Showing 219001 words to 222000 words out of 260401 words

Chapter 74 - Dare da Duhu complete

wacce ta

yi kwance a cinyar Inna sumarta gwanin sha'awa duk ta bayyana domin ita har tafi Abra tsayin suma.

"Ai ba zama bari a ki rawo kawonta sai an yi magana ta fahimta ko?"

"Hakan yafi ina son komawa,amma sai an tsayar da manufa" "Ƴar Baba maza jeki kira

kawonki yanzu" miƙewa tayi ganin Adnan

ɗ

in ne kuma yasa ba tai musu ba. Suna zaune ta dawo tare da kawon nata. Sun gaisa da Adnan cikin sakin fuska, da farin ciki bayan ya gama jin komai ya ce. "Allahamdulilla Allah abin godiya, yanzu dole mu fara ji idan

ita ƴar baba na son shi kuma zata aure shi ko?" Inna ta ce "Haka ne" ya juya kan Afra ya ce "Ƴar Baba kina son Adnan

ɗ

in?" Ta kalli Adnan wanda yake Kallonta yaji abin da zata ce duk a tsorace yake. Kamar daga sama yaji ta ce "Kawo gaskiya bana son shi, ka

wai iyaye na nake son a kawo mini ko akai ni wajansu amma ba zan aure shi ba" Innalillahi wata zufa ce ta shiga yankowa Adnan ya kasa cewa komai sai kansa da ya sunkuyar zuwa ƙasa.

"Yarona Adnan kada kaji komai, ina son ka kira wasu naka muyi magana ta

fahimta batun ƴar Baba ka barta akwai ƙuruciya kaji ko?" A sanyaye Adnan ya yi musu godiya kana yabar gidan.

Ikon Allah ne kawai ya kai Adnan gida yana zuwa wani zazza

ɓ

i ya rufe shi jikinsa sai rawa yake, barci ya gagari idanunshi rashin Afra tamkar ra

sa ransa ne. Da gari ya hawaye ya kira Abbi ya fa

ɗ

a masa komai tunda ya san Abba ba zai

ɗ

auki abin serious ba. Ya kira Uncle Khabir tare da Uncle Mustapha ya fa

ɗ

a musu komai.

Abu kamar wasa har Abbi ya yi dirar mikiya a ƙauyen shi da Salmanun-faris Adnan

bai iya cin komai ba, ya fito cikin ƙyakkyawar shiga ta amy colour

ɗ

in shadda wacce ta yi masa kyau. Lokacin suna ƙofar gidan Hakimi Salman na cikin mota yana vedio call da Mami little nayin dry.

Ganin Adnan ya sa Abbi ya yi Sallama dasu Hakimi idanunshi

akan Adnan ya ce "What happing to you son? You looks so Lean and weak" murmushi kawai Adnan ya yi ya ce "Am okay Abbi ya mutan gidan?"

"Lafiyarsu lou har little,tare muke da Salman ya dawo garin" shiru Adnan ya yi rabonsa da Salman har ya manta tun a

ɗ

akin da Abra ta rasu, daman ha

ɗ

uwar ƙarshe da sukai ba mai da

ɗ

i sukai ba, yasan zuciyar Salman

ɗ

in cike da jin zafin shi.

"Muje mota mu ƙarasa ko?" "Abbi a ƙasa za a shiga" Abbi ya ce "Ohh to bari na kira Salman" Salam na cikin mota Abbi ya bubbuga yana

kiran sunansa. "Yes Abbi" bu

ɗ

e motar da zai yi idanunshi ya sauka akan Adnan wanda yake tsaye ya zura hannunsa a cikin Aljihu.

Fitowa ya yi shaddar jikinsa na ƙara wacce take iri

ɗ

aya data Abbi, shi bai san me ya kawo su ƙauyen ba, bai ta

ɓ

a tunanin zai h

a

ɗ

u da wannan mugun mutumin ba da bai zo ba.

Babu wanda yaiwa

ɗ

an uwansa magana Abbi na lura dasu bai ce komai ba, duk da har yanzu babu wani babban dalilin daya sanya suke hakan a garesa zai ma iya

ɗ

auka ko rashin sabo da juna ne. A haka Adnan da Abbi

na gaba Salman na baya shima hannunsa a Aljihu yana ƙarewa ƙauyen kallo har suka isa ƙofar gidan su Afra daman kawon nata yana nan. Iso akai musu suka zauna saman tabarma Salman bai shigo ba ya tsaya

ɗ

aukan wayar Ammi dake tsokanar shi.

"Yaronku ya zo m

ana da zance wanda a garemu zance mai muhimmanci ne, duba da halin da yarinya ke ciki muna saka ran ta dalilinsa zamu samu iyayenta, shi ya sa na nemi ganin wani nasa mu tattauna akai da kuma ƙara jin ta bakin yarinyar a karo na biyu" Abbi ya jinjina kai g

aba

ɗ

aya hankalinsa ya yafi zuwa inda zai ga mai kama da Abransa ya fito a hankali ya ce "Masha daga namu

ɓ

angaren muma haka abin yake, zamu samu yarinya ta maye gurbin ƴar uwarta Sannan mu samu bayanin da zai taimaka mana wajan gano asalin abin da yake fa

ruwa, ina kuka tsinceta?"

"To a yadda murgayi ya fa

ɗ

a wata rana yaje wajan gari gefen jeji domin duba wasu magunguna na itace, acikin wannan lokacin ne kuma ya tsinci Yarinya a ƙasa ita ka

ɗ

ai, sai a sannan ya fahimci kamar ƴan daba ne suka shigo cikin j

ejin domin sama sama yake yajin ƙarar bindigogi, ya

ɗ

auki yarinya kawota wajan ƴan sanda suka ce sun bashi domin babu wasu iyayenta da za a samu, suka saka mata suna Afra wannan shi ne abin da muka sani"

"Ikon Allah, Ubangiji mai yadda ya su" Nan Abbi

ya fa

ɗ

a musu yasa ya tsinci Abra da komai har kawo rasuwarta "Yanzu ina ita yarinyar take, ai Wannan abin bana wasa bane muna buƙatar ta cikin familynmu" Inna ta shiga kiran sunan ƴar Baba fitowa tayi a

ɗ

aki cikin ƙyakƙyawan shiga mai kyau, Abbi ya tsora m

ata idanu dauriya kawai ya yi da bai je ya riƙeta ba, yana ƙara jinjina girman zatin Ubangiji da ƙuddirarsa. Zama tayi tana gai da Abbi suna ha

ɗ

a idanu da Adnan ta tura masa baki, ya yi mata kallon ki tausaya mini. Kawo ya gyara zama ya ce "Ƴar Baba zan ƙa

ra tambayarki a karo na biyu kina son Adnan zaki aure shi ya sadaki da iyayenka na gaskiya?" Afra na ƙoƙarin magana Sallamar Salman ta daki kunnenta juya sukai banda adnan da zuciyarsa take cike da fargaba.

Mutuwar tsaye Salman ya yi lokacin da idanunshi

ya sauka akan Afra bakinsa na rawa ya ce "Yaya...!!!"[11/16, 6:44 PM] Abk: A gigice Salman ya ƙarasa wurin da 'yar Baba ke zaune, ya rirriƙeta yana girgiza kai "Abbi ban gaya maka ba? Dama na san Angel ba ta mutu ba" ƙura masa idanu Afra ta yi, tana bin fa

raren idanuwansa da kallo, Masha Allah ga wani dadda

ɗ

an ƙamshi da yake fitarwa.

"Talk to me Angel, dan Allah ki yi magana Yaya".

A

ɗ

an shagwa

ɓ

e Afra ta ce "Kai ka cikani" wani malolon takaici ne ya ƙule zuciyar Adnan, ya yunƙura yana ƙoƙarin

ɓ

an

ɓ

are Salm

an daga jikin Afra.

Hanka

ɗ

e shi Salman ya yi, yana sake rirriƙe Afra.

Abbi ne ya

ɓ

an

ɓ

aro Salman daga jikin Afra, yana fa

ɗ

in "haba Faris, your sister is no more, wannan ba ita bace 'yar uwatta ce"

Dafe kai Salman ya yi, ya rintse idanunsa yana sauke aj

iyar zuciya, ya kwanta a jikin Abbi yana ta maida numfashi. Tsura masa idanu Afra ta yi, gaba

ɗ

aya tausayin Salman ya kamata, lallai suna matuƙar so da ƙaunar wannan yayar ta ta.

"Inna wannan ne baban nawa?" Tayi maganar tana kallon Abbi.

Abbi ya yi mu

rmushin ƙarfin hali yana ƙarewa Afra kallo, idan ba wanda ya yiwa Abra kyakykyawan sani ba, babu yadda za ayi kace ba Abra ba ce ba.

"Ni ne na tsinci 'yar uwakki, na riƙeta na raineta, har zuwa lokacin da Allah ya kar

ɓ

eta. Kamar ki

ɗ

aya sak da ita, tabbas

da a wani wurin na ganki zan iya cewa Abra ce"

Idanun Afra ya cika da hawaye ta ce "To ina babana, suwaye iyayenmu? Me yasa suka yar da mu? Ko mu ba 'yan halak bane?"

Abbi ya ce "Kul kika ƙara fa

ɗ

ar wannan maganar, ku 'yan halak ne nine nan uba a ga

re ku baki

ɗ

aya".

Sosai Afra ta sake fashewa da kuka tana girgiza kai.

Abbi ya ce "Ka bita a hankali, haka Abra ma take da yawan kuka" A hankali Salman ya gyara zamansa ya jingina da jikin Abbi, yana cigaba da bin Afra da kallo. Ita kuwa yadda Salman

ya kashingi

ɗ

a jikin Abbi ne abin ya burgeta, da alama shima shagwa

ɓ

a

ɓɓ

e ne.

Kawun su Afra ya ce "To yanzu ya muke ciki da batun neman Auren yarinyar nan da kuka zo?". Nan da nan Afra ta sake tsuke fuska tana harar Adnan.

Abbi ya ce "Wani hanzari ba

gudu ba, me zai hana a jinkirta batun neman Auren nan, yarinyar nan ta samu nutsuwa a karo na biyu sai a sake tambayar ta. Sannan dan Allah ina roƙon wata alfarma, ina son ku bani Afra in tafi da ita gidana, tun da ina kan neman iyayensu, kuma ko ba komai

Yarinyar da Abra ta rasu ta bari, zata samu shaƙuwa da kusanci da 'yar uwar mahaifiyarta".

Aikuwa Inna ta ce "Ai wannan abu ba mai yiwuwa bane, a gaskiya ba zan iya bada Afra ba, shekara da shekaru ina rainon a bata rana tsaka a rabani da ita ba, gaskiy

a ba zan iya ba" ta ƙarasa maganar a hasale.

Adnan dai ya rasa bakin Magana, sai bin su da ido kawai da yake yi, yayin da 'yar Baba ke ta zubar da hawaye, wanda ita kanta ba ta san dalilin hakan ba.

Salman ba kunya ya tashi, ya ƙarasa gaban Afra ya z

auna, ya tsura mata idanu wanda sai da hakan ya takurata, ta ji jikinta na tsuma, saboda kwarjinin da ya yi mata.

"Yaya" ya furta a sannu. A hankali ta

ɗ

ago fararen idanunta ta kalleshi, duk da bata san dalilin kiranta da hakan ba.

"A duk lokacin da na

ke tare da Abra, babban abin da yake jefani a cikin damuwa da tashin hankali, shi ne zubar hawayenta, kamar yadda ta rayu da son ganin Farinciki da murmushi a fuskata, dan Allah ki daina zub da hawaye, ina ganinki ne kamar Abranmu, ni haryanzu ban yadda ba

ke ce Abra ba, dan Allah ki bimu gidanmu ki maye mana gurbin Abra, duk da mahaifiyata na kula da Little, amma little na kewar mahaifiyarta. Ko zaki so ta rayu ba tare da sanin kowa nata ba, kamar yadda kuka rayu a mabanbantan duniyoyi ke da 'yar uwakki, d

an Allah ki Angel ki taimakawa rayuwarmu, we still needs you in our lives, Ni, Little, Mami Abbi da sauran su"

Inna kuwa kuka ta fara yi, tana share hawaye, tana fa

ɗ

in "Wallahi ba mai rabani da 'ya ta, ba in da zata je"

Kawun Su Musa ya ce "Hajara, w

annan kukan da kike kina ba za su tafi da ita ba ba shine masalaha ba, dan Yarinyar nan ba zata cigaba da zama ba tare da an san suwaye iyayenta ba, wataƙila tafiyar ta su da ita ya zamana silar sanin in da iyayenta suke ba"

Nan aka shiga jayayya,

ɓ

anga

ren su Abbi suna roƙon a basu Afra, Inna kuma ta dage ta ce ba zata bayar ba, Adnan ka sa jurewa ya yi, ya tashi ya bar gidan ya zauna a waje.

Sai da Inna ta ga an fi ƙarfinta, sannan ta amince ta ce sai an je wurin mai gari ayi abu a hukumance, kar a g

udar mata da 'ya.

Haka kuwa aka yi, aka je gaban maigari, aka kuma sake yin bayani, maigari ya sake jadadda musu bayanin yadda aka tsinci 'yar Baba da irin riƙon da marigayi ya yi mata.

Nan Abbi shima ya kuma yi masa bayanin yadda ya tsinci Abra a daji

wurin yaƙi, tare da nuna musu hotunan Abra, tare da yi musu bayanin buƙatar sa na a bashi Afra.

  Da haka sai da aka dangana da wurin 'yan sanda, na wannan ƙauye, in da file

ɗ

in Afra tsintar Afra yake, aka sake ka

ɗ

e File, Abbi yayi amfani da ƙarfin kaki

a wurin, aka yi rubutu tare da amincewa zai tafi da Afra.

Sai bayan la'asar su Abbi suka koma gidan su Afra, nan Baffa suka tabattar mata da cewa, an bawa Abbi izinin tafiya da Afra. Ita kanta Afra gaba

ɗ

aya ta ki

ɗ

ime, da jin wannan batun, tana da burin

ganin iyayenta a rayuwarta. Salman kuwa ji yake tamkar Abran sa ce ta dawo rayuwarsa, babban jin da

ɗ

in sa shi ne tafiya da za su yi da Afra gida.

Inna ta rungume Afra tana ta kuka, saboda sabo, shi kansa Yaya Musa sai da ya yi kuka, saboda 'yar Baba akwa

i shiga rai, tsawon shekarun da ta yi a tare da su, ba su ta

ɓ

a rabuwa tsawon lokaci ba, sai dai yanzu rana tsaka an musu fin ƙarfi an raba su da ita. Haka Inna ta ha

ɗ

awa Afra kayanta, tana kuka Afra na kuka su Abbi suka taho da ita.

Yau Little rikici

take ji, saboda zazza

ɓ

i da yake

ɗ

an damunta, Mami sai fama take da ita amma sai koke koke take yi, da ƙyar ta samu ta yi bacci, ta kwantar da ita a falo, ta shiga kitchen a gurguje tana gabatar da ayyukanta, dan tun da Abra ta yi Aure, ba ta yadda a kawo m

ata mai aiki ba, saboda ba ta son ƙazanta.

Tana girki tana Mamakin yadda aka yi Su Abbi suka da

ɗ

e haka ba su dawo ba, wayarta ta

ɗ

auka ta kira Abbi, amma bai

ɗ

aga ba, ta kira Salman, shima sai da ta yi masa kira biyu sannan ta samu ya

ɗ

aga.

"Hello Mami,

Ina daughter na?"

"Kai na kiraka in ji ya akai na ji ku shiru, amma kana mini zacen daughter".

Faris ya ce "Mami muna nan tafe da wani abin mamaki mai girgiza zukata".

Saroro Mami tayi ta ce "Faris bana son shirme, wane irin abu ne haka?"

Jiki

a sanyaye Faris ya ce "Mami ki kwantar da hankalinki, muna Lafiya mun kusa shigowa cikin Kano insha Allah".

"To shikenan, Allah ya kawo ku lafiya" ta ajiye wayar tare da komawa wurin da ta ajiye Little amma ba ta nan. Da sauri ta ƙarasa tana

ɗ

aga filon

kujera, amma ba ts ga Little ba.

"Ki daina wahalar da kan ki, ni na

ɗ

auketa kin ajiye yarinya a kan kujera, idan ta tashi ta fa

ɗ

o baki da asara, ko da yake ba abin mamaki bane, ita ma zaki mata irin riƙon da ki ka yiwa babarta ko?" Cewar Salima da ke wa

Mami Magana cike da gadara.

Wani marurun takaici ne ya tokarewa Mami wuya, amma cike da salo na goggaun matan da suka kwana biyu a duniya, ta yi murmushi ba ta tankawa Salima ba, dan ba ta fi sa'ar Abranta ba, ta nemi wuri ta zauna a kan kujera, ta fara

cin Abincin ta.

Salima ta so Mami ta tanka mata, ta yaga mata rashin mutunci son ranta, amma sai ta ga sa

ɓ

anin abin da ta yi tunani.

Mami ta cigaba da kallo, tana sipping tea, suka jiyo Little tana ta tsala kuka, daga sashin Salima, da sauri Salima ta ta

fi ta

ɗ

auki Little, sai dai juyin duniya, amma little ta ƙi yin shiru, sai cilla ƙafafuwa take tana rintse idanuwa, ba shiri ta fito da ita a kafa

ɗ

arta, tana miƙawa Mami ita.

Maimakon Mami ta kar

ɓ

eta sai ta miƙe, ta bar falon.

Salima ta rasa yadda za ta

yi da Little, gashi ita ba ta saba da kukan yaro ba.

Tun a hanya suka rabu,  Adnan ya nufi Kaduna, dan zuciyarsa ba zata iya jure cigaba da kallon Afra tana furta ba ta son sa ba, yana ji yana gani, Abbi Salman, da Afra suka nufi Kano, sai dai Adnan tun

kan ya ƙarasa Kaduna, wani irin zazzafan zazza

ɓ

i ya rufe shi, gaba

ɗ

aya al'amura sun caku

ɗ

e masa, bai san ya zai yi ba idan har ya rasa Auren Afra a wannan karon, bai san abin yi ba. 'Allah sarki Abra, a kallon Farko da na yi mata, na ga tsoro a fuskarta,

bayan nasarar kauda tsoron fuskarta da na yi, na maye gurbinsa da tsananin soyayyata a zuciyarta, sai dai kash na yi wautar da na sanya ƙiyayyata a zuciyar Abra, har kan ta rasu take sanar mini da bata ƙaunata, Allah ya jiƙanki matata ya yafe mini, Allah

ya sa 'yar uwakki ta yadda ta Aureni' yayi Maganar yana zubar da hawaye.

Afra tsayawa ta yi tana ƙarewa harabar gidan kallo, da ganin yadda sojoji ke kaiwa suna komowa a harabar gidan, ta jinjina Arziƙi da Allah ya yiwa mariƙin Abra, sai dai jikinta d

uk a sanyaye yake, dan tun yanzu kewar ƙauyensu ta fara damunta, sai dai ba ta da burin da ya wuce ace ta sadu da iyayenta, komai talaucinsu komai muninsu.

Kukan little ne ya kara

ɗ

e gidan, Abbi ya shigo falo da sallama, ya tarar da Salima tana tsaye tan

a ta jijjiga little da ke tsala uban ihu. Ya ƙarasa ya kar

ɓ

eta a hannunta, yana fa

ɗ

in "Garin yaya aka barta take kuka haka?".

Salima ta ce "Oho, ajiyeta ta yi a falo tai tafiyarta ta barta"

Abbi ya kar

ɓ

eta, ya nufi sashin Mami a fusace "Na'ima wane iri

n sakarci ne haka, zaki tafi ki bar Yarinya tana kuka a falo, kin san ƙyuya take kin barta da Salima sai kuka take mata, yanzu da tsautsayi ya sanya mun taho da mahaifin yarinyar nan, haka zai zo ya tarar da ita tana kuka".

"Kar ka sake yi mini tsawa Kh

amal, baka san maiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login