Showing 258001 words to 260401 words out of 260401 words

Chapter 87 - Dare da Duhu complete

kansa a ƙasa alamar martabawa ya ce.

"Allahamdulillah!. Allah kuma

ya mai da na aike" murmushi kawai tayi tana kallon Aishatul-humaira wacce ta ƙara wayo sosai ga wani kyau da Allah ya zuba mata, ta luff a jikin mahaifinta sai barci take.

"Mamana an zama ƴan mata, ta fara tafiya ne?" Abra ta ce "Tab ƴar aiki muka samu

Mami, wallahi komai ta samu fasa shi take, haka ta fasa wayar Abou-Aisha ta lalace ga surutu"

"Ah masha Allah, Allah ya raya mana ita" Salima ta fito tana musu Sannu da zuwa.

Bayan sun gaisheta, Mami taiwa Abra farin ciki ku

ɓ

utar Dr Bulama sosai tare d

a ƙara jajanta lamarin.

Daga nan

ɓ

angaren su Salman suka nufa, dake bayan tafiyar Salman

ɗ

in an sake gina sabon

ɓ

angaren a gidan Abbi, kuma babu kowa ciki shi ne Salman da Afra na dawowa suka sauka a nan. Mami tabi bayansu da kallo gwanin sha'awa kana ta

shiga kallon tilin kayan arziƙin da Adnan

ɗ

in ya kawo musu.

A zaune suka samu Salman rungome da Afra sai kuka take taƙi haƙura tana ganin kamar gangancinta ya sanya ta rasa abin cikinta.

"Kai baka jin kunyarmu ko"?

"Ni kam Yaya zanji kunya ko kai? Ku

rufe idanunku idan ba zaku iya ba" Adnan ya kwantar da Aishatul-humaira a cinyarsa yana

ɗ

an jijjigata sai gani ya yi ta fara

ɗ

aga kai da ƙafa kamar wacce akewa wasa.

"Babu abin da zamu gani wanda bamu san dashi ba, mun shige darasinku" Adnan ya fa

ɗ

a yana

zaunar da Little wacce take ƙoƙarin sakkowa zuwa wajan Salman domin tuni ta gane shi.

Abra ta koma kusa da ƴar uwarta tana dungure kan Salman.

Hira suka yi sosai kafin Abra ta janye Afra zuwa bedroom ta fara bata darasi mai zafin gaske.

"Little Kinga

mun rasa mijinki ko? Don't worry soon za a samaki wani" ya zauna yana mata wasa ina ita hankalinta na kan wayar shi.

"Yaushe kuka dawo daga ƙasar wajan ne?" Salman ya ce "Cikin satin nan, muna tunanin ma hawa jirgi ya kawo

ɓ

arin Allah dai ya barwa kan shi

sani"

"Ayyah Allah ya kawo ni soon" hira suka

ɗ

an ta

ɓ

a duk da Adnan hankalinsa yana kan Abra baya son tai nesa da shi baki

ɗ

aya.

Bayan sun yi sallah Mami ta aiko da lafiyayyan lunch mai tsari kala-kala.

Fitowa tayi daga kitchen zata shige bedroom

ɗ

i

n Afra ya yi saurin jawota jikinsa yana kissing wuyanta.

Ta marairaice fuska tana kallon shi, ya manna lips

ɗ

in shi akan nata tare da yin kissing ka

ɗ

an ya ce "kin barni kamar maraya, Allah zan fa

ɗ

awa Hajiya Mama"

Ta shafi gemun shi tare da wuyan shi ta c

e "Please mana, yau

ɗ

aya ka barni muci abinci da Afra kaji" ya langwa

ɓ

e tare da riƙe ƙugunta da kyau yana mannawa da nashi murya bata fita sosai ya ce.

"Ki gama yanzu,ina son mu gaisa da ƙanin Little" ta rungome shi sosai shi kuma ya fara ƙoƙarin kissing

bakinta..

Ƙ

afar shi yaji an riƙe ana miƙewa tsaye tare da bubbuga ƙofar.

"Oh my God, jeki madam tunda little tazo ba za ai abin arziƙi ba, yarinyar nan kinawa babanki baƙin ciki yasin" ya fa

ɗ

a yana miƙa hannu tare da

ɗ

aukan ta, shi bai ma san yaya akai t

a zo wajan ba.

Dry sosai Abra tayi tana shafa kan Little.

Da daddare Salman ya yi musu jagora zuwa gidan Ammi sosai taji da

ɗ

i, kamar ta ƙwace Little amma taƙi ta maƙale a jikin Salman sai ka rantse shi ne ya haifeta shi kam dry kawai yake, daga nan suk

a je gidan Uncle Shurem sun da

ɗ

e sosai, ko wanne gida sai Adnan ya ajjiye abin arziƙi.

Ganin Salman ya

ɗ

auki hanya daban ya sanya Abra fa

ɗ

in "Faris ina zamu?" Ya ce "Gidansu Mami angel"

Jin Salman ya ce angel ya sanya Adnan ta

ɓ

e baki, yaci ace ya saba am

ma a kullum Salman ya fa

ɗ

i haka sai yaji kishin Abra, yana dannewa ne kawai sbd yasan kawo yanzu babu komai a zuciyar Salman

ɗ

in.

Salman kuma ba zai ta

ɓ

a iya cewa Abra kai tsaye ba, bakinsa ya saba da angel babban dalili kuma Abra is his first love, yana

ganin girma ƙimar sunanta ainun, ba zai ta

ɓ

a iya manta abubuwa da suka faru ba, da yawan lokaci yana tuna first kiss

ɗ

in shi da ƴar mace kuma Abra ce sai ya yi saurin yin Asstagafirullah. Shi ya sa a kullum ba a son namiji ya

ɗ

inga zaƙewa yana aikata abu g

a mace, sbd rashin samun tabbaci kasancewar ta mata wajanka, idan bata zana matarka ba a kullum ka ganta sai abin ya fa

ɗ

o maka.

Bayan sun gaisa Anuty Suwaiba ta ce

"Abra nayi miki abubuwa da yawa, don Allah ki yafe mini ina cikin jarrabar rayuwa, tun

bayan aure na da rabuwar da mukai, har yanzu wani namiji bai ta

ɓ

a cewa yana so na, don Allah ki haƙuri ki yafe ko zan samu sassauci da rahamar Ubangiji"

Abra ta ce "na yafe miki har abada" haka Uncle Faisal, wanda ya auri mace bai san halinta ba, sai gash

i ashe maza take bi har sukai auren bata dai na ba.

Shima ta ce ta yafe masa babu komai, haka babar Mami. Daga nan shopping mall Salman ya shige ya dinga jidarwa Aishatul-humaira kaya kamar hauka, Adnan zai magana Abra ta ce ya rabu dashi ai yana da ku

ɗ

in

kuma shima babanta ne, bisa dole Adnan ya yi shiru.

A

ɓ

angaren Salman aka bawa Adnan da Abra wajan kwana Mami kuma ta

ɗ

auke Little. Cikin dare Adnan ya

ɗ

auke Abra zuwa bedroom

ɗ

insa, a ranar bata samu barci ba sai da sukai sallar asuba, sosai Adnan ya

tara mata gajiya ga yanayin cikin dake jikinta wanda kawo yanzu ta san da zaman shi.

Washegari motocin Major Khamal Khamis suka sauka a gidan,yana shigowa yaci karo da Little da sauri ya

ɗ

auke ta yana fa

ɗ

in "Matar zuwan yaushe" ta dinga tsalle a jikinsa,

Mami ta rungume shi ta baya tana cewa "Wlcm Man" ya jawota gaba yana riƙe hannunta.

Sosai Abbi yai farin ciki ya ƙara sakawa ko wanne albarka, a nan yake cewa ya kusa ritaya daga aiki ya dawo gida baki

ɗ

aya hakan ya yi wa su Mami da

ɗ

i.

Adnan ya kwashi i

yalan shi zuwa gidan abokinsa Fayyad sun jima suna hira..

Washegari gari jirgi ya

ɗ

aga dasu zuwa Kaduna.

Rayuwa kenan, komai ya yi farko yana da ƙarshe a hankali Ubangiji yake tafiyar da komai cikin iko da buwayar shi, sauyi da ci-gaba yana ta zuwarwa

Adnan da matsayinsa ya juye daga kan S.p ya dawo Inspector General of Police. Zaman gida ya yi masa wahala sosai. Da nacin su Abra da kuma addu'a ha

ɗ

i da magiyar da Dr Bulama yake Ummi ta amince suka mai da hankalinsu, amma ta kwashe komai nata, Adnan ya b

u

ɗ

e sabon asibiti babba ya mallakawa Dr Bulama.

Da gudu manyan motoci ke shigowa cikin Bulama's twins privet hospital. Jijiya na tashi kota ina, wasu manyan jami'an tsaron suka bu

ɗ

ewa Adnan ƙofa ya sako da ƙafarsa zuwa ƙasa cikin sauri kuma ya fito sany

e da blue

ɗ

in uniform wanda suka amshi jikinsa. _Ag ISP Adnan Aliyu Matawalle Inspector General of Police_.

Ya juyawa da sauri zuwa cikin hospital

ɗ

in yana

ɗ

agawa sauran hannu alamar su tsaya, kai tsaye emergency ya nufa, yana zuwa ya samu Hajiya Mama tsa

ye da Ummi wacce bata jima da zuwa ƙasar ba, Abdullah na zaune shi da matar shi Soumayyerh a gigice Adnan ya ce.

"Mama where's my wife? Tana ina?" Da hannu ta nuna masa labour ya nufi shiga Mama ta hana shi bai tsaya ba yai shigarwar shi ciki, yana shiga

idanunsa ya sauka akan Abra wacce take cikin halin ciwon naƙuda su duka sun tsorata domin cikin kusan watan shi goma sha

ɗ

aya, da sauri ya rungume ta yana shafa kanta.

"Sorry Beb, sorry sweetheart sorry" shi ne kawai abin da yake fa

ɗ

a, kuka sosai ta saka

tana riƙe Adnan zufa na yanko mata, iya wahala tasha Adnan ya yi zaman dirshan a gadon lokacin da Abra ta fasa ihu daidai lokacin data haihuwa shima ya saki kuka yana riƙeta sosai a jikinsa ganin ko motsi ta kasa, tausayinta ya kama shi sosai.

Likitoci su

ka zare babyn wane yake ƙato dashi tubarkallah, aka shirya shi cikin wasu kayan sanyi masu laushi sbd weather garin. Itama Abra aka gyara ta tare da mayar da ita

ɗ

akin hutawa. Adnan ya rungome Abra da baby boy

ɗ

in, jaririn uban shi ya yo baƙi ne sosai sai

jajayen la

ɓɓ

a da yake dasu sai motsi yake yana kai hannu baki, a hankali Adnan ya lumshe idanun tare da fa

ɗ

in.

"Allah ya raya mana Abdullah bin Adnan Aliyu Matawalle" Abra tai farin ciki sosai soyayyar Abdullah ta wanzu a zuciyarta musamman ganin kamar sh

i da Adnan.

Akai taron suna lafiya kayan da Abra ta samu

ɓ

ata baki ne, rasa inda zata saka kanta tayi kukan farin ciki tayi babu adadi.

_3yrs ltr_

Abubuwa da yawa sun faru, Salman ya gama karatu lafiya lokacin yana da yarinya

ɗ

aya mai suna Roumaisah k

yakkyawa da ita, wacce kai tsaye yayi alƙawarin bawa Abdullah aurenta ko bayan babu ran shi. Burin Salman ya cika domin a rayuwa babu abin da ke birge shi kamar siyasa kamar wasa ya fara neman takara, kasancewar mahaifinsa yana da manyan mutane Adnan ma ya

tsaya masa, sai ganshi yau Salman shi ne ke mulkar jama'a matsayin gwamnan garin. Gov Salman Khamal Khamis as governor of kano State.

Bulama hankali ya kwanta komai ya dawo daidai, baya ta

ɓ

a

ɗ

aukan wanda bai dace ba acikin asibitin sa. Salima ta haifaw

a Abbi kyakkyawar yarinya kai tsaye ya sanya mata suna Na'ima, Mami tai farin ciki soyayyar yarinyar ta shiga ranta sosai. Saudat na gidan yari har yanzu laifukan ta manya ne sosai, tunda har da laifin kisan P.a

ɗ

in Ummi ne a kanta...

Kaduna airport.

A

hankali suke tafiya hannu sarƙe cikin na juna, Adnan na riƙe da Aishatul-humaira wacce ta girma sosai kusan shekaru hu

ɗ

u kenan, Abra kuma na

ɗ

auke da Abdullah wanda yake kama da Adnan sak gashi da kuzarin shi sosai.

Ciki so da ƙaunar juna suke hawa kan s

teps

ɗ

in jirgin wanda suka samu zama can cikin vip, Adnan ya faki Idanun Aishatul-humaira ya mannawa Abra kiss ya ce. "I love You, babu abinda zan cewa Ubangiji sai godiya" ta

ɗ

ora kanta a wuyan shi tana sakin murmushi ta ce.

"Kai ne garkuwata duk abin da

na zama a rayuwa kai ne sila, burikanmu suna cika bisa saka hannun mazajanmu ko albarkarsu, kulawarka ka

ɗ

ai ta isa ta zama bar gwatance, ina cewa nayiwa sauran mata zarrah, ina son ka mijina Loving you has been a beautiful dream I never want to wake from.

You are a rare, beautiful soul. I love you so much"

Ya matseta a jikinsa farin ciki na ratsa zuciyarsa daidai kunnanta ya ce "My heart beats for you. Your love is a soft breeze, bending me gently, refreshing my soul. Allah ya yi miki Albarka, ya baki d

ukkan abin da kike so duniya da lahira nikam tuntuni na

ɗ

aga miki ƙafar shiga aljanna"

Murmushi tayi tana jan gemunsa ta ce "Ina son ka, Ubangiji yaci gaba da kare mini kai ya baka arziƙi na halak ya baka ikon sauke hakƙin iyalanka da al'ummar da suke kan

ka"

Ya saƙalo kanta yana kallon cikin idanunta ya ce. "I need your warm kiss once again" gaba

ɗ

aya sun manta da batun Aishatul-humaira yarinya mai shegen wayo da kaifin tunani, wani irin Fitinan nan kisses Abra kewa Adnan, ganin zata gigita masa lissafi

ya zame bakinsa yana kallon idanunta ya ce. "Uhm love"

Ta

ɗ

aga masa gira tana fa

ɗ

in. "I am the luckiest of all humans. When you look into my eyes, I see pure, beautiful love. My heart overflows with joy. I’m so blessed to be loved by you, handsome"

"In

a son ki matata" kafin su magana Aishatul-humaira ta shige tsakiyar su tana fa

ɗ

in "Ina son ku Ammi, Abbi." Adnan ya ha

ɗ

a da Abra da Aishatul-humaira da Abdullah ya rungome a jikinsa baki

ɗ

aya ya ce.

“Allahamdulillah”

*ALLAHAMDULILLAH* muma Bright pens

muka ce baki

ɗ

aya, anan muka sauke wannan littafin na *DARE DA DUHU* Abin da mukai kuskure Allah ya yafe mana, wanda mukai daidai Allah ya bamu ladan shi, Ubangiji ya sanya littafin ya zama hujja garemu ba hujja a kanmu ba.

_Muna godiya da masoya wanda

suka kasance damu, wasu Munyi musu kuskure wasu kuma munyi musu daidai, ko kalli labarin da idanun zuciyarku. Komai a tsari yake

👌🏾

kasance damu a sabuwar shekara har Ila yau mu na dai *Na'ima sulaiman sarauta Nimcyluv, marubuciyar Tsintacciya, Idan ba ke





🔥

* tare da *Zainab Shehu kumurya marubuciyar Komai nisan dare, da Neehal* sai *A'isha Adam marubuciyar Gaba Da gabanta, Aƙidata*_ domin magana da Bright pens kai tsaye duba nan 09047871750.

Ga samu wanda zai maye gurbin DARE DA DUHU a zuƙatanku litt

afin IDAN BA KE wanda Nimcyluv take rubutawa cikin salo na musamman. Domin jin labarin YAA SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU DA MATAYEN SHI BIYU, DA MUTUMIN DAKE SHIRIN RABA SHI DA ƳAR FILLON SHI zaku iya biyan 500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity

bank shaidar biya 08119237616.

Bright pens

Nimcyluv

Ayushercool

Zee kumurya





🔥





🔥





🔥

Thu/Dec/ 8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login