Showing 39001 words to 42000 words out of 287295 words
amsawa daga ƙarshe ma wayar a kashe take.
"To ban da shirme kuma kukan na menene? Ai lafiya ce take
ɓ
uya. Ki kira Nasir ko wani cikin abokanan sa na gurin aiki kiji ko suna tare tun da hankalin ki be kwanta ba. Amma
babu komai ma nasan tun da kina gida ma ai yana haka ku wuni ba kuyi magana ba se daga baya ya baki uzuri" abin da Mama ta fa
ɗ
a kenan amma hakan be sa naji hankali na ya kwanta ba tun da ni dai tun da mukayi aure ko ƙofar gida ze fita se ya gaya mun. Layin
ƙanin sa Abubakar na kira se dai shima na tarar a kashe wannan ya sake dugunzuma hankali na kawai na zauna na fashe da kuka na rashin madafa. Motsin bu
ɗ
e ƙofa ya farkar dani firgigit daga baccin daya sure ni ba tare da na sani ba ina tsaka da kuka. Dishi
dishi nake kallon sa ya tsaya shima yana kallo na kafin ya fara takowa cikin falon se na miƙe da sauri na nufe shi, tsayawa yayi na fa
ɗ
a jikin sa tare da fashe wa da kuka ina cewa
"Ina ka tafi? Hankali na ya tashi ina ta kiran wayarka baka amsawa me yas
a kayi mun haka?"
A dake cikin yanayin da banyi zato ba bayan ya janye ni daga jikin sa ya kalle ni yace
"Kin aike ni ne balle ki bi ba'asin in da na tsaya?"
Se na bishi da ido kawai na kasa cewa komai, ya yi tsaki tare da zagaye ni ya wuce ciki.
Kamar wata wawiya haka na rakashi da ido har ya shige cikin
ɗ
aki tare da banko ƙofa. Tamkar wacce ƙwai ya fashewa a ciki haka naja ƙafafu na da suka yi sanyi na zauna kan kujera ha
ɗ
i da zabga tagumi. So nake na tunano ta in da na kuskurewa Bilal, me nayi
masa da yayi zafi haka? Ina nan zaune ya sake fitowa fuu ya shige kitchen ina jiyo shi yana birkita kwanuka kafin ya sake fitowa da kofin shayi a hannun sa se dublan a plate. Nan cikin falon ya zauna bayan daya kunna Tv ya shiga shan shayin sa, yanda yayi
tamkar be san da wanzuwata a gurin ba yasa na fashe da kuka sosai har da shashsheƙa se gani nayi ya miƙe tsaye da kofin shayin sa da alama gurin ze bar mun. Bazan iya jurewa ba, ina buƙatar nasan takamaiman dalilin fushin da yake yi dani se na miƙe da sau
ri na isa gaban sa na durƙusa tare da riƙe ƙafar sa ina ci gaba da kukan nace
"Ka fa
ɗ
a mun me nayi maka kake mun irin wannan horon Bilal?"
"Baki ma san me kika mun ba kenan?" Ya fa
ɗ
a yana
ɗ
age kai sama a ƙoƙarin hana tausayi na yin tasiri a zuciyar sa.
Girgiza kai nayi ina ci gaba da kukan nace
"Wlh ban sani ba, ka taimaka ka gaya mun me na maka bazan iya cigaba da jure fushin ka irin haka ba"
"Shikenan tun da baki san me kika mun ba Halima, duk ranar da kika tuna se muyi maganar" ya fa
ɗ
a yana janye ƙ
afar sa ya wuce cikin
ɗ
aki se dai be kulle ƙofar ba a bu
ɗ
e ya barta. Zuciya ta na raya mun na rabu dashi da kansa ze zo in da nake idan ya gama fushin amma zuciyar dake cike da so da begensa ta rinjaye ni haka na sake bin sa
ɗ
aki ina kuka ina roƙon ya gaya
mun abin da na masa amma se da mula dan kansa kafin ya maido mun da zancen kilishi"
"Kayi haƙuri, ban kawo hakan ze
ɓ
ata maka rai ba amma zan kiyaye haka ba zata sake faruwa ba a gaba" na fa
ɗ
a ina goge hawaye. Duk da haka be wani sake mun koma yanda mu
ke gaba
ɗ
aya ba se da aka kwana biyu ranar laraba ya fita da yamma babu jimawa Mu'azzam ya zo ya kawo mun manya manyan kaji guda goma in ji Abba da ƙwai shima crate goma dake ya bu
ɗ
e gidab gona ana kiwon kaji da kifi yanzun an fitar da layers ne da suka de
na ƙwai shine aka kawo mun rabo na. Tuwo nayi niyyar yi ganin kajin yasa na fasa na ha
ɗ
a lafiyayyen farfe su irin wanda Bilal ke so na kwa
ɓ
a fulawa na gasa bread dan na lura yanzu abin laifi baya yiwa Bilal yawa tsaf idan na kira shi nace ya taho mana da b
red
ɗ
in se ya maida abin na rigima.
Se da akayi sallar isha'i kafin suka shigo gidan shi da Abubakar da Halifa
ɗ
an Babbar yayarsu Anty Na'ima. Can falon sa ya bu
ɗ
e musu suka shiga na kai musu ruwa da lemo ganin ya fito da laptop
ɗ
in sa yasa na fahimci
wani abun zasu yi ba yanzu zasu tafi ba dan haka na
ɗ
ora musu jallof
ɗ
in taliya na saka musu kazar a ciki, na sauke kenan na jiyo maganar su a tsakar gida alamun sun fito zasu wuce hakan yasa na leƙa da sauri na sanar musu ga abinci na sauke ina kuma zasu
tafi?
"Da kin barshi Anty sauri mukeyi" Abubakar
ɗ
in ya fa
ɗ
a, zanyi magana Bilal ya rigani yace
"Ku wuce kawai kasan na cewa Nasir ya jira ka kai masa flash
ɗ
in nan kar ku
ɓ
ata masa lokaci"
"Haba dai duk saurin da sukeyi ai sa jira dai su ci abincin
, idan kuma ba zaku ci anan ba bari in juye muku to se ku tafi dashi kawai" na tare shi. Naga irin kallon daya mun amma ban kawo komai ba na koma kitchen, falon suka shigo suma suka zauna Bilal ya bini kitchen, yana tsaye a kaina na juye musu taliyar gaba
ɗ
aya a kula tun da dama su na dafawa na saka a kwando na ha
ɗ
a musu da ruwan gora da lemo yana nan tsaye a kitchen
ɗ
in na fita na basu mukayi sallama suka tafi. Bana zaton sun kulle mana ƙofa Bilal ya hau ni da fa
ɗ
a tamkar ze doke ni, akan me yace su tafi z
an ce su tsaya in zuba musu abinci?
Mamaki ya sa na kasa ce masa komai, waccen ranar yayi fa
ɗ
a dan na yiwa yar uwata kyauta yau kuma yana yi saboda nayiwa nasa dangin menene matsalar Bilal ne? Ban san ya akayi ba kuma ya rage banbamin da yakeyi yana ce
wa
"Bana so, karki sake mun irin haka a gaban yara salon suce ban isa da ke ba kin raina ni in ba haka ba ya za ayi na baki umarni ki take kiyi wanda ranki ya raya miki? Yanzu da kika juye musu abincin duka ni wanne zanci"
"Allah ya baka haƙuri" na fa
ɗ
a
a sanyaye kafin na shige kitchen na barshi. Na zata ze shige
ɗ
aki ya kulle irin na waccen ranar se kuma na tarar dashi a zaune yana kallo, se da na gama jera abubuwan da zamuyi amfani dasu akan dining kafin nayi masa magana ya taso. Sosai yaci naman nayi
mamakin da ban ji ya tambaye ni daga in da aka samo su ba tun da yasan bamu da sauran naman kaza a gidan se wanda yake cikin miya. Kafin mu kwanta se da ya sake ci ya kuma jaddada mun in aje masa sauran a fridge karya nema gobe nace masa na bawa wani.
A haka muka cinye satin, zaman mu ya koma kamar da har ma ya zarce da da
ɗ
i da farin ciki. Cikin abin da yasa nake ƙara son Bilal mutum ne shi da baya son jikin sa, ina kwance zeyi shara yayi mopping wani lokacin har girki yake
ɗ
ora mun, ranar daya ga ina h
a
ɗ
e kayana da sukayi datti kafin na samu wanda ze yi mun wanki kamar wasa yace na fita dasu tsakar gida,
na yi tunanin almajiri ze nemo na fitar na ci gaba da gyaran
ɗ
aki na se kawai ganin sa nayi ta window yana shanya kayan ashe da kansa ya wanke mun. Wan
nan yasa na ke ƙara son sa saboda ya bani mamakin na same shi yanda ma banyi zato ba. Abu
ɗ
aya yake bani tsoro da halayyar sa yanda yake birkicewa lokaci
ɗ
aya akan
ɗ
an ƙaramin abu da be taka kara ya karya ba, wani lokacin ya sakko da wuri wani lokacin ko s
e naji na tsani kaina na tsani dalilin daya sa na za
ɓ
i rayuwa dashi kafin ya sakko idan komai ya wuce kuma se ya zama kamar wani sa
ɓ
ani be ta
ɓ
a shiga tsakanin mu ba.
A haka muka ci sati hu
ɗ
u da aure se lokacin kuma hutun daya
ɗ
auka ya ƙare ya koma baki
n aiki, da safe idan ze fita har kuka nake yi saboda sabon da nayi na kasancewa tare dashi a ko da yaushe bana ta
ɓ
a samun nutsuwa se naga ƙarfe hu
ɗ
u tayi lokacin shigowar sa gida yayi. Bahaushe yace yau da gobe bata bar komai ba, a hankali cefanen mu ya fa
ra ja baya. Ɗan yun kayan miya ne suka fara ƙarewa ya rage albasa kawai nake da, da yake ina da dafaffu a freezer marka
ɗ
e da jajjage se banyi azancin sanar dashi ba. Ranar wata asabar yana gida, da rana yace na dafa mana shinkafa da wake jollof nayi amfani
da bushashshen kifi. A plate
ɗ
aya na zuba mana, har mun fara ci yace na
ɗ
akko masa yaji wai abincin yayi masa salam da yawa dake da manja nayi. Dukda ya saka yajin ya ce beyi masa yanda yake so a bakin sa ba dan haka ya tashi ya tafi kitchen da kansa, se
da ya ƙwala mun kira naje yake tambaya ta ya yaga babu kayan miya?
"Sun ƙare ai, saboda ina da marka
ɗ
e a ajiye shiyasa ma ban gaya maka" na bashi amsa. Bece mun komai ba muka koma muka ƙarasa cin abincin kafin ya shirya yace mun ze
ɗ
an fita amma ba jim
awa zeyi ba.
"Dan Allah na shirya mu tafi tare" na shiga yi masa magiya amma kamar kullum ya ce Aa. Tun waccen ranar da muka je gidan su da namu ko ƙofar gida ban sake fita ba ba kalar magiya da nacin da ban masa ba amma yaƙi. Kafin muyi aure idan aka ce
mun Bilal Bilal zeyi kulle zan ƙaryata se gashi a take takensa na ga hakan. Da nayi masa ƙorafin duk sauran yan uwana da akayi mana aure tare sun je sun gaida iyayen mu ce mun yayi al'ada ce ba addini ba ni ba zani ba, abin da yasa na haƙura da na yiwa Ma
ma mita tace na haƙura ai dama yayi wuri wata
ɗ
aya ace na fara yawo. Ni yanzu gidan Anty Labiba na damu da naje, tun ranar da aka kawo gara bata dawo ba, a waya ma sau biyu ta kira ni akan wani saƙo da tace za'a kawo mun se bayan an kawo
ɗ
in ta sake kira t
ayi mun bayanin yanda zanyi dashi. Ko a chat idan ba ni nayi mata magana ba bata kulani, nasan fushi takeyi dani shi yasa kuma nake so naje gida na bata haƙuri mu sasanta dan bazan iya jure fushin nata ba.
Ba yanda na iya tun da yace Aa haka na koma ci
ki na zauna rai na duk babu da
ɗ
i se dai kamar yanda yace be jima ba ya dawo da cefane harda irish potatoe da doya tun da yaga su ma saura ka
ɗ
an. Se da na aje komai in da ya dace kafin na koma gurin sa. Washe gari kamar kullum da wuri na gama ha
ɗ
a abin kary
awa na soya dankali da ƙwai se ruwan tea, har na gama komai Bilal na
ɗ
aki be fito ba, ganinya kusa makara yasa na ha
ɗ
a masa shayi dan ya huce kafin yazo sha na wuce
ɗ
aki gurin sa. Seda na taimaka masa ya ƙarasa shiryawa kafin muka fito tare ina masa daru a
kan yayi kyau da yawa ina tsoron kar yammata su yi ta kallar mun shi a waje. Fusarsa washe da fara'a da alamu yana jin da
ɗ
in yanda nake kambama shi a ko da yaushe ina zuzuta kwalliyar sa. Se da na ja masa kujera ya zauna kafin 1na bu
ɗ
e bowl
ɗ
in dana zuba d
ankalin na janyo plate zan zuba masa,
"Meye wannan Halima?" Ya fa
ɗ
a da ƙarfi har se da na razana. Jiki na ya
ɗ
auki rawa na saki fork
ɗ
in hannuna tare da dafe ƙirji na dake harbawa ina ambaton innalillahi wa'inna ilahi raji'un a fili tare da baza ido ko z
an ga abin da ya saka shi wannan razanar haka amma iya hange na banga komai akan dining
ɗ
in ko kewayen in da muke ba.
"Banga komai ba Bilal" na fa
ɗ
a cikin rawar murya dan dagaske na tsorata. Cikin
ɓ
acin ran daya nuna har kan fuskar sa ya nuna bowl
ɗ
in
dankalin yana cewa
"Wannan uban dankalin da kika soya waye ze cinye shi? Almubazzaranci zaki fara ko Halima saboda baki san zafin ku
ɗ
i ba baki san yanda ake neman su ba? Yanzu cikin mu mu biyu ne zaki soya wannan abun? Ko da yake baki da asara shi yasa, s
e ki zauna kici" daga haka ya miƙe ya sa
ɓ
a jakarsa ya nufi ƙofa yana ci gaba da banbami. Ƙarar da ƙofa tayi bayan daya bugota ya dawo dani daga suman wucin gadin da mamakin Bilal ya sakani yi. Na sauke ajiyar zuciya me ƙarfi tare da jan kujera na zauna sab
oda ji nayi ƙafafu na sun yi sanyi kamar ba zasu iya cigaba da
ɗ
auka ta ba. Se na rasa ma tunanin me zanyi, akan dankali dai Bilal yake kirana almubazza?
Buhu
ɗ
ayan da muka cinye a sati biyar be saka ya danganta ni da almubazzaranci ba se yanzu saboda
na soya daga cikin kwano
ɗ
ayan daya siyo da ku
ɗ
in sa? Dankalin da yake cewa baya gajiya da cin sa, se muci da safe mu ci da rana da dare ma mu ci, Allah ke da kullum duk safiya har idan ya rigani shiga kitchen dankali ze feraye ko nayi marmarin doya idan b
a shi yaga dama yaci ba se yace sedai kowa yaci abin da yake so amma shine yake mun tijara akan sa yau?
Ina nan zaune kusan awa guda gaba
ɗ
aya kaina ya kulle har na rasa kalar tunanin da zanyi. Bugun get da kuma wayata da ta
ɗ
auki ƙara yasa na tattara
hankali na guri
ɗ
aya ganin Hansa'u ke kiran yasa na miƙe dan nasan itan ce take buga ƙofa tun da mun yi magana tun jiya ta gaya mun yau zata zo ta kawo mun atamfa da kace
ɗ
in ankon bikin ta da aka saka nan da sati shida. Fara'ar dole na ƙirƙira na
ɗ
orawa f
uskata bayan na bu
ɗ
e musu ƙofa suka shigo tana mun mitar sun da
ɗ
e suna bugu kuma dan wulaƙanci tana kira ban amsa ba. Bana yanayin da zan ja magana se kawai nayi murmushi muka shiga falo. Ƙanwar ta Abida ce ta wuce kan dining kai tsaye tana cewa
"Ni wlh
yunwa nakeji Anty Halima ban karya ba ta taso ni me kuka rage?" Bata ma jira na bata amsa ba ta dirar wa dankalin Bilal, Hansa'u zata hau ta da fa
ɗ
a na hanata, ina lura da yanda take kallo na nasan baze wuce ta karanci damuwa tattare dani bane tun da kuma
ban ce mata ba itama ba tayi karambanin tambayata komai ba, basu jima ba suka wuce bayan ta bar mun atamfa
ɗ
aya da lace
ɗ
in na zata ma wuni zatayi tace mun Aa yau take so duk wanda zata kaima ankon gida ta gama dasu. Abida bata daddara ba ta sake
ɗ
aukko k
walin exotic a fridge tasha ta tafi da sauran, yana cikin lemon da Bilal yafi so kuma shi ka
ɗ
ai ya rage kwali
ɗ
ayan ina kallon ta amma bazan iya cewa ta ajiye ba domin rowa ba hali na bace ba kuma zan koyeta a gidan aure ba sannan Abida na
ɗ
auke ta ne kama
r Amirah ƙanwa ta babu yanda za ayi na hanata wani abu da nake dashi.
Saboda yanda muka rabu da Bilal yasa na cire komai daga raina na yi masa girkin daya fi so kafin ya dawo na sake gyara gida na baza turare nima nayi wanka na canca
ɗ
a kwalliya na kame
a falo ina jiransa. Rai a ha
ɗ
e
sallama a ciki ya shigo falon, nayi kamar ban lura da yanayin sa ba na nufe shi ina masa sannu da zuwa. Be tare ni yanda muka saba ba be kuma gwasale ni yanda nayi zato ba se ya miƙo mun jakar hannun sa na kar
ɓ
a ina murmushi
tare da yi masa sannu da zuwa, yanda ya