Showing 3001 words to 6000 words out of 287295 words
yanzu.
"Halims" ya kira sunana hakan ya anka
rar dani zurfin da nayi a tunani. Na sakar masa murmushi ina gyara mayafin kaina daya zame yace
"Ina ta magana kinyi shiru akwai wani abun ne?"
Kai na girgiza masa ina murmushi nace "babu komai, ina sauraronka"
"Me na fa
ɗ
a daga ƙarshe to idan dai kina
jina?" Ya tambayeni, na sakeyin murmushi nace
"Cewa kayi kana so na" seya fashe da dariya yace
"Canka kikayi kawai saboda kinsan harshena baya gajiya da furta abinda yake cikin zuciyata. I love you whole heartedly Halims, wlh duk sanda nazo gurinki Alla
h ka
ɗ
ai yasan yanda name yaƙi da zuciyata amma ji nake kamar karmu rabu, na masu na kasance tare dake a matsayin matata ta sunna".
Ƙ
asa nayi da kaina ina murmushi cikin jin kunyar kalamansa, ya matso kusa dani yana cewa
"Dagaske nake Halims, kinga rashin
lafiyar nan da nayi duk magungunan da nasha ba wani aiki suka mun ba ina kwance se ince inama kina kusa dani nasan dakin shayar dani maganin dake tattare dake zan warke"
Zumbur na miƙe daga kusa dashi ina
ɓ
ata fuska cike da shagwa
ɓ
a kamar zanyi kuka ya
fashe da dariya yace
"Matsoraciya, ke ba dama a
ɗ
akko magana se ki wani birkice"
"Ni dai bana so" na fa
ɗ
a ya miƙe yana cewa "Na bari My Halims, bazan sake ba. Amma da gaske a matse nake da son kasancewa dake. Ki tayani da addu'a akwai abinda nake jira
da zarar ya tabbata za'ayi komai shikenan ki zama tawa ki dena mun ƙwalele kina hanani bacci da dare" ganin na nufi ƙofa yasa ya shiga dariya yana cewa
"Haba mana nace miki na dena ai yanzun ma baki nane ya su
ɓ
uce. Magriba tayi kizo muyi selfie na samu na
rage zafi kar na tafi ina mafarkin kwalliyar nan taki". Dakyar na tsaya ya
ɗ
auke mu selfie a wayarsa sannan yayi mun ni ka
ɗ
ai, har munje bakin kofa yace
"Ban ma san me zanci ba da daddare ba wlh. Wai tuwon Anty Murja tayi bayan tasan bana so ga kuma ba
ki na babu da
ɗ
i". A raina nayi murmushi nace "dama jira nake naji zakayi magana ko kuwa" a fili kuma nace
"Afuwan, ganinka ne duk ya rikitani. Bari nayi maka packaging sauran se kaci idan ka koma"
"Haba dai, su Amir ba zasu ci ba? " Ya fa
ɗ
a kamar gaske.
Sena wuce shi kawai a raina ina gulmar halinsa. Ko pure water na bashi seya tafi da sauran balle abinci shine zece wani su Amir ba zasu ci ba. A fararen robobi na juye masa sauran abincin da banda wanda na
ɗ
an
ɗ
ana da ina girkin ban sake jinsa a baki na ba.
Roba uku na masa
ɗ
aya shinkafa
ɗ
aya kaza se coslow a
ɗ
ayar lemon ma na juye masa a gorar Faro na ha
ɗ
e masa komai cikin ledar dana
ɗ
akko.
"Wannan halin naki yake tabbatar mun zaki kula da cikina idan mukayi aure, Allah dai yayi miki albarka ya barmu ta
re my Halims" ya fa
ɗ
a sanda ya kar
ɓ
i ledar. Muka jera yana mun surutu, seda na bu
ɗ
e masa get ya fita da mashin na rufe kafin na fita na same shi ya
ɗ
aure ledar yanda abin ciki ba zasu zube ba kafin ya hau mashin
ɗ
in yana kallona yace
"Da yanzu zaki wuce g
ida se mu tafi na
ɗ
ana ki". Tunda yazo nake raya in masa magana akan da canza mashin
ɗ
in da yayi dama gini ya cigaba ko yayi amfani ku
ɗ
in ya ha
ɗ
a kayan saka ranar tunda dai tsohon nasan babu abinda yayi ai amma gudun kar yaga na shiga rayuwarsa yasa nayi s
hiru se nace
"To bari kawai nayiwa Anty Labiba sallama se mu tafi dama na gaji gashi kuma gobe ina da practical exam ina so nayi karatu" na juya cikin gidan.
Toshe kunne kawai nayi na ha
ɗ
a kayana na gudu na bar mata wanke wanke ina tana fa
ɗ
in zan sake
zuwa ne na tafi, fa
ɗ
an mu ba wani jimawa yake ba da kanta ma zata nemo ni musamman yanzu da yara zasuyi hutun makaranta ga tsohon ciki tana dashi dole ta nemo me tayata da kayaniyar yaran. Na
ɗ
ane tsuntsun soyayya ya lula damu muna tafe yana mun surutan d
a ba wani ji nake sosai ba saboda iska har muka isa sabon titi gidan mu. A bakin gate ya tsaya na sauka ya kalli ginin benen da ake
ɗ
ora mana da har an fara fenti yace
"Ashe aikin nan yayi nisa haka, wato mu talakawa ne muke jin garin nan masu ku
ɗ
i sha'a
ninku kawai kikeyi". Fuska ta ba yabo ba fallasa ban dai ce masa komai ba ya shiga laluben aljihu, harga Allah na saka ran tunda yace mun ya siyi mashin idan ya tashi zuwa ko 5k ce ze bani shiyasa ma banji komai ba na kashe ku
ɗ
in transport
ɗ
ina na sati da
Abba ya bani nayi masa abinci ko be biyani duka ba a ƙalla zan rage wani abun musamman da yake ta ko
ɗ
a da
ɗ
in abincin yana fa
ɗ
in na cancanci tukuici ganin yana laluben Aljihun yasa nayi
ɗ
an murmushi ina jira se naga ya zaro wayarsa ya bu
ɗ
e kafin ya juyo yan
a cewa
"Bari in sake miki hoto wlh kin mun kyau yau
ɗ
in nan irin sosai fa My Halims.
Takaici ya kamani amma haka na gyara ya shiga
ɗ
auka na hoton seda aka kira sallah kafin yamun sallama ya burga mashin
ɗ
insa ya tafi na juya jiki ba ƙwari na shiga gid
a a raina ina ayyana ƙila se jibi da yace ze zo ko kuma ya mun transfer.
[5/18, 13:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS
WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana w
akiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi.*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 2*
Washe gari daƙyar na yakice bacci nayi shirin makaranta, ina gama karatu Bilal ya kirani har gurin ƙarfe
ɗ
aya muna hira kafin ya barni na kwanta dama ga gajiyar dana kwaso a makaranta jiyan na
ɗ
ora data girki sannan dana dawo gidan ma ban zaun
a ba na tarar anyi fenti a
ɗ
akina gaba
ɗ
aya an hargitsamun kaya seda na gyara su sannan na kwanta. Shaf na manta da munyi fa
ɗ
a da Hansa'u jiya na zauna jiran zuwanta har ƙarfe tara seda na kirata sau biyu bata amsa ba wanda nasan ba halin ta bane da wuya n
a kirata a waya bata amsa ba sedai irin haka idan munyi fa
ɗ
a. A fili nace
"Lallai, wai ita ta
ɗ
auki abun har zuci ashe. Ni da ya kamata nayi fushi ta zagar mun Habibi banyi ba se ita? To ai shikenan" na
ɗ
auki jakata da Lab coat na fito falo na tarar da Ma
ma tana ware atamfofi. Sau biyu ina ce mata zan tafi tana mun Allah ya tsare hanya. Ɗari biyar ce a jakata, zata kaini ta dawo dani amma bani da canjin da zanci wani abu kuma yau
ɗ
in wuni zamuyi se ƙarfe hu
ɗ
u zuwa biyar zamu taso. Ganin na tsaya yasa ta ta
mbayeni lafiya? Na shiga sosa kai, tsaki kawai Mama tayi ta bu
ɗ
e POS
ɗ
in ta dake gefe ta zaro dubu
ɗ
aya ta miƙa mun tana cewa
"Banda shegen iyayinki me yasa baki zo kin masa abincin a nan ba?" Kar
ɓ
a nayi tareda mata godiya na fita. Ina son Mama, bata zafa
fawa a lamuranta. Nasan ba wani son zancen aure na da Bilal take ba musamman yanda duk yan uwanta suke sukar abun amma tunda nida Abba muna son ita ma ta kar
ɓ
a tana mana addu'a.
Seda muka fito break kafin muka tsaya da Hansa'u nace mata "wai saboda mag
anar jiya yasa baki biyo mun ba yau kuma na kiraki baki amsa ba?"
"In biyo miki kuma? Ina ce kikayi kowa tasa ta fishsheki babu kr babu ni akan Bilal iyayenki ne kawai na zaki bari ba. To tunda ni ba iyayenki bace ai gara na tattara tsumman rayuwata na b
aki guri tunda baki na baze iya shiru ba har idan naga abinda ba daidai ba se nayi magana" Hansa'u ta bani amsa, sena rungumeta ina cewa
"Haba ƙawata ki barni in kama wa? Ai kin san dai tsakani na dake ya wuce ƙawance kema yar uwata ce kina cikin wa
ɗ
anda
bazan rabu dasu ba ai" ta mun banza, dake nasan nice da laifi dukda naji haushin abinda ta fa
ɗ
a akan Bilal amma kuma nima abinda na mata ya shallake wanda tamun hakan
tasa na ringa bata haƙuri harta sakko muka tafi siyo fanke da lemo. Bayan mun zauna nace
mata
"Amma tsakani da Hansy dole a ringa jin kanmu har idan zaki ringa ta
ɓ
a mun Yarima. Ya kamata ki ringa mun kara, ko baki son Bilal darajar ƙaunar dake tsakani na dashi ai yaci ki mun kara. Bana so ki dena zaginsa a gabana idan ma zaki zage shi kiyi ca
n a inda bazanji ba dan nima bazan miki kara ba sena rama masa"
"Ai shikenan, ni dai bazan zauna tare dake ina kallo kina ƙoƙarin jefa kanki a halaka kuma nayi shiru na barki ba dole in fa
ɗ
a miki gaskiya ko ki
ɗ
auka ko karki
ɗ
auka ruwanki" ta bani amsa,
a hasale nace
"Auren Bilal
ɗ
in ne kike kira da halaka Hansa'u? Wai me kike nufi da Bilal ne? Ki gaya mun me yake aikatawa da har kike kiran aurensa da jefa kai a halaka wane mugun hali yake dashi da ban sani ba?" Na ƙarasa ina miƙewa tsaye. Watsa hannu t
ayi tace
"Kin fini sanin halakar da nake nufi sedai idan kin so ne zakiwa maganata mummunar fassara. Akwai halakar duniya data wuce mace tayi rashin dacen mijin aure? Bilal be dace dake ba, kiso ko karki so sena fa
ɗ
a ke kike sonsa amma shi ba sonki yake b
a idan ma kuma yana sonki to akwai dalilinsa na hakan amma ba zaki fahimci abinda nake fa
ɗ
a miki yanzu ba ba kuma na miki fatan kiyi nadamar kin jij maganar masu sonki a sanda komai ya lalace miki. Tun wuri ga maza fululu masu ƙaunar ki dagaske ki nemi mij
in aure a cikinsu ina mai tabbatar miki har ba Allah ya ƙaddara ba Bilal ya samu wadda ta fiki sedai kiji wani zancen wlh" ta ƙarasa tana bari na a gurin. A maimakon sulhu se gashi mun sake tafka wani fa
ɗ
an dan da aka tashi ban tafi ba seda na sameta na sa
ke zazzaga mata rashin mutunchi na fa
ɗ
a mata nasan baƙin ciki take mun ba wani abu da saboda na samu me so na zamuyi auren soyayya da ƙuruciyarmu ba irinta ba da zata auri tsoho sa'an Babanta shine take mun baƙin ciki. Kwa
ɗ
ayin daya kaita ta amsa zata auri
tsoho shi zesa ta ha
ɗ
iyi baƙin cikinta ta kalle mu ni da Habibi na musha soyayya. A bakin titi na cimmata suna jiran Adaidaita da ƙawayenmu biyu Zainab da Hussaina duk yan unguwar mu ne tare muke tafiya dama. Hansa'u ta ringa kuka ko a jikina su biyun ma
da suka shigar mata nayi musu tatas nayi tafiyata na barsu raina fes domin ba wanda ya isa ya ta
ɓ
a Bilal na barshi, dama ta kama kanta ta fita a sabgata dashi se mu cigaba da lalla
ɓ
a zumunchin mu amma ta soka kanta a inda ba'a gayyaceta ba.
Dana koma g
ida tsaf na kwashe labari na bawa Bilal daya kirani, ga mamakina se yace wai ban kyauta ba me yasa zan mata haka ai kamata yayi naji uzurinta domin yanda muke da ita kowa yasan ba zata cutar dani ba
"Kenan ka yarda kana da mugun halin da har zata ringa fa
ɗ
ar irin Maganganun nan akanka?" Na tambayeshi, se yace
"No Halims ba haka bane. Abinda nake nufi da se ki mata uzuri ki bita a hankali kiji menene hujjojinta amma yanzu abinda kika mata gaskiya baki kyauta ba ai tsakaninku ya zarce haka gaskiya banji da
ɗ
i ba" ya ringa mun fa
ɗ
a har naji haushi ma na kashe wayar.
Kwana biyu da suka biyo baya banje makaranta ba mun samu interval kafin mu fara theory parts na jarabawa. Tun a washe gari da Mama taga har yamma bance zanje gidansu Hansa'u ba ita kuma bata ga
tazo ba ta tambayeni ko lafiya se kawai nace mata jiya da muka taho gadon ƙaya ta wuce gidan yayarsu. A washe garin ranar da rana Abba ya dawo daga Enugu sunje wani aiki da magriba bayan ya dawo daga masallaci ina
ɗ
akina na idar da sallah
na jiyo yana ƙwa
la mun kira, Abba bashi da fa
ɗ
a daga sautin muryarsa na san akwai wani abu abinda ya fara zuwar mun ko zancen Bilal ze mun tunda yace kafin ya dawo musan abinda muke ciki.
Ina fita naga Hansa'u a zaune, a raina nace lallai ma, ƙarata ta kawo ko me? Haka
na samu guri na zauna nan kuwa Abba ya ha
ɗ
a mu duk mu biyun ya mana kaca kaca kowa ya bata laifinta. A yanda yace tun da la'asar daya fita aka bashi labarin wai munyi fa
ɗ
a a makaranta a raina na ringa tsinewa munafukai nasan kuma baze wuce Nasir ko Musan
gidan inji ba sune yan unguwar mu kuma a gabansu mukayi fa
ɗ
an shine ashe sunzo unguwa suna yawo damu, Abba ya mana kaca kaca yace kuma mu bawa juna haƙuri kuma idan ya sake jin irin haka ba fa
ɗ
a ba seya ha
ɗ
a mana harda duka mun san kuma ze aikata. Yana da
sanyi da wasa da dariya amma fa kaifi
ɗ
aya ne muddin yace zeyi abu zeyi dan haka muka masa alƙawarin haka ba zata sake faruwa ba. Washe gari kuwa da mukaje makaranta komai ya wuce, dukda dai Hansa'u na lura bata gama hucewa ba amma ni na sake gaba
ɗ
aya ina
ta janta har daga ƙarshe ta huce muka cigaba da sabgoginmu.
Ranar Asabar Bilal yace ze zo, tun ha
ɗ
uwar mu a gidan Anty Labiba be samu ya dawo ba se waya mukeyi, sun sake komawa Abuja ance wannan watan in sha Allah albashinsu ze fara shiga harma za'a b
iya su na baya da basu samu ba. Naji da
ɗ
i sosai ko ba komai maganar aurenmu zata taso masu ganin ba aure na zeyi ba zasuji kunya. Allah ya sani ina son Bilal tamkar rai, yanayinsa da halayyar sa sun min a irin mijin da nake fatan aure na kuma fa
ɗ
a na ƙara
ciki wuya ko da
ɗ
i zan zauna dashi domin shi nake so ba wani abu ba duk wanda suke zuwa masu abin hannun da ake ganin sunfi dacewa dani ni basu gaba na shi
ɗ
in shi nake so kuma ina ji a jikina gaba se mun zama abinda ba'ayi zato ba duk masu gulma se sunji k
unya.
Kamar ko yaushe nayi masa snacks samosa da cake se dambun nama da Anty Hasiya ƙanwar Abbanmu ta kawo masa na
ɗ
ibar masa. Tsayin fara soyayyar mu Allah keda kullum amma duk sanda Bilal ze zo sena masa abinci ko wani abun ta
ɓ
awa da zan bashi. Tun M
ama na biye mun harta fita sabgata a cewarta abin nawa bana ƙare bane, harta kai shi ze fa
ɗ
a mun abinda yake so ko in tambaye shi babu ko sisinsa haka zanyi yazo ya cinye har ya tafi da saura balle kuma da azumi gidanmu yake shan ruwa idan be zoba zan aika
masa dashi haka in sallah tayi zan ha
ɗ
a sha tara ta arziƙi a kaiwa Hajja mahaifiyarsa sannan in ha
ɗ
a masa wanda zasu zo da abokanansa suci se an samu me mutunchin gaske ne cikinsu ze iya
ɗ
aukar wani abu yace mun ga tukuici amma hakan ni sam baya damuna do
min dan Allah nake masa kuma arziƙin so da ƙauna.
Seda a gama jere masa snacks
ɗ
in da kunun aya me sanyi kafin na zauna muka gaisa muna kashe juna da murmushin ƙauna. Na cika masa kofi da kunun ayar yasha ya gode Allah yana kallona yace
"Wato Halims,
bansan kalar murnar da zanyi ba ranar da aka ƙwala shelar
ɗ
aurin aure na dake, ina ga se na hau kan hasumiyar masallaci tsabar murna" na ƙyalƙyale da dariya nace
"Ka dai rufa mana asiri kar ace ango ya karye a garin murnar aurensa" yace
"Allah