Showing 96001 words to 99000 words out of 260401 words
kawo
ku Abuja?"
Shiru Baby ta yi ta fara sosa kanta tana rarraba idanuwa.
"I'm toking to you my friend." Ya fa
ɗ
a cikin tsawa.
Zabura ta yi ta ce. "Mun zo ganin wani mutumi ne?" Ya ce. "Wane wanin? Daga Kadunan kuke yanzu?"
"A'a, muna zaune a schoo
l hostel ne, daga can muka zo nan."
Jinjina kai ya yi cikin nazartar ta ya ce. "Okay, cigaba da bayani, gurinwa kuka zo?"
Cikin rawar murya ta ce. "Wani tsohon Soja ne, ita ƙawar tamu da aka kashe muka rako nan Abuja, don ta gana da shi akan wani ab
u." Tattara hankalinsa gaba
ɗ
aya D.P.O ya yi a kanta ya ce. "Wanne abu ne wannan da kuka taho tun daga Kaduna har Abuja saboda kawai su yi magana a kansa?"
Baby tana hawaye ta ba shi labarin duk abun da ya faru tsakanin Ihsan da General Ibrahim, ganin b
a ta da mafita, kuma tana son ta ku
ɓ
uta daga zargin su da ake yi. D.P.O ya ce. "Kin tabbata abun da kike fa
ɗ
a mini gaskiya ne?"
"Wallahi gaskiya ne ranka ya da
ɗ
e, kuma dalilin da ya sa ma ba mu fita tare da ita ba saboda zai zo su ha
ɗ
u a lokacin." D.P.O
ya ce. "Kuna da tabbas
ɗ
in ya zo sun ha
ɗ
un bayan kun fita? Kuma menene shaidar ku akan
abun da kika fa
ɗ
a." A raunane Baby ta ce. "Eh, lokacin da ya zo ta kira mu ta sanar mana zuwansa cikin murna, dan muna tunanin ya zo ya ba ta ku
ɗ
in da muka nema ne daga
hannunsa, shaidar kuma akwai short video na tattaunawarsu ita da shi akan cikin jikinta a cikin wayoyinmu, wanda muka yi masa barazanar da shi."
Numfashi D.P.O ya sauke tare da shafa kansa ya ce. "Ya sunan shi Sojan?"
"General Ibrahim A.M"
"Wha
t? General Ibrahim A.M? Are You sure?" Ya tambaya cikin shock.
Gya
ɗ
a masa kai ta yi cikin tabbatarwa.
Girgiza kai ya yi ya ce "Oh My God!"
Duban jami'in da ya kai Janna cell ya yi ya ce. "Officer."
"Yes sir." Ya fa
ɗ
a tare da ƙamewa.
"Ka shig
ar da wannan ciki ka fito
ɗ
ayar."
A ru
ɗ
e Baby ya ce. "Yalla
ɓ
ai dan Allah ka sallame ni tunda na fa
ɗ
a maka gaskiyar abin da ya faru, wallahi ba mu muka kashe ta ba, ba mu.."
"Shut up, tashi mu je." Officer ya buga mata tsawa da fa
ɗ
in haka. Kuka ta fas
he da shi tare da miƙewa ta yi gaba.
Exactly abun da Baby ta fa
ɗ
a shi Janna ta fa
ɗ
awa D.O.P, bayan ta gama yi masa jawabin ya bayar da umarni aka kawo masa wayoyinsu da aka kar
ɓ
a, ya cewa Janna ta
ɗ
auki tata ta cire key ta nuna masa videon tattaunawar I
hsan da General Ibrahim. Da wannan damar Janna ta yi amfani ta
ɗ
ora videon a social media in seconds, sannan ta miƙawa D.P.O wayar.
Bayan ya gama kalla ya dubi wani police dake tsaye a gabansa ya ce. "Inspector, a cigaba da tsare yaran nan har zuwa loka
cin da za mu gama bincike, sannan a je a taho da General Ibrahim A.M, yarinyar da aka kashe kuma a san yanda za a yi iyayenta su samu labari, and lastly aje a zo mini da Manager na hotel
ɗ
in da abun da ya faru a ciki yanzu, a kuma bincika CC TV camera domi
n a tabbatar da General Ibrahim ya je hotel
ɗ
in a yau ko akasin haka."
"Done Sir." Inspector ya fa
ɗ
a tare da sara masa.
Bayan ya fita D.O.P ya dubi Janna dake ta kuka ta ce. "Wannan ya isa ya zama izna a gare ku da masu hali irin naku, yara ƙanana d
a ku iyayenku sun tura ku karatu amma kuna irin wannan rayuwar, yanzu wa gari ya waya? A misali idan General
ɗ
in ne ya kashe ta hakan ya isa ku gane ba ku da wata daraja da ƙima a idanun irin wa
ɗ
annan Mazan da kuke bi, ba su
ɗ
auke ku a bakin komai ba, sun
mayar da ku kamar ledar pure water saboda yawan da kuka yi a gari. Ya kashe ta ne saboda ya tsira da mutuncinsa kar abun da yake aikatawa ya fito fili, kuma a lokacin da ya kashe tan yana fita idan ya ha
ɗ
u da wata
ɗ
aukarta zai yi ya je ya sheƙa ayarsa da i
ta hankali kwance, ita kuma wannan ya gama da ita, da ita da Dabba duk matsayinsu
ɗ
aya a gurinsa. Ina baki misali ne kawai ba wai ina fa
ɗ
a dan ya aikata ba, dafatan kin fahimta?"
Janna da kanta ke ƙasa tana hawaye ta gya
ɗ
a masa kai. Girgiza kai ya yi ci
kin takaici ya ce. "Allah ya shirya." Sannan ya bayar da umarnin a mayar da ita ciki.
General Ibrahim A.M ne zaune a gaban kujerar gaban table
ɗ
in D.O.P, cikin shiga ta kamala, ba zaka ta
ɓ
a cewa shi yake aikata ba
ɗ
ala da Ƴaƴan cikinsa a bayan fage b
a. Bayan sun gaisa cikin ƙwarewar aiki D.P.O ya ce. "General, muna son za mu yi maka wasu ƴan tambayoyi ne a kan kisan wata yarinya da aka yi mai suna Ihsan Sadam Malali a Aminci Hotel."
Damm zuciyar General Ibrahim ta buga, amma da yake cikakken
ɗ
an
duniya ne kuma ya san ta kan harkar bincike sai ya ce. "D.P.O ni kuma? Wacce yarinya ce wannan? Me ya sa kuka gayyato ni akan kisan ta? Ba na jin ko a cikin familynmu akwai mai sunan da ka ambata balle na yi tunanin ko ina da wata dangantaka ta jini da ita
, Ihsan ka ce ko wa?" Cikin nazartar shi D.P.O ya ce. "Bari ka ga hotonta, na san idan ka gani may be ka shaida ta." Bai jira cewar shi ba ya
ɗ
auki wayarsa ya latsa sannan ya nuna wa General Ibrahim pics
ɗ
in fuskar Ihsan da ya cika screen
ɗ
in wayar. Ƙar
ɓ
a
ya yi ya duba, cikin
ɓ
oye razanin da zuciyarsa take ciki ya ce. "Gaskiya ban san wannan yarinyar ba D.P.O."
"Ko?" D.P.O ya fa
ɗ
a tare da kar
ɓ
ar wayarsa.
"Ina jin mistake kuka yi ba ni za ku kira ba."
"Kai kuwa za mu kira, saboda bincikenmu ya tabba
tar mana da a guest house
ɗ
inka yarinyar ta sauka ita ƙawayenta shekaran jiya."
Cikin maziya General Ibrahim ya ce. "Eh hakan zai iya yiyuwa, saboda akwai abokaina da dama da suke saukar baƙinsu a gidan ba tare da na sani ba, because mun zama
ɗ
aya na ya
rje musu hakan. Cikin gya
ɗ
a kai D.P.O ya ce. "General please kar ka wahalar da mu ka wahalar da kanka, ka amsa kawai ka san yarinyar nan, in yi maka tambayoyin da zan yi maka, that is all."
"A'a fa, ban san ta ba zan amsa na san ta ne? Da kuka kira ni
in zo akan abun da ban sani ba na yi muku musu? Na taso na zo duk da ina gaba da ku a matsayi da miƙami, amma saboda ina girmama kaki da mahukunta ya sa na zo cikin salama ba tare da jayayya ba." General ya fa
ɗ
a cikin harzuƙa.
"Akan aikina nake General,
kuma sanin kanka ne babu ruwan doka da wani muƙami ko matsayi, idan abu ya biyo ta kan mutum ko waye shi dole a tuhume shi, but ba wannan ne a gabanmu ba yanzu, let me show you something." D.P.O ya fa
ɗ
i haka tare da ƙara
ɗ
aukar wayarsa a karo na biyu.
A
ɗ
arare ta shiga gida zuciyarta cike da tsoron Na'ima, kasancewar Major ba ya gari. Allah ya taimake ta Na'ima ba ta main Parlor tana
ɗ
akinta, ajiyar zuciya ta sauke ta shige
ɗ
akinta. A bakin gado ta zauna tare da ƙurawa wayarta ido, sai dai a zah
iri ba wayar take kallo ba, tunanin wanda ya ba ta wayar da kasancewar da suka yi tare na wasu mintuna take tunawa. Har yanzu zuciyarta ba ta daina bugawa ba, ta tsorata sosai da farko, dan wannan ne karo na farko da ta ta
ɓ
a da
ɗ
ewa tare da wani Namiji baya
n relatives
ɗ
inta. Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tare da kai wayarta kan hancinta ta shaƙi ƙamshinsa, tun a jikin i.d card
ɗ
inta ta ji tana son ƙamshin, sometimes idan za ta kwanta bacci sai ta
ɗ
auko ta shinshina. Mr unknown ne ya fa
ɗ
o mata a rai, da sa
uri ta latsa wayar ta cire password tare da cire ta daga Flight mode
ɗ
in take, kamar jira ake messages suka dinga shigowa. Hannunta har rawa yake wajen dannawa ta bu
ɗ
e ta karanta. Messages
ɗ
insa ya kai 15 ta gani, duk na yanda yake tsananin son ta ne da mi
ssing
ɗ
inta da ya yi, a ƙarshe kuma sai ya roƙe ta akan ta taimaka ta yi masa reply koda da "Okay" ne, dan ya ji da
ɗ
i a cikin ransa. Murmushi ta yi ta tura masa da.
"Hey, How are you."
Message
ɗ
in yana tafiya kira ya shigo cikin wayar da sabuwar N
umber, kallon special Numbern ta tsaya tana yi, sai da ta kusa katsewa sannan ta yi pick.
"Assalamu alaikum." Wata murya mai cike kamala da da
ɗ
in sauti ta doki kunnenta.
Sai da gabanta ya fa
ɗ
i jin muryar wanda ba ta za ta ba, lumshe ido ta yi a hanka
li tare da gyara zama ta amsa masa cikin sassanyar muryarta.
"Na kasa cigaba da driving a dalilin kyakkyawar fuskar matata dake ta mun gizo gami da tunaninta da ya addabi zuciyata, shi ya sa na kira ki don na samu nutsuwa, i hope kin shiga gida lafiya
?" Ya yi maganar cikin wani irin salo da ya ratsa zuciya gami da ko'ina a jikinta. Shiru ta yi ta rasa me za ta ce, jin al'amarin take wani mai girma a kanta.
"Ba na son ina magana ana ji na a yi shiru" Ya fa
ɗ
i haka a
ɗ
an kausashe kamar ba shi ya gama m
agana cikin kulawa yanzu ba.
Turo baki ta yi kamar yana gabanta ta ce. "I'm sorry, ban san me zan ce ba ne." Murmushi ya yi mai sauti ya ce. "Just say I love you My husband." Waro ido ta yi ba ta ce komai ba. Ya ce. "I'm waiting for you Madam." Nan ma s
hiru ta yi sai sauke numfashi kawai take yi. Murmushi ya ƙara yi ya ce. "Okay bye, thank you, take care of yourself." Bai jira amsar ta ba ya kashe wayar.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da zare wayar daga kunnenta. sai ta tsinci zuciyarta da blaming ka
nta, kamar ba ta kyauta masa ba da ta yi shiru, to
amma me za ta ce masa? Ita fa jinta take duk a takure, ga wani kwarjinin da yake yi mata, ga kunyar shi da take ji duk ita ka
ɗ
ai.
_Adnan_
ta ambaci sunansa a cikin zuciyarta, sunan ya yi mata da
ɗ
i ba ka
ɗ
an ba. Lumshe idanunta ta yi tana hango yanda yake magana cikin nutsuwa yana motsa ƙananun lips
ɗ
insa kamar ba ya son maganar ko wanda aka yiwa dole. Murmushi ne ya kufce mata ba tare da shirya yin sa ba, saboda tuno kyawawan fararen idanuwansa da
yake tsare ta da su.
"Angel!"
Salman ya fa
ɗ
a da
ɗ
an ƙarfi lokacin da ya shigo
ɗ
akin yana ƙare mata kallo. Da sauri ta bu
ɗ
e idonta cikin ƙoƙarin daidaita nutsuwarta.
"Me ya sa kika taho ba tare da kin sanar mini ba?"
Kalar tausayi ta yi ta
ce. "I'm sorry bloody, bayan na baro class
ɗ
inku na ji ina son shiga toilet, kuma ka san i can't use toilet
ɗ
in school, that is why na taho gida." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Shikenan, amma kin
ɗ
aga mini hankali sosai, kin san irin neman da na yi miki
kuwa?"
"Sorry sweet Bro, ka je ka huta bari na tashi na ha
ɗ
a maka delicious yanzun nan." Murmushi ya yi ya ce. "Baby girl, shi ne kika zo kika ba ni kunya a class."
Cikin shagwa
ɓ
a ta ce. "Kunyar me kuma Faris?"
"Ba ta komai, ni abun da ya fi ba
ni haushi yanda ake ta tanka ki, bayan mun fito harda masu cewa in ba su contact
ɗ
inki wai kin burge su." Ya ƙarashe zancen tare da jan tsaki. Murmushi kawai ta yi, ta rasa me ya sa Salman yake mata haka? Ba ya so ya ga maza suna kallon ta ko su yi mata ma
gana, yanzu zai shiga
ɓ
a
ɓɓ
ata rai da jan tsaki. Lalla
ɓ
a shi ta yi ya sauko daga kumburin da yake, ta nuna masa an ba ta wayarta yau, taya ta murna ya yi sannan suka fita tare, ta shiga kitchen shi kuma ya yi
ɗ
akinsa.
Ba ƙaramin firgicewa General Ibr
ahim ya yi ba da ganin wannan videon, wani irin gumi ya shiga tsatstsafowa a jikinsa. D.P.O dake karantarsa ya ce. "Zaka ce ba kai ba ne wani ne ya yi amfani da fuskarka? Wannan ƙaryar da ka yi ta ƙara sanya mini zargi a kanka." General dai kasa magana ya
yi, sai goge zufa yake yana zare ido. D.P.O ya janyo laptop
ɗ
in dake gabansa ya yi yan danne-danne sannan ya juya ta yanda za ta fuskanci General Ibrahim, bai ce komai ba sai wani kallo da yake bin sa da shi. General Ibrahim ya
ɗ
aga ido daƙyar ya dubi lapt
op
ɗ
in, videon lokacin da ya shiga reception
ɗ
in Aminci Hotel ne.
"Wannan ma ko za ka musa ne? Ka saka facemask a lokacin dan ka yi badda kama, ma'aikacin hotel
ɗ
in ya buƙaci ka bu
ɗ
e fuskarka ya gan ka, sai ka ba shi cin hanci na 20k dan ya ƙyale ka wu
ce ka je ka kashe ƴar mutane. A matsayinka na babban jami'in tsaron ƙasa, wanda ƙasa take alfahari da kai."
"Haba D.P.O ya zaka dinga alaƙanta ni da abun da ban sani ba? Ni fa ba ni ba ne wannan da kake magana akansa." General Ibrahim ya fa
ɗ
i haka ci
kin borin kunya zuciyarsa na tsananta bugu.
Miƙewa D.P.O ya yi ya ce. "Idan mun je gaba ka yi musu duk wannan bayanin." Bai jira cewarsa ba ya ƙwallawa Inspector kira, bayan ya shigo ya ce masa. "Ku tafi da shi headquarter tare da ƴan'matan nan, I.G y
ana jira, ya ce a mayar da case
ɗ
in can, i will fallow you back.
Kafin dare labarin kisan Ihsan da videon da ta
ɗ
auka nasu ita da General Ibrahim ya gama zagaye ƙasa da kewaye, duk inda ka je zancen ake yi. Al'amarin ya girgiza manyan ƙasa da Sojo
ji wa
ɗ
anda suka san General Ibrahim, saboda yadda yake nuna shi na Allah ne akan komai, da yawa ba su yi tunanin zai aikata hakan ba.
Kwance yake akan gadonsa ya mimmiƙe baƙaƙen ƙafafuwansa, wata mata wadda da alama Matarsa ce tana yi masa tausa. Ta
ba ce a hannunsa yana ƙarawa sama hazo daga kwancen da yake. Wayarsa dake gefensa ce ta shiga ruri, tsaki ya yi cikin maganar riƙaƙƙun ƴan daba ya ce. "Ba za a ta
ɓ
a barin mutum ya huta ba." Ɗaukar wayar ya yi ya
ɗ
aga ya kara a kunne, sai da ya zuga ya fesa
r sannan ya ce. "Ina jin ka ya aka yi ne? Kira da sakaliyar yammar nan?"
"Ban gane in hau WhatsApp za ka tura mini abu ba, kawai ka fa
ɗ
a mini, ka san ni yanar gizon nan ba wani gane mata nake ba."
"To na ji, tunda ka dage zan hau." Ya ƙara jan ts
aki sannan ya katse wayar. Yana ƴan mintocinsa ya siyi data ya kunna ya shiga WhatsApp. Wani uban ihu ya kurma tare da yar da wayar a ƙasa, cikin zafin zuciya ya cillar da tabar hannunsa tare da narka wani uban ashar ya ce. "Yata Ihsan
ɗ
in aka kashe? Sanna
n kuma wancan tsohon matsiyacin gajeren Sojan ake zargi? Bayan ya gama lalata da ita? Ta
ɓ
di jan, Ibrahim ya de
ɓ
o ruwan dafa kansa, wallahi, wallahi, wallahi sai na
ɗ
auki fansar jinin ƴata."
Aru
ɗ
e mahaifiyar Ihsan ta miƙe cikin ƙaraji ta ce. "Innalillahi
wa'inna'ilaihirra'un! Mai gida me kake cewa ne? Ban fahimta ba, wacce Ihsai
ɗ
in aka kashe? Ba dai yata ba?"
"Ita fa Rabi, wai tun rana abun ya faru, ana ta kiran wayarmu daga ni har ke ba a same mu ba. An ta
ɓ
o tsuliyar dodo Rabi, za a yi yaƙin da ba
a ta
ɓ
a yin kamar shi ba a duniya wallahi."
Rabi da ba fahimtar abun da yake cewa take ba ta
ɗ
auki wayar da ya cillar cikin rawar jiki ta latsa, videon gawar Ihsan da bayanin abun da ya faru ya bayyana, ƙara ta fasa tare da zubewa a ƙasa sumammiya.
Na'ima na zaune a parlour