Showing 72001 words to 75000 words out of 260401 words
haƙuran ba, wallahi in dai ƴar halak ce ni sai wannan abar ta bar
gidan nan a yanzun nan, munafuka ta san ba ta da gaskiya ai, sai fiƙi_fiƙi take da ido."
Marairaicewa Nai'ma ta yi ta ce. "Dan Allah Granny ki yi haƙuri, duk da ban san laifin da na aikata ba."
Mitsss, ta ja dogon tsaki tare da ƙanƙance ido tana jef
awa Nai'ma wani irin kallo ta cikin glass, ba tare da ta yi magana ba ta fice daga parlour'n fuu tana fa
ɗ
in. "Ka nuna mini ban isa da kai ba, bari na saka a kira mini wanda ya isa da kai, shi ai bai isa ya ƙetarewa umarnina ba."
"Oh My God, rigimar Gran
ny ta yi yawa, mene fa'idar wannan abun da ta zo ta yi?"
Hawayen munafurci Na'ima ta fara ta ce. "Ban san me na yiwa Kakarka ba Khamal ba ta so na, kullum zancenta za ta ƙaro maka Aure, ko kuma ta ce ka rabu da ni." Cikin rarrashi Khamal ya ce. "Halin G
ranny ne ba ki sani ba Wifey ko me? Rikicinta ne kawai ba wani abu ba, idan ya tashi kowa ma yi masa take babu wanda ta ƙyale."
"Wannan ba rikici ba ne Khamal, tsana ce kawai."
Daidai nan Granny ta dawo hannunta riƙe da wayar Driver ta miƙawa Khamal.
Ba tare da ya kar
ɓ
a ba ya ce. "Me zan yi da ita?"
"Huhuhu, yau na ga jaraba, to wacce ta yi cikinka ta tsuguna ta haife ka ce take son magana da kai." Granny ta fa
ɗ
i haka kamar za ta ki fa masa mari.
Kar
ɓ
ar wayar ya yi ya kara a kunnensa. Kafin y
a yi magana muryar Ammi ta doki kunnensa a kausashe da fa
ɗ
in. "Khamal ka yi abin da Granny ta ce."
"Amma Ammi..."
"Ba na son jin komai, ka yi ko mene ne, daga baya ma yi magana."
Jiki a sanyaye ya ce. "Shikenan." Tare da katse wayar. Kallon Nai'
ma ya yi ya ce. "Ki je gidan, I will come tomorrow." Fashewa da kuka ta yi ta ce. "Yanzu Khamal yau ni kake kora daga gidanka? Ni Nai'ma uwar Ƴaƴanka kake cewa in bar maka gida?"
"Babu yadda zan yi ne Nai'ma, umarnin mahaifiyata na bi, but don't worry,
everything will be okay insha Allahu." Daga haka ya miƙe ya nufi part dinsa.
"A tashi a tashi da Allah, gida ne tunda ba na Ubanki ba ne sai kin bar shi wallahi, kuma a cikin satin nan zan aurawa Kamalu zanka
ɗ
e
ɗ
iyar budurwa, kuma ta cikin gida ce ba ba
re ba, bari uban nasa ya dawo."
A zuciye Nai'ma ta goge hawayen fuskarta tare da miƙewa tsaye ta nufi
ɗ
akinta kamar za ta tashi sama. Tafa hannuwa Granny ta yi ta ce. "Au da bangaje ni za ki yi? To Uwarki kika yi niyyar bangajewa ba ni ba, kuma gidan ji
kana yau dole a bar shi." Guri ta samu ta zauna ta kunto goro dake
ɗ
aure a jikin zaninta ta basga tana karka
ɗ
a ƙafa, idanunta akan
ɗ
akin Na'ima."
Sai da Granny ta ga fitar Nai'ma daga gidan sannan ta tafi, zuciyarta fess yau ta kawo ƙarshen iskancin Na'
ima.
Fayyad na gaba Adnan yana bin shi a baya suka shiga parlour'n gidan, wata farar matashiyar matar dake zaune akan kujera ta amsa musu sallamar da suka yi cikin fara'a.
"Wow Masha Allah, yau ga Sp Adnan a gidana, kullum ana mini hirar ka, yau ma t
un safe ake maimaita mini zaka zo, welcome." Ta fa
ɗ
i haka tana miƙewa tsaye.
Murmurshi Adnan ya yi bai ce komai ba, gurin zama Fayyad ya nuna masa ya zauna. A hankali ya ce. "Yana yi miki gulmata kenan Maman Boy?" Still tana murmurshi ta ce. "Sosai ma,
kai dai a yi shiru kawai." Fayyad ya zauna a gefensa ya ce. "Ai bana gulamar tuzurai sai ta Ma'aurata." Ko kallon shi Adnan bai yi ba. Dariya Maman Boy ta yi ta haye upstairs.
Tare suka dawo da wata budurwar yarinya, wadda da alama K'anwarta ce saboda
kamar da suke. Tunda suka sauko ta zuba wa Adnan na mujiya, har plate
ɗ
in da ta
ɗ
oro drinks a kansa ya kusa su
ɓ
ucewa daga hannunta, cikin son burge shi ta gaishe shi, ba tare da ya
ɗ
ago ba ya amsa mata. Maman Boy ta miƙa masa Boy sannan suka koma saman.
Suna shiga
ɗ
aki K'anwar Maman Boy ta ce. "Wow amma Aunty guy
ɗ
in nan ya ha
ɗ
u, ga kyau ga aji, yanda kika san irin Black Americans
ɗ
in nan, ni na ta
ɓ
a ganin baƙin mutum mai kyan shi kuwa?"
"Kai Ramlah uwar zuzuta, daga ganin mutum sau
ɗ
aya har kin ƙare
masa kallo?"
"Aunty ba za ki gane ba ne, amma guy
ɗ
in ya ha
ɗ
u over, Matarsa ta more."
Murmurshi Maman Boy ta yi ta ce. "Ko dai kin ƙyasa ne?"
"Rufa mun asiri, kar Matarsa ta ji ta mun duka, kawai dai na fa
ɗ
i abun da yake da akwai ne, kin san ni ba
na gani in yi shiru."
Maman Boy ba ta kuma cewa komai ba, Ramlah kuwa cigaba ta yi da yaba kyawu da zubin halitta irin na Adnan.
"Ka sha juice
ɗ
in mana, ka wani lumshe ido ina magana ka mun shiru, tunanin me kake?" Fayyad da ya gama zuba drinks a
cikin glass cup ya fa
ɗ
i haka.
Ba tare da ya bu
ɗ
e idon ba ya ce. "I'm okay, thank you."
"Wannan ai wulaƙanci ne, Matata ta kawo maka abu amma ka ce ba za ka sha ba."
"I will drink, amma ba dan kai ba."
"Na ji
ɗ
in, Malam ka fa
ɗ
i gaskiyar abin d
a yake damun ka, ka zo ƴanmatan Kano sun ru
ɗ
a ka shine kake wani babbasarwa, wannan yanayin da kake daga gani na fall in love ne.
"Ka fi kowa sanin ba ni da time
ɗ
in shirme ko?" Ya yi maganar yana gyara kwanciyar Boy da ya yi bacci a jikinsa.
"Allah
ya nuna mun ranar da ka zo kana cewa, dama Fayad haka so yake, lokacin zan ci dariyata in more, wai wa ya ga su Adnan ana Baby please sorry, you know I love you more." Ya ƙarashe maganar cikin dariya.
Ta
ɓ
e baki kawai Adnan bai ƙara magana ba.
Abra
ba ta nan Granny ta zo, kuma har ta tafi ba su dawo ba, saboda sun biya siyo school bag ita da Salman bayan sun baro gidan Aunty Iman, saboda normal handbag ba za ta
ɗ
auki tarkacen school ba. Ba su farga Nai'ma ba ta gidan ba sai da daddare lokacin dinner
, saboda sun saba idan Khamal yana gari kodayaushe tana part
ɗ
insa.
Ganin Khamal ya fito shi ka
ɗ
ai yasa Salman ya ce. "Abbi Mami fa? Tunda muka dawo ban gan ta ba, na je
ɗ
akinta ba ta nan."
"Ta je gidan Mama." Ya ba shi amsa
"Mama kuma? Lafiya?"
Ya tambaya cikin mamaki.
"Lafiya ƙalau."
"Yaushe za ta dawo?"
"Gobe."
"Me ake yi a can Abbi?"
"I don't know, Mama ce ta kira ne za su tattauna akan something important."
"Me ne abun?"
"Na ce maka ban sani ba, Family issue ne, ka zama
ɗ
an jarida ne Salman da za ka titsiye ni da tambayoyi haka? ka ci abinka, kar na kuma jin bakinka." Khamal ya fa
ɗ
i haka cikin fa
ɗ
a.
Ƙ
asa Abra ta yi da kanta tana wasa da cokali a cikin abincinta, amma ta kasa
ɗ
iba ta kai bakinta.
"Ki ci abinci Malama
, ba wasa za ki tsaya ba." Khamal ya fa
ɗ
a mata haka ba yabo ba fallasa.
Gya
ɗ
a masa kai ta yi a hankali ta fara cin abinci. Ka
ɗ
an Khama ya tsakuri abincin ya ci ya miƙe, shi ma dan kada yaran nasa su yi tunanin da wata matsalar ne, musamman Salman da yak
e da saurin fahimtar abu. Daga dinning area
ɗ
in
ɗ
akinsa ya wuce ya dauko car key ya fice zuwa gidan Ammi.
"Yaya, ba ki yi tunanin wani abu ya faru ba da bama nan?" Salman ya tambayi Abra cikin nazari.
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Like what?"
"Ko Mami sun samu matsala ne da Abbi shi yasa ta tafi gida? dan yanayinsa ya nuna yana cikin damuwa."
"I don't think that gaskiya Faris, kuma insha Allah ba haka ba ne."
"To Allah yasa." Ya yi maganar tare da cigaba da cin abincinsa.
ita kuwa kasa
cigaba da cin abincin ta yi, don tana cikin damuwa,
ɓ
oyewa kawai take dan kar Salman ya fuskanta. Ta damu sosai akan fushin da Abbinta yake da ita, na makircin da Nai'ma ta shirya mata, ta ba shi haƙuri ya ce ya haƙura amma ya ƙi sakar mata kamar da.
Khamal ne zaune a
ɗ
akin Ammi yana zayyane mata abun da ya faru, bayan ya gama ta ce. "Yanzu ya kake so ayi?" Ya ce. "Toh Ammi, na rasa ma me zance, rigimar Granny ta yi yawa, haka kawai ta zo ta kora yar mutane gidansu, babu wani dalili." Ammi ta ce. "K
a kira Baffa ka sanar masa, zai yi mata magana kuma na san za ta haƙura." Numfashi ya sauke cikin damuwa ya ce. "Zan kira shi insha Allahu, amma ni Ammi ban so kika biyewa Granny ba, yanzu Nai'ma sai ta ga kamar na wulaƙantata ne."
"Hakan shi ne solutio
n da kwanciyar hankali, ko so kake yau Granny ta hana ni bacci da mitar na ƙi bin umarninta, saboda ba ita haife ni ba?"
Girgiza kai kawai Khamal ya yi, zuciyarsa cike da takaicin halin Granny, amma abu
ɗ
aya da ya daure masa kai shi ne, ya san duk jarab
ar Granny ba ta yin ta ba tare da dalili ba ko an ta
ɓ
o ta, idan haka ne kenan Na'ima ta yi mata laifin da gaske, amma wanne irin laifi ne? Ko dai rikicin tsufan nata ne ya ƙaro?
Hankali a tashe Nai'ma ta ƙarasa gidansu, Mama tana ganin ta, ta san ba ƙ
alau ba.
"Ke lafiyarki kika fa
ɗ
o mana gida babu ko sallama?"
"Ina fa lafiya Mama? Allah ya ha
ɗ
a ni da matsiyaciyar ƙaddararriyar kakar miji, ƴar kaza_kaza." Nai'ma ta fa
ɗ
i haka tana hawaye.
A ru
ɗ
e Mama ta ce. "Yanzu me ya faru, na gan ki a hargit
se?" Labarin abun da ya faru ta sanar mata.
Cikin takaici Mama ta ce, "Wannan mata akwai bala'i, mata kawai ki
ɗ
orawa kanki jaraba a rayuwa?"
"Shegiya ga shi ta ƙi mutuwa."
Jinjina kai Mama ta yi ta ce. "To ta je dan kanta, aniyarta ta bi ta, zam
a gidan Khamal ne yanzu kika fara, sai dai ta mutu dan baƙin ciki. Ki kwantar da hankalinki, na san Khamal
ɗ
in zai zo ya mayar da ke cikin ruwan sanyi."
"Hmm, Mama babban tashin hankalina kullum cikin cewa za ta yi masa Aure take, tsorona kar zancenta y
a tabbata, dan sai abun da ta ce iyayensa suke bi, idan ta dage amincewa fa za su yi." Ta yi maganar cikin tsantsar damuwa.
"Ba zai yiyu ba, wannan tatsuniya ce, ki daina damun kanki akan wannan soki burutsun tsohuwar mara ma'ana, ki
ɗ
auki zancenta shir
me kawai. Tashi ki wuce ciki ki huta, bari Suwaiba ta dawo ta dafa miki abin da zaki ci."
Zuciyar Nai'ma fal baƙin ciki ta miƙe ta shige ciki, wata irin tsanar Granny na cika mata zuciya, shegiyar mata ta yi sanadin da yau za ta kwana a cikin zafi ba a
cikin AC ba, ita da ko taro ake a gidansu ba ta kwana, sai dai ta zo da sassafe saboda ba ta iya baccin cikin kwanciyar hankali. Babban takaicinta ba ta san abun da ta yi Granny ta yi mata haka ba, don ko kusa ba ta yi tunanin Salman ne ya sanar musu abun
da ta yi wa Abra jiya ba.
Abra na
ɗ
akinta tana zuba abubuwan school a cikin new bag
ɗ
inta, sai a time
ɗ
in ta farga da rashin ganin I.d card
ɗ
inta. Ƙara checking tsohuwar jakarta ta yi ko za ta gan shi amma ba ta gani ba, parlour ta fito inda Salm
an yake zaune yana kallon Ball.
"Faris school i.d card
ɗ
ina yana gurinka?"
Ba tare da ya
ɗ
ago ba ya ce. "No." Cikin damuwa ta ce. "Na duba ban gani ba, Allah yasa ban yar da shi ba." Yana duban ta ya ce. "Ki ƙara dubawa dai sosai Yaya." Kamar za ta
yi kuka ta ce. "Na fa duba ko'ina ban gani ba."
"To mene abun damuwa? Kar ki mun kuka ni akan
ɗ
an wannan abun."
"Dole in damu Salman, idan aka hana ni shiga school fa saboda babu shi."
"Babu mai hana ki, wasu ma ba a ba su ba, ki bari gobe idan
muka je school sai mu yi report a sake miki wani, kafin a sake sai ki dinga nuna admission latter
ɗ
inki in za mu shiga."
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Amma na yi mamakin rasa abun nan, ko garin ya na yar oho?"
"Yarinya ce ke, shi ya sa komai naki s
ai addu'a, kuka, shagwa
ɓ
a, everything."
Dariya ta yi ta faki idonsa ta ja dogon hancinsa da ƙarfi ta ce. "Tazarar shekaru uku ba wasa ba ce yaro." Tana fa
ɗ
in hakan sai Salman ya yunƙura kamar zai kamo ta, ƙara ta saki tare da yin baya da sauri tana da
riya. Ƙwafa kawai ya yi bai ce komai ba.
Dawowa ta yi ta zauna a kusa da shi ta ce. "Please kar ka fa
ɗ
a wa Abbi na yi loosing i.d card
ɗ
ina, ya ce daga fara zuwa har na fara yarda abubuwa."
"An gama My Angel, zo ki taya ni kallo."
"Maƙe kafa
ɗ
a t
a yi ta ce. "Bacci zan yi, ka san gobe 8 muke da lecture, kai ma haka, saura kuma ka makarar da mu."
"Uhm, su Yaya ƴan University, inyee." Ya yi maganar cikin dariya."
"Na ji, ka kira Mami kuwa?"
"Na kira ta ba ta
ɗ
auka ba."
Jinjina kai kawai A
bra ta yi ta miƙe ta koma
ɗ
akinta.
Washegari da sassafe Ammi tana kitchen tana ha
ɗ
a breakfast Granny ta zo bakin kitchen
ɗ
in ta tsaya ta fara magana.
"Kai jama'a, mutane babu Allah a ransu,
ɗ
ana yana can gurin neman halak amma saboda rashin t
soron Allah an kira shi an ha
ɗ
a mu, jiya har na fara bacci kiran wayarsa ya tashe ni, to ni dai ba ruwana kowa ya haifa, kuma duk abun da mutum ya mun sai an yi masa shi ma, ato."
Murmurshi Ammi ta yi tare da juyowa tana duban Granny, cikin girmamawa
ta tsuguna ta ce. "Ina kwana Hajiya?"
"Lau." Granny ta ba ta amsa cikin
ɓ
ata fuska.
"Bari na kawo miki abincin Granny, yau na makara ban tashi da wuri ba ne.
"To ba yunwa ce ta taso ni ba, a ƙoshe nake, kin san ni ƴaƴana ba sa cewa in yi abu in ƙ
i yi, tunda ni ma suna mun biyayya daidai gwargwado, abun da Hamisu ya fa
ɗ
a mun ne na kwana da shi a raina, yau kuwa ina tashi na ce ba zan yi sanya ba, gidansu waccan gantalalliyar matar kamalun zan je in dawo da ita."
"Hajiya da kanki kuma? Da kin bar
i Khamal
ɗ
in ya je ya
ɗ
auko ta."
"Bar ni in je da kaina
ɗ
in, ni yanzu ba dogon surutu na zo mu yi ba, kira direba ya zo ya kai ni."
Ammi ta ce. "Toh, amma dan Allah ki tsaya ki karya Hajiya." Granny ta ce. "To na tsaya, kuma fa da gaskiyarki A'isha,
dan wa
ɗ
ancan ru
ɓ
a
ɓɓ
un idan na je babu abun da za su ba ni, sai dai su bar ni yunwa tai ta saka
ɗ
a ta, Allah na tuba ma ko sun ba ni ba ci zan yi ba, yo me zan yi da kayansu?"
Takwas da mintuna a ƙofar gidansu Nai'ma ta yi wa su Granny, tana zaune a b
ayan Mota take bin gidan da wani irin kallo. Tsaki ta ja ta ce. "Tirrrr, ban da ƙaddara me zai ha
ɗ
a Kamalu da ƴar wannan gidan? Gida
ɗ
an tsurut haka kamar kabari, don ma Allah ya yi mu masu ilimi, mun san Talaka da mai ku
ɗ
i duk Allah ne ya yi su." Ta ƙaras
he maganar tare da bu
ɗ
e Motar ta fita, fuskar nan babu fara'a ko ka
ɗ
an, sai fama take da ƙatuwar jaka a hannu. Murmurshi kawai driver yake.
Aunty Suwaiba tana tsakar gida tana alwala Granny ta rafka sallama, cikin mamaki take kallon ta, lokaci
ɗ
aya ta
ha
ɗ
e rai ta cigaba da abun da take yi.
"Ba mutane a gidan ne ko gidan na arna ne? Ana ta sallama an ƙi amsawa."
Hararar ƙasan ido Suwaiba ta wurga wa Granny, cikin raini ta ce. "Me Idonki ya gane miki?" Tafa hannuwa Granny ta yi ta ce. "A'a fa, kar
ki mun fitsara da farar safiyar nan, wallahi jibguwa zaki yi, kin san jikana soja ne, yanzu sai in