ba dan kawai ta ce tana son sa, da ya tuna ire-iren wannan abubuwan da suka faru, sai tsanar Adnan ta ninku a zuciyarsa, ban da zuciyar musulunci, da kuma yadda Mami ta dage da babu abin da za

i sanya ya zo duba Adnan. Kuma a wannan karon ya ƙudirce a zuciyarsa ko mai za ayi, ba zai barwa Adnan Afra ba, a wannan karon Afra tasa ce.

Wasa-wasa, sai da Bulama ya kwana biyar a Dubai, sannan passport

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login