Showing 267001 words to 270000 words out of 287295 words
ya rufa asiri amma dama na san sai anyi haka?"
"Sai anyi haka dame? Wai mai aka rubuta dan ubanka ka wani ninketa ba kai mana bayani ba?" Hajja ta zaburo masa, ya zauna yana
cewa
"Sammaci ne daga kotu, gidan da wannan budurwar tasa ta siya ya siyarwa da wani mutum ba tareda ta sani ba, yanzu kuma ita ta siyarwa wani dan haka wanda ya siyarwa ya makashi a kotu bisa zargin damfara. Ɗayar takardar kuma ita budurwarce ta yi ƙa
rarsa itama akan zargin sata, da kuma yaudara da zamba cikin aminci".
"Amma Allah ya tsinewa wannan yarinyar Jalilah, dama ashe ta shigo rayuwarmu ne dan ta jefa mu a masifa ta lalata mun
ɗ
a shine yanzu zata masa sharri ta ha
ɗ
ashi da hukuma saboda bai a
ureta na ko me?"
"Wlh na sharri ta masa ba duk abinda ake zarginsa ya aikata da bakinsa duk ya fa
ɗ
a mun, yanzu dai ku nemo shi kawai dan wannan sammacin ma na biyu ne kuma da garga
ɗ
i kotu zata iya
ɗ
aukar kowanne mataki idan bai bayyana gabanta nan da kw
ana biyu ba" Abubakar ya sake fa
ɗ
a yana duba takardar. Hajja ta fashe da kuka tana salallami duk sai jikin Anty Amina yayi sanyi tace
"Ba kuka zakiyi ba Hajja addu'a ya kamata kiyi"
"Yana zaman-zamansa yana lalla
ɓ
a rayuwarsa da yar matarsa haka kawai
ya rakitowa kansa masifa, ina amfanin tarayya da wannan shai
ɗ
aniyar yarinyar gashi yanzu tana nema ta tozarta mu ta jefa shi a masifa? Ni wlh tun ganina da ita dama hankali na bai kwanta ba, kawai dan shi
ɗ
in yace ba komai ne amma dama matan Habuja tun du
niya na kwance ma makiraine, mutanen da suke kashe mazajensu dan suci dukiya balle kuma yanzu da duniya ta tashi tsaye makirci ai sai wanda aka gani ni dai Allah ya isa tsakanina da ita wlh" Hajja ta sake fa
ɗ
a cikin kuka.
"Daga baya kenan, yanzu dai ki
gwada duka layukansa da kike dasu ki fa
ɗ
a masa ya dawo ayi komai a mutunche idan kuma ya za
ɓ
i asirinsa ya tonu kowa ya san halin da ake ciki shikenan" Abubakar ya fa
ɗ
a yana ficewa.
Anty Amina ce ta shiga kiran wayar Bilal amma layukansa biyu da take da
duk aka ce a kashe suke, ta kalli Hajja dake shar
ɓ
ar kuka kamar yar yarinya tace
"Hajja baki da wani layin nasa ni na kira wanda nake dasu duka a kashe"
"Guda biyu ne MTN da Airtel nima su
ɗ
in ne" ta bata amsa tana fyace majina. Anty Habiba ce tace
"Toh kin tambayi ita matar tasa ko ta san inda ya tafi?"
"Tace dai bata sani ba amma ban sani ba ko ƙarya takeyi" Hajja ta bata amsa dai-dai nan Abubakar ya dawo falon ya zauna yana cewa
"Kun same shi?"
"Aa duka layukansa a kashe suke" Anty Amina
ta bashi amsa a sanyaye, ya ce
"Ku kira Anty Halima ko zaku samu wata number".
Su ukun suka ha
ɗ
a baki gurin cewa
"Halima?"
"Eh, akwai wani layi da ya
ɗ
an yi amfani dashi can da da
ɗ
ewa, na duba shi naga banyi saving ba amma ƙila a samu a gurinta ita
" ya sake fa
ɗ
a.
"Ga matarsa wacce Halima za'a samu number sa a gurinta?" Anty Habiba ta fa
ɗ
a, ya kalleta ya ce
"Kada kiyi mamakin ta san inda yake yanzu haka"
"Sai ta yuwu dan zata rufa masa asiri ko mutum ya kashe" Hajja ta fa
ɗ
a a sanyaye, ya mi
ƙ
e yana cewa
"Kuma da Kinsan da haka kika goya masa baya ya rabu da ita, matar da duniya ma ta shaida abokiyar rufin asirice. Ai dai wlh ya tafka asara, gashi nan ya ƙare da yan balaja'u a gida da waje".
"Ni dai ba zan kirata ba wlh" Anty Amina tayi
saurin fa
ɗ
a ganin Hajja na kallonta, sai ta
ɗ
auki wayarta tana cewa
"Bu
ɗ
o mun lambar ni na kira".
HALIMA
Ajiye cokalin hannuna nayi ina
ɓ
ata fuska nace
"Ni dai ka daina kallona idan ba so kakeyi na ƙware ba"
Ɓ
ata fuska yayi ya ce
"Na gaya miki b
a zan iya daina kallonki ba Leemah". Sai da na lumshe ido kafin na bu
ɗ
e su akansa ina cewa
"Toh na ƙoshi" yayi saurin tashi daga kan kujerar sa ya nufo ni yana cewa
"Ai kuwa baki isa ba, harfa kakarin amai kikeyi saboda yunwa kuma ko spoons biyar bakiy
i ba kice kin ƙoshi? Ashe zan yi miki
ɗ
ura kuwa" ya ƙarasa yana na
ɗ
e sleeve
ɗ
in farar rigar jikinsa. Ji nayi kamar in tashi na taka rawa amma na kanne na
ɓ
ata fuska nace
"Allah Uncle Salman na ƙoshi, ka fa bani tea ko ka manta?"
Ƙ
arar da wayata dake a
je kan table tayi ya saka duk muka kalli gurin, sunan Hajja na gani yana yawo, na
ɗ
ago wayar ina bu
ɗ
e ido dan na tabbatar da ita
ɗ
in ce ko kuma idanuwane suke gizo? Ganin kiran na neman katsewa ba tareda na amsa ba Dr Salman dake tsaye kaina ya zare wayar
daga hannuna ya amsa tareda sakata a speaker.
Muryar Hajja ta cika kunnuwanmu ta rafka sallama kafin tace
"Hello Halima kina ji na?"
"Ina jin ki Hajja ina wuni?*" Na fa
ɗ
a bayan dana amsa mata sallamar, ta amsa da
"Lafiya lau, ya su Aminu da Sharif
a? Duk suna lafiya ko?"
Sai naji wani banbarakwai, ashe sun san da yayansu a hannuna? Shiru nayi ban amsa mata ba ta cigaba da cewa
"Dama lambar Bilal nake so ki tura mun, banda Mtn
ɗ
in sa da Airtel idan kina da wata daban su duk ba'a samunsa a su"
"Ai ni banida kowacce number sa ma yanzu Hajja" na bata amsa a dake, tayi shiru kafin tace
"Abubakar yace ba zaki rasa ba, ki taimaka wata matsala ce ta taso kuma ana ta nemansa a waya ba'a samunsa idan kuma kin san inda yake kawai ki fa
ɗ
a mana aje a sam
e shi"
Na saci kallon Dr Salman daya koma kujerarsa ya kafeni da ƙananun idanuwansa kamar farin shigar maita kafin nayi ƙasa da kai nace
"Sai dai ki kira Yaya Nasir ba zai rasa sanin inda yake ba ko ya baku number" sai tayi jumm kafin tace
"Shikenan
, kya gaida Mamarku sai anjima" daga haka ta katse wayar.
"Tashi mu tafi toh" Dr Salman ya fa
ɗ
a yana miƙewa tsaye. Na kalleshi, fuskarsa ta canza, yar fara'ar da yakeyi tunda na shiga office
ɗ
in duk ta gudu ya dawo boss
ɗ
in sa ga ƙananun idanuwan sun s
ake ƙanƙancewa. Ganin banida niyyar tashi ya saka ya wuce yana cewa
"Ki sameni a mota" ya fita ya barni.
Kada wadda ta tambayeni mai yake faruwa ko yaushe aka fara? Nima ban sani ba kuma daga nan zamu tashi
😂😂😂😂
*KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBU
TAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu
yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*Zanyi amfani da damar nan in roƙe ku, Dan girman Allah kada wacce ta ha
ɗ
a mun Document. Ban ta
ɓ
a yin Allah ya isa ba ko wata mummunar addu'a akan fitar mun da rubutu ba tareda izinina ba amma Allah ya sani ba zan yafewa duk wacce ta ha
ɗ
a mun Document ba.
Dukkanmu musulmi ne mun kuma san girman haƙƙi dan haka mu kiyaye.*
*PAGE 59 (SECOND TO THE LAST PAGE)
Sai dana tabbatar ya fice daga building
ɗ
in gaba
ɗ
aya kafin na fita daga office
ɗ
in ina kalle-kalle kamar mara gaskiya, ganin babu kowa ya saka na
shige Elevator da sauri, a reception na ha
ɗ
u da Juwairiyya ta kalleni fuska ba yabo ba fallasa kafin tace
"Ina kika tafi tun
ɗ
azu?"
Wucewa nayi ba tareda na bata amsa ba ta sake cewa
"Dr Sulaiman yana neman ki?" Na amsa da "Toh" ba tareda na tsaya ba
na fita.
A can kan hanya ya tarar dani, fuska ba annuri ya sauke glass yana kallona kafin ya ce
"Get in".
"Amma cewa nayi ki sameni a mota ko?" Ya fa
ɗ
a bayan dana zauna, na kalli gefe na ce
"Ni fa gaskiya bana son abunda kakeyi, yanzu wane ka
llo kake so a ringa yi mun kawai a wani ringa ganinmu tare?"
"Ko?" Ya fa
ɗ
a yana
ɗ
age gira
ɗ
aya, na tura baki cike da shagwa
ɓ
ar dana da
ɗ
e da daina yinta tun lokacin da Bilal yace haushi nake bashi idan ina abu kamar wata sakaltacciyar yarinyar idan ma k
uma nayi ko a jikinsa, sai yanzu da naga alamar idan nayi zan samu kulawa na
ɓ
ata fuska na ce
"Ni dai dan Allah ya zama sirri bana so kowa ya sani"
"Hakan yana nufin kin amsa tayi na kenan?" Ya fa
ɗ
a yana mun wani kallo da najishi har cikin jini da
ɓ
argona. Nayi ƙasa da kai ina sakin murmushi ba tareda nace komai ba,
"Leemahh.." ya kira na
ɗ
aga kai kamar mai ciwon wuya na saci kallonsa, yanda ya kwanta cikin kujera yana mun wani lalataccen kallo ya saka nayi saurin sauke kaina ƙasa ya sake maimaita k
iran sunan da sautin daya fi na farko taushi kafin ya ce
"Kin kar
ɓ
i soyayyata dagaske?"
Na sanya tafukan hannayena biyu na rufe fuska ina sakin murmushi kamar wata wawuya, ina jin nasa sautin murmushin kafin ya tayar da mota muka bar gurin. Har muka i
sa gida babu wanda ya sake cewa komai a tsakaninmu, lokaci-lokaci muna ha
ɗ
a ido tareda sakarwa juna murmushi. A hankali na ce
"Gobe bani da aiki" ina ƙoƙarin bu
ɗ
e motar amma najita a kulle, ganin kuma bai yi yunƙurin bu
ɗ
ewa ba ya saka na koma na zauna ina
kallonsa.
"Wanene Bilal?" Ya fa
ɗ
a ba tareda ya kalleni ba, nayi shiru ina kallonsa, ganin ya juyo ya sa nayi saurin sauke kai ƙasa ina jin idanuwansa na yawo a kaina. Kusan minti uku bai sake cewa komai ba alamar amsata yake jira kafin a hankali nace
"Babansu Al'amin ne".
Wani shirun ya sakw ratsawa kafin ya mula yace
"Ina da kishi sosai Leemah, bana tunanin akwai wani abu da yayi saura a tsakaninku; idan ma kuma akwai ina so ki gaggauta datse shi ko kuma ni ki datse ni"
Da sauri na kalleshi
jin abinda ya fa
ɗ
a, ya mun kallon dake tabbatar da gaskiyar maganarsa kafin ya cigaba da cewa
"Har idan mahaifiyarsa zata kiraki tana tambayarsa kenan kuna tare"
"Wlh bama tare, ni rabona dashi tun ranar daya sakeni ko yanzun ban san dalilin daya sa
ka ta kirani ba" nayi saurin fa
ɗ
a har muryata tana rawa.
Murmushi mai kyau Salman ya saki kafin yace
"Na yarda". Na saki ajiyar zuciya ina dafe goshina take kuma haushin kaina ya rufeni, to rikicewar da nayi mata mecece? Sai kace wacce Alƙali ya rutsa
. Wata jakar takarda ya
ɗ
akko a kujerar baya ya
ɗ
ora mun a cinya yana cewa
"Gobe zan koma Abuja, ya kamata idan na tafi a ƙalla na
ɗ
auki tsayin wata biyu ko sama kafin na waiwayo Kano amma babu hali tunda na ajiye mutum"
Nayi murmushi jin wai ya ajiy
e mutum kafin a hankali nayi masa godiyar abinda ban san ko menene ba, da kansa ya fita ya bu
ɗ
e mun ƙofa na fita ina jina kamar wata sarauniya, sai da na shiga gida kafin ya ja motar ya wuce nima na shige ciki.
Anty Labiba na zaune a kan kujera tana wa
ya dan haka na wuce ciki kawai bayan na mata sannu da gida, kayan jikina na shiga ragewa na tafi tunanin da Dr Salman ya hanani yi.
Mai ya faru ake neman Bilal har Hajja zata kirani? Na zauna gefen gado, saƙon daya turamun ranar nan ya fa
ɗ
o mun a rai s
ai naji hankalina yana so ya tashi. Wayata na
ɗ
auka na shiga Whatsapp na lalubo chat
ɗ
in, bai sake mun magana ba tun waccen ranar. Na shiga sake biya saƙon, matsalar mecece? Na shiga tambayar kaina amma bani da amsa dan haka na ajiye wayar na shiga wanka i
na jin yanayi na gaba
ɗ
aya ya canza daga farincikin dana shigo dashi zuwa damuwa.
Haka na ƙarasa yinin ranar sukuku sai bayan Magriba da Faisal ya zo ne ma na zauna muka
ɗ
an yi hira amma ina kwanciya na sake shiga tunanin, kasa bacci nayi daga ƙarshe n
a bi abinda zuciyata take ta saƙamun. Sai da na murza key a ƙofa kafin na shige ban
ɗ
aki na lalubo number na kira. Ringing biyu aka
ɗ
aga, daga can ya kira sunana ya ce
"Haleems! Dama na san ba zaki rabu dani ba dole zaki nemeni".
"Kana ina? Mai yake far
uwa" Na fa
ɗ
a, ya marairaice murya yana cewa
"Maganar ba zata yuwu a waya ba My Haleems muna buƙatar mu zauna idan kin amince zaki zo zan turo a
ɗ
auki gobe".
Cikin kaushin murya nace
"Babu wani abu da yayi saura tsakanina da kai Bilal, Hajja ta kirani
tana neman number ka daga yanayinta kuma na fahimci akwai wani abu da yake faruwa shiyasa kawai na kiraka".
Murmushi yayi kafin ya ce
"Ni dama na san ba zaki daina so na ba Haleems, kada ki biyewa su Anty Labiba kin sani dama tun usuli bata ta
ɓ
a son ta
rayyata dake ba. Ina sonki, kuma nayi nadamar duk wasu abubuwa sa suka faru a baya and nayi miki alƙawarin soyayya da farinciki mara yankewa har idan kika dawo gareni kiyi haƙuri kinji My Haleems".
Zare wayar nayi daga kunnena, har zan kashe sai kuma na
fasa naja numfashi na ce
"Ba zan iya zuwa in da kake ba, amma ka fa
ɗ
a mun abinda yake faruwa idan ina da halin taimaka maka zanyi"
"Wata yar matsala ce ta faru, wasu ku
ɗ
i Jalilah ta bani nake juyawa kuma tsautsayi ya fa
ɗ
a musu suka narke shine ta mak
ani a kotu akan na biyata ku
ɗ
in sannan akwai gidanta da yake hannuna shima da aka siyar ban sani ba ashe gidan takaddun bogi yake dasu yanzu kuma ta zagaya ta sake siyarwa da wani daban ta ha
ɗ
ani rigima da wanda ya siya a hannuna" ya fa
ɗ
a tamkar zai fashe
da kuka.
Tunda ya ambaci sunan Jalilah wani abu mai
ɗ
aci ya taso ya tsaya mun a maƙogaro, ba abinda nake gani sai hotonsu ganin da nayi masa na ƙarshe yana kwance akan cinyarta, daƙyar na bu
ɗ
e baki na ce
"Ashe baka rabu da wannan matar ba Bilal?"
"
Wlh na rabu da ita Halima shiyasa nace miki ina so mu ha
ɗ
u akwai maganganu da yawa da nake so na fa
ɗ
a miki wanda ba zasu yiwu a waya ba" yayi saurin tarata, na ja hanci saboda hawayen da suke neman ƙwace mun na ce
"Ya kamata tuntuni ka san cewa alaƙarka
da ita ba zata ta
ɓ
a kasancewa mai riba ba, ka biye mata ka kaucewa haryar Allah da tarbiyyar addininka, da aurenka Bilal ka za
ɓ
i bibiyar macen banza a waje mai ya sa? Dame na rageka?" Na ƙarasa ina sakin kukan dana kasa riƙewa.
Shiru yayi kafin a hank
ali ya ce
"Kiyi haƙuri Halima, tabbas na zalinceki kuma nayi nadamar duk abubuwan da suka faru a baya, dagaske nakeyi ki yafe mun nayi miki alƙawari abinda ya faru a baya ba zai maimaita kansa ba"
"Yanzu kana ina?" Na fa
ɗ
a bayan dana tsagaita kukan, ya
ɗ
an yi jumm kafin ya ce
"Ina Minjibir zaki zo?"
"Hajja tana nemanka kuma hankalinta a tashe yake ya kamata ka kirata ta san kana lafiya" na fa
ɗ
a ina jin yana ƙoƙarin sake yin magana amma na katse wayar take kuma nayi blocking layin. Kwanciya nayi lamo
cikin yanayin da ni kaina bazan iya fasaltawa ba ina sauraron bugun da zuciyata takeyi. Na rasa yanda zanyi in daina jin sa a zuciyata, ina jin haushinsa da zafin abinda ya aikata mun amma kuma zuciyata ta kasa daina sonsa.
Vibration wayar ta shigayi n
a
ɗ
agota na duba, nayi zaton shi ya canza layi ya sake kira amma sai naga Dr Salman ne. Sai da na duba agogo sha biyu saura kwata kafin na tashi zaune dakyau na amsa murya can ƙasa kamar wadda ta farka daga bacci nayi sallama.
"Bacci kikeyi?" ya fa
ɗ
a ba
yan daya amsa sallamar na bashi amsa da
"Eh" mukayi shiru, kusan minti
ɗ
aya kafin yaja iska yace
"Baki kirani kinji ya na isa gida ba anya dagaske na samu kar
ɓ
uwa kuwa Leemah?"
Kunya naji a hankali nace
"Kayi haƙuri mantawa