Showing 174001 words to 177000 words out of 260401 words
Shiru tai masa ya s
unkuyar da kansa yana zaro Wayarsa tare da fa
ɗ
in "Jikina yana bani daman zan sake ganinki please samin number ki" wayam babu Abra babu mai kama da ita, neman duniya babu ita a haka ya koma gida rai
ɓ
ace.
Yanayin Yadda ya shiga ya sanya ƙyakkyawar matar da
ke zaune saman Kujera hannunta riƙe da littafi tana dubawa
ɗ
ago kanta cikin kulawa ta ce "Lafiya dai Abdullah?" Girgiza kai yai ya ce "Ummi kai na ke ciwo" da ido ta kallesa haka nan taji bata yarda ba, a nutse ta ce "Ciwon kai?" "E, Ummi maybe gajiya ne"
numfashi ta sauke ta ce "Allah ya sawwaƙe, kasha magani ina son muyi magana akan Sabon Companyn da aka bu
ɗ
e last year,bana gane kan komai na Companyn Abdullah na zuba biliyoyin ku
ɗ
i amma yanzu duk babu su, hankalina ya fara tashi" Abdullah ya ce "Waye mana
ger na Companyn ma Ummi?" Girgiza kai tayi tana
ɗ
aukan Jarida ta ce "Jeka huta, we'll talk later" "Ok Ummi" part
ɗ
insa ya shige Ummi ta bisa da kallo.
Cike da tsoro Abra ta kwanta amma tana Mmkin gani na biyu da idanunta suka sake yiwa Abdullah waye shi
? Mene yasa yake bibiyarta har haka? Da wannan tunani bacci ya
ɗ
auke ta, cikin dare ta farka da matsanancin zazza
ɓ
i hannunta ta miƙe da nufin riƙe kanta amma sai taji gashin kanta yana marmasuwa, da sauri ta saka hannunta duk biyu ai kam nan gaba
ɗ
aya gash
in ya shiga cirewa gefe guda na kanta tamkar wacce akai wa aski.....
Littafin ku
ɗ
i ne, mai buƙata ya yi magana ta wannan number 09047871750
[10/27, 3:04 PM] Abk: Gabanta ne yayi mummunar fa
ɗ
uwa, wane irin abu ne haka gashin kanta zai dinga zuba? Shir
u ta yi tana tunani, a iya saninta bata ta
ɓ
a abu makamancin haka ba. 'may be sauyin weather ne' wata zuciyar ta bata amsa, haka ta yi shiru tana Adduointa, har bacci
ɓ
arawo ya saceta.
Bayan sallar Asubahi ma, gado ta koma ta cigaba da bacci, tana cikin ba
ccin taji an
ɗ
agota daga kwanciyar da take gaba
ɗ
aya.
Bu
ɗ
e ido ta yi tana tura baki, ta kalli fuskar Adnan ta ce "Meye haka? Bacci fa nake yi".
"Ai na san baccin ki ke yi, ke baki san Yakamata ba ko? Kina da juna biyu amma har wannan lokacin kina bacci
, ba zaki tashi ki nemi abin da zaki ci ba, baki san sai kin ci shima abin da ke cikin ki zai ci ba?".
"Au haba? Ya da
ɗ
e bai ci ba, ba zan ci Abincin ba, sai dai wahala ta kashe shi na huta nima".
"Aikuwa sai dai ku mutu tare, da in rasa abun cikinki
gara ke in rasa ki, dama can ba ta taki nake ba, ki yi ƙoƙari mu rabu lafiya, ki haife mini yarona salin alin".
"Mu rabu ka ce?" Tayi maganar tana kallon fuskarsa.
"Eh mu rabu, ko da yake fa ashe ba zaki iya rayuwa babu ni ba ko?".
Abra tayi wani
murmushi mai ciwo ta ce "Ai ko kashin awaki muka zo duniya da kai, na tsaneka ko sunan ka bana ƙaunar ji, idan har zamu rabu ka yiwa Allah da ma'aikinsa mu rabu yanzu kan mu koma Nigeria, daga nan in wuce gidan ubana".
"Gidan riƙo dai, a zatonki zan r
abu da ke ne ki tafi da cikina gidan riƙo ya zama
ɗ
an riƙo kamar yadda kika zama, no iya wuya banga wanda ya isa rabani da ke da cikin nan a jikinki ba".
Abra ta ce"Wanda yayi ni yaui cikin fa?" Kallonta yayi amma bai ce komai ba, ya basar ya ce "Malama
ki tashi kije ki karya".
"Idan ka damu
ɗ
anka ya ci Abinci, zaka iya zuwa ka ha
ɗ
o Abincin ka kawo mini nan in ci, idan kuma ba ka matsu ba, kana iya ƙyaleni in cigaba da abin da yake gabana"
Tana rufe baki ya wani irin fizgota daga kan gadon, Innalil
lahi wa Innalillahi raji'un, Abra ji tayi tamkar an ha
ɗ
a ilahirin ƙasusuwan jikinta ana ƙoƙarin kakkaryawa saboda azabar ciwon da ya ratsata tun daga kwanyarta zuwa yatsun ƙafarta.
"Na shiga uku Adnan, kasheni zaka yi ne? Ka san yadda nake jin jikina ku
wa?".
"Ban damu da duk abin da kike ji ba, wannan ke ta shafa ba ni ba, burina
ɗ
ana ya rayu, ki lafiya ko kar kiyi matsalar ki ce, akan ina Magana kina mini gaddama, mussaman a kan abin da ya shafi cikin nan, sai na
ɓ
ata miki rai" yana gama maganar ya s
higa janta, wanda jan nan da yake mata ji take tamkar yana ƙoƙarin rabata da ƙasusuwan hannunta.
"Adnan Allah yana kallonka fa" ta fa
ɗ
a cikin tsananin rauni.
"Kar ki sake gatsa mini sunana haka kamar ke kika ra
ɗ
a mini, mara tarbiyya shi ma uban riƙon
naki baki samu tarbiyya a hannunsa ba kenan, da har kike iya kallon tsabar idona ki kirani da sunana".
Ja tayi ta tsaya tare da riƙe ƙofa ta ce "Zan iya haƙuri idan ka zagi mahaifina, saboda ban san shi ba ban san mai ya ha
ɗ
aku ba, amma ba zan juri ka
zagi Abbina ba duk wani rashin mutunci da zaka yi mini ya ƙare a kaina ban da Abbi, kuma da ka auroni ai ina
ɓ
oye sunan naka, amma na ga lamarinka babu mutunci dan haka na fa
ɗ
a ADNAN ALIYU MATAWALLE, aka fa
ɗ
i sunan Annabi ma balle sunan Azzalimin mutum iri
nka" rigarta ya sa ya shaƙo wuyanta yana huci, idanun Abra suka yo waje tana wani irin kakari, ya ƙarasa janyota cikin falon, ya jefata kan kujera. Ya
ɗ
auko Abinci ya dinga
ɗ
ura mata tana kuka tana kakarin amai, amma babu tausayi ko imani a zuciyar Adnan.
Zaune take a kan wasu irin katafaren kujeru, tana zaune hannunta riƙe da waya, tana jujjuya wayar fuskarta
ɗ
auke da damuwa, a hankali ta fara daddanna wayar, sannan ta kara a kunnenta, sai da wayar ta kusa katsewa sannan aka
ɗ
auka, sallama tayi tare da
yin ajiyar zuciya.
Daga can
ɓ
angaren cikin wayar aka amsa mata.
"Kana ina ne Yanzu?".
"Ina nan lafiya, akwai damuwa ne?".
"Ina son in ji Yaushe zaka zo ne, saboda akwai damuwa, ina son mu tattauna wata magana da kai"
"Wace irin damuwa ce hak
a wadda har kike son in zo?".
Ta sake sauke ajiyar zuciya, fuskarta na bayyanar da tsantsar damuwa ta ce "Nifa gaba
ɗ
aya na kasa gane kan kasuwancin nan, shekara da shekaru abu yaƙi gaba yaƙi baya, akwai buƙatar mu dakatar da deal
ɗ
in nan, zan tsayar da
duk wasu harkokina na nan ƙasar, in sako jami'an tsaro da manyan accontants a gudanar da bincike, a gano a ina matsalar take"
Daga cikin wayar mutumin ya ce "Haba Khair, kamar ba musulma ba, baki yadda da ƙaddara ba? Ki bi komai a hankali mana, idan ki
ka dakatar da harkar kasuwanci shikenan a daina juya ku
ɗ
a
ɗ
en su lalace a haka? Bai kamata a dakatar da kasuwanci ba, a cigaba da harkokin idan ya so sai ayi binciken zuwa ƙarshen shekara idan Allah ya kaimu".
"Na gaji ne, na gaji da irin yadda abubuwa s
uke gidana a harkokina, akwai wani abu wanda ban sani ba, da nake buƙatar gano shi a nan kusa".
"Kiyi haƙuri ki bi komai a hankali, ki kwantar da hankalinki komai zai tafi daidai insha Allah"
"Shikenan, amma yakamata ko mai kake yi ka zo, ka san ka
da
ɗ
e dai baka zo ba"
"Haka ne, zan zo insha Allah"
"Ok sai an jima" ta ajiye wayar jiki a sanyaye tana tunani.
Sallamar Abdallah ce ta katseta daga dogon tunanin da take yi.
Ta amsa masa ya ƙaraso ya zauna, a
ɗ
aya daga cikin kujerun falon. Ya d
ubeta ya ce "Lafiya kuwa Ummi?"
Ummi ta
ɗ
an girgiza kai ta ce "Abdullah, Ina cikin damuwa a kan harkar kasuwanci na, gaba
ɗ
aya na kasa gane kan harkar nan, nayi waya da shi, ya ce mini yana nan zuwa, amma abin yana damuna".
Abdallah ya ce "Kiyi haƙur
i tin da yace zai zo da kansa, ki
ɗ
an ƙara haƙuri".
"Shikenan, bari ya zo
ɗ
in in ji shawaa da zai yanke, amma zan gaya masa dole a bincika yadda al'amuran nan suke gudana".
Abdallah ya ce "Hakane, Allah ya yi mana jagora".
Ta amsa da "Ameen"
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, kusan satin su Abra biyu a Dubai, al'amarin Adnan babu sassauci, dan ko zata ci Abinci tana amai sai ta ci, ko tana so ko ba ta so. Kuma bai fasa zuwar mata da buƙatarsa ta Aure ba, duk da yadda yanayin jikinta yake.
Abra
ita ka
ɗ
ai ta san irin wahalar da take sha a kan cikin nan, yana tsufa tana cigaba da shan baƙar wahala, wani irin zazza
ɓ
i take wanda ba ta ta
ɓ
a tunanin akwai irinsa ba, taji kamar ana sassara ƙasusuwanta, ga wani irin azabar ra
ɗ
a
ɗ
i da take ji a ƙasan fatar
ta abin ba ya misaltuwa.
Ta ƙara wata uwar rama ga duhu tayi sosai, ga gashi yana ta zubewa ta rasa abin da yake mata da
ɗ
i, gaba
ɗ
aya ta sake zama wata so silent.
Satinsu biyu, suka baro Dubai sai dai babban abin da ya yiwa Abra da
ɗ
i da bata ta
ɓ
a zato
ba shi ne yadda suka sauka a Kano, wanda rabonta da Kano tun da aka
ɗ
aura mata Aure aka kaita gidan Adnan.
Taji da
ɗ
in ganin Mami, sai dai Mamin ta tsorata da ganin yadda Abra ta koma, amma sai tayi zaton kawai laulayi ne ya mayar da ita haka, ga cikin
ya fito Sosai kai kace da ta durƙusa za ta haife shi.
Bayan Adnan ya kaita gida, a Hotel shi yaje ya sauka, ita kuma ya barta a nan gidan.
Ganin gidan ta din ga yi duk ya sauya mata, ta dinga tuna irin rayuwar da tayi a gidan, duk da irin cuzguna mata da
Hajiya Na'ima ta din ga yi, amma rayuwar gidan ta fi mata da
ɗ
i a kan wadda take yi a yanzu.
Sai dai tana tuna cewa ba gidan mahaifinta bane, ita
ɗ
in Tsintacciya ce, sai jikinta ya ƙara yin sanyi, amma duk da haka rayuwarta da Faris ta fa
ɗ
o mata, rayuwa m
ai cike da ƙauna da soyayya.
Jiki a sanyaye ta ce "Mami, wai kuna waya da Faris kuwa? Nifa bani da lambarsa duk ina cikin damuwa".
"Wallahi Abra duk lambobinsa ba sa shiga, ina ta lalla
ɓ
a Abbinku ya je ya dubo mini shi".
"Garin yaya lambobinsa ba s
a shiga? Ni tun da yaje gidana ban samu na kar
ɓ
i lambarsa ba".
Cikin mamaki Mami ta ce "What? Me kike nufi yaje gidanki fa ki ka ce?".
"Eh mana Mami, bai gaya miki ya zo ba?".
Shiri mami tayi sannan tace "Yaushe ya je gidan naki?".
"Almost 5 Mo
nths ago, wai be zo nan ba?"
Mami ta ce "No ya zo, ban san yaje gidanki ba ne" da haka ta kawar da wannan hirar.
Abra kuwa satar jiki tayi, ta tafi
ɗ
akin Salman, komai yana nan yadda yake, gani take tamkar zata ganshi kamar yadda ta saba, ta kalli ka
tafaren hotonsa da yake
ɗ
akin da wanda suka yi su biyu, a sa
ɓ
ule ta zauna a kan gadonsa, ta fashe da kuka "Please Faris come back to me, i need you my caring brother, am missing you, kalli halin da Yaya ta shiga, mai yasa kayi nisa da Angel
ɗ
in ka, ma one
and only caring brother" ta ƙarasa Maganar cikin kuka mai tsuma zuciya.
A hankali ta tashi zaune, ta shiga Gmail
ɗ
in ta, ta fara rubutawa Salman saƙo mai cike da tsantsar nuna kewa, mai matuƙar ratsa rai da girgiza zukata, tana rubutawa tana zubar da ha
waye, ta kammala ta ajiye wayar tare da lumshe idanunta.
Meenal ce zaune a kan makeken gadonta, tana kiran layin Usman, tun safe take kiran wayarsa amm yaƙi
ɗ
agawa, ba ta haƙura ba ta cigaba da nacin kira, sai da babu zato ba tsammani taji ya
ɗ
aga
bai ko yi mata Sallama ba ya fara fa
ɗ
a "Wai me kike nema a gurina ne, tun safe kin hanani sukuni kin addabeni da kira meye haka?".
"Haba Usy, ai ka
ɗ
aga kaji dalilin kiran ko?".
"Ba zan
ɗ
aga ba idan na
ɗ
aga me zan miki?".
Cikin shagwa
ɓ
a ta ce "Pl
ease calm down baby, dan Allah ka fuskance ni".
'malama ki fa
ɗ
i abin da zaki fa
ɗ
a ina da ayuukan yi".
"Amma ai naga yanzu ba lokacin aiki bane".
"Zaki fa
ɗ
a ko sai na kashe wayata?"
Meenal ta marairaice ta ce "Yaushe zaka zo, sai mu yi magana".
"Haba Meenal, ai ni da gidanku har abada, ko har kin manta wulaƙancin da ki ka yi mini?"
"Dan Allah baby ka daina tunawa, sharrin shai
ɗ
an ne, Please come to me haba My usy".
Usman ya ce "Ke dakata, ba wata yaudara ko kalaman ƙarya da zaki yaudaren
i da su in amince da ke".
Kawai ta fashe da kuka "Allah ba kalaman yaudara bane, dan Allah baby ka zo, Wallahi kai nake so".
Usman ya ce "Eh saboda wancan ya gudu ko?"
"Wallahi be gudu ba, kawai dai zuciyata kai take so".
"Kin manta da rashin
ɗ
aga wayata, da wulaƙanci da ki ka dinga yi mini a kan saurayinki ko?".
"Dan Allah ka daina tunawa, kuskure ne ba zan sake ba".
"Shikenan zan yi shawara".
"A'a dan Allah ba sai kayi ba, Please Baby me, wlh Ina sonka Sosai na yi missing
ɗ
in ka".
'hmm Allah yasa da gaske ki ke".
"Wallahi da gaske nake".
"Shikenan zan duba".
"Yawwa Baby ina nan ina jiranka" bayan sun yi sallama tayi ajiyar zuciya ta kalli wayar ta ce "Gara tun wuri in yiwa kai na ƙiyamul laili, in lala
ɓ
o shi ya dawo".
Ji
n Abra ta zo, ya sanya su Ammi suka zo, suka cika gidan wanda hakan ba ƙaramin da
ɗ
i ya yiwa Abra ba, Mutanen da ba ta da wata alaƙa da su ta jini, amma suna nuna mata soyayya haka, har hawaye ta dinga yi wanda basu san dalili ba, suka din ga yi mata nasih
a a zatonsu duk kewarsu ce ta sanya ta haka.
Sai da duk sun lura da irin ramar da tayi, ba wanda yayi Magana sai granny, da ta dinga bin ƙwaƙƙwafi a kan lallai sai ta ji mai ya samu Abra haka dan da alama ba iya laulayi ke damunta ba, amma Abran ta ƙi fa
ɗ
a.
Kwanan Abra biyu Adnan ya zo ya ce tafiya za suyi, Abra tamkar ta
ɗ
ora hannu a ka tayi ihu, gashi tun da ta zo Abbi baya gari basu ha
ɗ
u ba, ta shiga cikin fargabar komawa cikin uƙubar Adnan, amma ta koma duba abinda ka iya faruwa idan da ta sanar da
halin da take ciki, haka nan ba yadda ta iya, ta bishi suka koma Kaduna.
Faris na zaune a aji ana mus lectures, sai dai ya ji bugun zuciyarsa na matuƙar ƙaruwa, ya rasa abin da yake masa da
ɗ
i, kuma ya rasa dalilin faruwar hakan, yayi ta maimaita "Hasbun
allah wa ni'imal wakil" hakan ya sanya ya
ɗ
an samu sassauci.
Malamin da ke musu lectures na Anatomy yace su yi connecting Wifi a system
ɗ
in su, zai tura musu wani abu.
Salman yana Connecting, yaga messages na shigowa ta Gmail
ɗ
insa, dan rabonsa da am
fani da daya har ya manta.
Ana tsaka da lectures, amma hankalinsa na kan saƙonnin, ya fita ya tafi Gmail
ɗ
in sa, ya ci karo da saƙon Abra. Cikin hanzari ya bu
ɗ
e ya fara karantawa.
Subhanallah duk da yadda sanyin A.c ke Ratsa ko ina a ajin, amma wani ir
in gumi ne ya shiga karyo masa, ya kasa gane kan in da saƙon nata ya dosa gaba
ɗ
aya, take jikinsa ya
ɗ
au rawa ya kasa mayar da hankali a kan karatun.
Har aka kammala bai fuskanci komai ba, haka ya koma masaukinsa, ya karanta saƙon nan ya fi sau talatin ya
na sake jujjuya saƙon a zuciyarsa.
Tuni zuciyarsa ta fara raya masa ya bar abin da yake, ya shirya ya tafi Nigeria ya ga Abra.
"No she's married now" ya fa
ɗ
a da ƙarfi yana rintse idanunsa.
So yake ya cire Abra daga ransa, ya manta da shafin soyayyarta,
dan haka dole ya nesanta kansa da duk wani abu da ya shafe ta.
Kai tsaye ya fara ƙoƙarin goge message
ɗ
in da ta turo masa, amma hannunsa ya hau rawa, ga wasu zafafan hawaye da suka fara sauka a fuskar sa.
Copying
ɗ
in message
ɗ
in yayi, daga nan ya goge sh
i gaba
ɗ
aya ya dangwarar da system
ɗ
in ya zauna yana kuka.
Tafiyar Abra da kwanaki uku Abbi ya dawo gari, sai dai haryanzu tsawon wannan lokaci ya ƙi sakin jiki da Mami su koma kamar da.
Ta same shi a part
ɗ
insa, ta kai masa Abinci, bai ce