Showing 162001 words to 165000 words out of 260401 words

Chapter 55 - Dare da Duhu complete

ta dawo gidan sai ta cigaba i

ta ma. Har ƙaton Gen. ta siya saboda ba za ta iya rayuwa cikin sauro da zafi ba, ga shi Mama kullum cikin cewa ta yi mata kaza ta saya mata kaza take. Gaba

ɗ

aya ta rame ta yi baƙi saboda damuwa da rashin kwanciyar hankali.

Ammi tana

ɗ

akin Baffa tan

a yi masa tausa a lokacin, kiran Na'ima ya shigo wayarta. Miƙewa ta yi ta

ɗ

auko wayar, ganin Na'ima ce ya sa ta fa

ɗ

in. "Alhaji ka ga ƴar halak, yanzun nan na gama zancen su ita ƴarta, na ce kwana biyu shiru ba mu gaisa ba, duk da ita Abran Babanta ya ce wa

yarta ce ta samu matsala." Ta ƙarashe maganar tare da daga wayar ta kara a kunnenta tare da yin sallama. Daga can Mama ta amsa mata, cikin mamaki Ammi ta ce. "Au Hajiya ke ce? Ina Na'iman?"

"Tana nan ƙalau, daga yanda na ji maganarki da alama ba ku san

abin yake faruwa ba."

"Me ya faru kuma? Allah ya sa dai lafiya?" Ammi ta tambaya a ru

ɗ

e.

Sanar da Ammi sakin Na'iman ta yi. Cikin jimantawa Ammi ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un! Subhanallahi! Baban nawa ne ya aikata haka? Da k'uruciya ma ba

i yi haka ba sai yanzu da girma ya fara kama su har an kai 'ya

ɗ

akin miji? Wallahi ba mu sani ba bai sanar mana ba."

"To dai yau kwananta hu

ɗ

u a gida, abin dai ba da

ɗ

in ji."

"Ku yi haƙuri Hajiya, insha Allahu za a daidaita tunda saki

ɗ

aya ne, bari i

n kira shi yanzu."

"Tom shikenan Hajiya mun gode, sai na ji ki."

Bayan sun gama wayar Ammi ta kira layin Abbi, ta yi masa har 2 missed call amma bai

ɗ

aga ba. Baffa dake sauraren duk abin da suka tattauna ya ce. "May be yana wani uzurin ne, idan ya

gama na san zai kira, sai mu ji gaskiyar abin da yake faruwa." Ammi ta ce. "Haka ne, amma wannan abu bai da

ɗ

i ba ko ka

ɗ

an."

"Allah ya kyauta kawai." Cewar Baffa cikin jimantawa.

Kwance take a kan gado ta lullu

ɓ

e jikinta da bargo, fuskarta ce

kawai a waje ta ƙura wa wuri

ɗ

aya ido, ga dukkan alamu sana'ar tata take yi wato tunani. A haka Adnan ya shigo

ɗ

akin ya same ta ba tare da ya yi sallama ba, uniform

ɗ

insa na police guda biyu ya watsa mata a jikinta, cikin ba da umarni ya ce. "Gashi nan ki

wanke mini su yanzu-yanzu." Kallon kayan ta yi ta kalle shi ba ta ce komai ba, don ko magana ba ta son yi, saboda tarin damuwar dake cikin ranta, ga shi yau ta tashi ba ta jin da

ɗ

in jikinta, ga

ɓ

o

ɓ

in jikinta duka ciwo suke mata, ga ciwon kai da idan ana sab

o da shi ta saba da shi, ga wata irin kasala da take ji.

"I'm talking to you Madam!" Adnan ya fa

ɗ

a cikin tsawa tare yin kanta.

Cikin

ɗ

aga murya gami da kuka ta ce. "Ba zan yi ba, idan ka tashi ka kashe ni, haba! Na gaji da wannan azabtarwar taka

Adnan, ka yi mini duk abin da ka ga dama!" Ta ƙarashe maganar tare da tashi zaune ta

ɗ

auki uniform

ɗ

in nasa da niyyar ta cillar da shi, hakan ya sa ƙamshinsa dake manne a kayan bugar hancinta, da sauri ta saki kayan tare da toshe hancinta, don wani irin ha

utsinawa ta ji jikinta ya yi mata lokaci

ɗ

aya. Dama tunda ya shigo ta shaƙi ƙamshin ta ji kamar za ta yi amai. Cikin masifa ya bu

ɗ

e baki da nufin zazzage mata kwandon bala'i, miƙewar da ta yi cikin sauri kamar wadda aka tsikara ya hana shi abin da ya yi ni

yya, sakamakon ganin ta nufi toilet a guje ta fara kelaya amai kamar za ta amayar da kayan cikinta.

It's not for free, contact us for more information. 09047871750

[10/24, 12:28 PM] Abk: Ta da

ɗ

e tana aman, sannan ta fito gaba

ɗ

aya ga

ɓ

o

ɓ

inta sun saki

, saboda yunƙurin amai. Ko da yake ba sabon abu bane a gurinta, dan haka kan faru da ita lokacin period

ɗ

in ta.

Ba ta ko kalli Adnan ba, ta wuce ta fara ƙoƙarin hayewa kan gado.

  "Wai me kika mayar da ni ne? Na umarce ki ki mini abu, amma kin koma gado

me kike nufi?".

"Abin da idanunka suka gane maka, shi nake nufi" a sukwane ya yo kan gadon yana cigaba da bala'i "Ke kin isa babanki ya wulaƙantani, kema kice zaki mini rashin mutunci? Wato kin gado halin dabbanci irin na babanki".

"Adnan! Kar ka sake za

gin ubana,uba fa bai fi uba ba".

"Kina nufin nima zagina za kiyi kenan?" Yayi Maganar yana nuna kansa da yatsa.

"Allah ya tsare ni in zageka, ni mahaifinka uba na

ɗ

auke shi, uba na gari makuwa, abin tausayi Allah ya bashi azzalumin

ɗ

a mai fuska biyu".

Taku

ɗ

aya yayi, ya fizgota daga kan gadon, zai wanka mata mari, amma yaji jikinta zafi rauu, kamar an kunna wuta, hanka

ɗ

ata yayi ta fa

ɗ

a ƙasa ya nuna ta da yatsansa ya ce "Ko ki

ɗ

au ubana uba, koma me kike

ɗ

auke shi, abin da na sani shi ne, ubana yafi uba

nki imani da mutunci, kuma na dawo na tarar da kayan nan baki wanke ba, sai na tattaka ki".

Binsa ta yi da ido har ya fice.

Girgiza kai kawai tayi, dan Yanzu zuciyarta ta fara bushewa da lamarin Adnan, dan haka a nan kan tiles ta gyara kwanciyarta, ta y

i shiru abubuwa daban-daban na kai komo a kwanyarta.

Hannu ya sa cikin sumarsa ya yamutsa ta, ya rintse idanunsa, a tunaninsa zuwan da yayi ya ga Abra, zai rage masa ra

ɗ

a

ɗ

in da yake cikin zuciyarsa, da samun sassauci akan halin da yake ciki, duk d

a ya san hakan bai kyautu ba, kasancewar ita matar wani ce a yanzu, kuma ga alƙawarin da yayi, na ba zai sake zuwa Nigeria ba, amma ya kasa daurewa sai da yaje, amma zuwan nasa bai amfana masa Komai ba sai sake jefa shi cikin tarin damuwa da tambayoyi.

Ab

ra tana auren wanda take so amma ta furta masa kalmar so, yayi shiru tare da tuna yadda Adnan ya mari Abra saboda kishi, da yadda ya kira shi da loser "No! Am not a loser" ya fa

ɗ

a yana dukan kan mirror.

"Abra zata dawo gareni, amma ta yaya how? Wa zai b

ani goyon baya?"

Can kuma sai wata zuciyar ta garga

ɗ

e shi 'Ina imaninka da iliminka na Addini, duk wani abu da zakai yinƙurin aikatawa, don mallakarta alhalin tana matar wani ya sa

ɓ

awa Shari'a'

Rintse idanunsa yayi, tare da taune lips

ɗ

insa na ƙasa,

da ya tuna yanzu Yaya ta san wacece ita, ta san matsayinta. Ko wani hali ta shiga lokacin da ta sani? Amma ya a kai ma ta sani, sam wannan bahagon mijin nata, ya hana shi ya samu ya sake da ita su yi hira. A hankali ya taka zuwa baki gado ya zauna, ya sunk

uyar da kansa yana tunani.

Abbi ya rasa ta ina ya kamata ya fara binciken iyayen Abra, sai yanzu ya gane cewar yayi kuskure, tsananin son Abra da tausayin ta lokacin da ya tsince ta, ya rufe masa idanu, ya kasa tsayawa yayi bincike a kan su waye iyaye

n Abra, ba tare da tunanin akwai rana kamar irin ta yau da zata zo ba, wanda dole Abra zata buƙaci sanin haƙiƙanin suwaye iyayenta.

A hankali ya sauke ajiyar zuciya, ya fara laluben wayarsa, sai dai yana dubawa ya ga missed calls ciki har da na su Ammi.

Cikin hanzari ya shiga ƙoƙarin bin kiran Ammin. Ammi na

ɗ

agawa cikin girmamawa suka gaisa. "Babana ina ka shiga ne haka? Ake ta kiranka baka

ɗ

agawa?"

Major ya ce "Afuwan Ammi, wayarce a silent".

Ammi ta ce "Shikenan, kana gari ne?"

"A'a Ammi, ina

wurin aiki".

"To duk abin da kake da ka shigo gari ka zo?".

"Lafiya kuwa Ammi?"

"Idan ka zo ka ji"

"Shikenan dama shari'ar nan ce ta sanya na taho wurin aiki, amma tunda an kammala insha Allah zan biyo jirgin dare in taho".

"To shikenan, All

ah ya kawo ka lafiya"

Ya amsa da "Ameen"

Kamar yadda Abbi ya fa

ɗ

a, a daren ya dawo gida, washegari da wuri ya shirya ya nufi gida, Mintuna ka

ɗ

an suka kai Abbi gidansu.

Tun da ya ga Baffa a gidan a daidai wannan lokacin kuma da alama duk shi suke jir

a, ya sha jinin jikinsa.

Ya gaishesu cikin girmamawa, sannan ya

ɗ

ora da Ammi "Gani, Allah yasa lafiya naji kin ce kuna nemana?"

Baffa ya ce "Au tambaya ka ke ko lafiya? Kai ba abin kunya ne ba abin da ka aikata Kamal, da ƙuruciyarka ba ka saki matarka

ba sai yanzu, kuma ace ba wanda ka kira ka gayawa wannan maganar? Sai su daga can gidan nasu ne aka kiramu aka sanar mana, me ka aikata kenana Khama? Wane laifi zata aikata maka a yanzu, wanda ba kayi haƙuri a baya ba, da har za ta kai ku ga saki, bayan ha

r 'ya kun kai

ɗ

aki".

"Baffa dan Allah kuyi haƙuri, amma abin da Na'ima tayi mini bani da za

ɓ

in da ya wuce aikata hakan".

"Ka kyauta ai, sai ka tashi mu tafi can gidan nasu, mu zauna mu tattauna, a gano bakin zaren".

Major ya ce "Baffa, zamu iya ta

ttauna komai a nan, in gaya muku duk abin da ya faru".

"Ba shawarar ka muke nema ba, tashi koma menene muje can a tattauna" ba yadda Major ya iya, haka ya tashi suka tafi gidansu Na'ima.

Bacci ne mai nauyin gaske ya

ɗ

auke Abra, sanyin tiles

ɗ

in nan d

a ke ratsa ta ya sanya zazza

ɓ

i ya ƙara rufeta sosai da sosai.

Sai can azahar sannan ta farka daga nannauyan baccin da ya

ɗ

auketa, har wani duhu take gani, saboda wata irin yunwa da take ji, ga jikinta babu da

ɗ

i. Ta kalli gurin da kayan Adnan suke a zube

, kallon kayan kawai da tayi ta ji cikinta ya sake yamutsawa, zuciyarta ta fara tashi.

Tsaki tayi ta

ɗ

au kayan, tana toshe hanci, ga jiri na

ɗ

ibar ta ta tafi

ɗ

akinsa, tana zuwa ta shiga toilet

ɗ

insa, ta zuba kayan a bucket ta fice.

Ta nufi kitchen ta shi

ga bu

ɗ

e bu

ɗ

en kwanuka, ba abinda ta girka balle ta ci.

Bredi ta tarar a kan dining, wanda Adnan ya karya ya fita, ta zauna ta dinga ci kamar mayunwaciya, sai da ta ci ta ƙoshi sosai, ta koma fridge ta

ɗ

auko lemo mai sanyi ta sha sai da ta ji babu gurin zu

bawa komai sannan ta haƙura.

A haka ta

ɗ

ora ruwa dan tayi wanka ta

ɗ

ora girkin rana, ta

ɗ

an fara gyara gidan, duk da gidan ba wani datti yayi ba, tana yi tana kwanciya saboda gaba

ɗ

aya jikinta babu da

ɗ

i. Cikinta ne ya fara juyawa kamar

ɗ

azu da safe, nan

ta dinga kwara amai, sai da ta amayar da duk abin da ta ci, ta dawo falo ta kwanta gaba

ɗ

aya ta galabaita.

Tun tana jin aman ta tashi ta tafi ban

ɗ

aki, har ta koma toilet ta zauna gaba

ɗ

aya, kan kace kwabo, Abra ta fita hayyacinta. Da ƙyar ta iya lalla

ɓ

aw

a ta yi wanka, shima ba sabulu iya ruwa ta watsa, ta dawo tai salla a zaune, ta kwanta. Amma amai bai tsaya ba dan ba ta fasa yinsa ba.

"Kai muke saurara, kayi wa mutane bayani ya aka yi ka aikata wannan

ɗ

anyen aikin, bamu sani ba laifin me tayi mak

a?".

Major yayi ajiyar zuciya ya ce "Tun da na auri Na'ima, muka yi auren soyayya muke zane lafiya da ni da ita, har zuwa lokacin da na tsinci Abra, wanda tun daga wannan lokacin ta dinga bijiro mini da wasu irin halaye akan yarinyar, tana iƙrarin ni na

haifi yarinyar da karuwa a waje, kuma ba zata riƙe ta ba. Idan ban manta ba a wancan lokacin na yi mata wani furuci na cewa, idan har ta bari wani yasan ba ni na haifi Abra ba daga gareta a bakin Aurenta. Sai ta dinga nuna mini bakomai, a gabana ta kula d

a Abra a bayan idona ta cutar da ita, wanda na da

ɗ

e da fukantar hakan amma nayi shiru na ƙyle. Ashe matar nan ta riga ta sanar da

ɗ

anta cewar bamu muka haifi Abra ba, ina wurin aiki, na samu wayar mijin Abra ya ha

ɗ

ani da ita, yarinyar tana kuka ta sanar mi

ni da cewa wai ashe bamu muka haifeta ba? Wanda na san ba mai gayamata sai Na'ima, kuma na dawo gida na tarar da wasiƙar da Salman ya bari a kan cewar ba zai sake dawowa Nigeria ba, ashe ya san Abra ba 'yar uwassa bace, ya fara sonta kuma ta sani duk ta mu

nafunce ni, Wallahi Ammi bakiga a mawuyacin halin da na baro Abra ba, dan haka taje tayi rayuwarta nima in yi tawa, zan tabattar da samun farincikin yarana".

Na'ima ta fashe da kuka tana fa

ɗ

in "Wallahi ni ban gaya mata ba"

Ammi ta ce "Innalillahi wa

Innalillahi raji'un, yanzu kana nufin Abra ta san ba kai ka haifeta ba?".

"Ta sani Ammi, ba kiga a yadda na baro ta ba, cikin matsanancin tashin hankali da damuwa, yanzu irin tsananin soyayya da shaƙuwar da ke tsakaninta da Salman da wani abu da ba a so

ya shiga tsakaninsu fa a dalilin sanin su ba 'yan uwa bane? Duk bata kalli wannan ba amma ta sanar musu, ba yadda ban da Abra ba a kan ta gaya mini wanda ya gaya mata amma taƙi, wanda nasan dama ba zata gaya mini ba, saboda ba ta san ace ga laifin Na'ima

dan ita uwa ta

ɗ

auketa".

"Wallahi ni bani na gaya mata". Ta sake Maganar cikin raunin murya.

Baffa ya ce "Kuskure ne dai an riga an yi shi, amma kayi haƙuri ka maida yarinyar nan

ɗ

akinta, ba shawara ba ce umarni ne".

Abbi yayi jimm, yayin da ƙanin

mahaifin Na'ima shima haƙurin yake bayarwa.

Khamal ya ce "Shikenan, batun

ɗ

an ta da ta sa na tura China kuma, sai taje ta nemo shi da kanta, dan dama ita tace a kai shi can, tun da yace ba zai dawo ba shikenan, dama mugunta ai fitsarin faƙo ce".

Amm

i ta ce "A'a ai duk ba za'ai haka ba, haƙurin dai shi zaka yi" aka ha

ɗ

u akai ta bawa Abbi haƙuri, ya amince Mami ta koma

ɗ

akinta.

SP Adnan a gajiye ya dawo gida, saboda wani ƙauye suka je aiki, ya sha zirga-zirga, salla kawai yayi, ya duba fridge ya sam

u sauran juice da Abra take ha

ɗ

awa ya sha.

Bai nemi wurin da Abra take ba, ya shige

ɗ

akinsa ya fa

ɗ

a toilet dan yayi wanka, amma ya ga kayansa a cikin bokiti a ban

ɗ

aki.

Jinjina kai yayi da jinjina yadda Abra ta koyi taurin kai, wankansa yayi da niyyar ya

kammala ya ci Abinci, ya ci ƙaniyar Abra.

Sai dai bai ƙara tsinkewa da lamarin Abra ba, sai da ya duba ya ga ba tayi girki ba, ya duba kitchen ma bakomai.

  A fusace ya nufi

ɗ

akinta, yana zuwa ya tarar da ita a duƙunƙune cikin hijjabi tana ta bacci. Ƙafa

rsa ya sa yana takata ta tashi, amma ko motsi ba ta yi ba, baccinta kawai take.

Yasa hannu ya

ɗ

agota yayi wurgi da ita, zafin buguwar da ta yi ne ya sanya ta farka cikin wani irin razani. Adnan ta gani a gabanta yana wani irin zazzare idanu.

"Dame kike t

aƙama har kike mini wannan iskancin a gida? Baki girki da safe ba, na bar miki wanki ba kiyi ba, dan kin mai da ni

ɗ

an isaka, shine kika kai kayan ban

ɗ

akina kika watsar, kuma still ba ki girki ba, me kike nufi?" Ikon Allah kawai take kallo, yadda yake ta z

azzaga bala'i, babu alamar ma zai bata damar kare kanta.

Sai da yayi ya gama ba tace uffan ba, ta miƙe a hankali ta fara ƙoƙarin gyara zaman towel

ɗ

in jikinta.

"Am i not talking to you Abra?" Ya sake tambayarta cikin tsawa.

Hannayenta biyu ta sanya ta

toshe kunnuwanta, dan ji take kamar a cikin kanta yake wannan ihun. Ganin ta toshe kunne ya sanya ya kuma harzuƙa, ya sauketa mata wani wawan mari a kan hannunta da toshe kunnen, wani irin zafi ya ratsata ta shiga zubar da hawaye, amma taƙi ce masa uffan,

hannunsa ya sanya ya shaƙeta yadda ba zai mata illa ba ya ce "idan har kika cigaba da ƙoƙarin bijirewa umarnina a cikin gidan nan, Wallahi wahala zaki sha a gidan nan, sai kin gwammace ki

ɗ

a da karatu". Ai yana tsaka da maganar ta kyalayo masa amai a jikin

sa, kallon Abra yayi cikin tsananin baƙin ciki ya hanka

ɗ

eta ta fa

ɗ

i ƙasa, ta cigaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login