Showing 246001 words to 249000 words out of 260401 words
ko kuma ta koma sbd yarinyar badan halin Adnan ba.
Hajiya Mama ta ci-gaba da kula da Little yarinya mai shiga rai. Ɓangaren Sa
lman da Afra soyayya mai zafi ake tun tana jin kunyar shi har ta daina ya shagwa
ɓ
ata da tarin soyayyar shi da kalar nasa salon mai mantar da duk wanda ƴa mace duniyar da take ciki. Har ta kai idan ba shi sam ba zata iya bacci ba ta sama da rayuwar auren ka
mar yadda yake buri tattali take samu sosai cikin sati guda daga Salman har Afra suka ƙara wani haske da ƙima Masha Allah.
Ummi da Abdullah suka koma Dubai bayan an mata al'ƙawarin zuwan twins
ɗ
in nata, burinta na son tafiya dasu bai cika ba, Dr Bulama
har yanzu yana tsare domin an gano manya-manyan laifukan daya aikata a asibitin shi da
ɗ
aukan ma'aikatan wanda sam basu dace ba, uwa uba kuma Ummi ta ƙara sawa akai masa sammacin cinye mata dukiya da ya yi, domin har yanzu wasu ku
ɗ
in basu fita ba, tare da
cewa ya bata takardar sakin ta.
Wannan abu ya zaga ko'ina har kunan gwamna, aka shiga binciken ko wanne asibiti tare da tabbatar da ingancin ma'aikatan. Aka ƙi bada belin Dr Bulama yana tsare labarin ya
ɗ
aga hankalin Abra da Afra duk da laifin na Mahaifi
nsu ne amma ta wani
ɓ
angaren suna tausaya masa ainun.
A week later.
Tana durƙushe gaban Abbi tare da sauraran abin da zai fa
ɗ
a mata, zuciyarta sai bugawa take..
Abbi ya gyara zama ya ce "kamar yadda na baki umarnin sati guda ki fito da miji, na zuba
miki ido amma shiru, to a yau bayan sakkowa masallaci na
ɗ
aura miki aure da wanda zuciyata ta amince da shi, ga sadakin" ya fa
ɗ
a yana miƙa mata damin ku
ɗ
i a lokacin nan idanun zuciyarta yarinyarta Aishatul-humaira da tsohuwun mijinta Sp Adnan Aliyu Matawal
le kawai suke hango mata, har bata gane mai Abbi yake ce mata.
"Daughter?" Ya kira sunanta da ƙarfi ta saurin cewa "Na'am Abbi" ya kalleta da kyau ya ce.
"Kiyi mini alfarma a matsayin na wanda na isa a gareki, duk mijin da kika riska a matsayin shi ne
mijin ki, ki amince da shi don Allah Abrana, kada ki watsa miki ƙasa a idanu, a wannan karan miji mai nagarta na za
ɓ
a miki wanda ya dace da rayuwar da kike mafarki,
Kada kiyi baƙin ciki da duk wanda kika gani don Allah ki yarda dashi,ki bisa sau da ƙafa
aljannar ki na ƙarƙashin shi, wanda kuma sai kin yi biyayya zaki same ta, maza tashi kije yana waje yana jiranki zaku shige ba zaki sake kwanar mini a gida ba"
Abra ta rushe da kukan da ita kanta bata san na menene ba, a karon farko hukuncin Abbi ya yi
mata tsauri, ba damuwarta wanda ya za
ɓ
a mata ba,
Kawai Aishatul-humaira take tunani.
"Insha Allah Abbi, nayi maka al'ƙawari"
"Allah ya yi miki Albarka" ta fa
ɗ
a jikin Mami tana kuka kamar ranta zai fita. Salima murmushi kawai take wacce take
ɗ
auke da
jaririn cikin Abbi a jikinta.
Mami taiwa Abra nasiha sosai mai ratsa jiki. A tare suka rakata waje idan akace mijin nata yana nan.
Wani magidanci ta gani tsaye fari ba sosai ba, suka ha
ɗ
a idanu haka kurum ƙunci ya kama zuciyarta a haka ta shiga mota suk
a
ɗ
auki hanyar da ita kanta bata sani ba.
Bata kula shi ba, bai kulata ba har bacci ya
ɗ
auke ta.
Sai dare suka shigo garin cikin wata hadaddiyar unguwa mai kyau da tsari, har cikin gidan ya yi parking ya fita, itama ta fito tana mamakin abin da yana mutu
min magana ita ko sunan shi bata sani ba.
Ya kalleta ya ce "Madam shiga ciki, ina zuwa just 10 minutes" bata ce komai ba ta nufi hanyar shiga gidan tun a parlour ta san Mai gidan Ubangiji ya hure masa arziƙi ba a magana.
Ta za
ɓ
i
ɗ
aki guda
ɗ
aya wanda ya h
a
ɗ
u sosai, ta jima zaune kafin tai sallah ta kwanta har barci ya
ɗ
auke ta bata ji motsin Mai gidan ba.
Can cikin barci taji an rungome ta tsam a lallausan ƙirji wani ƙamshi na ratsa hancinta, ya sumbaci labbanta masu taushi a hankali ya ce "Wake up My Que
en, heartbeat, my rigimammiyar matata" yaja hancinta yana ƙarasa zame rigar jikinta cike da soyayya, yai holding nata very tight. Abin da taji ya sanya Abra ta bu
ɗ
e idanunta, da sauri ta ƙarasa bu
ɗ
e idanun mamaki ya kasheta muryarta na rawa ta ce "Adnan...
. You?' ya
ɗ
ora bakinsa akan nata ya yi kissing sosai yana kashe mata ido ya ce "Yes My Queen waye yace zan iya rabuwa dake?" Ya fa
ɗ
a yana mirgina ta zuwa ƙasa.....
*
🔥
IDAN BA KE 17
🔥
*
Marubuciyar
Tsintacciya (Published)
Kwaila ce
Moon
Uncle ne
Sirrin mu
Zain Abeed (Published)
Auren fansa
Abu maleek
Lamrat
Jidda
Juyayi
Raino ne sila
Sai na aureta
Izzar so
Dare da duhu
The new emir
Ban sani ba ko wannan zai samu daidaito a zuciyoyinku? Tafiyar ƙaddara ce wacce ban saba
yinta zallah ba... A wannan karan nace me zai hana muyi labari zallah akan *SOYAYYA*
*SOYAYYA TSAKANIN MUTUM DA ALJANI???* Idan kun ta
ɓ
a ji to labarin zai zo da salo na musamman.
*IDAN BA KE* zan kashe dubban rayukan jama'a,na kuma shirya kashe duk
mai son raba tsakanin ruhina da naki.... Shi ne alwashin da *ALJANI PRINCE BILAL* ya yi.
Labarin *IDAN BA KE* Labari ne dana share shekara a zuciyata ina tsara yadda zan labaranta muku shi, Labarin Babban Malami
ɗ
an kimanin shekaru 34 da haihuwa wato *
YAA SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU* da yarinyar da *ALJANI PRINCE BILAL* ya aura. Waye zai ci galaba? An bashi shekara guda domin kare rayuwarta tunda ya dai na yi mata kallon matar shi ta aure da sunan tai masa ƙanƙata kuma *MATSAYIN ƳA* take a wajansa. Kwatsa
m sai ciki ya bayyana, cikin waye? *YAA SHEIKH KO PRINCE BILAL???*
Yayin da ya gama lalacewa da soyayyar ta a zuciyar shi, a lokacin aka raba zuciyoyin su da ƙaddara mafi muni ta yadda sam bazu zatta ba. TAYAYA Suka fito daga *CIKI ƊAYA?*
gaba
ɗ
aya w
annan a cikin labarin IDAN BA KE. Wanda bai karanta ba ya nema ya karanta. Mun jima da gama free pages GOBE 29/11/22 zamu
ɗ
ora da posting ga wanda suka siya iya PAID GRP.
Hanzarta biya ta nan 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank. Ka tura s
haidar biya ta nan 08119237616.... Salon na musamman ne
🔥
TEAM HALISA DANEJO ROME a shirya masoya ALJANI PRINCE BILAL A shirya. tawagar YAA SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU a shirya
🔥🔥🔥
yanzu zamu fara...
SARAUTAR MARUBUTA
[12/2, 2:49 PM] Abk: A gigice Abr
a ta ce "Adnan, you again? Wai me ya dawo da kai cikin rayuwata, a kan me zaka kuma dawo mini, ka shirya sake ƙarasa ni har lahira kenan?".
"No Angel, please understand me"
"Shut up Adnan, you have nothing to tell me, babu abin da zaka gaya mini, in
dai halinka ne sai dai na gayawa wani".
"Wallahi Abra nayi nadama, dan Allah dan Annabi ki taimaka mini ki yafe mini"
"Kaga saurara mini,
ɗ
an cikani malam"
Adnan ya sake marairaicewa ya ce "Abra please, dan girman Allah ki saurareni ki yi haƙuri".
"Adn
an ka rabu dani nace maka, haryanzu ina kan bakana bana sonka bana ƙaunarka, kuma har in koma ga Allah ba zan manta cin zarafin da kayi mini a rayuwar aurenmu ba, dan haka ka ƙyaleni" a zuciye tayi Maganar, wanda hakan ya tilasatawa Adnan cikata, bata saur
ari komai ba ta diro daga kan gadon, ta nufi hanyar barin
ɗ
akin. Bashi da za
ɓ
i illa ya bi bayan Abra yana fa
ɗ
in "Dan Allah ki tsaya ki saurareni" tsaki tayi ta koma falo, ta hau kan doguwar kujera ta kwanta.
"Shikenan, ba zan kwana a
ɗ
akinki ba, zan kwana
a
ɗ
aya bedroom
ɗ
in, ki koma
ɗ
akinki ki kwanta Please".
"Malam dan Allah ka rabu dani Adnan, meye haka ne wai, Wallahi ka matasa mini barin gidan zan yi a daren nan, ba sai zuwa wani lokaci ba"
"Yi haƙuri na ƙyaleki, amma dan Allah kar ki kwana a kan kuj
erar nan wuyanki zai yi ciwo" ko kallonsa ba tayi ba ta gyara kwanciyarta, ta rufe idanunta, sai da ya bar falon sannan ta tashi ta koma
ɗ
akinta, ta kulle ƙofar ta saka key.
Adnan kuwa kasa bacci yayi gaba
ɗ
aya, juyi kawai yake a kan gadon nan, zuciyars
a na masa wani nauyi, yana tuna irin abubuwan da ya aikatawa Abra, duk da a lokacin yana sonta, da yadda yake fama da ita yanzu, taƙi ta tsaya ta saurare shi, balle ta bashi damar da zai gwada mata irin son da yake mata.
"Koma me kika zama laifina ne Ange
l, ni ne silar sauyawar halayenki, amma ki yafe mini, na shirya baki dukkanin farinciki Abra Khamal Khamis" ya fa
ɗ
s yana ƙanƙame pillow a ƙirjinsa, yana jin wata irin kewarta na ƙara ratsa zuciyarsa, ya tuna yadda ya dinga zuwar mata kamar ba matarsa ba, b
a shi da tabbacin a zaman da suka yi Abra ta san menene ma da
ɗ
in auren, saboda buƙtarsa kawai a gabansa.
"Am sorry Angel, ki yafe mini mana, Allah yana son bayinsa masu afuwa da yafiya".
Abra kam zullumi ta shiga da tunanin kar da wani sabon salon yauda
rar Adnan ya kuma zuwar mata, amma yanayinsa ya nuna tabbas yayi nadama, kuma ta san su Abbi ba zasu za
ɓ
a mata abinda zai cutar da ita ba, sai dai duk ƙoƙarin da za tayi wurin manta abinda Adnan ya aikata mata ta kasa, saboda girman tarin laifukansa a gare
ta, da haka wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita.
Duk wata kulawa da ta dace mace ta samu a wurin miji, Salman ya dage yana nunawa Afra yadda ya dace, gaba
ɗ
aya Salman ya mantar da ita tarin damuwa da ƙuncin rayuwa da ya samu kansa a baya, Yanzu
haka shirye shirye sun yi nisa, zai koma china dan
ɗ
ora karatunsa daga in da ya tsaya, kuma tare da Afra zai koma, domin ita ma ta cigaba da nata karatun a can.
Washegari da safe, Adnan ya tashi ya gyara komai, ya dafa tea da kansa ya sayo bredi, alread
y akwai kayan tea dan duk wani kayan Abinci ya saya ya ajiye. A falo ya koma ya zauna, yana jiran Abra ta fito, dan yana tsoron kar yaje tasota ta kuma yi masa wulaƙanci.
Sai wurin ƙarfe goma ta fito, ta fito cikin wata doguwar riga mai matuƙar kyau da
ɗ
a
ukar hankali, rigar tabi jikinta ta kwanta luf.
Kallo
ɗ
aya tayi masa ta
ɗ
auke kanta, shi kuwa gogan murmushi ya yi ya ce "Good morning my Angel".
"Ina ne kitchen, zan samawa kaina abin da zan ci ina jin yunwa".
"Ai na ha
ɗ
a breakfast, gasu can a kan dini
ng na ajiye komai, ga kazar kuma ki a fridge idan ita ki ke so, sai in warming
ɗ
in ta ki ci". Ba ta bashi amsa ba ta wuce dining, ta zauna ta fara ha
ɗ
a tea.
Dining
ɗ
in ya bi Abra ya zauna, yana satar kallonta da yadda ta ƙara kyau da ƙiba, wata irin kew
arta na kuma ratsa shi, wannan dogon gashin da ya zube lokacin da tayi rashin lafiya, duk ya dawo. Yayi mata do tun daga gaban goshinta gashin yake, baƙi ƙirin ya kwanta a bayanta.
Tana ankare da yadda ya zuba mata ido kamar bai ta
ɓ
a ganin mace ba, ta far
a karyawa tana ka
ɗ
a ƙafarta, kamar ba san da wanzuwar sa a wurin ba.
Shima karyawar yake yi, amma hankalinsa gaba
ɗ
aya yana kanta, can ba tare da yayi tsammani ba yaji ta ce "Ammm nace ba, ina ka kai mini 'ya ta ne? Ina buƙatar ka bani abata".
" 'yarki
tana nan lafiya"
"Ba lafiyarta na tambaya ba, ina ka kai mini ita, ina buƙatar a dawo mini da ita".
"Tana wurin... Bai ƙarasa ba, suka ji ana ka
ɗ
a ƙararrawar falo. Adnan ne ya miƙe ya tafi ya bu
ɗ
e.
Direban gidansu ne, ya kawo Abinci daga gida, wanda H
ajiya Mama ta aiko musu da shi.
Adnan ya kar
ɓ
a ya maida ƙofar ya rufe ya dawo dining.
"Angel kinga Mama ta aiko da Abinci, bari in ajiye a kitchen maci da rana ko?" Ba ta ko
ɗ
aga kai ta kalleshi ba,balle ya sa ran zata amsa masa. Ya tafi kai fulasan kitc
hen kar ya dawo ta bar falon.
Akwatunan dake
ɗ
akinsa ya kwaso, ya kai
ɗ
akin Abra, Akwatuna duga shida ya zube a gaban Abra, da murnarsa ya ce "Angel, ga kaya na saya muku ke da little, gashi nan naki akwatuna hu
ɗ
u nata kuma biyu, dama sauran kayan lefenk
i na wancan gidan ma suna gidanmu, suma zan
ɗ
auko miki su".
Abra ta kalli Akwatunan ta ce "Madalla, little ta gode, ni kuma ka bar kayanka, babana na riƙo bai bar ni tsirara ba"
"Abra Wannan ai wani abu ne na daban, wannan hakkina ne nayi muku".
"Ka
yiwa 'yar ka dai, ai ni ban cancanci ka mini ba, ni da nake jinin Bulama, ai bai kamata ka mini abin da zaka kyautata mini ba, tunda auren na fansa ne" Dafe kansa Adnan ya yi ya ce "Abra why, na gaya miki nayi nadama, mai yasa kika canza hali ne?".
"Ko
ma menene ai kai ka koya mini ba wani ba, a waccan rayuwar ka sanar mini zaman bauta zan yi, ka
ɗ
au fansa, ban sani ba ko a wannan karon ma fuska biyu kake mini kamar yadda ka saba".
Sunkuyar da kai ya yi, a hankali ya matsa kusa da ita, yana kallon yad
da doguwar rigarta ta
ɗ
age santala santalan ƙafafuwanta suka bayyana, ya dubeta tare da
ɗ
ora hannunsa a kan cinyarta, ya ce "Believe me please, ba zan sake cutar da ke ba Abra"
Kallonsa tayi ido cikin ido, yadda suka samu kusanci da juna, har tana iya jin
saukar numfashin sa a jikinta, ta kalli faffa
ɗ
an ƙirjinsa da take missing, ta cigaba da kallonsa zuwa kan lips
ɗ
insa, da idanunsa da suka yi jawur cike da nadama, ji tayi wani abu na taso mata, tsohuwar soyayyar Adnan na ƙoƙarin taso mata. Dakewa tayi a l
okacin da wani sashi na zuciyarta ya garga
ɗ
eta 'Me kike shirin yi ne Abra, kamar baki da zuciya?'.
Ha
ɗ
e rai tayi ta ce "Ka zo ne dan kayi abin da ka saba, ka biya buƙatar ka sannan ka koreni a wulaƙance, kar warin abin da na fitar ya hautsina maka ciki? K
o kuma fya
ɗ
en kake ƙoƙarin sake yi mini, kamar yadda kayi mini a ranata ta farko da kasancewa da
ɗ
a namiji?"
Wata irin ajiyar zuciya Adnan ya sauke, ya dubi Abra yana tuna abubuwan da suka shu
ɗ
e, da wasu ya manta ma da ya aikata hakan.
"Ba zan gaza da ci
gaba da baki haƙuri ba Abra, na san ni mai laifi ne a wurinki, dan Allah ina mai kuma sake baki haƙuri".
"Can You excuse me please?" Abra ta fa
ɗ
a in a serious tone, tana sake nuna masa bata buƙatarsa a in da take. Jiki babu ƙwari haka Adnan ya tashi ya ba
r mata
ɗ
akin.
Kwanaki biyu da tarewar Abra, Hajiya Mama da Abba suka zo gidan da daddare, tare da little kasancewar dama tana wurin Hajiya Mama.
Abra tayi murna da zuwansu, tayi musu kyakywar kar
ɓ
a cike da farinciki. Gefe guda ga murnar ganin 'yarta da
tayi.
Abba ya yi musu nasiha me shiga jiki, da mahimmancin yafiya da haƙuri a zamantakewar aure, da kuma sake kashedi da jan kunne ga Adnan, a kan mahimmanci amana da riƙon iyali da adalci. Abra nasihar Abba ta ratsata, amma ba ta iya ji a ranta ta yafewa
Adnan muzgunawar da yayi mata ba.
Da zasu tafi ta so Mama ta bar mata little, amma Mama ta ce ba yanzu ba, sai an kwan biyu tukuna.
Labari ya ishe sauran 'yan uwan Bulama, a kan iftila'in da ya afka masa, amma babu mutum guda da ya iya jajanta hal
in da yake ciki, ciki kuwa har da 'yan uwan mahaifinsa, saboda yadda ya watsar da su, tun bayan aurensa da Saudat, da yadda ya daina zuwa inda suke, shi kuma babu wanda ya san in da yake zaune a cikinsu, dan haka babu wanda yabi ta kan a tallafa masa sabod
a yanayin da yake ciki.
Hajiya Saudat kuwa Nijar ta gudi can wurin wata ƙawarta ita da Meenal, sai dai tun bayan aikin da aka yiwa Meenal, aka cire mata mahaifa, ba ta samu lafiya ba, take ta rashin lafiya, duk ta ƙare ta rame, saboda kullum cikin ciwon
ciki da zubar jini take. 'yan sanda kuma tuni suka baza komarsu dan ganin an daƙumo Hajiya Saudat bisa ga laifin da ta aikata.
Adnan yana ji yana gani, yana zaune gida
ɗ
aya da Abra, amma tafi ƙarfinsa, saboda