Showing 12001 words to 15000 words out of 287295 words

Chapter 5 - KURA A RUMBU COMPLETE

story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*

*WOMEN OF WORDS

WRITERS ASSOCIATION (WOW)*

*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*

*Wattpad @MaryamahMrsAm*

*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*

*Ku

ɗ

in karatu yana w

akiltar mutum

ɗ

aya ne, kiji tsoron Allah karki

ɗ

auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*

*KURA A RUMBU littafin ku

ɗ

i ne, a biya naira 800, biya a asusun*

*1840175439*

*Access bank*

*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 5*

A motar Nasir na ganshi, ya kame a ciki yanda kasan tasa. A raina nace ku

ɗ

i dai ze yi wa Bilal kyau dan kalarsu aka masa. Yanayin surarsa da irin kayan da yake sakawa ba zaka kalli gidansu kace daga nan ya fito ba. Yana son gayu, sau tari na ka

n raya a raina nan yake kashe ku

ɗ

in sa gurin siyan sutura da takalma ha

ɗ

i da agogo masu tsada duk abin da samari sa'anninsa suke yayi zaka ganshi dashi hakan kuma yana burge ni duk da ba wadata ce dashi ba amma ba yanda za'a yi ka ganshi ka raina shi.

A gaban motar nima na kame Inayah ta shiga baya muka tafi muna hirar mu gwanin sha'awa, ban tambaye shi in da zamu je ba shima be gaya mun ba har muka isa Goron dutse cikin GRA dake bayan matatar ruwa (WRECA). Na ringa kallon unguwar, a iya sani na banda k

owa a gurin shima kuma bamu ta

ɓ

a hirar wani nasu a nan

ɗ

in ba, cikin wani da ke jere da gidaje hagu da dama muka shiga, gidaje uku ne ba kammalallu ba a ciki

ɗ

aya ma kamar da mutane a ciki benen sama ne ba'a ƙarasa ba se fili da aka zagaye da alama ba'a fa

ra gina shi ba. A ƙofar kangon dake ƙarshe layin ya tsaye dake layin baya

ɓ

ullewa, ya kashe motar muka fita na cigaba da kallon gurin ganin ya nufi kofar shiga gidan ya bu

ɗ

e da muƙulli yasa muka bi bayansa se dai ban shiga ba na tsaya a waje ina kallon cik

in gidan.

"Ya kuka tsaya a waje? Ku shigo mana" ya fada bayan daya juya ya ganmu a tsaye. Se da na

ɗ

an yi jumm ina kallon cikin gidan kafin nayi bismillah na shiga. Tsakar gidan bashi da girma sosai amma ze iya cin mota

ɗ

aya ko ma biyu. Duk da ginin ba

'a kammala shi ba amma yana yin tsarin yayi kyau. Akwai babbar ƙofa dake tsakiya tana kallon get, se kuma daga gefe can akwai wata ƙofar ƙarama. Ya bu

ɗ

e babbar kofar ya shiga muka bishi, a cikin falon da ba'a yiwa fulasta ba ya tsaya yana kallona yace

"Ba

rka da zuwa gidan Bilal". Se na saki murmushi, wato nan ne gidan da yake gina mana. Ya nuna bangon hagu in da ƙofa take yace

"Bedrooms ne guda biyu kowanne da toilet, suna da girma nasan zasu ci kowanne irin saitin gado". Seya matsa ya bu

ɗ

e kofar dake ban

gon gabas yana cewa

"Nan kuma kitchen ne da store", waccen ƙofar ta waje kuma

ɗ

aki ne da falo a ciki Master room kenan ina tunanin ko a faso da ƙofa ta nan" ya nuna mun

ɗ

an corridor dake gefe yace

"Saboda sauƙaƙa miki zirga zirga tsakanin nan da can ko d

an yanayi na ruwa da sanyi". Ni dai murmushi kawai nake kamar wata sokuwa. Ya bu

ɗ

e

ɗ

akunan muka leƙa har cikin toilets

ɗ

in kamar yan da ya fa

ɗ

a suna da girma sosai kam zasu

ɗ

auki kaya har a samu gurin shimfi

ɗ

a carpet me

ɗ

an girma. Har can part

ɗ

in da yace

nasa se da muka shiga, a nan naga ya aje buhunhunan sumunti da sauran kwanon da akayi rufi dukda saman gota ce se kayan toilet da sink na kitchen.Tsakar gida muka koma ya nuna mun

ɗ

an filin dake kusa da part

ɗ

in yace

"Da nan gurin Hajja tace se ayi

ɗ

aki t

un da ga ban

ɗ

aki a tsakar gida dama ko da zamuyi baƙi maza masu kwana"

"Uhm" kawai na ce a raina ina lissafa

ɗ

an abinda nake ganin ya rage a aikin ginin. Fulastar ciki ce dan an yi ta waje da

ɗ

akuna guda biyu nawa, falo ne da kitchen suka rage se can

ɓ

a

ngaren sa.

"Yau kin ga gidanki" ya fa

ɗ

a bayan da muka zauna a mota. Nayi murmushi nace "guri yayi kyau sosai Allah ya sa rai aka yi wa"

"Amin My Halims ai se ma an gama aiki an gwagwaje gurin da kaya yan kamfani kyansa ze sake fitowa" ya bani amsa na

amsa masa da

"Haka ne, to Allah ya nuna mana lokaci". Shirun minti biyar ya gifta tsakaninmu ya ci gaba da tuƙi ni kuma na tsunduma tunanin abinda ya rage a aikin gidan yanzu wanda a gani na saura ne kawai tun da an yi me wuyar kammala ginin da rufi. Ni

duk da yake ta zancen gini na zata irin ko linta be kai ba ashe ma ƙarashe ne kawai.

"Yanzu kin ga abin da nake gaya miki na akwai sauran shiri a gaba na ko?" Ya katse mun shirun, se na kalle shi. Ya ci gaba da cewa

"Ban siyi ko kwali

ɗ

aya na Tiles

ba. Ga gilasan winduna kin ga boggler kawai aka saka. Ban da ƙarashen fulasta sannan azo uwa uba wiring

ɗ

in wuta da ruwa ga fenti dasu pop aikin fa ba ƙarami bane Halima".

Nayi kasaƙe ina sauraronsa, se da ya kai aya kafin nace

"Allahn daya hore akayi

wannan ze rufa asiri in sha Allah"

"Haka ne" ya bani amsa daga nan be sake cewa komai ba har muka je unguwar mu. A hanya muka sauka ya wuce ina

ɗ

aga masa hannu, se da na sake komawa gidansu Hansa'u cikin sa'a na tarar ta dawo nan muka zauna na shiga laba

rta mata yanda gida na yake.

"Lallai Halima ba kunya kika bishi ganin gida ko?" Ta fa

ɗ

a se na harare ta nace

"Ji banza wai kunya. Kawai naje naga gidan ne wani abu da zan ji kunya lallai ma". Seda Mama ta kira ni kafin muka fito ta rakani rabin hanya.

Sau biyu cikin zirgilli na ina kusan gaya wa Mama zancen munje ganin gidan se Allah ya cece ni na canza maganar da wata. Abin na mintsili na, nayi kamar na gayawa Anty Labiba se dai nasan yanda take a cike dani tsaf zata ha

ɗ

a ni da Mama se kawai na kama k

aina na bar murna ta a ciki na. Bilal dai da ake ganin be kai ba gashi nan cikin hukuncin ubangiji ze yi abinda kowa se yayi mamaki ga dai gida nan na nunawa sa'a da nasan iya kar masu ƙaryar ku

ɗ

in dai suyi kamar shi ko wanda be kai shi ba kuma a unguwar y

an gayu da na tabbatar ƙasa tana tsada a gurin.

Shi ma a yanda yace filin na gadon sa ne ya adana gashi kuwa ya masa rana babu yanda masu gidajen kusa dashi da ma na nesa basuyi akan ya bar musu ba har musanyan ginannen gida aka bashi da cikon ku

ɗ

i duk

yaƙi a cewar sa baze maida kamar sa ba kuma unguwar ta masa da irin tsarin rayuwar da yake so ya gudanar da iyalansa.

Watanni uku suka shu

ɗ

e cikin wata shida na ranar auren mu data rage har sannan kuma daga

ɓ

angare biyu nawa dana Bilal ba zan ce ga wa

ni shiri da aka fara na biki ba. A gidanmu dai nasan Abba ya yiwa Mama magana akan abin da ya kamata ayi tace masa suna kan lissafi ne idan ta gama ha

ɗ

a komai zata sanar masa ban sake jin sun tada maganar ba. Ina da abubuwan da nake so a mun daga kan za

ɓ

in

kayan

ɗ

aki zuwa sauran kayan amfani se dai ban ga fuskar da zan sakowa Mama maganar ba. Anty Labiba ko yanzu ban ma isa na doshe ta da wannan zancen ba tun da ƙiris take jira dama ta samu nayi mun. A haka a ka fara azumi, na ƙudurce a raina har aka sallac

e ban ga an motsa ba to fa zanyi magana se dai ace nayi rashin kunya.

A

ɓ

angaren Bilal ma dai shiru ne, nayi zaton yanda nake cike da

ɗ

oki shima hakan ce zata kasance dashi amma sam ba haka ba. Kullum yazo bashi da zance se na gini, ya rasa ya ze yi, k

aza ya ƙara tsada se ya kashe kaza akan yin abu kaza kuma shi bashi dasu ko waya ya kira ko na kira shi zancen kenan har na fara gundura da jin sa daya fara akwai se in bashi uzurin zan yi wani abu na kashe wayar. Ban sake shan mamaki ba se wata rana daya

zo bayan shan ruwa yake nuna mun ci gaban aikin da akayi a wayar sa se na ga babu banbanci da wancan zuwan da mukayi, fulasta ka

ɗ

ai aka ƙarasa se wiring

ɗ

in ruwa da yace anyi.

Rai na ya so su, tun ku san sati

ɗ

aya kenan Hansa'u take ta mun magana akan

ya kamata mu fitar da anko in gaya wa Bilal ya bani ku

ɗ

i muje kasuwa. Nasan haka akeyi to amma tausayin sa da nake ji da yanda kullum yake ƙorafin gini ya hana shi sakat yasa nace bazan tambaye shi ba ƙarshe se Abba na tambaya da Mama ta ji ma tace ba yanz

u ba in bari se bayan ƙaramar sallah tunda bikin ze kama bayan babbar sallah ne da kwana goma a lissafi. Ni ina ta tunanin ƙila ma an kusa gama fenti ashe shi tafiyar hawainiya ma yake yiwa aikin. Kasa daurewa nayi nace masa

"Yanzu tsahon lokacin nan as

he babu abin da aka ci gaba a ginin nan? Yau fa sauran kwana casa'in da biyar ace ba'a ma

ɗ

akko hanyar kammala gini ba balle a fara sauran hidimomin biki?" Se ya kalle ni yace

"Wace irin magana kike yi haka Halima? Ashe ma baki yaba abinda nake yi ba ki

n san tsadar kayan gini kuwa a wannan zamanin? Karfa ki manta Halima ni nake yiwa kaina komai ba wani bane yake tallafa mun sannan hidimar nan ba iya tawa bace ba sanin kanki ne ga auren Naja ni zan mata kayan

ɗ

aki bayan kuma albashi na kin san ba wata han

ya ce dani ta samun ku

ɗ

i ba". Nayi shiru saboda na hango gaskiya a cikin tasa maganar shima, ba shi da matallafi se Allah ga kuma hidimar ƙanwar sa kamar yanda yace ita ma abar dubace.

"Shi yasa tun farko na guji a saka mun rana ba tare da na gama shir

i na tsaf ba, kuma da aka je ma ni shakara

ɗ

aya nace aka tashi aka sa wata shida bayan an san ba lallai na shirya a wannan lokacin ba" ya sake fa

ɗ

a kamar cikin fushi. Se na kalle shi na ce

"To me kake nufi yanzu?"

"Ni babu abinda nake nufi kawai raina be

ji da

ɗ

in yan da kika raina ƙoƙari na bane har kina cewa wai duk tsahon lokaci babu abin da nayi".

Shiru kawai nayi ina kallon sa na rasa ma abin da zan ce har ya gama yayi shiru dan kansa. Haka dai ba da

ɗ

i muka yi sallama ya tafi, ko abincin da nayi niy

yar bashi ban

ɗ

auko ba shima kuma be tambaya ba, da asuba ma be kira ni ba har gari ya waye gurin ƙarfe goma se kuma duk naji na damu. Nasan dai ba wata magana na gaya masa da ya kamata ace ta masa zafi ba amma hakan nan na danne zuciya ta albarka cin son

da nake masa na kira shi.

"Raina ya

ɓ

aci Halims, ya za ayi duk fafutukar da nakeyi akan naga nayi komai cikin rufin asiri amma kina rai nawa? Ke baki ga girman gidan bane ba kiga irin tsarin da aka

ɗ

akko ba?" Ya fa

ɗ

a bayan dana gama ban baki. Nace

"G

aba

ɗ

aya ka juyawa magana ta manufa ne amma ni ban raina ƙoƙarin ka ba kawai a nawa tunanin dai zuwa yanzu ko za'a ce da sauran aiki to ƙarashe irin wanda ma be zama dole ba. Kuma ni da zan baka wata shawara kaji, me ze hana ka mayar da hankali kawai ka gy

ara iya

ɓ

angaren da zan zauna a ciki? Tun da dai mu biyu ne kawai a cikin gidan ko da ace ka gyara can

ɗ

in ma ba lallai ace za'a yi amfani dashi yanzu ba. Kawai ka barshi ka tsayar da hankalin ka a guri

ɗ

aya ina ganin ze fi".

Se yayi shiru kafin yace

"Na yi tunanin hakan amma kuma bana son raini"

"Wane irin raini kuma?" Nayi saurin katse shi, se yace

"Ba zaki gane ba. Ki kwantar da hankalin ki za ayi komai kafin lokacin, naga alamar kin fini matsuwa fa Halims to ki cigaba da daurewa saura ƙiris ba z

aki maimaita azumi a gida ba". Na rufe fuska kamar ina gaban sa nace

"Kasan bana son irin haka"

"Surutun kawai, zaki yi baya ni ne duk ranar da kika shiga hannu yarinya" ya sake fa

ɗ

a se nayi saurin datse wayar jin yana neman sakin layi da azumi a bakin m

u. Shikenan muka shirya aka ci gaba da azumi kwanci tashi har satin sallah ya kama.

Shakara biyar muna tare da Bilal be ta

ɓ

a mun toshi ba har ga Allah wannan sallar na tsammaci ze yi tun da dai yanzu ai kusan na zama tasa za'a ce se dai shiru kake ji h

ar sallah ta rage yan kwanaki babu wani labari. Ranar da ya rage kwana uku idi bayan an sha ruwa yazo kamar ko yaushe ina shirin zuwa gidan Anty Labiba zan kai mata saƙo daga nan na kar

ɓ

o mana

ɗ

inku nan mu ni da Mama. Tare da Bilal muka tafi, bamu jima ba

muka dawo tun a hanya yake ce mun wai

"Iye yar gatan Abba da Mama. Yanzu duk ledojin nan kayan sallar ki ne, ni ina nan ko rigar da zan saka naje idi bani da ita. Takaici yasa na masa banza har ya sauke ni a ƙofar gida, na shiga na aje kayan sannan na fit

o mu kan

ɗ

an ta

ɓ

a hira kafin yayi haramar tafiya, dubu uku ya bani yace gashi nan nayi kitso da lalle.

"Na bawa Hashir sautun abaya, na

ɗ

auka ze dawo lafin sallah se jiya yake ce mun wai jirginsu washe garin sallah ne kiyi haƙuri da wannan" ya fa

ɗ

a bay

an daya bani dubu ukun. Gashi dai ba wasu ku

ɗ

in azo a gani ya bani ba, a yanda nake tsaye ma ina da ninkinsu a jikina amma se naji da

ɗ

in kyautar tamkar wanda ya bani miliyan uku. Na ringa murmushi ina cewa na gode shi

kuma ya basar wai akan 3k ai ba haka y

aso ba in yi haƙuri da hakan kawai. Dana shiga gida haka na tarar da Mama ina dariya na bata ku

ɗ

in ta kalle ni ta kalle su da taji daga in da suka fito ina ga takaici ne ya saka ta dariya kawai tace ya kyauta. Washe gari tun da wuri na tafi gidan lalle kaf

in azahar an gama mun da daddare kuma naje gidan su Hansa'u ta yarfa mun kitso a nan naga abin arziƙin da Alhaji Bala ya kawo mata na toshi akwati guda harda kit kamar lefen bazawara ba abin da babu ciki tun azumi na tsakiya dama ya zo gaisuwar azumi nan m

a ya kai musu sha tara ta arziƙi naji mata da

ɗ

i amma ba wai abun ya burge ni ba dan ni dai wlh da dai na auri dattijo kamar Alhaji Balan saboda ku

ɗ

i gara in ƙare a talauci tare da wanda nake so.

Ranar idi haka na shaƙe kuloli saiti biyu da abinci,

ɗ

aya

na Bilal

ɗ

aya na Hajjan su na bawa Aliyu ne Adaidaita ya kai musu Mama dai kamar yanda tace taga ikon Allah amma tunda me kawo abincin yace babu ruwanta a bar ni nayi yanda naso sadaka ce dole ta kama bakinta tun da dama ni nasha wahalar girka miya, wai n

a da tuwo kuma matar dake mana duk sallah ce ta zo tayi. Da yamma Bilal yazo, mutumin da yace beyi

ɗ

inkin sallah ba se gashi da sabuwar kwalliya ba wadda ya turo mun hotunan idi da ita ba. Daya tashi tafiya nan ma a karon farko ya bani rafar yan naira goma

sabbi yace na bawa Imam da Amirah barka da sallah Mama kuma na gaya mata jibi zasu zo gaishe ta da abokanansa.

An ci sallah an cinye watan shawwal ya mutu har an shiga zulƙida ya raba a taƙaice ce dai ƙasa da kwanaki sittin a lissafin kwanakin ranar a

uren mu. Gidan Baba Salahu su Sauda da za ayi bikinmu tare suna ta shiru tu ni sun fitar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login