Showing 168001 words to 171000 words out of 287295 words
da muka koma Asibiti check up
a gwajin da aka mun likita yace an samu cigaba sosai sai
ɗ
an abinda baza'a rasa ba kawai yayi saura. Dukda haka can ƙasan raina ina jin Bilal sai dai tasirin addu'ar da nakeyi ya disashe duk wani abu da a baya nakeji a duk sanda na tuna shi, bana jin fari
n ciki haka bana jin baƙin ciki, gaba
ɗ
aya na zama neutral.
Dana fuskanci yawan shirun da nakeyi yake sakani tunani a dole na fara tilastawa kaina zama cikin mutane dukda na rasa yanda zanyi da Mama akan fushin da ta
ɗ
auka dani har magana nayi mata na r
oƙi tayi haƙuri idan ma wani abu na mata daya
ɓ
ata mata rai take fushi dani amma tace babu komai a hakan nake shisshige mata ina mata magana wani lokacin ta kulani muyi hira wani lokacin sai sai na haƙura na tashi, Abba dai ba ruwansa da
ɗ
i sosai yakeji da
canzawar da nayi dan haka idan yana gida muna tare dan wani lokacin har sai na gaji ma da hira nace masa zanje na kwanta kafin zai rabu dani na kuma sha jin sa yana yiwa Maman magana akan abinda yaga tana yi mun yanzu amma shima
ɗ
in sai dai tace masa babu
komai.
Yau
ɗ
in ma ni ka
ɗ
ai ce a gidan Mama sun fita tareda Zainab da Sharifa dubo Inaayan Anty Labiba da bata da lafiya. Har na shirya zan bisu kuma kawai na fasa dan na san gidan nata ba zai rasa yan dubiya dan dangin Mijinta nasa raina abun taro ciwo
n kai wani yayi har idan sun samu labari haka zasu yo ƙungiya suzo a wuni ana cecekuce.
Waya ta dake gefe ta
ɗ
auki ƙara, sunan Suhaila da na gani yana yawo ya saka na janyota na amsa da ƙaramar sallama. Daga can
ɓ
angaren tace
"Ashe bacci kukeyi tun
ɗ
az
u ina ta buga ƙofa na
ɗ
auka ma ko bakya nan". Na
ɗ
an yi shiru kafin na fahimci abinda take nufi can gidana taje dan haka nace mata
"Ai kuwa dai bana nan wlh"
"Subhanallahi, dama Honey ya mun baki yace na kiraki kar nazo bakya nan gashi kuwa, idan ba n
isa kikayi ba sai in jira ki dan wuni nazo miki yau" ta sake fa
ɗ
a a ƙoƙarin ta ƙyaleni ta tafi sai na ce
"Ai kuwa nayi nisa ina can gidanmu wlh" na ajiye wayar bayan da tace mun "toh shikenan".
Tunani na tafi bayan na ajiye wayar shin Mijinta bai fa
ɗ
a
mata bana gidan bane ko kuwa shima bai sani ba? Amma dai da wahala yanda suke da Bilal ace bai sani ba dukda dai Aisha Matar Nasir ma ba'a fi kwana uku ba ta kirani tana tambayar ina gida ne zata zo nace mata Aa, ƙila bai fa
ɗ
awa abokanan sa ba ko kuma ya f
a
ɗ
a musu matayen nasu ne basu fa
ɗ
awa ba oho musu dai.
Jin an fara shirin shiga sallah da yake juma'a ce ya saka na miƙe na
ɗ
auro alwala domin dai yanzu Alhamdulillah na hau saiti ina matuƙar ƙoƙari gurin dai daita ibadah ta da kuma yinta akan kari, ina
raka'ar ƙarshe na jiyo sallamar Suraj daga falo, sai da na sallame kafin na fito har sannan kuma yana tsaye ya ce mun wai nayi baƙuwa tana waje amma basu bu
ɗ
e mata get ba dan basu santa ba gashi kuma ni ka
ɗ
ai ce a gidan sun ce ta kira ni a waya tana ta ki
ra ban
ɗ
aga ba. Wayar na
ɗ
auko naga Suhaila ce ta kira har sau hu
ɗ
u nace ya bu
ɗ
e mata ta shigo dukda nayi mamaki ban zaci zata ce zata biyo ni nan ba.
Sai da na kawo mata ruwa na koma na zubo mana abinci kafin na zauna muka sake gaisawa tana kallo na t
ace
"Amma kinyi rashin lafiya Maman Dady?"
Nayi
ɗ
an murmushi kawai ba tareda nace komai ba ita
ɗ
in ma sakin maganar tayi ta kamo wata, bata bar gidan ba sai bayan la'asar har sannan kuma su Mama basu tafi ba sai na ringajin kamar kar ta tafi dan sosai k
uma naji da
ɗ
in zuwanta dan Suhaila akwai hira, muna tsaye jikin motarta bayan dana rakata waje ta kalleni tace
"Kinga zan manta Honey yace idan mun ha
ɗ
u da Bilal in ce yana gaishe shi kuma Allah ya bashi haƙuri idan laifi yayi masa haka da ya share shiz
toh na bar miki sallahu tunda bamu ha
ɗ
u ba" daga haka taja motarta ina tsaye harta fice daga gidan kafin na koma ciki raina cike da tunanin sallahun data bar mun. Yanda Bilal ya
ɗ
aukaka Hafiz mai zai saka ace har yana cigiyarsa a gurina? Naga kusan kullum
suna tare idan ba a office ba Bilal
ɗ
in ze je can gidansa ko gurin siyar da motocinsa, na ta
ɓ
e baki a fili na ce
"Sun fi kusa" daga haka na shiga tattare gurin da muka zauna bayan na gama na shiga kitchen na fara ƙoƙarin
ɗ
ora abincin dare ganin yamma tay
i har sannan kuma basu dawo ba.
Ranar Juma'a ta kama sadakar Arba'in
ɗ
in Mahaifinsu Zulaiha a ranar kuma kamar yanda kawunsu yayi alƙawari bayan an sakko daga masallaci
ɗ
ai
ɗ
aikun mutane suka shaid
ɗ
aurin auren Bilal da Zulaiha sai kuma Nuratu da Zahradd
ini angonga. A zauren gidansu aka
ɗ
aura auren cikin mutanen da suka halarta kuma mutum biyu ne daga
ɓ
angaren Bilal, Kawu Sani sai Baba Mudan shima kawunsu ne abokanan wasa suke da Kawu Sanin da kuna mahaifinsu Bilal. Shi ka
ɗ
ai Kawu Sanin ya kira ya shaida
masa komai suka tafi tare, basu baro gidansu Zulaihan ba sai ƙarfe biyar da wani abu saboda Kawunta daya tsayar dasu da waliyyan
ɗ
aya angon ya nemi tayar musu da sabuwar rigima akan shi fa sai dai azo a
ɗ
auke amare a yau
ɗ
in domin bai ga dalilin da zai sak
a a
ɗ
aura aure kuma a bar yara su cigaba da zama a gida ba. Daga Kawu Sanin har wa
ɗ
ancan waliyyan angon su kuma suka ce basu san zance ba domin aure yace azo a
ɗ
aura kuma sunzo yara kuma basu gama gyara in da zasu ajiye mata ba idan da yasan haka ne sai ya
bari ayi komai a nutse ba yanzu ya sake cewa zaiyi musu titsiye tofa sai a warware auren can ya aura musu duk wanda yaga dama tunda abun nasa kuma ya zama da
ɗ
iban albarka.
Kamar hatsaniya zata kaure har saida matan cikin gida dangin Mamansu da da wata
yayar Babansu suka fito ita ta tsawatarwa ƙanin nata ta basu haƙuri kafin suka watse kowa ya fito a fusace. Kawu Sani ya kalli Baba Mudan ya ce
"Anya Mudansiru mutanen nan na kirki ne kuwa? kaga fa yanda mutumin nan yake zare mana ido kamar wasu yayansa
yana fa
ɗ
a mana maganganu, ni wlh shaf na sha'afa na tambayi yaron nan ya ma yi bincike da kyau akan asalin yarinyar ko kuwa dan ni kwatancen da ya mun sai da muka zo naga ashe ba Sulaimanun da nake zato bane Babannasu". Baba Mudan yaja numfashi ya ce
"G
askiya dai wannan ƙanin uban nasu ba za'a kwashe da da
ɗ
i dashi ba mutum ba lafazi ba magana mai da
ɗ
i wai mu muka sani idan ma sama zamu kai su shi dai a kwashe masa yara daga gida ya dena ganinsu ni wlh sai naga ma kamar ba cikakkun hausawa ba ƙirar jikins
u tafi kama data gwarawa". Haka suka cigaba da tattaunawa har suka
ɓ
ullo layin su Anty Labiba, a ƙofar gidan suka ci karo da Mama suna shirin shiga mota Anty Labiba na jikin get ta rako su. Maman ta gane shi tsaf saboda shi ya ringa zarya lokacin auren Hal
ima da Bilal, suna ha
ɗ
a ido kamar mara gaskiya yayi saurin
ɗ
auke kai gefe kamar bai ganeta ba harda ƙara sauri suka wuce.
Anty Labiba da taga ta bisu da kallo ta tambayeta ko ta sanshi ne ta ce
"Surukin Halima ne ƙanin Babansu Bilal shi yayi masa walic
ci ma", Anty Labiba ta saki wani murmushi ha
ɗ
i da girgiza kai tace
"Allah sarki, ƙila bai ganeki bane" Maman ta bata amsa da cewa
"Da alama" sannan ta bu
ɗ
e mota ta shiga, Anty Labiba ta zura kai ta window tace mata
"Wai ya kuwa zo Bilal
ɗ
in ko har yan
zu?"
"Ina fa yazo Labiba?" Mama ta bata amsa sai ta ta
ɓ
e baki tace
"Toh Allah ya rufa asiri bari na koma kar su ce na barsu su ka
ɗ
ai" daga haka ta koma cikin gida Mu'azzam ya tayar da mota suka wuce.
Sanda suka dawo har na sauke jollop
ɗ
in shinkafar
da nayiz naji da
ɗ
i sosai yanda Mama ta nuna jin da
ɗ
in girkin da nayi, a daren har hira mukayi na gaya mata zuwan Suhaila, ina so in mata zancen Hafiz da yake cigiyar Bilal kuma naji tsoro kar na
ɓ
ata
ɗ
an shirin da muka fara sai kawai nayi shiru.
A
ɓ
anga
ren Bilal kuwa wunin Juma'ar cur kashe wayarsa yayi yana kuma gida sallar Juma'a kawai ya fita ana idarwa kuma ya dawo ya sake kulle ƙofa, sanda Suhaila taje ma yana ji har ta gama bugu ta haƙura ta tafi ya
ɗ
auka matan unguwar ne masu zuwa gulma da sunan t
ambayar ko Halima ta dawo shiyasa ko za'a fasa ƙofar saboda bugu yana ciki ba zai ta
ɓ
a amsawa ba balle ya bu
ɗ
e. Shi yanzu ko mazan layin ma ba duka yake gaisawa dasu ba, sai kace akansa aka fara samun sa
ɓ
ani da mace har tayi yaji kowa da dogon bakinsa sai
ya tare shi yace zai masa fa
ɗ
a wai bai kyauta ba ganin suna nema su raina masa wayau ya saka ya dena tsayawa idan zai fita a mota glass
ɗ
in sa a sama haka idan ya dawo in kuwa tafiyar ƙafa ce ko zuwa masallaci nan ma zai ha
ɗ
e fuska ta yanda ko ka masa maga
na zaiyi kamar bai ji ba ya share.
Yau
ɗ
in ma sai da akayi magriba kafin yayi wanka ya shirya cikin wata sabuwar shadda yayi kyau sosai kuwa ya hau mota ya fito. Jin sa yake kamar wani sabon mutum musamman daya kunna wayar sa saƙon Kawu Sani ya shigo ya
na sanar masa an
ɗ
aura aure idan ya kunna wayarsa kuma ya kira shi ko kuma yaje gida ya same shi, itama Zulaihan ta yiwo masa text mai nuna zallar farin cikin ganin wannan rana a rayuwarta da kuma ƙorafin rashin halartarsa gurin
ɗ
aurin auren.
Gidan Kaw
u Sanin ya fara zuwa, a waje suka ha
ɗ
u zai tafi sallar isha'i dan haka suka wuce masallacin tare sai bayan da aka idar kafin suka ke
ɓ
e Kawu Sani na kallon sa yace
"Munje an
ɗ
auro aure amma fa wannan Kawun nata yaso ya mana hauka wai sai mu jira mu taho da
ita su ba za'a bar musu ya a gida ba bayan an
ɗ
aura mata aure".
Ido ya bu
ɗ
e da mamaki kafin ya ce
"Sai kuka ce masa me Kawu?"
"Mai zamu ce masa kuwa? Muma bu
ɗ
e masa ido mukayi tunda munga abinda yafi ganewa kenan dan waliyyin
ɗ
aya yaron ma cewa yay
i sai a warware auren tunda abun nasa ya zama da iya shege a ciki idan yaso in an shirya gaba
ɗ
aya sai a dawo ayi". Bilal ya shafa kai yana murmushi Kawu Sani ya cigaba da cewa
"Ni wlh duk sai jiki na yayi sanyi da al'amarin, anya kuwa ba gidan ƙananan
mutane ka nemo auren nan ba Bilal?"
"Shi
ɗ
in shine me matsala Kawu dan baka san irin wahalar da suke sha a hannun sa bane wlh mutumin bashi da kirki amma mahaifinsu ai kace k sanshi mutumin kirki ne haka mahaifiyar su ita kanta yarinyar na gaya maka munf
i shekara goma tare tun tana yar yarinya dan haka halayyarta babu wacce ban sani ba babu wata matsala wlh" Bilal yayi saurin fa
ɗ
a, Kawu Sani ya gya
ɗ
a kai ya ce
"Toh Allah ya tabbatar da Alkhairi ya sa anyi a sa'a, gobe idan Allah ya kaimu zanjw in samu Ha
jjan in mata bayani".
Sosai yayi masa godiya kafin ya cika shi da ku
ɗ
a
ɗ
e sukayi sallama ya wuce yana jin farin ciki na ratsa shi ta ko ina.
Gidan su Zulaihan ya wuce dan bashi da wani buri kuma a yanzu illah ganin fuskarta kuma a matsayin matarsa. A
kan kwana sukayi clashing da Alhaji Saleh da Anty Labiba, fes ya gansu kamar yanda suma suka ganshi sai da yaji kamar yayi reverse ko yayi layar zana ya
ɓ
ace
ɓ
at kawai daga gurin. Tun da suka dawo unguwar duk ranar da zaizo gurin Zulaihan tunda aka tashi h
anyar da ake shigowa ta can baya sai yayi doguwar Addu'ar Allah ya sa
ɓ
a ha
ɗ
uwar sa da duk wani wanda ya sanshi a unguwar kuma yana cin sa'a addu'ar sa tana kar
ɓ
uwa dan sau
ɗ
aya ya ta
ɓ
a ha
ɗ
uwa da Alhaji Salen har suka gaisa a lokacin ya ce masa gurin wani a
bokinsa ya zo can ƙasansu bai kuma damu ba dan ya san ba lallai ma ya ce mata ya ganshi ita
ɗ
in ma sau
ɗ
aya ya ta
ɓ
a hangen motar ta lokacin ma da mashin yake zuwa ya kuma gota gidan sosai ya waigo ya hango ta fito ya san kuma bata ganshi ba amma a yau
ɗ
in
sai yake jin kamar duk wanda ya kalle shi zai gane abinda yake faruwa.
Haka yaja mota jiki ba ƙwari ya wuce yana hangensu ta mirror, ita kuwa yi tayi tamkar ma bata ganshi ba har sai da Alhaji Saleh yace mata
"Kamar Bilal ne ya wuce a waccen motar ko?
"
Ta
ɗ
an juya ta kallo bayan motar tace
"An ya kuwa? Bilal ai bashi da mota".
"Ina ganin sa jefi jefi a wannan motar, a nan
ɗ
in ma mun ta
ɓ
a gaisawa sau
ɗ
aya yace gidansu wani abokinsa yazo can ƙasa". Cikin rashin mayar da hankali tana danna waya ta ce
"Allah sarki".
Bilal kuwa ganin Zulaiha ya mantar dashi ha
ɗ
uwar su dasu Anty Labiba. Sun da
ɗ
e a mota suna hira cikin shauƙi dan basu farga da lokaci ba har sai da Ummansu ta turo Nuratu ta buga musu glass lokacin sha
ɗ
aya har da rabi da wasu mintuna
kafin ta wuce ta barshi yana ƙoƙarin saita nutsuwarsa kafin ya tayar da motar ya wuce gida. A hanya yana tafe shi ka
ɗ
ai yana tunani, so yake ya kori waswasin da shai
ɗ
an yake ƙoƙarin cusa masa amma kuma tunanin yana nema yafi ƙarfin sa.
Bai tsammaci ya
nda Zulaihan ta sake dashi a tashin farko da irin ha
ɗ
in kan da ta bashi ba. Sai ya tuna irin wannan ha
ɗ
uwar tasu ta farko da Halima, yanda ta ringa rawar jiki a lokacin har ƙarar bugun zuciyarta ya ringa ji numfashinta yayi
ɗ
umi baka buƙatar a fa
ɗ
a maka a
matuƙar tsorace take lokacin. Sun fi ƙarfin wata shida kafin ta fara gane kan harkoki sosai dan ko kiss bata iya ba shi ya koya mata fara tarayyarsa da Jalilah kuma ya sake fayyace masa tsakanin macen da ta saba da maza da yawa da kuma wacce namiji
ɗ
aya ta
sani, akwai banbanci sosai domin duk ƙwarewar matar aure ba zata kamo ƙafar macen bariki ba.
Guri ya samu yayi parking abubuwan da suka gabata suka fara dawo masa daki daki. Ita ta fara kawo hannu jikin sa, shi bai ma yi niyyar yi mata wani abu ba a y
anzu ba bayan riƙe hannunta amma ta ringa shige masa ƙila da bai kama kansa bama ya biye mata da a motar zasuyi mai gaba
ɗ
ayan. Ji yayi zufa ta fara tsattsafo masa duk da sanyin AC da ta cika motar, can wani
ɓ
angare na zuciyarsa ya ayyana masa ba abinda ya
ke zato bane Zulaiha ba zata ta
ɓ
a zama irin wa
ɗ
annan matan ba. Ya santa tun ƙuruciya ya kuma yarda da tarbiyyarta hakan ba zai ta
ɓ
a kasancewa halinta ba. Da wannan tunanin ya ringa tausar kansa har ya samu nutsuwa duk da ba wai tunanin ya barshi gaba
ɗ
aya
bane ya kasa cire kokonton gaba
ɗ
aya amma ganin idan ya bari shai
ɗ
an yayi galaba akansa ya saka masa wasi wasi na banza wanda ba gaskiya ba dole ya kore komai ya tada mota yaci gaba da tafiya.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MAR
YAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare