Showing 114001 words to 117000 words out of 260401 words
Adnan, a matsayin siriki.
Abra sai tambaya take ina Faris, amma ba wanda ya bata wata gamshashiyar amsa, ta kira wayarsa amma shiru ba ta shiga.
Bayan la'asar
aka sallami Abra, Sai da Adnan ya rakasu har gida, wanda a nan ne Abbi ya sanar masa da larurar Abra, na rashin ji sosai sai da hearin aid, da kuma halin da take shiga idan ta shiga firgici da damuwa.
Adnan ya nunawa Abbi babu matsala, A nan Adnan ya san
arwa da Abbi Kaduna zai kai Abra, a nan Abbi ya ce bai amince ba, ba ta da kowa a Kaduna, kuma ga batun karatunta, kasancewar su Shureim ma suna gidan, su suka yi tausar Abbi, sun nuna masa aure ba in da baya kai mace, kuma sai a mata transfer, ko ta sake
fresh tun da karatun ba nisa tayi ba.
Ƙ
arfe takwas na dare, Abra ta
ɗ
aga hankalin kowa a gidan, a kan ina Faris
ɗ
inta, ta je
ɗ
akinsa baya nan.
Abba ya zaunar da Abra ya ce "Abra, ni mahaifinku ne, ba zamu ta
ɓ
a za
ɓ
a muku abunda zai cutar da ku ba, Far
is jirginsa ya tashi ƙarfe sha biyu na rana, yanzu haka ya kusa China!!!
LITTAFIN RUƊI NE ₦300 NE
Via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne
ɗ
ari uku kacal.
Evidence of payment 07063065680 ko 0904787
1750
[10/6, 5:01 PM] Abk: Kallon Abbi kawai Abra take yi kamar ba ta fahimci me ya ce ba, idanunta duka a waje cikin kuka ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, why Abbi, me ya sa za ku nesanta ni da jinin jikina, Abbi dan Allah ka dawo da shi, ba zan i
ya rayuwa babu Salman a kusa da ni ba." Cikin rarrashi Abbi ya ce. "I'm sorry Daughter, na san dole ki ji babu da
ɗ
i, amma haƙuri zaki yi, ni ma ba son raina ba ne hakan." Kuka ta fashe da shi tare da fa
ɗ
in. "Amma Abbi me ya sa ya tafi ba mu yi sallama ba?
Me ya sa bai zo na gan shi ba?"
"Ya zo da safe kina bacci." Abbi ya yi maganar tare da kamo hannunta, za ta kuma magana ya hana ta da fa
ɗ
in. "Just pray for him Daughter, shi ne kawai soyayyar da zaki nuna masa, ki bar wannan koke-koken kin ga baki da la
fiya, kar ki ƙarawa kanki wani ciwon." Numfashi ta sauke mai zafi tare da miƙewa ba tare da ta ce komai ba,
ɗ
akinta ta shiga ta fa
ɗ
a kan gado ta shiga raira kuka mai tsuma zuciya. 'Shikenan Salman ya tafi? Ya yi nesa da ganin ta? Anya za ta iya rayuwa mai
tsayi ba tare da Salman ba? Faris
ɗ
inta mai share mata hawaye akodayaushe, mai fifita farincikinta akan nasa. Wata irin kewar shi ta ji tana nuƙurƙusar zuciyarta.
Kuka sosai Abra ta yi akan tafiyar Salman, tunda ta shiga
ɗ
aki ba ta fito ba har bayan
isha'i, Sallah ce kawai take
ɗ
aga ta, ita ma da ƙyar take iya tashi ta yi saboda wani azababben ciwon kai da yake damun ta, ji take kamar kan nata zai tsage gida biyu. Tana jin wayarta na ta vibrate amma ba ta kula ba, duk da ta san Adnan ne yake kiran ta.
Hajiya Na'ima ce zaune a gefen Khamal cikin farinciki, zuciyarta fess take jin ta yau, tamkar wadda aka yiwa bushara da wani babban albishir. Kallon ta Khamal ya yi na wasu sakanni cikin murmurshi ya ce. "Wai yau nisha
ɗ
in me kike yi ne Wifey? Na ga k
amar ma ko kewar
ɗ
an gaban goshin naki ba kya yi?" Yalwataccen murmushi ta saki ta ce. "Ai ko da bakina na fa
ɗ
a maka ban yi kewar Salman ba na san ba za ka yarda ba My Man, kawai ina
ɓ
oyewa ne saboda ban san na damu kaina akan abin da ya zama dole, nisha
ɗ
i
n da nake yi kuma na kasancewa tare da kai ne Mijina." Ta ƙarashe maganar tare da kashe masa ido. Murmushi Khamal ya yi ya ce. "Bayan wannan kamar akwai wani abun a ranki, ki fa
ɗ
a mini mana sai na taya ki farincikin."
"Babu komai, idan ma da akwai bai w
uce na zumu
ɗ
in ganin ranar Auren Daughter ba."
"Uhm, saboda kin kusa zama surika ko?"
"Suruka kuma ta nawa? sai dai ka ce saboda na kusa zama granny."
Murmurshi suka yi a tare, duban time Abbi ya yi ya ce. "Har 9 ta kusa amma Daughter ba ta fi
to ba? Allah ya sa ba jikin nata ba ne?" Ta
ɓ
e baki Na'ima ta yi ta ce. "Ko dai sakarcin nata ne ya motsa ba, na san yanzu tana can tana ta aikin kuka saboda tafiyar Salman."
"Kin ga lefinta dan ta damu? Ni kaina sai bayan ya tafin kuma jikina ya yi s
anyi, na san tsananin shaƙuwar yaran nan, ba ƙaramar damuwa za su shiga da rashin juna ba."
"Ai gara su saba, tunda ko ba su rabu ba yanzu za su rabu lokacin da za ta yi aure, bari na je na dubo ta." Na'ima ta fa
ɗ
i haka tare da miƙewa.
"Abra! Abra.
"
A hankali ta bu
ɗ
e idanunta da suka gaji da tsiyayar da hawaye tare da juya kanta da ƙyar ta dubi Nai'ma. Cikin raunin murya ta ce. "Mami Faris...."
"Shiiiii! kar ki ishe ni da wani zancen Faris, ki tashi ki ci abinci ki sha magungunanki."
"B
akina
ɗ
aci Mami, ba zan iya cin komai ba, Faris kawai nake son gani, dan Allah Mami ki lalla
ɓ
a Abbi ya dawo mini da
ɗ
an'uwana kusa da ni." Ta yi maganar wasu hawaye masu
ɗ
umi na kwaranyo daga cikin idonta. Cikin takaici Mami ta ce. "Sai dai nai uban lalla
ɓ
a Abbi, yarinya sai masifar tsiya, ina murna hankalina ya fara kwanciya kina ƙoƙarin tayar mini da shi, saboda wannan damuwar da kika yi har ya fara cewa jikinsa ya yi sanyi da ma bai tura shi karatun ba, nan gaba kuma na san zai iya cewa zai dawo da shi,
tunda ba ya son ganin ki cikin damuwa. Wallahi idan baki bar koke-koken banzan nan ba sai na sa
ɓ
ar miki, ki tashi ki je ki wanke fuskarki mu tafi parlour ki ci abinci, saura kuma idan kin je ki cigaba da nuna wannan damuwar, ni da ke ne."
Cikin dauri
ya Abra ta tashi ta shiga toilet, Na'ima ta bi ta da harara. Sai da ta sake yin wani kukan sannan wanke fuskarta ta fito.
Sosai Abbi ya dinga lalla
ɓ
a Abra tare da ba ta baki, dan duk da ta
ɓ
oye damurta amma kallo
ɗ
aya ya yi mata ya san tana cikin dam
uwa. Ya sanar mata Salman ya kira ya ce ya sauka lafiya, lokacin tana
ɗ
aki. Da sauri ta ce. "Abbi ba ni numbern da ya kira in kira shi."
"Ba numbernsa ba ce ara ya yi, sai gobe idan Allah ya kai mu zai siya nasa sim
ɗ
in, na san kuma ke zai fara kira da
shi." Abbi ya ba ta amsa cikin murmurshi.
Murmushin yaƙe ta yi ba ta ce komai ba ta cigaba da cin abincin dake gabanta, wanda take jin shi tamkar ma
ɗ
aciya a bakinta, da ƙyar take iya taunawa ta ha
ɗ
iye. Kallon seat
ɗ
in da Salman yake yawan zama ta yi
idan za su ci abinci, ƙwalla ce ta tarar mata a ido, ƙoƙarin mayar da ita ta yi tare da lumshe idanunta, can ƙasan mak'oshi ta ce. "I'm missing you Bloody, yaushe zaka dawo gare ni?"
Adnan ne zaune akan two seater a guest parlour'n gidan Fayya
d, hankalinsa gaba
ɗ
aya yana kan wayarsa yana tura wa Abra text, na k'auna da irin missing
ɗ
inta da ya yi daga yamma zuwa dare da bai ji muryarta ba, sai tarin addu'oi da fatan samun lafiya. Fayyad dake kallon shi ya yi murmurshi ya ce. "Thank God, yau Alla
h ya nuna mini wannan ranar, kamar a mafarki sai ga Adnan a cikin soyayya dumu-dumu." Murmurshi Adnan ya yi bai ce komai ba.
Gyara zama Fayyad ya yi ya ce. "Ya kamata zuwa yanzu a ce mun fara shirye-shiryen abubuwan da za a yi a bikin nan fa, na ga kai
ta soyayyar ka kawai kake, kuma ga lokaci yana ta motsowa."
"Shirye-shirye like how?"
"Su dinner da sauransu."
"No need,
ɗ
aurin Aure kawai za a yi a kawo mini matata."
Hararar shi Fayyad ya yi ya ce. "Wallahi ba ka isa ba, dole mu warwasa." W
ith serious Adnan ya ce. "Sai dai ku warwasa ku ka
ɗ
ai, amma babu wani abu da zan yi, kawai matata ta yi kwalliya a gama kalle mini ita, a yi ta mata pictures ana
ɗ
orawa a media kowane kare da biri ya gani, ba zai yiyu ba gaskiya." Murmurshi Fayyad ya yi ya
ce. "Mayar da wuƙar Baban kishi, mu duk da aka kalle namu matan ai ba ma son su." Ɗage kafa
ɗ
a Adnan ya yi bai kuma magana ba.
Sai after 10 na dare sannan Abra ta kira Adnan, time
ɗ
in ya koma masaukinsa fitowar shi kenan daga wanka ya ji wayarsa na
ƙ
ara, with special sound
ɗ
in da ya saka wa Numbern Abra. Cike da zaƙuwa da son jin muryarta ya
ɗ
aga kiran.
"Matata!" Ya fa
ɗ
a cikin tsantsar k'auna.
A hankali ta ce. "Na'am." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "I missed you Baby, ya jikin naki?"
"Alham
dulillah, na ji sauƙi."
"Are You sure?"
Gya
ɗ
a masa kai kawai ta yi, saboda da ƙyar take iya magana.
"Ya na ji muryarki haka kuma? Ko dai jikin ne Sweetheart?" Ya yi maganar cikin kulawa.
Ya sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi, hakan ya sa ta fas
he masa da kuka. A rud'e ya ce. "Subhanallahi, Angel what happened? Are you okay?" Cikin kuka ta ce. "Faris ya tafi China."
"Oh My God, sorry Angel, yaushe ya tafi?"
"Ɗazu, kuma ko sallama ba mu yi ba."
Cikin rarrashi ya ce. "Stop crying please
My love, ai dan ya yafi China ba yana nufin kun rabu ba ne har abada, tunda ga waya duk time
ɗ
in da kike so zaki yi magana da shi. Please ki bar damun kanki, ko so kike in kasa bacci?"
"A'a."
"To ki yi shiru, na yi miki alƙawari bayan mun yi aure da
kaina zan kai ki ki ga Salman
ɗ
inki."
Cikin farinciki ta ce. "Dagaske?"
"Eh mana, mene a ciki, duk abun da zai saka ki farinciki kome ne zan yi miki, kin wuce haka a gurina."
Ajiyar zuciya ta sauke cikin jin da
ɗ
i, cikin murna ta ce. "Thank you."
"Don't mind Dear, bari na saka kaya, fitowata kenan daga wanka kika kira ni, i will call you later."
"Okay sai ka gama."
Cikin shagwa
ɓ
a ya ce. "Ki zo ki shirya ni my love, I'm tried."
Murmurshi ta yi mai sauti cikin kunya ba ta ce komai ba,
shi ma murmushin ya yi ya ce. "Bye, Sarkin kunya, soon zan cire miki duk wannan kunyar taki, wuyarta a kawo ki gidana mu kwana tar...." Bai ƙarasa ba ta kashe wayar still tana murmurshi, wani irin son Adnan na ƙara mamaye zuciyarta, wayar da suka yi yanzu
ta sa ta fara jin sauƙin damuwar tafiyar Faris da kewar shi.
Cikin takunta na
ɗ
aukar hankali mai cike da izza ta shiga parlour'n part
ɗ
in Momy. A shagwab'e take kiran sunan, "Mommy, Mommy."
"Na'am Daughter har kin dawo?"
"Na dawo Mommy."
"Welcome" Hajiya Saudat ta fa
ɗ
a tare da rungume Meenal."
"Thank you Mom, I want to take Bath, ki saka wata a cikin baƙaƙen yaran nan ta ha
ɗ
a mini ruwa a toilet yanzu."
Shafa kanta Mommy ta yi ta ce. "Yanzu kuwa."
Around 11pm Meenal tana online
tana chat mutumin da suka ha
ɗ
u
ɗ
azu ya yi mata magana, babu bata lokaci ta yi masa reply. Introducing kansa ya yi mata ya sanar mata sunansa Abdul. Daga nan suka fara hira, Abdul ya iya tsara mace, hakan ya sa a cikin daren ya sace zuciyar Meenal. Dama 2 d
ays ta rasa gane kan Usman, ya canza mata gaba-d'aya.
Har 2 na dare suka kai suna chat
ɗ
in, wanda rabi duk stickers ne da emoji na love da hug da kisses Abdul ya cika ta da shi.
Cikin lokacin ƙanƙani Meenal suka saba da Abdul sosai, kodayaushe cik
in chat da waya suke, video call kam kusan raba dare suke suna yi. 1 week da ha
ɗ
uwarsu ya zo gidansu, aka sauke shi a parlour'n saukar baƙin Bulama. Abdul Sa
ɓ
anin Usman yake, sun banbanta a halayya, dan shi Meenal tana zuwa ya rungume ta tare da kissing
ɗ
i
nta. Hakan ko a jikin Meenal, ta biye masa sukai ta shashanci.
Shirye-shiryen biki ya kankama ta kowanne
ɓ
angare, su Hajiya Na'ima ba zama, ana ta shirye-shiryen yanda abubuwa za su kasance. Yanda Na'ima take murna da rawar ƙafa akan bakin ba ƙarami
n mamaki ya ba wa su Aunty Iman ba, sanadiyyar ƙin Abra da suka san Na'ima tana yi.
A
ɓ
angaren Amarya kuwa tana cikin tashin hankali da damuwa, sakamakon kewar Salman dake addabar ta. Kullum sai ta
ɓ
uya a
ɗ
aki ta ci kuka ta ƙoshi. Ko kuma ta zauna ta s
aka hoton shi a gaba tay ta kallo tana hawaye, ko ta faki ikon Mami ta shiga
ɗ
akinsa ta kwanta tana shaƙar ƙamshinsa da har lokacin bai bar
ɗ
akin ba. Babbar damuwarta rashin ji daga Salman tun da ya tafi, komai take yi wayarta na hannunta cikin tsammanin k
iran shi ko ganin text
ɗ
insa amma shiru. Ta kar
ɓ
i sabuwar Numbernsa ta ƙasar Chinan a gurin Abbi, amma idan ta kira ba ta shiga, ta duba kuma numbern ba a WhatsApp da ita. Abun da yake rage mata damuwa Adnan, saboda wata irin kulawa da ƙauna gami da tattal
i na musamman yake nuna mata. Damuwar rashin Salman a kusa da ita ya sa duk ta rame.
Meenal ce tsaye a gaban mudubi tana shiryawa, sanye take cikin wasu matsatstsun kaya riga da wando, wanda suka bayyana surar jikinta. Wani yalolon mayafi net
ɗ
an ƙa
rami ta saka akanta, rabin gashinta daga gaba duk a waje, mayafin kuma iya ƙasan wuyanta ya tsaya.
Cikin takunta na ƙasaita da ji da kai ta fice ta sauka ƙasa. Hajiya Saudat na zaune ita da wata k'anwar BULAMA da ta kawo mata ziyara suna hira, takun sa
ukowar Meenal daga kan step ya sa su
ɗ
aga ido suna kallon ta. Tun kafin ta ƙaraso ƙamshinta ya gama cika parlour'n. Baki bu
ɗ
e Aunty Murja take kallon ta cikin
ɗ
aurewar kai. Hajiya Saudat kuwa murmurshi ta saki ta ce. "Wow, Daughter irin wannan kyau haka? Y
ou look so beautiful!" Murmurshi Meenal ta yi cikin jin da
ɗ
i tare da juya ido ta ce. "Thank you Mom." Sannan ta dubi Aunty Murja daga tsayen da take ta ce. "Ina Yini Aunty?" Numfashi Aunty Murja ta sauke ta ce. "Lafiya ƙalau Meenal." Duban Hajiya Saudat ta
yi ta ce. "Bye Mommy sai na dawo, Abdul na jira na tun
ɗ
azu."
"To a dawo lafiya, Allah ya kiyaye ya tsare."
Bayan Meenal ta fita cike da al'ajabi Aunty Murja ta ce. "Aunty Saudat! Yanzu da wannan shigar kamar ta ƴaƴan turai kika bar Meenal ta fita
?"
Ɓ
ata fuska Hajiya Saudat ta yi ta ce. "Ban gane ba? Me ne laifin shigar jikin Meenal?"
"Haba Aunty Murja, ƴar taki guda
ɗ
aya tal a duniya kikewa irin wannan tarbiyyar? Gaskiya wannan al'amarin naki da sake, kamar ba ki ga yanayin shigar tata ba n
e? Kuma idan na ji da kyau kamar wani ta ce yana jiran ta."
"To sai me? Kawai sai in hana yarinya sakewa ta yi abun da take so? Mene a ciki dan sun fita da saurayi? Kuma ba wani gurin za ta je ba birthdayn ƙawarta zai raka ta."
"Ta
ɓ
di can! To ko m
a ina zai raka ta ai bai dace ba, yaran yanzu ka yi iya yinka ma ya aka ƙare balle ka yi musu irin wannan riƙon sakainar kashin."
Ha
ɗ
e rai Hajiya Saudat ta yi ta ce. "Me kike nufi Murja? Wacce irin magana ce wannan? Ni fa ba na son irin wannan sa ido
n, haba daga yarinya ta fita sai ki fara wani zancen mara tushe?"
"Zancen nawa ne mara tushe Aunty Saudat? Shikenan Allah ya kyauta ya kare."
Tunda ta fito ya ƙura mata ido ta cikin glass
ɗ
in Motarsa, lips
ɗ
insa na ƙasa ya lasa cikin duniyanci.
"Oh My God! Irin wannan kyau haka Baby na?" Abdul ya fa
ɗ
a lokacin da Meenal ta bu
ɗ
e Motar ta shiga.
Murmurshi ta yi tare da yin fari da ido ba ta ce komai ba. Hugging
ɗ
inta ya yi suka fara shashancinsu. Bayan wasu mintuna ya kunna Motar suka tafi.
Wani
ɗ
an ƙaramin gida mai kyau suka je, babu kowa