Showing 72001 words to 75000 words out of 268949 words

Chapter 25 - KURMAN ALLO COMPLATE

zo ta zauna gafda ita tana ƙarewa yanayinta kallo a hankali Sadiya ta miƙe zaune ta saka bayanta kan

pillow sai lokacin ta cire glass

ɗ

in da ya mamaye rabin fuskarta idonta cikin na Sarah da take kallon fuskarta harma da idanunta. cikin rawar murya Sarah ke fa

ɗ

in."ke lafiyarki kuwa?"Kinga idanunki!

"Ina cikin matsananciyar damuwa Sarah ki bani shawara na

tabbata ƙwaƙwalwata tana gafda tabuwa.

Ta karasa maganar muryarta na wani irin hardewa, anan kuma ta soma bai wa Sarah labarin mutuwar aurenta dan koda wasa bata ta

ɓ

a gayawa ƙawayen nata wai sun yi divorce ita da yaya Abba. Cike da tashin hankali Sarah k

e fa

ɗ

in."kuma mahaifin naku ya rasa wacce zai aura masa sai autarku wannan 'yar mitsiyaya yarinya yaushe za ta iya

ɗ

aukar ƙato irin yaya Abba? inama laifin Siyama, kai gaskiya Daddyn nan naku bai yi ba Sady-B ni yanzu nama rasa wane kalar tunani zan yi ya

kamata dai ki fara samun bacci dan yanzu baki da natsuwar da zamu yi magana. Duk wanda ya kalle ki zai san you're suffer from depression dole sai kin

ɗ

an sami bacci ko da ka

ɗ

an ne da haka sarah ta dauko wata bag ta zuge bag

ɗ

in ta fitar da wata kwalba ta k

alli Sadiya da murmushi cikin fuskarta tana fa

ɗ

in "yanzu dai ki shanye duka wannan ha

ɗ

in Insha Allahu baƙaƙen maganganun da Abba ,ya fa

ɗ

a maki tuni zasu fice miki akai ke baza ki masan wannan na musamman bane yana da dandano sai kin shanyesa dukka. Lokaci



ɗ

aya yanayin fuskar Sadiya ya canja tana girgizawa Sarah kai take fa

ɗ

in."banda wannan. Wata dariya Sarah ta saki tana fa

ɗ

in."ki sha na yau kawai Sady-B ni na fa

ɗ

a miki damuwar nan zata rage dan Allah ki sha.

Da haka Sarah ta kwance marfin batare da dogon

tunani ba ta kai sa daidai bakin Sadiya dakyar Sadiya ta bu

ɗ

e bakint tana fara sha ta wani irin ya mutse fuska da sauri ta janye kwalbar daga bakinta tana girgizawa Sarah kai haka tana jin kanta

na wani irin juyawa lokaci

ɗ

aya. Sarah ta dinga yi mata daba

ra har ta shanye dukka ta dauki bottle water ta miƙa mata ta sha rabi anan ta baje tsakiyar

ɗ

akin ta koma ta kishingi

ɗ

a tana jin yadda kanta yayi wani mugun nauyi babu shiri ta lumshe idanunta. Gefe Sarah ta koma tana ta lura da yanayin ƙawarta ta har na k

usan minti goma sha biyu kafin bacci mai nauyin gaske ya Sadiya. murmushi Sarah ta yi tana fa

ɗ

in."idan kika farka ke da kanki za ki nemi ƙari wani.

ƙ

arfe biyu AB ya fita restaurant yaci abinci saboda yadda hanjin cikinsa ke ha

ɗ

ewa wuri

ɗ

aya babu abunda ke

cikin cikinsa, tun safe yana gamawa ya koma office bai bar office ba sai karfe biyar tilas gida ya koma dan yin wanka yana ta tunanin zuwa wurin Rumaisa da yamma, ya kamata ya fa

ɗ

a mata hukuncin da Daddy ya yanke ganin kwanakin nata matsowa. Bai shiga da

motarsa cikin gida ba a waje yabarta dan ko ka

ɗ

an baya son ha

ɗ

uwa da mami. Har ya shige

ɓ

angarensa bai ha

ɗ

u da kowa ba kayan jikinsa ya cire yayi wanka.

Yana cikin shiryawa ne ya ji ana buga masa door bell dan bu

ɗ

e idonsa yayi da mamaki jallabiyya ya nema

ya saka ajikinsa dan ko creams

ɗ

insa bai gama shafawa ba ya saka (casual slippers)a ƙafarsa ya nufi kofa yana bu

ɗ

e kofar idonsa cikin na Siyama

da murmushi a fuskarta ta gaishesa ya kalli tray

ɗ

in dake hannunta

"Sannu da dawowa yayanmu ya office?" Mami

ta ce a kawo maka lunch, da haka ta isa kan dinning

ɗ

in dake cikin parlorn ta aje masa. Sosai yayi mamakin yadda Mami tasan ya shigo gidan, bai san da cewa Mami magana ta yi da Balmo maigadi akan idan Abba ,ya dawo kai tsaye ya kirata a waya haka ko aka yi

yana ganin dawowarsa ya kira Mamin a wayar har yana ce mata bai shigo da motar na kila zai ƙara fita ne. murmushi kawai Mami ta yi watau Abba ya mayar da ita yar iska a lokacin suna zaune da Siyama a parlor Mami ta mata umurnin ta zuba abincin ta kai masa

acan bangarensa. Yana tsaye a bakin ƙofa har Siyama ta aje ta dawo.

"Ki jira ni"

Ya ce da Siyama yana barin bakin ƙofar

ɗ

akinsa ya wuce ya bu

ɗ

e bedside drawer ya ciro keys

ɗ

in motarta ita da Sadiya, tun da ya miƙa mata take kallonsa da murna take fa

ɗ

in.

"mungode sosai yayanmu amman ka jawa babynka kunne ta daina yimana rashin kunya.

"Ai bama sai na ja mata kunne ba ita ma motarta na zuwa kwanan nan. Ɗan bu

ɗ

e ido ta yi tana kallon yayan nasu sai dai ba tace komai ba ta juya tare da ficewa daga part

ɗ

in ta

na murmushi tasan wasa yake wane mahaukacine zai siyawa Aydah mota, daman ko kallon abincin da Siyama ta aje bai yi ba ya koma master bedroom

ɗ

insa ya ci-gaba da shiryawa yana gama shiryawa ya fice daga gidan sai da ya fito gidan ya sauke wata irin ajiyar

zuciya sosai Mami ,tasha mamakin Abba yadda ya mayar da ita wata shashasha ya ƙara ficewa batare da ya shigo ba. Yana driving ya yi dialling lambar Rumaisa tamkar jiran kiran nasa take ta dauka agagauce cikin muryar kuka take fa

ɗ

in."wallahi ka daina sona h

abeebi.

"Ina hanya.

Ya fa

ɗ

a tare da saurin katse mata hanzari duk sai haka sai da take furta

"Da gaske kake yi Habibi?

"ko na koma ne?"

Da sauri tace "A'ah sai ka ƙaraso.

Da haka ya sauke wayar wannan karon kuma bai san ta yaya Rumaisa zata karbi wa

nnan al'amarin ba. ƙofar gidansu Rumaisa ya yi parking motarsa ya kirata a waya bai fi minti goma ba da kiran nata sai ga ta, ta bu

ɗ

e ƙaramar ƙofar dake

ha

ɗ

e da gate

ɗ

in gidansu tun kafin ta karaso ya sauke glass

ɗ

in motar riga da skirt ne ajikinta na Atam

fa sun yi mata kyau sosai sai dan karamin veil

ɗ

in da ta

ɗ

ora kan kafa

ɗ

arta light make up ne akan fuskarta wanda ya kara fito da asalin kyawunta ta yi masa kyau ba ka

ɗ

an ba.

Kallonsa kawai take cin karo da fuskarsa kawai da ta yi yanzu duk wani haushinsa

da take ji tun jiya ya

ɓ

ace daga zuciyarta.

Tana mamakin yadda bata iya fushi dashi, fitowa ya yi daga motar yana ci-gaba da kallonta ƙasa-ƙasa kamar yadda ita ma take kallonsa girar ta dukka biyu ta dage."kayi kyau sosai Habibina!

Ta fa

ɗ

a a hankali ,kaf

in ta kuma ta cigaba da ƙarewa kayan jikinsa kallo na tsanake baƙin yadin filtex ne ajikinsa sai links da aka yiwa hannuwan wani sanyayyen murmushi ya sakar mata irin mai shiga jiki yana shafa sumar kansa mai kama da ta labarawan asali murya can ciki ya ce

"Ban kai ki ba habibty.

"Zagina kake yi.

Bu

ɗ

e mata manyan fararen idanunsa yayi ,camera wayarta ta saita ta shiga daukarsa pics tana fa

ɗ

in "kai ba zaka gane kyan da kayi bane.

Bai ce da ita komai ba iyankacin sa ya yi murmushi dawowa tayi daf dashi ta

shiga daukarsu video duk da bai yi dariya ba Amman a hakan ya yi mata kyau sosai. Ya girgiza kai ya rasa soyayyar Rumaisa da son hotuna.

Idan kaga hotonsa to Rumaisa ce ta tilasta masa yinsa. "Mu shiga daga ciki wai meyasa kake parking motar ka a waje?."

Ta fa

ɗ

a da yanayin marar da

ɗ

i a muryarta, kin manta Daddy..

Da sauri ta katsesa tana fa

ɗ

in."baya gari fa ta kar

ɓ

e car key

ɗ

in motarsa ta shiga

ɓ

angaren driver ta tada motar ta doshi get

ɗ

in gidansu tana yiwa maigadi horn sai da ya leƙo ganin Rumaisa ce y

a bu

ɗ

e gate

ɗ

in da wani irin kallo ta bisa ganin yadda yasata take ta danna masa horn sai kace wani kurma gyara parking motar tayi.

Har lokacin tana mamakin AB da yaki shigowa ,tana kawowa wurin maigadi ta yi masa wani shegen kallo ta fice daga gate

ɗ

in a

tsaye ta samu AB yana jiranta ƙarasawa tayi wurinsa tana fa

ɗ

in."kaga na shiga mota kaki shiga kuma ka zo ka yi tsaye anan mu karasa aciki mana.

Kallonta yake da wani yanayi dake kwance cikin idanunsa mai cike da zallar ƙaunarta bin bayanta ya yi har zuwa

parlorn da suka saba zama duk lokacin da yazo gidan. Kayan motsa baki ta aje masa agabansa ta dauki glass cup ta zuba masa lemu..

#Love story 2023/2024

#Jeeddah Aliyu

#Asmy b Aliyu

#Team tagwaye novels

#Kurman Allo.

Domin biyan ƙudin litt

afin nan 500 Naira only

ACCOUNT NUMBER

0020428430

Ishaq Fatima A. Gtb

Or

8098456130

Fatima Ishaq

Opay digital services

Shaidar biya

08098456130

KATIN MTN Ta

👇

07043079282

Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi

08086207764

0816 1

14 6563

+234 704 040 2435

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.

*BAQEER*

Ayusher Muhd

Umm Asghar

*KURMAN ALLO*

Asmy b Aliyu

Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*

Zee Bawa

Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*

Nana Diso

Billy S Fari

*K

ULUWA*

Zee yabour

Sadiya Dan

Duka Biyar

ɗ

in akan 2k

Hudu 1600

Uku 1200

Biyu 800

Ɗ

aya 500

VIP

💕🔥

Duk guda

ɗ

aya 1k

NORMAL GROUP 500

VIP 1000

[12/19/2023, 11:07 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*

(A beautiful Love story)

NA

JEEDDAH ALIYU

&

ASMY B ALIYU

*AREWABOOK*:3256

Love Story

#Gwagwarmaya

#Team Tagwaye

030.

"Habeebi!" Rumaisa ta kirasa cikin sanyi murya ganin yanayinsa ba haka ta saba ganinsa ba, sai da ta ƙarewa masa kallo ta sauke numfashi kafin ta ce "meke damunka

ne kwanan nan?"duk ka zama wani iri.

murmushin iya fatar baki ya yi mata yana shafa beard

ɗ

insa yana kallon yadda take wani bin jikinsa da kallonsa tamkar mai neman wani abu a jikin sa tana kallon yadda idanunsa suka fada duk girmansu sai da suka shige "k

a rame bakada natsuwa tare da kai ka daina boyemin damuwarka.

Rumaisa ta fa

ɗ

a da wani yanayi a muryarta da tasa zuciyarsa wani irin dokawa.

"Zan kara yimaki laifi Rumaisa amman karki manta a kowanne yanayi sonki ne manne a zuciyata karki dauka da son rai

na zan yi miki wannan laifin ina sonki!"inason ki Rumaisa wallahi ke ce macce ta farko da zuciyata ta fara so da ƙauna.

Yadda yake ta maimaita yana sonta yana kara narkar mata zuciya har ya fara daga mata hankali kamar wani abu mai girma zai gifta a tsaka

ninsu.

"Zan dauki kowanne irin laifin da za kayi min banda....

Tun kafin ta karasa ya katseta dan yasan me zata fa

ɗ

a."Daddy ya yanke shawarar auramin Aydah a karo na biyu nan da jibi.!"

Shi kansa yadda ya fa

ɗ

i kalamar cikin da sauri yasha mamaki yana ka

llon yanayin Rumaisa da ya canja lokaci

ɗ

aya, tamkar bata fahimce me yake nufi ba. Ganin yadda ta zama lokaci

ɗ

aya yasa ya dawo kusa da ita hannunta ya kama ya damƙe cikin nasa yana ganin yadda idanunta suka cicciko da kwallah lokaci

ɗ

aya, "Ki sani Rumaisa

aurena da Aydah ba zai canja alakarmu ba Rumaisa idan mahaifinki ya amince dani bayan aurena da Aydah zan aureki saboda ke ce za

ɓ

in zuciyata.

Kalamansa banda ƙona mata rai babu abunda suke cikin tsanani

ɓ

acin rai ta ce "ka aureni a ina? Na haƙura Bashir

da gaske na haƙura da kai.

Ta fa

ɗ

a cikin fita hayacinta.wasu irin hawaye ne ke fita akan fuskarta tana jin yadda jikinta ya dauki wani kalar dumi kamar zazza

ɓ

i zai rufeta lokaci

ɗ

aya.babu abunda zai canja Rumaisa."meyasa kike shakkar soyayyar da nake yima

ki,aure zakayi meyayi saura a tsakanin mu kuma auren da Aydah

Wani irin murmushi take saki wanda bai da alaƙa da farin ciki "Daga ranar da ka ha

ɗ

a gado da wata macce daga ranar zan daina sonka.! Ba zan boye maka ba ina da kishin da Ni kaina ban san kalars

a ba musamman akan ka Bashir. Tun kafin ma hakan ya faru na fa

ɗ

a maka kar ya faru kaga na canja ka ce dan me?"

Kallonta yake yana juya Kalamanta aransa, kina nufin da ƙanwar tawa zan ha

ɗ

a gado Aydah ce fa?

Ya fa

ɗ

a a hassale hakikanin gaskiya Rumaisa ta f

ara harzuƙa shi akan me za ta ce ya ha

ɗ

a gado da Aydah, sai kace bashi da ƙwaƙwalwa a kokon kansa, maganganun ta su yi matuƙar yi masa muni.

Rumaisa ta kalle shi a lalace ta ce "Wannan

ɓ

angaren bai da yare"!

Ni dai na hakur....

Tun kafin ta ƙarasa ya fi

sgota cikin jikinsa abunda bai ta

ɓ

a faruwa ba a tsakaninsu tana jikinsa tana jin yadda ƙirjinsa ke wani irin bugawa sosai ta rungumesa hawayenta na sauka kan ƙirjinsa "Zan iya mutuwa habibty idan kika sake cewa na ha

ɗ

a gado da Aydah she's like a daughter t

o me babu wannan zance a tsakanin mu

na amincewa Daddy da aurenta ne saboda ba zan iya masa musu ba Rumaisa dukka Aydah nawa take da za ki yi wannan kalar tunanin me ma ta sani acikin rayuwar aure? ki kwantar da hankalin ki Rumaisa babu abunda zai canja n

i naki ne na har abada Aydah kawai zata cigaba da zama a karkashin kulawata da ta girma ta mallaki hankali kanta ni kaina zan samu mata mijin da ya dace da ita zan rabu da ita cikin sauki batare da Daddy ya ji zafina ba.

Ita ma Aydah a matsayin yaya take

kallona na kuma tabbata har abada ba za ta canza min wannan matsayin ba. Na maki alƙawarin babu abunda zai canja matsayin Aydah a zuciyata.

Ɗ

agowa ta yi daga cikin jikinsa tana dan ja da baya kusancinsu yasa take jin wani iri kalamansa kuma ba karamin san

yayya mata zuciya suka yi ba tasan halin AB baya magana biyu kuma tasan babu abunda zai cira ajikin Aydah yarinyar da ma nonuwa basu gama tsayawa a kirjinta ba me za ya yi da ita  amma sanin da ta yiwa butulci irin na

ɗ

a namiji sai kawai ta ce "Habibi na y

arda da kai

ɗ

ari bisa

ɗ

ari amma inaso kauda duk wani kokwanto da zai zo min anan gaba Habibi me zai hana ka rantse da Alqur'ani ta hakan ne ka

ɗ

ai zan ƙara yarda da kai

ɗ

in nawa ne ni ka

ɗ

ai.

Wani malalaci murmushi ya yi yana fa

ɗ

in "Habibty ba ki yarda dani

ba.

"No Habibi wallahi na yarda da kai the only problem ku maza ba ku da tabbas yanayin ku tamkar na hawainiya ne koda yaushe kuna iya canza kala.

"Habibty da kin yarda dani da ba za ki nemi na rantse da Alqur'ani ba ki tuna Rumaisa Alqur'ani ba abin wa

sa bane.

"Ai shiyasa na ce ka rantse dashi idan har ka amince ka yi rantsuwa dashi ni kuma zan nemi hanyar da zan sa Abbana ya amince da aurenmu, yanzu za

ɓ

i ya rage naka kuma ta wannan hanyar ce zan ƙara tabbatar da ni ka

ɗ

ai ce a zuciyarka.

Duk yadda AB

yaso Rumaisa ta janye zance rantsuwa da Alqur'ani amma ta kafe lallai idan da gaske yana sonta dole sai ya yi abinda take so daga karshe baram-baram suka rabu a fusace ya yi mata sallama ya koma gida.

Sai dab da magarib Sadiya ta tashi daga naunnaye bacc

in da ya

ɗ

auke ta a

ɗ

akin Sarah da kyar ta iya tashi zaune wani irin azababben ciwon kai take ji a hankali ta dafe goshinta tare da runtse jajjayen idanuwanta da suka mata dankaran nauyi ta dauki ten minutes a haka kafin ta yada ganinta a cikin

ɗ

akin Sarah

bata nan room mate

ɗ

inta ka

ɗ

ai ta gani kwance a nata gado tana chatting da wayarta

Sadiya ta ja deep breath tare da sauke wa ta kalli Esha cikin nauyin harshe ta kira sunanta "Esha!

Da hanzari Esha ta waiga gafen da Sadiya take cikin fara'a ta ce "Ah! Sa

di-B kin falka?

"Uhm! Ina Sarah?

"Ai kuwa Sarah ta da

ɗ

e da fita ita ce ma ta bani gadinki da tuntuni na fita kin ga babu da

ɗ

i kina bacci mufi ce mu barki ke ka

ɗ

ai a kwance.

"Nagode Esha! Ni zan wuce gida idan Sarah ta dawo ki ce ta kira ni dan Allah tu

n da ta fita gantalinta nasan ko na kira ta ba zan same taba, ta kashe wayarta.

"Shi kenan zan fa

ɗ

a mata ki gaida min da Siyama.

"Za ta ji!

Sadiya ta fa

ɗ

a a takaice tare da

ɗ

aukar handbag

ɗ

inta, ta fice Esha ta bi ta da kallo tana murmushi sai kuma ta t

a

ɓ

e baki ta maida ganinta kan wayarta, Sadiya tana tafe dizzy yana

ɗ

ibar ta adaddafe ta isa wurin da ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login