Showing 150001 words to 153000 words out of 287295 words
da mutunchi bani ba. Duk inda kika
ɗ
auki laifina kika kai kafin a saurareki sai an miki dariya ko kin manta kin za
ɓ
eni akan kowa da komai naki? Duk kuma aje a dawo ba zaki ta
ɓ
a iy
a rayuwa babu ni ba dan haka za
ɓ
i ya rage naki ko kiyi haƙuri da abinda kika gani mu cigaba da zamanmu cikin rufin asiri ko kuma ki tafi ki zubar mana da mutunchi kuma ki dawo
ɗ
in mu zauna, za
ɓ
i ya rage naki" ya ƙarasa yana watsa hannaye alamar matsalata c
e ba tashi ba kafin yasa kai ya fice daga
ɗ
akin.
Ban ta
ɓ
a riskar dare mai tsayi irin na ranar ba, na ringaji inama ina da ikon janyo safiya ko kuma na fito da masu abin hawa domin na samu wanda zai kaini gida? A cikin dare na ha
ɗ
a mana kaya na fitar das
u barander na ajiye dan na ƙudurce ko da jinin jaka Bilal ya tsafance ni da yardar Allah sai na karya asirin yau na bar masa gidan sa koda kuwa hakan yana nufin tsayawar numfashi na a doron ƙasa. Ƙarfe shida na goya Sharifa daƙyar dan tun cikin dare ciwon
kai da zafin ƙirji ya sake dawo mun, na riƙe hannun Al'amin dake tafiya daƙyar dan ko farkawa baiyi daga bacci ba ni na
ɗ
aga shi na aje shi kan ƙafafunsa. Muna fitowa falo naji ƙarar bu
ɗ
e Get, wani dunƙule ya taso daga cikina ya tsaya mun a maƙogaro.
H
aka na ringa jansa muka fito daga falon lokacin har ya fita da mota ya dawo yana zuge Get
ɗ
in na kalli kan Barander inda na aje kaya basa nan sai ji nayi ya ce
"Gasu can a mota muje na kaiku tunda kin san babu yanda za'a yi ku fita da sassafen nan da kaya
duk yan unguwa suna kallonki".
Nayi murmushin da yafi kuka ciwo, wato maganar yan unguwa yake gudu amma baya kunyar ubangijin sa yake kiran Zina da Normal abu. Ina buƙatar na isa gidan da wuri na san kuma tafiyar tawa bata dame shi ba zai ma fi farin
ciki da hakan shiyasa na yarda na shiga motar muka tafi. Har muka isa gidan babu wanda ya cw uffan a tsakaninmu har muka isa ƙofar gidanmu. Ina ƙoƙarin bu
ɗ
e motar naji ya ce
"Ina sake jaddada miki dariyar da za'a miki sai tafi laifina da zasu gani yawa, i
nfact sai kin tsani kanki Halima muddin aibu na ya fita daga bakinki" sai na waiwaya na kalle shi na ce
"Barazana kake yi mun kenan?" Ya
ɗ
age kafa
ɗ
a n ƙarasa
ɓ
alle murfin motar na fita ban ko lura da Abba dake tsaye bakin Get da maƙwafcinmu Alhaji Bala su
na magana ba na shige ciki.
A tsakiyar falo na kwance goyon Sharifa dan ji nake kamar zan fa
ɗ
i na mutu a gurin kai tsaye kuma na shige tsohon
ɗ
aki na sama sama ina jiyo kamar muryar Amirah tana kiran sunana amma ban tsaya ba.
[5/19, 22:05] Buhainat: *
KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da
izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaida
r biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 35*
Amirah ta
ɗ
aga Sharifa data saka kuka daidai lokacin da Mama ta fito daga kitchen lokacin kuma Al'amin shima ya shigo Suraj na biye dashi da akwatin mu.
"Ku kuma daga ina haka da sassafe?" Mama ta tambaya
, Suraj ya ajiye kayan yana cewa
"Tareda Babansu suke" ya juya ya fita sai Amirah tace
"Yaya Haliman tana ciki itama". Tsaye Mama tayi kafin tace
"Toh lafiya dai?"
"Gaskiya ba lafiya ba kinga fa jefar da Sharifa tayi ta wuce ina mata magana ko sauraro
na ma batayi ba" Amirah ta amsa mata. Jumm tayi tana kallon Al'amin daya haye kan kujera ya kwanta alamar baccin sa zai cigaba, sai ta juya kitchen ba tareda tace komai ba amma zuciyarta cike da saƙe saƙe.
Kan gado na fa
ɗ
a bayan dana shiga
ɗ
akin dafe d
a ƙirjina da nake ji tamkar an
ɗ
aure ni da igiya, daƙyar nake fuzgar numfashi, na ringa juyi a kan gado ni ka
ɗ
ai tsayin lokaci kafin ubangiji ya kawo mun rangwamen abinda nakeji ta hanyar rabani da numfashina na wani lokaci.
A waya Mama ta kira Abba, t
ambayar sa tayi ko Bilal yace masa wani abu ne tunda ance tare muka zo sai ya ce mata
"Bai tsaya ba yana sauke musu kayan su ya juya ko gaisawa bamuyi ba"
"Ikon Allah, to mai ya faru?" Ta sake tambaya cikin jimami. Daga can yace
"Ni kam ina zan sani ne
Amina? Ba gata nan a cikin gidan ki tambayeta mana", jin kamar ya fara fusata ua saka tace
"Toh shikenan sai ka dawo" ba tareda ya bata amsa ba ya katse wayar dan ransa y sosu matuƙa da ko in kulan da Bilal ya musu. Sosai yaji ba da
ɗ
i sanda Alhaji Bala d
a suke tsaye yace masa
"Wannan ba Mijin Halima bane naga yaja mota bai ko tsaya ya gaida mu ba? Koda yake yanda ta shige itama kamar dai akwai matsala dan na lura bata ma ga tsayuwarmu ba, amma shi ai idan
ɗ
an arziƙi ne yaci ko matsala suka samu ya tsaya
nan ya maka bayani ba yaja mota ya tafi ba".
Wannan maganar ta dame shi har ta saka ya fasa komawa cikin gidan da yayi niyya ya sallami Alhaji Balan kawai ya wuce inda zashi ya a tafe kuma yana tunanin dalilin zuwan Halima da sassafen nan.
Sai gurin
ƙ
arfe tara Mama tace Amirah ta shiga ta kirawo Halima ta karya lokacin har tayiwa su Al'amin wanka sun ƙoshi sun shiga sabgogin su, ihun da Amirah ta fasa bayan shigar ta
ɗ
akin ya saka Maman tashi da sauri tamkar zata hantsila ta shiga
ɗ
akin, gabanta ya ya
nke ya fa
ɗ
i ganin Amirah tsugunne kan Halima tana girgiza ta haditda kiran sunanta amma ko gezau bata motsa ba, cikin tashin hankali ta isa gaban gadon ta
ɗ
agota jikinta ta shiga jijjigata da ƙarfi amma bata koyi alamar zata farka ba.
"Ta mutu innalill
ahi mun shiga uku Yaya Halima ta mutu" Amirah ta fa
ɗ
a hannu biyu akai cikin matsanancin kuka Mama dake rungume da Halima ta
ɗ
aga mata hannu tana cewa
"Bata mutu ba fita ki kira Mu'azzam, kiyi sauri dan Allah yazo mu kaita asibiti" ta ƙarasa tana ƙoƙarin b
u
ɗ
e idanun Haliman. Da gudu Amirah ta nufi ƙofa sai kuma ta juyo cikin kuka tace
"Kin manta ya tafi makaranta tun
ɗ
azu yana da exam yau?"
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Amirah ki fita kowa kika gani ki kira mu kaita Asibiti" Mama ta fa
ɗ
a tana fa
shewa da kuka itama. Tareda Samari biyu Amirah ta dawo wanda a waje ta taresu sun taho a mota su suka
ɗ
auki Haliman suka fito da ita daga Mama har Amiran babu wanda ya tsaya neman koda Takalmi suka biyo su Zainab na kuka riƙe da Sharifa haka Al'amin dukda
ba wai sanin mai yake faruwa yayi ba kawai ganin sunayi ya saka shima ya kama. Suna ƙoƙarin sakata a motarsu Suraj ya iso ƙofar gidan dan dama tare suka fita da Abba ya kaishi Airport zai tafi Lagos, motar sa Mama tace su sakata suka shiga ita da Amirah ya
ja motar da gudun gaske suka nufi asibiti.
Bayan tsayin lokacin dana
ɗ
auka tsakanin mutuwa da rayuwa na farka, na bu
ɗ
e idanuwana da naji tamkar an manne mun su da super glue daƙyar na iya bu
ɗ
e su na kalli in da nake saidai ban fahimci komai ba hakan y
a saka na sake mayar da idanuwan nawa na kulle ina jin sautuka sama sama kamar daga can nesa. Mama dake zaune kan kujerar dake kusa dani ta miƙe da sauri saboda ƙafata dana motsa, ta kira sunana, dukda ba wai na fahimci mai ta fa
ɗ
a ba sautin da naji ya sak
a na sake bu
ɗ
e idona na sauke akan fuskarta. Ta kama hannuna hawaye na ziraro mata tace
"Kin farka Halima?" A hankali tamkar mai koyon magana na kira sunanta a rarrabe "Ma..ma" ha
ɗ
i da matsa hannunta data riƙe nawa dashi. Cikin kuka mai ha
ɗ
e da dariya t
a amsa da
"Na'am Halima kin farka? Alhamdulillah". Ji nayi maganganunta suna hau mun kai sai na sake mayar da idona na rufe tayi azamar kamo fuskata tana cewa
"Ki tashi dan Allah kada ki sake komawa Halima dan Allah ki bu
ɗ
e idonki ko hankalina zai kwant
a" ta ƙarasa cikin kuka. Na sake bu
ɗ
e idona na kalleta, tabbas naga ƙauna mai tsanani ha
ɗ
i da tausayi cikin ƙwayar idanunta dake tsiyayar da hawaye, kalaman Bilal da ya ce "Da uwarki nayi zina" suka dirar mun tamkar saukar mashi take wani abu ya taso ya sa
ke tokare mun maƙogaro, ban iya yin abinda ta buƙata ba na sake mayar da idanuna ruf na rufe su sai ta saki hannuna ta nufi ƙofa kusan da gudu ta fice daga
ɗ
akin ba jimawa suka dawo tareda likita da Nurses biyu. Sai da ya gama dubani kafin ya kalleta cikin
kalaman kwantar da hankali yace
"Kiyi haƙuri Hajiya na fa
ɗ
a miki jikinta yana da buƙatar hutu sosai zata farka idan lokacin hakan yayi in sha Allahu ki daina damuwa zata samu lafiya da yardar Allah"
"Likita ta farka fa, ta bu
ɗ
e idonta har magana ta
yi mun kafin ta sake komawa dan Allah likita kayi wani abun yarinya ta ta farka kaifa kace mun awanni ka
ɗ
an amma gashi kwana biyu kenan bata farka ba". Kwana biyun data ambata ya saka na sake bu
ɗ
e idona na kalle su, hannu biyu ta
ɗ
aga tana cewa
"Alhamduli
llah, ka gani ko idonta biyu". Ganin tana ƙoƙarin
ɗ
ago ni ya saka ya dakatar da ita, a hankali ya kira sunana na kalle shi yace
"Kina jina Halima?" Nayi shiru badan bana jin sa ba sai dan bansan ta yanda zan amsa masa ba. Bakina yayi mun nauyi tamkar an
ɗ
aure mun harshe. Cikin taushi ya sake kiran sunana da maimaita tambaya ina jinsa amma na kasa amsawa. Mama ta fashe da kuka tana cewa
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Dr mai ya samu yarinyata dan Allah kayi mun bayani ni Musulma ce koma menene zany
i haƙuri na kar
ɓ
i ƙaddarar data samemu".
"Dan Allah Hajiya ki nutsu, idan ba zaki iya shiru ba kuma ki fita waje. An gaya miki babu abinda ya sameta kawai tana buƙatar lokaci ne babu yanda za'ayi mutum ya tashi daga dogon suma irin haka kiyi tsammanin
nan take tunanin sa zai dawo tamkar yanda yake a da sannan wannan hayaniyar da kukan da kikeyi shima kina ƙara mata wata damuwar ne cikin wadda take"
ɗ
aya
ɗ
aga cikin Nurses
ɗ
in ta fa
ɗ
a a hasale, sai ta juya cikin kuka ta nufi ƙofa na bita da kallo ina so i
n tsayar da ita amma kuma banida ikon yin hakan.
Wata yar fitila likitan ya kunna ya shiga haska idanuwana bayan ya gama ya zaro biro daga aljihun rigarsa yace
"Idan kina jina ina so ki ringa bin biron nan da idonki duk inda nayi dashi kinji?" Na lums
he idona kafin na bu
ɗ
e nayi abinda ya ce. Ya mayar da biron aljihu yana cewa
"Yawwa Halima, yanzu ki motsa ƙafar ki na gani" nayi yanda yace sannan ya kama hannuna yace in matsa hannun sa nan ma nayi sannan ya sakeni, cewa yayi na tashi na zauna. Nayi j
imm dan kwata kwata banajin alamar ƙashi ko tsoka a jikina ji nake tamkar a iska nace, sai da ya sake maimaitawa kafin na yunƙura a hankali naja jikina Nurse tayi saurin saka mun pillow a bayana na jingina ina mayar da numfashi tamkar wadda tayi tseren gud
u. Hamdala yayi kafin ya kar
ɓ
i folder dake hannun Nurse yayi rubutu ya bata yace taje pharmacy ta kar
ɓ
o abinda ya rubuta sannan idan ta fita ta turo masa Mama.
Tare suka shigo da Abba, Mu'azzam, Anty Labiba da Mijinta sai Mama Fauziyya. Gaba
ɗ
ayan su k
allo
ɗ
aya zaka musu ka karanci hashin hankalin da suke ciki, Abba ya matso ya dafa kaina nayi karfin halin tattaro kalmomi na ha
ɗ
a na kira sunansa, "Abba" ya amsa yana shafa kaina
"Na'am Halimana kin tashi?" Sai na gya
ɗ
a masa kai lokaci
ɗ
aya kuka ya kwace
mun Abba ya rungume ni yana cewa
"Kuka kuma Halima menene? Kiyi shiru dan Allah kinga halin da kike ciki babu abinda zai faru ki dena kuka kinji?"
"Ina ganin kuyi haƙuri ku koma waje ƙila ganinku ne ya dawo mata da wani abun kuma a yanayin da take
ciki yanzu bama son duk wani abu da zai sosa mata rai balle ya sake ƙara mata wata damuwar" likita ya fa
ɗ
a. Duka suka fita banda Abba dake rungume dani idanuwansa sunyi jajir tamkar shima zai yi kukan yana ta bubbuga bayana da cewa nayi shiru, Nurse
ɗ
in da
Dr ya aika ta dawo da allurai da da drip ya kar
ɓ
a ya fara ha
ɗ
awa, zai zare ruwan dake hannuna Abba ya dakatar dashi yace
"Dan Allah kada ka saka mata abinda zai sake mayar da ita wannan baccin"
"Amma Alhaji saboda lafiyarta ne" cewar Dr, sai Abba ya g
irgiza masa kai yace
"Na sani amma ka
ɗ
anyi haƙuri ku bamu guri zanyi magana da ita". Tsayawa yayi kamar ba zai fita ba kafin ya juya, Nurse
ɗ
in da ta yiwa Mama magana
ɗ
azun ta bu
ɗ
e baki zata sake magana yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa su fita.
Sai sa suka rufo ƙofar kafin Abba ya
ɗ
ago kaina daga kafa
ɗ
ar sa yace
"Kukan ya isa haka Halima kiyi shiru kinji"
"Tsoro nakeji Abba" na fa
ɗ
a daƙyar kafin na kama hannunsa na
ɗ
ora saitin zuciyata da nakejin ciwo tamkar an hura mun wuta nace
"Zuciyat
a zafi takeyi Abba mutuwa zanyi"
"Ba zaki mutu ba Halima har sai lokacin da ubangiji ya rubuta faruwar hakan, duk wani tsanani a rayuwa yana tareda sauƙi kiyita nanata Hasbunallahu wani'imal wakeel a zuciyarki in sha Allahu zaki samu salama kinji?"
Ka
i na
ɗ
aga masa alamar naji take kuma na kama na shiga nanata Hasbunallahu a hankali a hankali na fara jin abinda ya tokare mun maƙoshi yana zagwanyewa, zafin da zuciyata take mun ma ya fara raguwa inayi Abba ma na biyawa a fili sannu sannu har bacci ya
ɗ
au
ke ni. Ajiyar zuciya ya sauke ganin nayi bacci, sai da ya
ɗ
auke ƙwallar data zubo masa kafin ya gyara mun kwanciya akan gadon ya lullu
ɓ
a mun bargo sannan ya koma kan kujerar dake gaban gadon ya zauna yana kallona.
Har ya sauka Lagos zuciyarsa babu da
ɗ
i
gaba
ɗ
aya hankalin sa na ga son sanin dalilin zuwan Halima gida da sassafe haka da kuma yanayin daya ganta a ciki. Yana so ya kira Mama yaji ko ta fa
ɗ
a mata wani abu amma kuma baya son yaji abinda zai
ɗ
aga masa hankali ya hanshi nutsuwar yin abinda zajeyi
Lagos
ɗ
in. Da zai shiga meeting ya saka wayarsa a Flight mood dan haka sai bayan Magriba lokacin sun tashi gaba
ɗ
aya ya shiga hotel room
ɗ
in sa kafin ya bu
ɗ
e wayar yana so ya kira wani Abokinsa, Network na daidaita kuma saƙon Mama ya fa
ɗ
o tana gaya masa H
alina na Asibiti sun sameta a sume a
ɗ
aki har lokacin kuma dukda bai san ƙarfe nawa ta tura saƙon ba bata farka ba kuma likita yaƙi ce musu komai yace dashi zai yi magana.
Cikin tsananin tashin hankali ya shiga neman layin Maman amma bai samu ba dan ha
ka ya mayar da akalar kiran kan Mu'azzam wanda bugu
ɗ
aya ya
ɗ
auka kuma yanda ya jishi da bayanin da ya masa akan yanayin Haliman ya saka yaji ba zai iya ƙara koda awa
ɗ
aya a Lagos
ɗ
in ba duk kuwa da bai kammala uzurin da yaje yi ba, sai dai yayi rashin sa'
ar rasa jirgi, haka ya kwana a zaune tamkar yanda suma a Kano suka kwana cikin tashin hankali da zullumin halin da Halima take ciki da gari ya waye kuwa ko wanka bai tsaya yiba ya hawo jirgi ya taho musamman yanda Mama ta kira tana rusa masa kuka akan yayi
wa likita magana ita dai ayi mata bayanin halin da yarta take ciki idan ma mutuwa tayi a gaya mata kawai saboda tunda aka kawota take nan kwance kan gado bata motsa ba gara