Showing 132001 words to 135000 words out of 260401 words
tsawa ya ce "bance ki yarda ba, amma ni da Abbin naki musan cewa ke ba ƴarsa bace kiyi tunani kaf dangin ku dawa ki ke kama? Just think bance ki yarda ba, amma zaki rayu a gidan nan tamkar baiwa!"
[10/13, 11:29 AM] Abk:
Jiki na rawa, Khairy ta kira Mami tana salati tana salallami, Mami ta
ɗ
aga wayar ta ce "Ya aka yi? Ta na ina ne, mutane sun fara taruwa fa?".
Khairy murya na rawa ta ce "Mami na kira mai kwalliyar ta ce mini tun uku, aka gama kwalliyar, kuma ta tafi".
Mami ta ce "Ta tafi taje ina?"
"Mami Wallahi ban sani ba, ba guri
ɗ
aya muka je kwalliyar da ita ba, ni gurin da naje daban".
Mami ta ajiye waya tana fa
ɗ
in "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yarinyar nan gidan ubanwa ta tafi ne? Ace an gama kwalli
ya tun uku amma har ha
ɗ
u da rabi ba ta iso gida ba, ga mutane sun fara taruwa".
Anty suwaiba ta ce"Allah yasa ba guduwa ta yi ba".
Mami ta zare ido ta ce "Ta gudu ta je gidan uban wa? Lallai ma yarinyar nan".
Abu kamar wasa, ba Abra babu dalilinta
, tun ana maganar ƙasa_ƙasa, har mutane suka fara jin halin da ake ciki.
Abokan aikin Adnan ne, suke ta shiri cikin shigarsu ta police, domin dai za'a yi parrate na ban girma ga Adnan da amarayarsa.
Usman ne ya kalli Adnan da ke ta ha
ɗ
e rai ya ce "
Wai ha
ɗ
e ran me kake ne?".
Adnan ya ce "Am jealous ne, duk wannan garadan sai kun je kun kalle mini mata".
Aminu ya ce "Kai dalla ware, ai kaima gardin ne, sai kace a kanka aka fara Aure, ko da yake tsiyar mutum ya zama tuzuru kenan, duk sai ya fara
behaving abnormal".
"Meye banbancina da kai? Har gara ma ni yanzu zan shige daga ciki, kai kana waje".
"Nima ina hanya ne" Usman yayi Maganar yana murmushi.
Daga haka suka kammala shirinsu, suka fara haramar tafiya gidansu Abra.
Granny ce t
a shiga sashin Na'ima tana fa
ɗ
in "Ke Na'ima, wai wace Maganar banza nake ji ne? Wai kamar Ana Abra ta
ɓ
ata, gidan ubanwa ki kai ta?"
"Haba granny, Ina kuwa zan Kai ta, daga zuwa kwalliya ba ta dawo ba".
"Ƙarya ki keyi, ana Magana kina wani ƙifta ido
kamar ta Allah, ki fito da yarinyar nan duk in da ki ka kaita, kan in samo madoki in shemeki a gurin nan".
Ammi ce ta ce "Granny ki yi haƙuri, ya za'ayi ta aikata haka ga 'yar ta, Yanzu dai muyi ta addu'a, kuma a kira shi angon a sanar masa dan a san ab
un yi".
Granny ta ce "Wai ke Yaushe zaki gane kan makircin wannan yarinyar ne? Ai duk abun da akace tayi babu mamaki, yau duk abun da za'ayi sai an nemo mini jikata. Amm ke nace ina tabarau na ne? in ƙarewa wannan mara Kunyar kallo, in kalli idanunta so
sai, dan ni idan na kalli idon mara gaskiya ina gane shi".
Ammi ta ce "Glass
ɗ
inki yana in da ki ka yi salla, amma dan Allah ki dena wannan maganganun, bari a san abunyi, ko a tura wasu gurin mai kwalliyar".
Na'ima kuwa iya ƙuluwa ta ƙulu, ji take ka
mar ta rufe Granny da duka, shegiyar tsohuwa hayyataciya, sai tsawon rai kamar dabino, ta ƙi mutuwa kuma kullum cikin rikici take, tsawon shekarun da Na'ima tayi tare da Khamal Granny ba ta ƙaunarta sam.
Gida ya rikice ana neman Abra, ita kuma Granny ta
rikice tana neman tabarau, ta
ɗ
ora da masifar cewa bayan sace Abra da Na'ima tayi, ta kuma sace mata glashinta, saboda baƙin hali.
Anty Suwaiba ta ce "Wai ke Na'ima ba wani mataki da zaki
ɗ
auka a kan wannan sokuwar tsohuwar, shegen surutun tsiya kamar
an jefeta a ka?".
"To ni ya zan yi da ita? Wannan kaidinta ya fi yadda kike tunani, yanzun nan za ta ƙullawa mutum sharri.
Ɗ
akin Salman Granny ta nufa, tana cigaba da zage Na'ima, Ammi ta ce "Granny me zaki yi a nan kuma?".
"Tabarau na nake nema".
"To mai ze kai glass
ɗ
inki nan kuma? Na ga tunda muka zo baki je nan ba".
"A'a, ance idan raƙuminka ya
ɓ
ata ka neme shi har kura tandu, yo na sani ko wannan algungumar ta yi garkuwa shi ta kai ta
ɓ
oye" ta ƙarasa Maganar, tana nufar
ɗ
akin Salman.
Sai dai tana shiga
ɗ
akin, ta ƙwala uban ihun da ya janyo hankalin 'yan biki.
"Gata nan ku zo gata!" Ta yi maganar cikin ihu.
Su Ammi na zuwa, suka tarar da Abra a zaune, fuskarta sharkaf hawaye.
Ashe tun bai fi uku da rabi ta dawo gida ba, ta shig
a ta ƙofar baya, tabi ta kitchen ta shige
ɗ
akin Salman abunta, kuma ta kashe wayoyinta.
Ammi ta ce "Abra, dama kina nan ki ka
ɗ
agawa mutane hankali? Kuma kalli duk kin fara
ɓ
ata kwalliyar".
Cikin kuka Abra ta ce "Ammi Faris
ɗ
ina, zan yi Aure baya nan
, dan Allah Ammi kice musu na fasa Auren nan a dawo mini da Faris
ɗ
ina".
N'a'ima a fusace ta ce "wannan wane irin sakarci ne haka Abra? Mun tara mutane kina neman ki bamu Kunya? Kawai kin
ɗ
agawa mutane hankali".
"Mami ni bana son Auren nan na fasa, d
an girman Allah Ku dawo mini da
ɗ
an uwana" tayi maganar tana ƙoƙarin cire
ɗ
aurin kanta, ga numfashinta da ya fara sama.
Ammi ta girgiza wa Na'ima kai, alamar ta dena yiwa Abra fa
ɗ
a.
Granny ta ce "Ji min 'ya da wauta, ke yanzu sai ki fasa Auren, aikuw
a da kin yiwa kanki kutunguilar tsiya, hmm jiya ba yau ba tsohuwa ta tuna kwanan turaka, yarinya karki cuci kanki" Granny ta yi maganar tana watsa guntun goronta a baki, ta bar
ɗ
akin, murmushi Ammi ta yi, Granny ba ruwanta haka take sakin 'yan maganganunta
idan ta raya mata".
Ammi ta maida hankalinta kan Abra, ta din ga yi mata Nasiha tana rarrashinta, ƙarshe sai da aka kira Abbi video call, shima yayi ta rarrashinta, Sannan ta haƙura.
Aka samo wata mai kwalliyar ta gyara mata kwalliyar da ta fara
ɓ
ataw
a da hawaye.
Na'ima ma ha
ɗ
awa tayi cikin wani rantsatsten leshi fari da golden, tun daga wuyanta zuwa yatsunta gwal ne.
Hakan yayi daidai da ƙarasowar Adnan da da abokansa, haka zalika mota mota na 'yan uwan Adnan
ɗ
in suka hallara a ƙatuwar harabar gid
an Major Khamal Khamis, wadda akai matuƙar ƙawatawa.
Mami ce da kanta ta kamo hannun Abra ta fito da ita daga cikin gida, duk da kanta a sunkuye yake, ta rufe jikinta da mayafi, amma hakan be hana Adnan tsinkayen farar fatarta da ta sha gyara ba.
Nan m
asu police band suka sauke gangunan su, suka fara bugawa domin gabatar da parrate na ban girma ga Ango sha gu
ɗ
a Sp Adnan Aliyu Matawalle, da matarsa gimbiya Abra Khamal Khamis, abun na masu
ɗ
amara ne, dan haka parrate
ɗ
in ya ƙayatar matuƙa, tare da crossin
g sword da aka gabatar duk dan murna ga amarya da ango.
A ka zo
ɓ
angaren kamu, a kama amarya ta bu
ɗ
e fuskarta, ƙanwar Hajiyar Adnan, ta ce sun biya dubu
ɗ
ari biyar a bu
ɗ
e musu fuskar Amarya.
Nan wasu suka shiga tafi, yayin da Mami ta ce "ita dubu
ɗ
ari bi
yar yayi ka
ɗ
an". Ammi ce tsawatar dan kar ayi halin ƙaranta.
Nan aka shiga gudanar da shagali, bayan Abra ta bu
ɗ
e fuskarta, wanda ba su santa ba, suka dinga jinjina kyawunta, wasu kuma suna gulmar ya za tayi da Adnan, dan da ka
ɗ
an ta wuce cikinsa.
"Swe
etheart,yau ranar farinciki ce, amma ya naga kamar za kiyi kuka?" Adnan ya fa
ɗ
a a saitin kunnenta.
"Wani farinciki bai ta
ɓ
a riskata, Faris baya kusa da ni ba, sai a wannan lokacin, wannan ne karo na farko, ban ta
ɓ
a tunanin Faris ba zai kasance da ni ba,
Ranar Aurena akan high table, ana mana hotuna da ni da shi da angona ba, sai dai....." Hawaye ne suka fara saukowa da ga idanunta.
Da sauri Adnan ya ciro hanky yana share mata ya ce "dan Allah kar ki
ɓ
ata mana Wannan Farincikin, ba kowane buri namu ne
yake zuwa ya cika a yadda muke so ba, kiyi haƙuri" haka ya rarrasheta, aka kammala event
ɗ
in wannan ranar.
Daren ranar, haka Adnan ya kasance da ita a waya, yana cigba da aikin rarrashi.
Zuba mata idanunsa yayi yana kallonta, yadda take may
e, cike da rashin Sabo, sai tam
ɓ
ele take ya sakata a gaba kawai yana murmushi, yana zuƙar shisha yana fesar da hayaƙin a cikin iska.
Ganin tana ƙoƙarin fa
ɗ
uwa ne ya sanya shi tashi da sauri ya riƙota yana murmushi "Sweetheart, it seems like you are enjoyi
ng the moment" yayi Maganar tare da kissing
ɗ
in goshinta.
Kan makeken gadon dake tsakiyar
ɗ
akin ya kaita, ya kwantar da ita, yana shafa dogon gashinta. Gaba
ɗ
aya Meenal ba ta hayyacinta, ba ta tashi farkawa daga mayen da take yi ba, sai bayan magariba.
A hankali ta bu
ɗ
e idanunta ta kalli in da ya idar da salla, ta tashi da sauri ta kalli agogo, a gigice ta ce "Ya a kai na kai wannan lokacin? Me ka bani haka na sha?".
"Calm down Baby, kayan caji ne fa kawai"
"Kamar yaya kayan caji, lokacin komawata
gida tuni ya ƙure, me zanje in ce a gida?"
"Haba ke kuwa, kamar ba babbar yarinya ba, da alama fa kin ji da
ɗ
in cajin nan da kika yi"
Wani gululun baƙin ciki ne ya cunkushe mata zuciya, a gurguje ta tattara kayanta da mukullin motarta, tai waje.
G
udu take tamkar zata tashi sama, saboda tsananin tashin hankali, cike da fargaba da zullumi ta shiga cikin gidan, a Falo ta tarar da Mummy tana kaiwa tana komowa, tana ganin Meenal a rikice ta ce "Ke daga gidan ubanwa kike Yanzu?".
"Amm...mm..... Mummy
da..dama".
"Dama me? Gidan ubanwa kika tafi? Ƙarfe nawa yanzu? Kin sanya ya tayar mini da hankali, yanzu haka ya tafi kai report gurin hukuma, akan cewar kin
ɓ
ata, ina ki ka je?".
Kan Meenal ta bata amsa, sai ga Doctor Bulama ya shigo, yana ganin Mee
nal rai a
ɓ
ace ya ce "Ke! Daga ina kike?"
"Ba ko ina".
"Daga ina kike?!" Ya sake tambayar cikin tsawa.
Rawar baki ta fara yi, amma ta kasa Magana, aikuwa yayi kanta ya shaƙota yana zazzare ido tare da maimaita tambayar daga ina take?"
"Haba doc
tor,ka bita a hankali mana, idan ka illata ta fa, ko ka manta uta ka
ɗ
aice da mu?".
"Dan ita ka
ɗ
aice da mu ba shi ya bata lasisin yin iskancin da ta ga dama ba, gidan wa kika je?".
A shaƙe Meenal ta ce "Dan Allah Daddy ka yi haƙuri, ƙawata na bi gidan
su, muka tafi gurin biki daga school".
"Meyasa baki kira kin gaya mini ba, aka dinga kiran wayarki amma a kashe?".
"Nayi kuskure, amma dan Allah kayi haƙuri kar ka kasheni" da Doctor ya ƙyale Meenal, bayan ta sha shaƙar da sai da ta kusa zuwa lahira.
Hall ya ha
ɗ
u iya ha
ɗ
uwa, Abra ta ha
ɗ
e cikin wani danƙareren Material, kai da gani ka san ba duk jiki ba, sai jikin 'yar gata.
Adnan kuwa gaba
ɗ
aya kishi ne ya mamaye masa zuciya, yadda kowa ke
ɗ
aukar hoton matarsa a waya, shifa wannan taron bidi'ar da
n anfi ƙarfinsa ne, amma da babu dalilin da zai sanya ayi wannan taron ana kallon matarsa.
MC ne ya kira Amarya, tare da umartar ta da taje ta taho da mamanta.
Cikin takun Abra na nutsuwa, taje gaban table
ɗ
in da Hajiya Na'ima take, ta durƙusa ta kamo
hannunta zuwa filin rawa.
MC ya ce "Ki kalli Mamanki, ki ce nata kin gode, kuma kina sonta"
Abra ta kama hannun Hajiya Na'ima, ta kalli idonta murya na rawa ta ce "Thank you very much Mamina, for all you did for me Bani da Abun da zance miki sai Allah
ya baki Aljanna ma
ɗ
aukaiya, and I love You Mamina" ta ƙarasa Maganar tana rungume Na'ima, tare da sakin wani irin kuka mai ban tausayi.
Nan dj ya saki waƙar Wayyo Allah mamana, Na'ima ma rungume Abran ta yi tana
ɗ
an dukan bayanta alamar rarrashi. Yayin da
ta
ɓ
alle bakin jaka, ta dinga zubawa Abra ku
ɗ
i kamar ba gobe, ji take dama Abra 'yar ta ce ta halak, da shagalin da za tayi a bikin nan yafi haka.
Haka aka yi Dinner, 'yan uwa da abokan arziki, duk sun yi bajinta, ta hanyar liƙi da bada gudunmawa.
Abb
i tuni ya sauka garin Kano tare da tasa tawagar, kasancewar bayan
ɗ
aurin Aure akwai reception na mussaman, da kuma parrate na sojoji, abunka da masu abu da abunsu.
A can birnin Sin kuwa, Salman ne zaune a wani katafaren
ɗ
aki, a gaban madubi ya sanya hot
on Abra a gaba, ya ƙura masa idanu, idan lissafinsa daidai ne, yau ne ake
ɗ
aurawa Abra Aure, Abran da ya ƙallafa a rai, ya taso ya rayu da soyayyarta, a yau ta zama mallakin wani ba shi ba, ina ma Mami ba ta sanar masa Abra ba 'yar uwassa ba ce ta jini, da
duk wannan al'amuran basu faru ba, gaba
ɗ
aya tun da ya zo China ba ya jin da
ɗ
in garin, komai nasu daban kamar ba Normal Mutane ba, gashi ko turancin ma ba kowane ya iya ba a cikinsu, dan haka abubuwa suna masa wahala, duk da wai kafin su fara lectures, sa
i sunyi wata shida ana koya musu Yaren Chinese.
An
ɗ
aura Auren Adnan da Abra, wanda dubban mutane suka sheda hakan,
ɗ
aurin Auren da ya samu halartar manyan ƙasa daga
ɓ
angarori daban-daban ciki har da Captain Faruk da aka tsinto Abra da shi.
Daidai
gwargwado an yiwa Abra Nasiha mai ratsa zuciya game da rayuwar Aure, yayin da Granny ta ta Nasihar mai
ɓ
aro_
ɓ
aro ce ba rufi ba kunyar komai.
Da la'asar aka shirya Abra cikin wata dakakkiyar rantsatsiyar lafaya, Mami ta kaita gurin Abbi, yayi mata nasiha
sosai tare da Adduoi da fatan shiga
ɗ
akin miji a sa'a.
Dangin Adnan sun zo da manyan motoci, domin
ɗ
aukar Amarayar su.
Sai dai Abra ta ƙanƙame Mami tana kuka, karo na farko a rayuwar Na'ima, tun da ta fara riƙon Abra, taji jikinta yayi sanyi, dan tun
a gurin Dinner jiya Abran ta sa jikin Na'ima yin sanyi.
Abra ta ƙanƙame Na'ima tana fa
ɗ
in "Mamina, a zaman mu idan na yi miki laifi ki yafe mini, Mami bana son barinki".
Anty Suwaiba ce cikin masifa ta ce "Wai ke bayinki ne mutanen da suka tsaya suna j
iran ki, dalla ki fito ki wuce mu tafi"
A hankali Na'ima ta shafa bayan Abra ta ce "Na yafe miki Abra, Allah ya baku zaman lafiya, muje in rakaki bakin Mota".
"Mami to ke yaushe zaki zo?".
"Very soon" daga haka ta ja hannun Abra zuwa bakin mota. D
a ƙyar Abra ta yadda ta shiga, tana kuka tana
ɗ
agawa Mami hannu.
Anty Suwaiba ta ce "Ke Na'ima, wai me kike yi hakane kamar kin damu da tafiyar yarinyar nan? Allah ya raba ki da ƙwallon mangwaro kin huta da ƙuda, amma naga kamar kina cikin damuwa? Wai n
i fa kamar ƙwalla nake gani a idanun ki".
Jiki a sanyaye Na'ima ta ce "Gaskiyar Husawa da suka ce, 'Sabo turken wawa' a zamana da yarinyar nan ban ta
ɓ
a jin abunda na ji ba jiya da ta kalli idanuna tana mini Addu'a tare da jaddada soyayyarta a gareni, id
anunta
ɗ
auke da zallar soyayyar uwa da
ɗ
a, duk da kwashe shekarun da nayi ina azabtar da ita, amma tana mini biyayya fiye da yadda
ɗ
an da na durƙusa na haifa yake mini, ko ba komai da ina ganin gilmawar ta da ta Salman, amma Yanzu shi ya tafi, ita ma kuma
haka".
"To shine me? Ke ba hutunki bane bama, ta je can ta ƙarata Allah ya tsare miki mijinki da
ɗ
an ki".
Na'ima ta ce "Hakane, dama babban fatana kenan, ta bar mini gida, shekarun da mukayi Allah ya amfana, kawai dai kin san zuciya".
"Ke dalla ca
n manta da ita".
Awanni uku cif, da magariba su Abra suka isa garin Kaduna, aka fara kaita gidan su Adnan, aka yi mata nasiha, suka bata kyaututtuka, sannan suka wuce da ita gidanta.
Tubarkallah Adnan ya ƙera mata gida na gani na fa
ɗ
a, Abbi kuma da
Hajiya Na'ima sun cika gidan da kaya na kerewa sa'a, Masha Allah gida yayi komai tsaf.
Wanda suka rako Abra daga Kano, suka koma gidansu Adnan su kwana a can, daga nan su koma Kano, Abra ji tayi Kamar ta tashi ta bisu, haka suka watse suka bar Abra.
Abra ta zauna jiran shigowar Ango, sai dai har ƙarfe goma sha
ɗ
aya ba ango ba dalilinsa, tun Abra na jira har ta fara gajiya, tsoro ya fara kamata, ta takure a ƙuryar gado, gaba
ɗ
aya tsoro ya baibayeta.
Abu kamar wasa