Showing 150001 words to 153000 words out of 260401 words
/>
"Idan za su biya sai a sanya masa, in kuma ba haka ba maza ku sallame su".
"Please doctor...."
"J
amila out of my office, Asibiti na ba na taimako ba ne, na neman ku
ɗ
i ne".
"Amma....
"Ohhh my God, Jamila kina daf da kai ni bango a Asibitin nan, get out".
Jamila ta fita jiki a sanyaye, Musa na ganin ta ya ce "'yar uwa zo kiga abin da yake yi, d
an Allah ki kira mana likitan ya duba shi" Musa ya yi Maganar kamar zai fashe da kuka.
Jiki a sanyaye Jamila ta ƙarasa, ta tarar da dattijuwar matar ta riƙe hannun dattijon da yake ta kokawa da numfashi. Wani irin tausayinsu ya sake kama ta.
Duk da w
annan hali da dattijon ke ciki, nuna musu wani guri yake yana fa
ɗ
in "'yar Baba"
"Me 'yar Baban tayi Malam, ka kwantar da hankalinka, in Allah ya yarda lafiya za mu koma gida, ka ga 'yar Baba".
Jamila ta ce "Ku yi haƙuri, yana duba wani mara lafiyan n
e, idan ya gama zai zo".
"Ba wani likitan da zai zo kansa ne?" Dattijiwar tayi maganar tana share hawaye.
"Shika
ɗ
ai ne likitan zuciya, bari in koma in gani ko ya gama".
Jamila ba ta karaya ba, ta koma gurin Bulama, amma ya balbaleta da masifa, ya
ce "Ba zan je kansa ba, ko naje ba zan hana shi mutuwa ba, dan haka ki je ki yi abin da na ce ki sallame su, su je su kai shi wani wurin".
"Doctor ba zan iya fa
ɗ
a musu haka ba, dan Allah ko ganin ka ne ka je su yi a kan mara lafiyan su, sai ka gaya musu
da bakinka".
"Fitar mini daga office, wace irin masifa ce haka, shi kansa doctor Shamsu zan ja masa kunne, Asibitina ba na taimako bane, ya daina turo mini Mutanen da ya san they can not afford our services".
Jamila ta kuma komawa, Musa ya tare ta y
ana fa
ɗ
in "Dan Allah ni ki nuna mini likitan in roƙe shi, kar mu rasa shi, yana da wata 'ya da idan muka rasa shi bamu san halin da zata shiga ba".
"Ɗan uwa kayi haƙuri, likita ba zai iya cire masa ciwon ba, sai dai ya taimaka masa, mu je in ga idan da
Allurar da zan iya yi masa ko bacci ya samu".
"Suna shiga ta tarar Wannan dattijo ya kai gargara, sai numfarfashi yake yana kiran " 'Yar Baba, ki zo....ki zo. ...kusa da ni, abi....abin da.....zan fa
ɗ
a mu.......muku.... 'yar Baba".
Jamila ta ce "wa
ce wannan 'yar baban da yake ta fa
ɗ
a?"
Musa ya ce " 'yar sa ce, ku taimaka mana, Wallahi zamu iya yin rashi biyu, mu rasashi mu rasata, a duniya soyayyar da yake mata ba kowa yakewa ba".
Cikin hanzari Nurse Jamila ta fara ƙoƙarin neman allurar da za
ta yi wa dattijon, idan yaso ko me doctor zai yi ya yi. Sai dai kash tana dawowa ta tarar Dattijon ya yi kalmar shahada ya cika!!!.
A
ɗ
aki Adnan ya samu Abra ya ce "Sai ki tashi, ga babanki na riƙo can ya zo" duk tsananin jiri da zafin zazza
ɓ
in da k
e jikin Abra, ba shiri ta miƙe ta sakko zata fita.
"Ke mahaukaciya, ba fa babanki ne mahaifi ba, babanki ne na riƙo haka zaki fita da wannan rigar? Wuce ki wanke fuskar ki, ki sanya kaya".
A gaggauce ta iya dafa bango ta zura doguwar riga tayi falo d
a sauri, tana zuwa ta zube a jikin Abbi tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka.
Cikin jarumta Abbi ya ce "Haba Sweetheart, kinga yadda kika rame kuwa? Kin yi duhu haka meke damunki?".
Adnan da ya kamile a gefe ya ce "Ai Abbi tun da aka yi Au
ren nan a haka muke, ko Abincin kirki ba ta iya ci, ba bacci kullum cikin kuka, na rasa a ina ta ji wannan mummunar Maganar".
Abra har mamakin makircin Adnan take, kamar wani mace, amma dayake ba ta tashi take ba, cikin kuka ta ce "Abbi, tun da aka kawo
ni, ba ka zo ka ganni ba, Mami ba ta zo ba, su Ammi ma haka, Faris
ɗ
ina ma.... Sai ta sake rushewa da kuka".
Abbi ya shiga goge mata hawaye yana fa
ɗ
in "Am sorry daughter, kin san an na
ɗ
ani a shugabancin kwamitin binciken General Ibrahim, ko weekends ba
na iya zuwa, kina raina, Ammi ce kuma ta hana kowa zuwa, ta ce bai kamata daga kawoki a dinga yi muku sintiri ba, amma kiyi haƙuri" ya ƙarasa Maganar yana sake gyara mata zaman hearing aid
ɗ
inta.
"Abbi waye babana? Dagaske tsinto ni ka yi?"
Abbi yayi
shiru sannan ya ce "Waye ya gaya miki wannan maganar ne?".
"Abbi ka daina binciken waye ya gaya mini, dan Allah Abbi ka gaya mini gaskiya" wata irin karaya da tausayin Abra ya kama Abbi.
Abra ta fara ƙoƙarin sanya idanunta a cikin na Abbi, amma ya
ɗ
auke kasa ya ƙi kallon ta yana girgiza kai.
"Abbi kar kace mini zancen nan gaskiya ne? Abbi idan ba kaine babana ba waye?".
"Abra bani da amsar tambayar ki"
"Abbi ta tabbata tsinto ni kayi kenan?".
"A'a ba haka ba ne Abra"
"To Abbina yaya ne
? Abbi baka yi mini ƙarya tun tasowata, hasali da kai nake koyi gurin gaskiya da riƙon amana, Abbi daga bakinka ne kawai zan iya jin abin da zai fidda zuciyata daga shakku komai
ɗ
acinsa ka gaya mini zan dake".
Adnan ya ce "Kinga Abra, ki ƙyale Abbi, dag
a zuwansa ba gaisuwa baki bashi Abinci ba, amma kin cika shi da tambayoyi marasa ma'ana".
"Dalla ka rufe mini baki, kai mini shiru ba da kai nake ba, Abbi kayi Magana dan Allah". Ta yiwa Adnan Magana cikin tsawa.
Abbi ya ce "Ya na ji jikinki da zaf
i haka? bari temperature jikinki ta saki sai mu yi Magana".
"Abbi ta tabatta haka ne kenan? Zargina gaskiya ne? Abbi kar ƙwaƙwalwa ta ta juye in haukace, ka gaya mini dan Allah". Gaba
ɗ
aya Abra ta fara fita hayyacinta, ga hawaye ga gumi ga majina, ga ji
kinta na rawar sanyi saboda zazza
ɓ
i.
"Haka ne Abra haka ne, amma...." Toshe wa Abbi baki tayi, ta fara maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" tare da miƙewa tsaye ta tsaya cak, can ta yi wata irin shaƙuwa tamkar fitar rai, ta fa
ɗ
i a gurin!
Littafin ku
ɗ
i ne,biya ₦300 via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank... Idan katin waya ne zaka Turo 500 shaidar biya 08081012143 or 09047871750
[10/20, 12:46 PM] Abk: A kusan tare cikin gigita da firgici Abbi da Adnan suka fasa ƙara tare da fa
ɗ
in
"Abra!" Kafin Abbi ya Ƙarasa gareta Adnan ya rigasa gaba
ɗ
aya ya sanya hannunsa tare da
ɗ
agota zuwa jikinsa yana bubbuga ta tare da kiran sunanta.
"Angel.. Angel... Angel"
Ya fa
ɗ
a yana girgiza ta da iya ƙarfinsa ganin ko motsi ba tayi sai ya kalli Abbi
da Yake tsugune dab da su hannunsa riƙe dana Abra yana murzawa.
Cikin tashin hankali Adnan ya dubi Abra hannunsa na rawa ya kama nata hannun, jin babu alamar jijiyar hannun na harbawa ya sanya shi kara kunnensa a ƙirjinta nan ma bai ji bugawar zuciyar
ta ba, hannunsa ya mayar kan hancin ta sai a lokacin ya ji kamar huci na fita. Muryarsa na rawa sosai ya dubi Abbi ya ce.
"Help me Abbi I don't want to lose my wife. Angel, open your eyes" Adnan ya fa
ɗ
a a gigice,tare da nuna kulawarsa ga Abra wacce ke k
wance kan cinyarsa. Seeing Abbi in front of him made him pretend to be worried about Abra's illness but in his mind it was all a plan.
"Adnan tunda ta zo gidan ka tayi Irin haka?" Girgiza kai Adnan yayi still holding onto her yana shafa kanta ya ce. "No,
she didn't, Abbi. we are happy. Tunda ta samu wannan maganar komai ya lalace,she is not happy, she has stopped everything, eating, talking, she is always crying in her room. Ta rame tai baƙi ta damu kanta. Mahaifiyata har ganin laifina tayi"
Shiru Abbi
yayi shi kansa, baya cikin hayyacinsa komai nasa ya tsaya dauriya kawai yake na ganin ya nuna babu komai, amma rashin iyaye a wannan rayuwa babbar illa ne ga mutum. Musamman ga Abra wacce ta
ɗ
auki
soyayya mai tarin yawa ta
ɗ
ora akan su, ba lallai ta jure z
afin wannan ƙaddara ba, ya san tana da haƙuri da kar
ɓ
ar dukkan abin da ya zo mata da hannu bibbiyu. Amma wannan abu ne wanda kai tsaye ba zaka iya gane al'amarin sa ba, bayan tsintar ta da ya yi ita
ɗ
in halattacciyar ƴa ce kamar ko wanne yaro? Ko kuma an s
ameta ne ta gur
ɓ
atacciyar hanya? Wannan abin shi ke kaiwa da dawowa cikin tunanin Major Khamal Khamis.
"take her to the car"
Abbi ya fa
ɗ
a yana mai
ɗ
auke kansa cike da kamewa ganin yadda Adnan ko kunya babu yake ta rungome ta a jikinsa. Kamar wanda yake
jira haka ya sunkuceta zuwa mota. Abbi yabi bayan su, Adnan na baya da Abra, Abbi na gaba sai driver a haka suka nufi asibiti har lokacin babu inda yake motsi a jikinta tamkar gawa haka ta kasance kwance jikin Adnan. Shi kuma ya tsura mata shanyayyun idan
unsa yana ƙare fuskarta kallo ganin yadda tai duhu sai dugun hanci, da wuyanta da ya ƙara tsayi. Abin mamaki kuma ƙirjinta Ma sha Allah a cike yake kamar ana ƙara masa girma kullum!.
Har suka isa Asibiti Adnan yana riƙe da Abra a jikinsa,He shows his
compassion and care for her. Da sauri Nurses suka amshi Abra daga hannun Adnan wanda da ƙyar ya amince ya bada ita, sai da Abbi ya bashi haƙuri tare da rarrashin sa, sannan ya bawa Nurse's
ɗ
in ita. Kai tsaye Emergency suka shiga da ita, Oxcgyen aka sanya m
ata bayan sun kammala bincikar abin da ya ke damunta, kafin suka sanya mata drip tare da injection.
Abbi na tsaye ya goya hannunsa a bayansa, tare da ƙorawa ƙofar Room da aka kwantar da Abra ido. Tunanin yadda zata iya fuskanta rayuwar ta a nan gaba yak
e, ba zata ta
ɓ
a jurewa ba, zuciyar ta, ta raunata ainun.
Yana tsaye wani Doctor ya fito yana goge zufa, da sauri Adnan ya miƙe yana kallon likitan baki na rawa ya ce.
"Ya matata likita? she recovered from her coma,Don't say anything happened to my wif
e"
Kafa
ɗ
ar Adnan Likitan ya
ɗ
an buga idanunsa akan Abbi ganin yadda shi ka
ɗ
ai yake girgiza kai kafin ya maida ganinsa zuwa ga Adnan wanda yake da tabbacin shi ne mijin yarinyar da aka kawo,
ganin kamar yafi Abbi ru
ɗ
ewa da shiga tashin hankali kallo
ɗ
ay
a zakai masa ka fahimci hakan a kwance saman baƙar fuskarsa.
"pray for her, she will get relief from the pain that is bothering her". Ya ƙare maganar yana ƙara bubbuga kafa
ɗ
ar Adnan can kuma ya ce.
"Who is the husband of Abra Khamal Khamis?"
Abbi da
ke tsaye ganin Adnan ya kasa magana sai ya kalli Likitan tare da nuna Adnan ya ce.
"Gashi nan" Kallon Adnan Dr ya yi kafin ya
ɗ
an yi tako
ɗ
aya zuwa biyu yana fa
ɗ
in "Oh! I see."
"Follow me to my office" ya ƙara cewa yana yin gaba. Sai a lokacin Adnan
ya bu
ɗ
e baki da ƙyar ya ce "Ni? Ko Abbi?"
Likitan ya tsaya yana duban Abbi kafin ya ce "Who is he to her?"
"Her father"
Cewar Adnan yana kallon ƙofar Room da Abran ke ciki, a zuciyarsa yana tunanin wani abu nada ban.
"Oops. Both of you follow me"
yana fa
ɗ
in hakan ya shige Office nasa, Adnan ne ya fara yin gaba dai Abbi yabi bayan sa jiki a sanyaye, tare da tsoran abin da likitan zai fa
ɗ
a masa wanda yake damun Abra a wannan karon duk da ya san larurar Abran amma yanzu tunaninsa ya sa
ɓ
a zatonsa.
A zaune ya samu Adnan a gaban Likitan shi ma ya ja Kujera ya zauna. Shiru sukai tare da zaman jiran jin ta bakin Likitan.
Gyara zama Dr ya yi yana duban su, kafin ya zame farin Photochromic glasses
ɗ
in idanunsa. Cikin nutsuwa ya du bi Adnan ya ce.
"Bef
ore even bringing her to the hospital, what happened to her at home?"
Ganin yadda Adnan ya rikice kamar ma baya cikin hankalinsa ya sa Abbi fa
ɗ
awa Dr cewa fa
ɗ
uwa tayi.
"Haka kawai ta fa
ɗ
i, or something was said to her that upset her. or something bad
she heard or saw?"
"It's almost like that Doctor" Abbi ya fa
ɗ
a a taƙaice, domin baya son maganar tai tsayi har ya kai ga an maimaita zancan da kunnuwansa a yanzu basa buƙatar sake jinsa. Yana son Abra ta kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali.
Dr bai damu da sanin abin da ya sanya Abra cikin halin suma ba, ya gyara zama in a serious tone ya ce.
"She is having breathing problems, wanda duk sanda ta samu rikicewa ko wani abu ya sameta wanda zuciyarta ta kasa
ɗ
auka zata iya suma a ko wanne hali
take ciki. This is the reason why her lungs started having problems. Munyi ƙoƙarin Seeing that she regained consciousness, Allhamdulillah yanzu bacci take amma sai an dinga ki ya ye wa, domin wannan Matsalar babba ce banda Ubangiji ya taƙaita".
"Thank y
ou Doctor"
"It's my responsibility. Allah ya bata lafiya" cewar Dr yana kallon Abbi da ya yi maganar.
"Doctor I can see her now" "why not?" Adnan ya jinjina kai yana Miƙewa tsaye tare da fa
ɗ
in.
"Thank you"
Kai tsaye Room da aka kwantar da ita ya
nufa, a hankali ya mur
ɗ
a handle
ɗ
in without making any sounds wanda zai iya damunta, duk tunaninsa Abbi na biye da shi. Tsaye yayi yana ƙare mata kallo tare da bin Oxcgyen
ɗ
in dake maƙale da ita wacce take taimaka mata wajan yin numfashi.
Ta
ɓ
e bakinsa y
a yi, irin ko a ƙafarsa
ɗ
in nan, kafin ya Ƙarasa gefenta ya zauna yana kallon yadda take sauke numfashi gaba
ɗ
aya ta fa
ɗ
a ta zama wata kala tamkar ba Abra Khamal Khamis. Sai ka
ɗ
auka ta shekara tana
jinya, lallai anyi gaskiya da akace damuwa itace hanya ta
farko wajan latata mutum.
There is no compassion or compassion in Adnan's heart. Wutar
ɗ
aukan fansa ce kawai ke ƙara ruruwa a cikin zuciyarsa, tare da tunanin duk wata hanya da zaibi ya datse ƙaddarar da zata sada Abra da Real father
ɗ
inta. Baya so bay
a kuma ƙaunar ganin haka, Imma mahaifin Abra zai ganta sai dai cikin makara yayin jana'izar ta. Ko kuma ita ta gan shi yayin tasa jana'izar. Zuciyarsa ta kasa jure abin da aka aikata a garesa, da ace zai yafe da tuni ya yafe amma wannan ba ƙaddara bace za
llar son zuciya ne bama za'a ha
ɗ
asa da kuskure ba.
Ajjiyar zuciya ya sauke yana jan idanunsa tare da rufewa zuciyarsa nayi masa nauyi tamkar yanzu ne abin da akai masa yake faruwa. Baya jin koda Abra zata mutu ta dawo ƙarƙashin inuwar auren shi zai yafe
wannan laifin dole sai ya
ɗ
auki fansa. Domin da wutar
ɗ
aukan fansa ya RAYU.
China.
Mirginawa ya yi daga kwancan da ya ke. Idanunsa dake a lumshe ya bu
ɗ
e yana ƙara kallon A.c. dake
ɗ
akin, gently kuma ya juyar da kansa idanunsa ya sauka akan makeken pho
ton sanyin idaniyarsa, wanda ya kai aka bu
ɗ
a masa shi ya zama babba. Tashi ya yi daga kwanciyar da yake ya nufi inda ya ajjiye photon daidai wajan ya tsuguna tare da miƙa hannunsa ya
ɗ
auki photon, idan ba gizo idanunsa suke masa ba sai yaga photon kamar ya
sauya idanunta sai sheƙi suke tamkar zasu zub da ƙwalla.
A nutse ya shafi fuskarta idanunsa akan ƙaramin bakinta cikin muryarsa mai nutsuwa da kamala wacce girma da samartaka suka ƙara kamata ya ce.
"Yaya"
Ya fa
ɗ
a yana kallon Fuskarta sai kuma ya
ce "Akwai matsala yaya, na kasa samun nutsuwa me ya sa kike zuwa cikin baccina kina kiran sunana tare da yi min kuka? Why Angel ko akwai abin da ya ke damunki? Bai kamata ki damu ba, kina tare da wanda kike so kika za
ɓ
a matsayin abokin Rayuwar ki. Uba ga y
aranki kin samu abin da ki ke so. Nima kuma zan maki tawa rantsuwar yanzu"
Miƙewa tsaye ya yi hannunsa zube cikin Aljihu gashin ƙirjinsa ya kwantar lub sai sheƙi yake a saman farar fatarsa abin ka da farin bafulatani. Da
ɗ
an sauri-sauri yake duba cikin
wata box har ya samu sabuwar reza jikinsa na rawa ya
ɗ
auki reza
ɗ
in tare da tsayawa akan photon Abra ya ce.
"I, Salman Khamal Khamis, promise you if I don't find you as my wife... Ni ba
ɗ
an halak bane Abra" yana fa
ɗ
in hakan ya tsaga tafin hannunsa da re
zar nan ta ke jini ya fara zuba, Murmushi ya yi yana zubawa photonta ido ganin jinin da ke zuba a jikinsa yana sauka a photon ya ce.
"Ban damu da shekara nawa za kuyi