Showing 225001 words to 228000 words out of 260401 words
farar fatarta. Kallon kanta ta tsaya yi a mirror cikin murmurshi, gani take ba kamar ba ita ba saboda kyawun da ta ga ta yi. Sai da Salima ta ƙara dawowa ta kira ta sannan suka fita tare.
Abb
i na zaune a dinning suka shiga parlour'n,
ɗ
agowa ya yi yana kallon su tare da amsa sallamar, cikin girmamawa Afra ta tsugunna ta ce. "Ina kwana?"
"Lafiya ƙalau, ya kwanan baƙunta?" Ya amsa cikin fara'a.
"Alhamdulillah." Ta fa
ɗ
a cikin sanyin muryar
da ta ara daga jiya, don sosai ta ji jikinta ya yi mata wani irin sanyi ba tare da ta san dalili ba.
"Ƙaraso mu karya." Cewar Salima tana nufar dinning area.
"Bari na fara gaishe da Mami idan ta tashi."
Cikin jin haushin abin da ta fa
ɗ
a Salima ta
ce. "Ai ko da ƙyar in ta tashi."
"Ta tashi, mu je na raka ki." Abbi ya fa
ɗ
a cikin jin da
ɗ
in yadda ta nuna girmamawa ga Mami.
Da kallo Salima ta bi su zuciyarta cike da baƙin ciki, ta gama yi wa yarinya hidima sannan tana fitowa ta ce wani za ta ga
ishe da Mami? Lallai dole ta tashi tsaye don ganin ta ja Afra jikinta sosai, ta san hakan zai ƙara ninka ƙaunar da Abbi yake mata.
Mami tana shirya little suka shigo
ɗ
akin, da fara'a ta
ɗ
ago tana duban Afra, Abbi kuwa juyawa ya yi ya koma parlour.
"Daughter har kin tashi?"
Gya
ɗ
a mata kai ta yi tare da gaishe ta, rungume ta Nai'ma ta yi hawaye na cika mata ido saboda tuno Abra da ta yi, don ganin Afra cikin abaya ba ƙaramin ƙara kamar su da Abra ya yi ba, kasancewar ta ma'abociyar saka ta.
"L
afiya ƙalau daughter, dafatan kin tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau." Ta amsa tare da
ɗ
aukar little, kamar wadda aka fa
ɗ
awa yarinyar sai ba ta yi mata ƙiwa ba, sai ma dariya da ta shiga bangala mata. Socks Mami ta
ɗ
auko ta fara saka mata tare da fa
ɗ
in. "Lall
ai yarinyar nan, wato ke ba kya yi wa iyayenki ƙiwa ko? Da wani ne ya
ɗ
auke ta da tuni kin cika
ɗ
akin nan da kuka da ciccilla ƙafafuwa." Murmushi Afra ta yi tare da shafa sumar kan little, tana jin duk duniya babu abin da take so sama da yarinyar. Tare da
suka koma parlour da Mami, lokacin har Salima da Abbi sun fara karyawa. Cikin son gwaninta Salima ta miƙe ta yi serving
ɗ
insu, don a gaban Abbi biyayya da girmamawa take yi wa Nai'ma. Ciki-ciki Mami ta ce. "Thanks." Abbi bai ji da
ɗ
in hakan ba, amma ya dann
e saboda Afra dake gurin bai nuna ba, fahimtar hakan ya sa Salima sakin murmushi cikin jin da
ɗ
i, dama abin da take so kenan a kodayaushe, Abbi ya dinga ganin lefin Mami a zamantakewar su.
Tsurawa kayan breakfast
ɗ
in ido Afra ta yi, a kallon farko
da ta yi masa ta ji yawunta ya tsinke, ga ƙamshinsa da ya cika mata hanci, tun kafin ta ci ta san ba ƙaramin da
ɗ
i zai yi ba. Inna da Yaya Musa ne suka fa
ɗ
o mata a rai, ji ta yi dama a ce tare da su za su kwashi wannan da
ɗ
in, ga masoyin nata bread ƙatoto a
gurin. A hankali ta
ɗ
auki cup
ɗ
in da Salima ta ha
ɗ
a mata tea ta yi Bismillah ta fara sha, daidai lokacin Salman ya shigo parlour'n. Gabansa ne ya yanke ya fa
ɗ
i ganin Afra, don gani ya yi tamkar Abra ce zaune a gurin, hakan ya tuno masa lokuta da dama da su
ke yin breakfast exactly like this da Abra. Addu'a ya yi mata sannan ya ƙarasa dinning area
ɗ
in cikin sanyin jiki. Bayan ya gaishe da su Abbi ya
ɗ
auki little dake bacci sannan ya zauna. Kamar yadda Salima ta yiwa kowa haka ta tashi ta yi serving
ɗ
in shi. B
a yabo ba fallasa ya yi mata godiya. A hankali Afra ta
ɗ
aga kyawawan idanunta ta kalle shi tare da sakar masa murmushi, mayar da mata murmushin ya yi tare da yin ƙasa da murya ya ce mata. "Morning Angel, da fatan kin tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau"
Ma
mi dake lura da su ta yi gyaran murya, hakan ya sa Salman ha
ɗ
iye abin da yake son fa
ɗ
a, sanin da ya yi ƙa'idar Abbi ne idan ana cin abinci ba a magana idan ba dole ba, gyaran muryar da Mami ta yi kuma ya san tuna masa hakan take. Bayan kowa ya gama cin abi
ncin Abbi ya dubi Afra ya ce. "Yata a ina kika tsaya da karatu ne?"
"Na yi Candy."
Gya
ɗ
a ya yi ya ce. "Da kyau, islamiyya fa?"
"Muna izifi Ashirin."
"Masha Allah, yanzu kina da takardun WAEC da NECO?"
"Eh, na taho da ita ma, Inna ta ha
ɗ
o
mini a cikin kayana, amma NECO kawai na yi."
"Okay." Abbi ya fa
ɗ
a tare da mayar da duban shi ga Salman ya ce. "Idan Allah ya kai mu gobe Monday ka je ka yi mata registration a school
ɗ
in English Academy, saboda ta samu bakinta ya fa
ɗ
a a Turanci kafin ta
shiga University, idan an fara registration na JAMB sai a yi mata, Islamiyya ma ka kai ta wadda kuka yi ta cigaba da karatun a can."
"Insha Allahu Abbi."
Cikin matuƙar farinciki Afra ta ce. "Na gode sosai Abbi, Allah ya ƙara girma da arziƙi."
"A
min Daughter, babu komai. Yanzu sai ka kai ta, ta gaishe da su Ammi, idan kun dawo sai ku je tare da Auntinku ku yi mata shopping na kayan sawa da sauran abubuwan amfani." Ya ƙarashe maganar idanunsa a kan Salman.
Godiya sosai Afra ta yi masa har da h
awayenta, ta so a ce Baba yana raye ya ga wannan ranar, don ba shi da buri da ya wuce na ganin ta yi karatu mai zurfi na addini da na boko, karamcin da Abbi ya nuna mata a yanzu ya ƙara tabbatar mata da an yi wa ƴar'uwarta riƙon mutunci a gidan, hakan ya ƙ
ara kwantar mata da hankali akan zamanta a gidan.
Daren jiya Adnan bai samu ishashshen bacci ba saboda damuwar dake cunkushe a cikin ransa gami da fargabar rasa Afra. Raba dare ya yi yana kallon hotunan Abra cikin zubar hawaye tare da surutai, ta ta
fi ta bar shi cikin tsananin kewa da ƙaunar ta, ya samu wacce yake ganin za ta
ɗ
ebe masa kewar ta amma ita ma yana ƙoƙarin rasa ta. Sai bayan Sallar Asuba wani wahalallen bacci ya
ɗ
auke shi, bai farka ba sai da goma ta wuce, ko sakkowa bai yi daga kan gado
n ba ya lalubi wayarsa ya kira Mami, bayan sun gaisa ya
ɓ
ukaci ta ba wa Afra saboda muryar ta kawai yake son ji ko zai samu nutsuwa a cikin zuciyarsa, lokacin su kuma sun tafi gidan Ammi, cikin rashin jin da
ɗ
i ya yiwa Mami sallama, a ransa yana ƙudirce dol
e gobe ya yi wa Kano dirar mikiya.
Littafin ku
ɗ
i ne, don neman ƙarin bayani: 09047871750
[11/20, 7:09 AM] Abk: Washegari kamar yadda Adnan ya sanya a ransa haka ne ya kasance. Tun asuba ya shirya cikin wata shadda shampoo maroon colour ya murza hula
duk da bata dame shi sosai ba, amma ganin weather ya sanya ya yi shiga mai kyau. Sai ƙamshin Pur oud yake lokacin daya fito gari ya yi duhu sbd hadarin dake kwance a garin Kadunan.
Ba tare da sanin Hajiya Mama da Abba ba ya nufi Kano cikin duhun asuba s
ai gudu yake shararawa burinsa kafin 11 na safe ya yiwa Kano tsinke idanunsu ya sauka akan Afra ko ya samu sauƙin ciwon da zuciyarsa ke masa akoda yaushe. Cikin wannan tunanin ya ƙarawa motar giya.
Afra na zaune cikin wata white-collared t-shirts tare d
a wani red cropped trousers ta
ɗ
ora wata red
ɗ
in kinomo a saman kayan, tayi kyau sosai domin duk a cikin kayan da Abbi ya bada akai mata shopping ne. Hannunta riƙe da Aishatul-humaira wacce a kullum ƙara wayo take. Mami data fito ta ce.
"My dear kinji da
ɗ
i Little bata miki halin nata, ko dai ta gane ke Mother
ɗ
in ta ce?"
"Wallahi Mami ina sonta sosai, bana son rabuwa da ita kamar muna kama ko?" Kafin Mami tayi magana Salman dake gyara zaman babbar rigarsa ya ce.
"Dake da ita ban san wanda nafi so, ina
tunanin burina ya kusa cika"
"What are you saying Salman?" Ya shafa sajan fuskarsa yana basarwa ya ce "No Mami,ina breakfast
ɗ
ina?" Mami ta Harare shi ta ce.
"Liar, It's like I heard you say something?" Ya girgiza yana zama kusa da Afra idanun shi a
kanta ya ce.
"It seems that Mami's ear is starting to have problems. Amma breakfast na ce ta, yunwa zata hallaka miki
ɗ
an yaro Mami"
"Allah ya shiryaka Salman, yunwar ka kewa haka?" Ya marairaice fuska sosai wanda ya bawa Afra mamaki ya sanya ta bu
ɗ
e
baki tana kallon ƙato da shagwa
ɓ
a. Da ƙyar ya ce
"Da gaske Mami yunwa na keji sosai, Yaya Please abinci" ya fa
ɗ
a tare da juyawa ya kalli Afra wacce ke riƙe da Aishatul-humaira tana mata tsalle tsalle da ƙafa a cinya.
Barin wajan Mami tayi cike da fat
an samawa Salman nasara domin ta riga da taji abin da ya ce.
"Why are shy yaya my angel?" Ya fa
ɗ
a yana saka hannunsa zuwa ha
ɓ
arta tare da juyo da fuskarta suka fuskanci juna. Fararen idanunsa masu kaifi wanda suke ƙara sawa Afra kwarjinin Salman a idanu
nta ya zuba mata ya ce.
"Ba haka yaya Abra ke mini ba, na sama hira da yayata sosai wani lokacin daja hancina kamar like this" ya ƙare maganar yana jan hancinta cike da ƙaunar ta wacce lokaci guda ta mamaye dukkan zuciyar shi.
Cikin siririyar muryar ta
ta ce "Uhm to aini ban girmeka ba" ya lumshe idanunsa yana mai girgiza kansa ka
ɗ
an tare da tura hular kansa zuwa gaba ya ce.
"Injiwa? Tsakanina da Abra good 3yrs ne, ke da Abra twins shekara
ɗ
aya aka haife ku Kinga kin zama yayata"
"Kuma na ganka ƙat
oto ni kuma ƙarama" zuba mata gajiyayyun idanun shi ya yi yana karantar yanayin ta sosai kafin speaking calmly ya ce.
"Sbd ni ne mijin ai" ta ware ido ta ce "me kace?" Ya girgiza yana miƙewa tsaye tare da
ɗ
aukan Little ya ce "I'll explain later" kafin t
ai magana ya miƙar da ita tsaye ba zato taji ya jawota
ɓ
arin jikinsa ya yi musu photo yana murmushi ya ce "My family my happiness, zuri'ar Salmanun-faris" ita dai bata fahimta ba, sai saurin zame jikinta da tayi zuciyarta na bugawa da
ɗ
an ƙarfi.
Dining
room suka nufa a can suka samu Salima Abbi daman tun 7 yabar gida yin binciken asalin iyayen Afra da Abra. Jikin Salima na
ɗ
an rawa ta ce "Salman my son bari na serving naka abinci" idanun shi akan Afra ya ce. "No thanks, Afra please serve me" ya fa
ɗ
a fus
ka a kame.
Salima bata so hakan ba domin gaba
ɗ
aya Salman birgeta yake tana neman duk yadda da zata samu connection da shi amma ya toshe ba lallai idan yana mata kallon matar Mahaifin nasa ba.
Afra tai serving nasa a nutse take har kar nan gudun kada ta
kwafsa, ta nuna ƙauyancin nata shi ya sa ta kame kanta da kyau domin siyawa kanta martaba da ƙima a idanun jama'ar gidan.
Ganin daga Afra har Salman abinci suke ci babu wanda yako kalli inda Salima take, ya sanya jiki a sanyaye ta miƙe kamar zata
ɗ
auki Li
ttle wacce take barci a jikin Salman ta wani ƙanƙame shi da duk hannunta biyu sai kawai ta fasa da
ɗ
an sauri tabar wajan.
Suna cin Abinci Mami ta fito cikin kwalliya sai ƙamshi take, ganin Afra da Salman ya bata sha'awa. Ta
ɗ
auki Little tare da bar musu
wajan. Lokaci zuwa lokaci Salman ke satar kallon Afra yana jin kamar ya fa
ɗ
a mata abin da ke zuciyarsa kada ya ƙara rasa damar shi a wannan karon.
"I love You"
Ya furta a hankali daidai yadda za taji da sauri ya
ɗ
ago kanta ta kalle shi ganin kamar ba
shi ne ya yi maganar ba, yasa ta
ɗ
auke taci gaba da cin abincin maybe kunnuwanta ne kawai suka ji haka.
Murmushi mai laushi Salman ya yi kyansa na fita calmly ya kuma cewa.
"Ina son ki Afra, and I ready to marry you....."
"Kai da Afra har abada domi
n ta haramta a gare ka ni ne zan aureta" daga Afra har Salman suka
ɗ
ago kansu, ganin mutum dake tsaye ya sanya Salman yin murmushi wato tarihi zai maimaita kansa kenan. Jikin Afra na rawa ta miƙe tsaye domin bata tsammani ganinsa ba a daidai wannan lokacin
. Ƙoƙarin guduwa take ya sanya hannu tare da cafkota idanun shi sun ka
ɗ
a tare da yin jaa sosai kamar gauta cikin rawar murya ya ce.
"Ni nake son ki ƴar baba tun kina ƙauye, ni ne na yi sanadiyar zuwanki nan gida, kuma a shirye nake da aurenki idan kin a
mince Wallahi ina son ki Please don't say No!"
"Wallahi bana son ka, ba zan ta
ɓ
a son ka ba, koda zaka mutu, ni ka rabu dani ka takura mini" Innalillahi Adnan gani yake da wannan maganar gwara ta
ɗ
auki wuƙa ta caka masa zai fi masa sauƙin fahimta. Cikin
damuwa ya ƙara matsawa gareta tare da
ɗ
ora hannunta a saitin ƙirjinsa idanunsa na sauya kala yana cika da hawaye ya ce.
"Ki taimaka, ki taimaki rayuwata Afra, ko baki so na ki aure ni haka, indai zaki zauna dani matsayin miji ban damu da rashin soyayyar b
a.
"Ni dai ka sakeni, ba zan iya auren wanda bana so ba, sbd ba zan masa biyayya ba ga mata nan da yawa a duniya haba"
Tashin hankali ya bayyana akan fuskar Adnan yau shi ne mace ke wahalar da rayuwar shi har yake zubar mata da hawaye? Lallai soyayyar
Abra tayi tasiri a zuciyar shi,
Domin son da yake mata ya sanya ba zai iya rayuwa babu Afra ba a yanzu komai nasu iri amma me ya sa halinsu ya bambanta?.
Yi ya yi kamar zai jawota jikinsa tayi saurin ja baya kusa da Salman hawaye na zuba a fuskar Adna
n sosai ya ce.
"Don darajar Allah ki duba halin da zuciyata take ciki, ki sassauta yanayin ki a kai na, ki bani dama na sauya tunani zaki so ni ina da tabbacin zan sauya miki ra'ayi da kanki zaki furta kina so na, zan fifitaki da sauran mata, zan baki far
in ciki da duk abin da kikeso, zaki rayuwar ƴan ci a gidan Adnan Aliyu Matawalle..... I love You Afra, i love You to the rest of my life, I can't imagine life without you wlh ina son ki ba zaki ta
ɓ
a samun wanda zai so ki kamar ni ba"
Salman ya gyara tsa
iwa tare da gyara zaman babbar rigarsa cikin nutsuwa ya kalli Adnan kana ya juya ya kalli Afra a hankali ya saka hannu ya kama nata cikin nutsuwa ya ce.
"Look into my eyes yaya" kasa kallonsa tayi Ubangiji yana gani Salman mugun kwarjini yake mata, yana y
iwa idanunta tasiri sosai ba ka
ɗ
an ba.
"Please yaya" ya ƙara fa
ɗ
a a taushashe har ƙamshin spraymintt mouth freshener
ɗ
in bakinsa yana dokan hancinta wanda ya sanya tayi saurin lumshe idanunta. ganin da gaske ba zata kalle shi ba ya sanya gaba
ɗ
aya ya tall
afo ha
ɓ
arta yana sauke mata numfashi a fuska kamar zai ha
ɗ
e fuskokinsu ya ce.
"I love You Afra, From the moment I first laid eyes on you, I knew you were a perfect match for me. I love everything about you. Ina son ki so mai yawa, ina kishin da zai
ɗ
auke
numfashin sarrafa rayuwata, kada ki yi mamakin ganin bamu da
ɗ
e ba, ina jinki tamkar yaya a raina, ki bani dama na bayyanawa kowa irin soyayyar da nake maki, bana son nayi zurfin cikin da nayi a kan Abra. I will be always by your side in good and bad times,
in happy and sad moments… because I love you! Accept my request please yaya"
Ya kama fuskarta da dukkan hannunsa wanda itama a lokacin ta bu
ɗ
e idanunta tare zuba masa su. Tana son fahimtar da gaske wannan kyakkyawan farin ne yake son ta kuma yake son a
urenta?
"Please yaya"
Ya marairaice fuska yana narke mata. Kasancewar rayuwar ƙauye tayi babu wanda kunya sosai a tare da ita bakinta kuma baya sarrafa wani abubuwan kafin ta fa
ɗ
a. Muryar ta na rawa ta ce.
"Ina son ka ni ma, kuma zan aureka in dai da
gaske kake zaka aure ni"
Ɓ
oyayyiyar Ajjiyar zuciya Salman ya sauke yana ƙara riƙe fuskarta da kyau! Wani farin ciki na ratsa zuciyarsa.
A fusace Adnan ya fisge Afra daga wajan Salman idanunsa na zubar da ruwa bakinsa da gaba
ɗ
aya jikinsa suna rawa kama
r ana ka