Showing 1 words to 3000 words out of 287295 words
[5/18, 13:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfar
ouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fit
ar mun da littafi*
*littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI*
Zaku ce ya akayi haka
🥲
na fiku takaici da
baƙin ciki rasa rubutun nan a karo na biyu
😭😭
in shiga in duba folder tace dubani in da kika ajiye. Komai ya goge wlh. Bazance dan me ba domin bansan hikimar ubangiji cikin al'amarin ba. A kullum ina addu'ar Allah ya bani ikon rubuta alkhairi. Idan da ra
bo zan sake rubuta WASU MATAN amma abun da ciwo kayi rubutu ya goge.
Ban cika baki ba amma se kunce gara da akayi haka. It was meant to come in the next 1 year or more ashe yanzu Allah ya nufa. Asha karatu lafiya.
*PAGE 1*
"Malam idan kaje ƊAN ALJA
NNAH zan sauka" na fa
ɗ
a ina nunowa me Adaidaitan da muke ciki saitin in da ze ajiye ni, bayan daya gama daidaita parking na sauka ba tareda na kalli Hansa'u data kalli
ɗ
aya
ɓ
angaren ba nace
"Da ace kuturwa Allah yayi ni se inji haushi dan kince ba zaki ta
yani aiki ba, dake ko babu ke bazan rasa wanda zasu rufamun asiri ba" na fa
ɗ
a ina miƙawa me Adaidaita
ɗ
ari biyar. Bata tankamun ba na juya ba tareda na amsa tambayar da me mashin
ɗ
in yake mun ba akan iya ku
ɗ
i na ze
ɗ
auka ko na mu biyun na shige kantin. Na
rigada na rubuta list
ɗ
in abubuwan da zan siya dan haka kai tsaye na shiga
ɗ
auka cikin abinda be wuce minti sha biyar ba na gama dan ma na tarar da layi gurin biyan ku
ɗ
i. Wani Adaidaitan na tare ya ƙarasa dani kofar Nasarawa gidan Anty Labiba. Munir na ƙof
ar gida da abokinsa ina hango su naji raina ya sake
ɓ
aci dan nasan ƙarshe yanzu Anty Labiba se ta tado da zancen da bana so amma ganin ya riga da ya ganni in na ce mu juya ma ze ga ai saboda shi ne yasa nacewa me Adaidaitan ya faka na sauka ina cin magani
na biyashi ku
ɗ
in sa.
"Barka da zuwa Hajiya Halima" Abokin nasa wanda seda na sauka na gane Yahuza ne ya fa
ɗ
a yana mun murmushi, na
ɗ
auke kai sama ciki ciki nace "yawwa". Kafin na miƙawa me Adaidaita ku
ɗ
in sa Munir daya iso kusada dani ya rigani,
ɗ
ari b
iyar ya bashi sannan ya duƙa ya shiga
ɗ
aukar ledojin siyayyar dana zube a ƙasa. Murmushin sa me kyau yayi kafin yace
"Ashe kece zaki zo shiyasa na kasa tafiya". Na wuce cikin gidan ba tare da na tankashi ba ina ji ya biyo bayana. Anty Labiba na zaune kan
tudun gurin wanke wanke tana cire hancin kayan miya ta
ɗ
ago tana amsa sallamar mu.
"Aa, Munir. Ashe baku tafi ba?" Ta fa
ɗ
a tana tsame hannunta daga abinda takeyi, a ƙasa ya aje kayan yana cewa
"Eh wlh, haka nan fa muka tsaya ashe rabon na ganta ne yasa"
ya fa
ɗ
a yana nuna ni. Na tura baki gaba ina wucewa falon Antyn ina jiyo ta tana cewa
"Billahillazi dai Munir se in ce baka da zuciya, yanzu saboda Allah ba zaka bar yarinyar nan ga mata nan fululu a gari masu sonka kamar suyi me ba? Wlh idan nice kai inu
war Halima bazan sake kallo ba balle har maganar arziƙi ta ha
ɗ
a mu".
Ya shafa kansa yace
"Ba zaki gane ba Anty" se tayi saurin tare shi tace "dama ta ina zan gane? To dai tun wuri gara kawa kanka fa
ɗ
a ka nemi wata dan nan kusa banga Halima nada rabon g
ane wautar data tafka ko in ce take shirin tafkawa ba. Ita tayi asara wlh samun saurayi nagartacce kamarka me abinyi a zamanin nan" .
"Bari na wuce, adai cigaba da taya mu da addu'a a kuma sake tayani rarrashinta Anty" ya fa
ɗ
a jin zata
ɓ
aro wani zancen sa
nnan ya juya ya fita nan kuwa Anty Labiba ta dasa mitar da bata gajiya dayi tunda na watsa mata ƙasa a ido nace bana son ƙanin mijinta kuma
ɗ
an
ɗ
akinta. Seda na jiyo ƙarar tashin mota alamar sun tafi kafin na aje mayafina na, kujera na aje kusada inda ya z
ube mun kayan na shiga gaida Anty Labiba ta wani amsa mun a
ɗ
age ni se ta bani dariya ma irin wannan
ɗ
aukar dumar magaji da nishi. Shikenan kuma se akace dan ya mata dole nima ya mun in so shi? Kowa fa da ra'ayinsa a rayuwar nan, ni da wanda nake so shima
rashin zuciya yasa har ya bari maganar ta fito bayan tun ni dashi daya furta mun na sanar masa ina da wanda nake so ba kuma na ra'ayinsa.
Kayan na shiga fito dasu daga leda Anty Labiba ta kalleni tace
"Ban gaya miki karki sake zuwa gidan nan kice zak
i wa wancan santolon cima zaunen abinci ba?" Nan da nan na ha
ɗ
a rai nayi kicin kicin bata damu ba taci gaba da cewa
"Tsabar rashin sanin ciwon kai, mazan arziƙi na wahaltawa yammatansu amma shi mace ce take wahalta masa yana kwance ba cas ba as gaki yar w
ahala ki ringa dafa abinci ki kai masa ba godi bare na gode balle a baki tukuici to ba'a gidan ba dan gas
ɗ
ina bana gomnati bane kije can gidanku kiyi". Kan ince wani abu Uncle Sale ya fito daga falo yana cewa
"Meye haka Labiba?" Kitchen
ɗ
in ta dake tsaka
r gida ta shige ba tareda ta amsa masa ba na gaishe shi ya amsa yana tambayata su Anty kafin ya bita kitchen
ɗ
in ni kuma na wuce falo
ɗ
auko wayata dan na manta ban tambayi Bilal abincin me miya yake so ko kuma jallof ba.
Sau biya na kirshi be amsa ba h
akan yasa na barshi na tafi akan nayi masa jollop
ɗ
in kawai tunda na siyo kaza harda cabbage da zanyi coslow. Seda na jira Anty Labiba ta gama miyarta ta fita daga kitchen
ɗ
in kafin na shiga nawa aikin, nasan magana Uncle Sale ya mata shiyasa ta barni dukd
a haka shiga goma fita goma seta mun habaicin ni yar wahala ce ina wa wani can ƙaton banza girki, tsakani da Allah ta ina mijin da zan aura ya zama ƙaton banza? Laifi ne idan na dafa abinci na basa?
Ana kiran la'asar na kammala komai, cikin sababbin kulo
linta na shirya abincin dama na gyara ƙaramin falonta na saka turaren wuta na kulle, ban
bari ta lura ba na shige da kulolin da plates na sake kullo
ɗ
akin kafin na koma
ɗ
akin su Amir na shiga wanka. Ina tsaka da shiryawa ta shigo tana cewa
"Naga kin aje m
ana tsurar shinkafa da salad ina kazar?"
"Guda
ɗ
aya ce fa Anty" na fa
ɗ
a zuge zip
ɗ
in skit
ɗ
ina, ta ballamun harara tace
"Ko
ɗ
an tsako ne wlh se na ci, ban muƙullin falo na" sena yi waje da sauri ina cewa
"Amma tsakani da Allah dai an san abun nan na
mutum
ɗ
aya ne kuma za'a sa masa rani, bafa shi da lafiya banda ma bani da ku
ɗ
i me kaza
ɗ
aya zata masa ma" na wuce falon tareda maido ƙofa dan karta biyo no taga kulolinta ta dasa mun sabuwar tijara. Fukafukai na
ɗ
akko mata da ƙundu na zubo mata albasa da k
oren tattasan da nayi garnishing pepper chicken
ɗ
in dasu ina ajiyewa kuwa ta fara auna mun zagi wai mayya na maida ita ko me? A karo na biyu Uncle Sale daya dawo daga sallah ya sake ceto na, sanin yau weekend yana gidan ma yasa har nayi karambanin zuwa bad
an haka ba gara in zauna a gidanmu ƙarshe dai nayi raba daidain duk abinda na dafa dasu Mu'azzam amma babu wanda ze zageni ya mun gori.
Ƙ
arfe biyar Bilal ya kirani akan ya iso yana waje, na sake gyara fuska ta na ƙara turare kafin na fita bayan na gaya
wa Anty Labiba zuwan nasa ta zage ni ta zage shi sannan ta shige
ɗ
aki. A jikin sabon mashin
ɗ
in daya ce mun ya siya Lifan na tarar dashi, yasha kwalliya da wata shadda ruwan ƙasa datayi matuƙar kar
ɓ
ar kalar fatarsa me
ɗ
an duhu. Sabon askin da yayi ya ƙara
fito da tsantsar kyansa ga gemun dake ƙara matar dani a soyayyar sa se na ringa jin kamar na tafi da gudu na rungume sa ko zanji sauƙin ra
ɗ
a
ɗ
in da sonsa yake haifar mun cikin zuciyata. Cikin taku
ɗ
a
ɗɗ
aya na isa inda yake ina murmushi kamar yanda shima yake
doka mun murmushi. Cikin ƙasa da murya kamar me tsoron wani yaji abinda zan fa
ɗ
a nace
"Barka da zuwa yarimana", ya saki murmushin jin da
ɗ
i tareda gyara tsayuwarsa kafin yace
"Kin san wani abu?" Na girgiza masa kai alamar aa se ya ce
"Kaina yana ƙasa ka
wai naji wani haske ya dalle mun ido, na
ɗ
ago da mamakin wace fitila ce aka kunna haka domin dai rana tayi nisa da nan gurin balle nace kaifinta ne ya haska ni seda na kalla naga ashe kece. Kyanki da annurin fuskarki kullum ƙaruwa suke Halims, anya bazan f
ara saka baƙin glass ba kafin ƙyallin fuskarki ya makantar dani?"
Wata dariya nayi kaina ya fasu, irin kalaman nan na Bilal su suke ƙara saka naji duk duniya bani da sauran buri daya wuce na kasance matar sa idan hakan kuwa ta tabbata nasan na kere sa'
a, ni da baƙin ciki har abada domin ko babu abinci irin wannan maganganun nasa sun isa su ƙosar dani.
Cikin murya me cike da shagwa
ɓ
a nace
"Bana son wasa"
"Wane irin wasa? Kina raina irin baiwar da ubangiji ya miki ko? Baki san hasken idanunki ka
ɗ
ai s
un wadaci a zauna a cikin
ɗ
aki ba tareda an kunna fitila ba?" Ya sake fa
ɗ
a yana mun kallon dake kashe mun jiki, sena juya ina cewa
"Ni dai barni haka muje ciki kaida baka jin da
ɗ
i ka tsaya kana ta surutu"
"Au, surutu ma nakeyi ko? Shikenan bari na koma
inda na fito tunda yabonki da nakeyi sututun banza ne a gurinki" Ya fa
ɗ
a yana
ɓ
ata fuska kamar ransa ya
ɓ
aci nan da nan hankali na ya
ɗ
aga na juya da sauri ina cewa
"Haba mana ya zaka ce haka? Nifa ina magana ne akan baka jin da
ɗ
i kana gajiyar mun da ƙafa
funka da tsayuwa amma kaima kasan bana ta
ɓ
a gajiyawa da sauraron kalamanka. Ni a duniya ma bayan karatun alƙur'ani akawai wani sauti da nake mararin sauraro ne bayan muryarka?"
Yanda yayi ya tabbatar mun yaji da
ɗ
in maganata yace
"A ina zan aje mashin
ɗ
ina, ko da yake ma baki ko lura dashi ba balle ki tayani murna"
"Wlh Yarima murnar ganinka da da
ɗ
in kalamanka suka sa kai ka
ɗ
ai nake ji da gani a gabana. Mashin yayi kyau, Allah yasa lafiya ta kashe Allah kuma ya tsare ka daga sharrin ƙarfe da titi" ya am
sa mun da
"Amin Halims". Seda na bu
ɗ
e masa get ya shiga da mashin
ɗ
in kafin muka jera zuwa cikin gidan tabbas nida Bilal ha
ɗ
in nan da bature yake cewa *MADE FOR EACH OTHER*. Ko magulmata dan suke ganin bamu dace da juna ba suna fa
ɗ
ar haka ne ta wasu fusko
kin da a ganinsu muka banbanta bawai a zahirance ba domin duk wanda ya kalle mu seya ce mun dace da juna, daga kuma sanda na ha
ɗ
u dashi na yardarwa zuciyata tare aka halitto ruhikanmu babu kuma wani al'amari da ze raba mu face mutuwa.
Bilal ya ringa ka
llon falon kafin yace
"Amma gyaran gida su Anty Labiba sukayi?" Seda na miƙa masa kofin dana cika da ruwan lemon exotic me sanyi ya kar
ɓ
a kafin nace
"Eh mana, gidan gefensu ne suka fitar da rabin filinsu shine ya siya yayi ƙari. Wannan falon ma ai sabon
gini ne ka manta da babu shi"
"Lallai Alhaji Sale bayajin garin nan, a yanda ake kukan babu shi har ya samu rarar gyaran gida ba shakka ƙasar a hannunsu take" ya fa
ɗ
a bayan daya shanye lemon. Shiru na masa dan nasan yanzu ze fara surutansa da basu nake s
on ji ba, ilai kuwa yace
"Yanzu me gida kamar wannan be ishe shi ba har ƙari yayo ni
ɗ
an akurkin nawa ma tunda na kai linta na gagara cigaba, koda yake su yan oil and gas dama ai arziƙin ƙasar a hannunsu yake. Da ace muma za'a bu
ɗ
a mana mu
ɗ
an samu se kig
a a wata shida na warware har na fara aje tumbi fa".
Da "uhm" na amsa shi na sauka na fara zuba masa soyayyar jallop
ɗ
in basmati da taji gurzajjen karas da albasa na
ɗ
ora masa ƙirjin kaza in da yafi so da ha
ɗ
in coslow daya ji kwai da madara da. Tun kaf
in na gama zubawa ya sakko kan carpet ya zauna yana cewa
"Kin san fa tunda kika ce zaki mun girki ko karyawar kirki banyi ba yau ciki na empty yake" nayi murmushi na aje masa plate
ɗ
in ina cewa
"Ai da dai ka ci wani abun ko ba yawa bafa na so ka ringa ba
rin mun cikin ka da yunwa ka sani"
"Ai na
ɗ
auka da safe zaki abincin ne shiyasa da naga har goma tayi baki kirani bane ma nasha Tea" ya fa
ɗ
a yana kai lomar farko bakinsa. Yanda ya lumshe ido yana tauna abincin kana gani kasan da
ɗ
in ya kai masa ko ina, se
da yayi loma uku kafin ya kalle ni yace
"Wato Halims bana zaton a duniyar nan akwai macen data kaiki iya sarrafa abinci, wai carkwai ma
ɗ
agwai. Badan kar inyi sa
ɓ
o ba se in ce wannan abinci ko hurul'ayni ta dafa ai se haka".
Kaina ya sake fasuwa, na zub
a masa zo
ɓ
o roba
ɗ
aya ne na sata a fridge
ɗ
in Anty Labiba yana cin abincin yana santi seda yafi rabi kafin yace na sakko muci na girgiza masa kai ina murmushi naci gaba da kallonsa yana zuba loma, yanda yake cin abincin ya kamata ace ya bani haushi irin ya
nda yake cika baki kamar wanda be ta
ɓ
a ci ba amma kuma dake zuciyar cike take
da so da begensa burge ni yakeyi ina ganin so da shaƙuwar dake tsakaninmu tasa baya kunyata yake iya cin abinci a gabana. Tas ya tada abincin da iri na mu hu
ɗ
u ma ba lallai mu iy
a cinyewa ba, shi kansa ina mamakin sa dukda nasan maza suna da cin abinci amma na Bilal kam daban ne kodan yana ƙwallo ne?
Mun da
ɗ
e muna hira yana kashe ni da kalaman dake ƙara mun sonsa da ƙaguwar na zamto tasa, ina so ma sako maza zancen tunin da Ab
ba yace na masa akan turo magabatansa a saka ranar auren mu kusan wata uku kenan shiru bece komai ba, yanda yake ta sako mun ƙorafin har yanzu wata shida kenan daya samu aiki wai ba'a fara biyansu albashi ba. Sati uku baya sukaje Abuja akayi capturing nasu
IPPIS sun saka ran samun albashi a watan da aka shiga sedai shiru har anci kwana goma babu labari. Wannan dalilin yasa nake masa uzuri tunda koda ace an saka ranar bashi da ƙwaƙwƙwarar hanyar da ze tara ku
ɗ
in da ze ƙarasa gininsa har azo maganar lefe da s
auran hidimar aure. Samuwar aikin dama da ita muka dogara to gashi kuma har yanzu ba'a samu yanda ake so ba amma kuma dukda haka kamar yanda Abba yace suzo a saka rana ko da shekara biyu suka ce lokaci ne da an kirashi ze zo yafi ace ayi ta tafiya haka bab
u cigaba. Tun muna ND 2 aka kawo ku
ɗ
in aure gashi yanzu satuttuka suka rage da mu gama HND.
Duk ƙawayena da muka fara karatu tare wasu sunyi aure harda yayayensu wa
ɗ
anda basuyi ba da yawa da sa ranarsu da zarar mun ƙarasa karatu se wa
ɗ
anda Allah be kaw
o musu mazan ba, a ciki kuma zan iya cewa nice ka
ɗ
ai na fara karatu ina da tsayayyen saurayi dan tun ina SS3 muka ha
ɗ
u da Bilal lokacin daya zo NYSC makarantar mu gashi ana lissafin shekaru kusan biyar kenan