Showing 129001 words to 132000 words out of 287295 words
kawowa kenan? Sannu Bilal" Na fa
ɗ
a ina tsare shi da ido.
"Gori zaki yi mun kenan?" Ya fa
ɗ
a lokaci
ɗ
aya fuskar sa na rinewa da
ɓ
acin rai. Na ture kwanon gaba na na miƙe na ce
"Gaskiya ce kawai na fa
ɗ
a ba gori na maka ba, na zata ai yau sabon muna da kayan abinci ya sa ka manta ka fita
ba tare da ka bar mun abinda zan ci ba ashe kai duk a tunanin za'a kawo mun Gara daga gidan mu".
Ya mun kallon bani da lokacin ki a yanzu kafin yayi tashin Magajin Dagacin Ƙauye da Al'amin a hannun sa, na yi ta jira ya dawo ya rufe ni da masifar da ya
saba amma shiru har na gama tunane tunane na bacci ya kwashe ni bai shigo ba balle ya dawo da Al'amin
ɗ
in sai cikin dare na farka na ganshi a kusa da ni.
Bayan na yi fitsari na canza masa diaper muka sake komawa bacci. Gurin ƙarfe bakwai da rabi ina ts
aka da mopping dan tun asuba da na tashi sallah shima Al'amin ya farka ya kuma ƙi komawa dan haka na goya shi kawai na shiga aika ce aika ce na naji ana buga get, Hijab na zura na fita, jin muryar Sunusi maigadin maƙwaftan mu ya saka na bu
ɗ
e kofar.
Ya
gaishe ni na amsa ina mamakin tsadadden warmer na da na gani a hannun sa, a iya tunani na ban tuna sanda na fitar da shi ba da har zai je hannun Sunusi. Miƙo mun ya yi da baƙar leda na kar
ɓ
a ina masa kallon rashin fahimta ya ce
"Yalla
ɓ
ai ne ya bani tun ji
ya da dare ya ce a siyo Ƙosai da Kunu".
A kan dining na ajiye kayan na bu
ɗ
e Ƙosan da basu fi ƙwaya goma sha biyar ba na rufe, Kunun ma ƙulli biyu ne tsululu da shi da gani ma na masara ne ina jin ko
ɗ
umin kirki babu sai wani ƙullin sugar abin dai kamar
na rusa kuka saboda takaici. A gurin na barsu na cigaba da abinda nake yi ina jiyo motsin bu
ɗ
e ƙofar sa lokacin ina mopping kan barander dan tun da ya dawo daga masallaci na jiyo shi yana share compound
ɗ
in ya kuma wanke na
ɗ
auka ma harda barander ya wank
e sai da na fita kar
ɓ
o ƙosan na ga gurin da datti shine na sake shareta na goge.
Fuska ba yabo ba fallasa ya tsaya yana kallo na, na gaishe shi daga in da nake tsaye ina
ɗ
auraye mopper ya amsa kafin ya shige cikin falon. Sai da na shanya mopper na kwas
he kayan wankin da na manta ban
ɗ
auke ba jiya kafin na shiga falon nima.
"Ina abin karyawa?" Ya fa
ɗ
a dai dai ina ƙoƙarin shigewa
ɗ
aki na, na nuna masa kan dining ba tare da na ce komai ba na shige
ɗ
akin, ban fito ba sai da na yi wanka na yiwa Al'amin n
a tarar ya bar mun Ƙosan guda bakwai sai ƙullin Kunu
ɗ
aya, Hijabi kawai na saka na goya Al'amin bayan na juye Ƙosan a farar leda na fita da su na bawa wani Almajiri sannan na wuce kanti na siyo abinda nake buƙata. Sai bayan na gama karyawa sannan na lura d
a dubu
ɗ
ayar dake ajiye kan dining da yar takarda a samanta na
ɗ
auka na bu
ɗ
e
"Ga ku
ɗ
in cefane nan" abinda ya rubuta a jiki kenan. Na ringa juya dubu
ɗ
ayar ina kallon ta a raina ina lissafa me zan siya da ita?
Cefanen yaushe ma yake nufi na rana kenan
ko kuwa har da dare? Da yake na siyo Indomie da rana ita na dafa da ƙwai na ci duk da ba wani ji na yi na ƙoshi ba ni tunda na dawo gidan ma nake ji na kamar wacce ulcer ta kama komai na ci bana ƙoshi ga Al'amin da tsotso har na fara tunanin ko dai na ha
ɗ
a masa da madara ko zan samu sauƙi.
A hanya bayan na dawo daga cefanen girkin dare wanda sai da na yi cikon dubu uku kafin na samu siyo abinda nake buƙata ina ƙoƙarin bu
ɗ
e gida na jiyo Maman Yusuf na kiran sunana, sai da na zura ledar hannu na ciki na
janyo ƙofar kafin na juya ina murmushi a raina ina addu'ar Allah ya sa bata ga kayan hannu na ba.
"Na aiko Khairat ta ce bakya nan sai Sunusi ya ce kin tafi cefane, maimakon ki bawa Sunusin ko kuma ki aiko nan ko Hauwa ce na turo miki ta yo miki cefanen
shine zaki ringa fita da kanki Amarya? Haka jiya ma fa na ganki can bakin titi da tsakar rana har ina cewa mai kama da ke ce ashe dai ke
ɗ
in ce dagaske ni na zata ma Oga ya koma Abujan ne shiyasa kike yawon cefane da kanki ashe yana gari" ta fa
ɗ
a tana kall
o na.
Na yi guntun murmushi na ce
"Aiken sauri ne kin san halin Sunusi kuma idan ka aike shi wani lokacin sai ka manta ma kafin ya dawo Hauwa kuma ai na ji randa kika shigo kin ce ta je gida an musu rasuwa ban san ta dawo ba ai".
Na
ɗ
auka zata wuc
e amma ta tsaya da alama shiga take so tayi ba'a son raina ba na bu
ɗ
e ƙofar muka shiga tare. Sai da na kai kayan kitchen kafin na dawo falo muka sake gaisawa ta ce
"Kiyi haƙuri kin sanni da shegen surutu da shiga abun da babu ruwana. Da safe Sunusi ya ce
mun maigidan nan ya aike shi siyan ƙosai da Kunu, naga an kwana da wuta Amarya ga blander ki babu abinda bata niƙawa
ɗ
an ƙosan da baifi kiyi na gwangwani biyu kuci har kuyi sadaka ba shine zaki bari a siyo muku a inda baku san tsaftar sa ba? Kunun ma ai ga
ra ki siyo geron kiyi gasara tunda yana so, In da kin aiko ma ni ina da gasarar sai na baki ki dama".
"Ni ce nayi sha'awar kunu da ƙosan ma naga kuma kafin na yi zan
ɓ
ata lokaci" na fa
ɗ
a ina murmushin yaƙe, tayi jumm kamar dai ba iya maganar da ta kawo
ta ba kenan kafin kuma ta miƙe tana cewa
"Shikenan dai bari na je dama baya zan zagaya gidan Maman Anisa kin san yaronta da ya tafi makarantar Sojoji Aliyu shine ya fa
ɗ
o daga sama suna training an dawo da shi gida jinya zan shiga duba shi".
"Ayya Alla
h ya bashi lafiya ya kiyaye gaba ayi masa sannu" na fa
ɗ
a ina taka mata, a bakin ƙofa ta tsaya ta ce
"Da babu abinda zakiyi ma se mu je tare tunda ba zama zanyi ba nima"
"Eh wlh girki zan yi da munje taren na fa
ɗ
a ina kallon Bilal dake tahowa daga
ɗ
akin
sa mamakin sanda ya dawo gidan ya kamani, ganin sa ya saka ta wuce ita ma ni kuma na koma ciki.
Tare muka shiga cikin falon ya dakatar da ni cikin
ɗ
aga murya yace
"Daga yau na soke shigowar duk wata matar unguwar nan cikin gidan nan kema kuma na hana
miki hul
ɗ
a da su tunda a gurin su kike koyon duk wani rashin mutunchin da kikeyi".
Nayi kasaƙe ina kallon sa kawai, wai nake koyon rashin mutunchi, ya cigaba da cewa
"Ita ga munafuka ta fito kai tsaye ta ce kina fita cefane za'a ce Mijinki baya kulawa
dake shine take ta wani zagaye zagaye. Shi Mijin nasu da ya gina musu ƙaton gida ya basu motoci suke wani jin kansu waye bai san
ɗ
an damfara bane ba? In sake ganin ta a gidan nan wlh sai na mata rashin mutunchi aikin banza kawai" fuuu ya fice.
Nayi mu
rmushin takaici a fili na ce
"Ashe kasan mutane zasu ringa kallonka a matsayin wanda bai iya riƙe gidan nasa ba amma saboda rashin son gaskiya zaka
ɓ
ige da fa
ɗ
an rashin dalili. Da ya dawo can falon sa ya ce na kai masa abinci na ha
ɗ
a komai na kai masa bay
an ya gama ya kira ni a waya ya ce na zo na kwashe kwanukan bayan na kwashe ya ce idan na kai su kitchen na je yana son magana da ni.
Kayan abinci ya nuna mun da ban san sanda ya shigo da su gidan ba, ya ce
"Gashi nan na siyo kafin ki cigaba da yi mun
Gorin tunda na aureki abincin da kika zo da shi daga gidan ku kike ci". Ni dai na yi murmushi kawai yace na je na shirya na dawo yana jira na, na san me yake nufi.
Washe gari da safe sauran abincin dare na
ɗ
umama muka karya da shi, mun tashi da walwal
a ba laifi saboda yanda daren jiyan ya kasance mana. Har ya gama shirin fita banga ya fito da kayan abincin ya kai su store ba dan haka na tuna masa, ina tsaye ya shiga kitchen ya fito da kwanuka na ringa kallon sa ina mamakin mai zaiyi ya wuce ya koma can
ɗ
akin ba da
ɗ
ewa ya ƙwala mun kira na je, ya nuna mun shinkafar daya auna cikin roba da ba zata wuce gwangwani uku ba sai mai da maggi, ya zaro
ɗ
ari biyar daga aljihun sa ya miƙa mun. Na ringa kallon kayan da ku
ɗ
in gaba
ɗ
aya na rasa kalmar da zan yi amfani
da ita gurin magana, shi kam ko a jikin sa ya ce
"Ki
ɗ
auka zan rufe ƙofa sauri nake yi kada na makara". Haka na fito da kwanon shinkafa da mai da Maggi na guda biyar akai kamar wacce ta je roƙo maƙwafta. Na da
ɗ
e a zaune baƙin ƙofar falo na mamakin abun
bai sake ni ba. Kenan awo Bilal zai ringa mun ko me? Ni bani da yancin da zan
ɗ
ibi abinci na dafa a cikin gida na sai iya abinda yaga dama ya
ɗ
ebo ya bani shi zanyi amfani da shi kenan?
Mai yake damun Bilal? Wai dama haka yake ko kuwa dai wani abun ne y
a canza shi da ban sani ba?
Yini guda na kasa kata
ɓ
us duk in na kalli shinkafar sai na ji duniyar ta mun duhu wani abu ya tsaya mun a ƙahon zuci na ma kasa dafata balle na ci. Gashi na rasa wanda zan kira na samu sauƙin abinda nake ji a raina, wai wa za
n ma zan iya gayawa wannan abun takaicin? Haka nan daga ƙarshe na ganin la'asar ta kawo kai na dafa masa da sauran cefanen da nake da shi amma ban iya ci ba cikin provision
ɗ
in da na
ɗ
an yi nayi ta dama Golden morn da cornflakes yini guda ina sha. Da yamma
daya dawo ya taho da nama, kifi harda kayan miya. Haka ya zauna ya raba su ya ƙulla a ledoji ya zuba a frizeer tare da gaya mun tsahon lokacin da yake da yaƙinin zasu kai kafin su ƙare.
Tun daga sannan muka
ɗ
oru akan sabon tsari, yawanci da safe zai s
iyo Lipton da sugar da buredi, wata rana in ya ga dama ya siyo madara da Milo ko ya siyo ƙwai. Su dankali, doya duk zai siyo ya ajiye sai dai irin ikon da yake gwadamun akan abinci ya saka lokuta da yawa nake haƙura da ko menene ya kawo sai dai na bar masa
kayan sa ya ci.
Da rana kuma shi zai
ɗ
iba mun iya abunda zan dafa cikina da nashi. Sau
ɗ
aya na masa magana akan idan kuma muka yi baƙi fa? Yaya zanyi tunda kulle
ɗ
akin yake yi? Bai bani amsa ba nima kuma ban sake tayar da zancen ba, sauƙin ta ban fiya
yin baƙi daga
ɓ
angare na ba, shima yan uwansan da suke zuwa a da yanzu duk sun
ɗ
auke ƙafa Abubakar ne ka
ɗ
ai zan ce har yanzu alaƙar mu take nan bai canza layi ba sai kuma Anty Amina ita kuma tsakanin mu gaisuwa a waya ne ko kuma idan mun ha
ɗ
u a gidan Hajj
a.
A haka rayuwa ta bu
ɗ
e sabon shafi, na yaye Al'amin na
ɗ
auki cikin Sharifa. Tun ina ganin bazan iya jurewa ba har na haƙura na saba abin ma ya dena damuna musamman da hakan ya kasance silar dawowar nutsuwa da kuma walwala cikin zamantakewa ta da Bila
l. Mun dena fa
ɗ
a, soyayya da tattalin da nake kwa
ɗ
ayin ina samun su da na zauna nayi tunani sai naga dama ita rayuwa bata ta
ɓ
a zamowa mutum
ɗ
ari bisa
ɗ
ari yanda yake burin ta kasance masa.
Wasu matan sukan samu biyan buƙata na ababen more rayuwa amma k
uma su rasa kula da farin ciki a gurin mazajen su. Wasu kuma su rasa wadata amma su samu farin cikin. Ni da na fa
ɗ
a a tsaka tsaki domin dai ko da bana samun abinda na saba da shi ko nake so bai bar ni da yunwa ba. Sannan ina samun soyayya da tattalin da na
tabbatar ba kowacce mace ke samun irin haka a gidan auren ta ba, amma duk da haka na sani Son da nake masa ne ya lullu
ɓ
e komai a ido na. Allah ya sani ina son Bilal son da ban san iyakar sa ba ba kuma na fatan ruyuwa babu shi dan nasan bazan iya ba.
C
ikin ku
ɗ
in da nake dasu a hannu na da na account nake cira nayi duk abinda nake da buƙata wanda bai bani ba. Sau tari zuciya ta takan raya mun na siya abinda nake so na dafa na ci ni ka
ɗ
ai idan baya nan amma sam na kasa yarda da hakan, ko gida na je na sam
o abu bazan iya
ɓ
oye masa ba. Tunda kuma ya fahimci akwai ku
ɗ
i a hannu na
ɗ
ari biyar
ɗ
in da ya fara bani a matsayin ku
ɗ
in cefane ma ya daina kwata kwata. A cewar sa babu abinda baya siyowa bai kuma ta
ɓ
a tunanin abinda yake siyowar ko yake
ɗ
ibar mun baya is
a ba. Zan dafa abinci da naman kaza ya ci har ya fini iko akai ba tare da ya tambaye ni a ina na samu ku
ɗ
in da na siyi kazar ba.
Bai ta
ɓ
a gani na da wata sutura ko abin kwalliya wanda ba shi ya siya mun ba kuma ya tambaye ni a ina na samu, idan akwai a
binda nake jin damuwa akai har ya jefa ni a tunani bai wuci yanda bai damu da komai ba har idan ba hurumin sa na shiga ba. Amma kuma daga ranar da ya fa
ɗ
a mun wata magana, daga lokacin na fahimci kuskuren da mutane suke ta fa
ɗ
in na yi akan auren Bilal, a r
anar kuma na fara shakkun sahihancin ƙaunar da nake tunanin yana yi mun ya saka mun kokwanto akan aihinin manufar sa akan aure na.
Kuyi haƙuri, In sha Allahu daga yau har Friday zanyi post. Daga nan zamu tafi hutun azumi idan Allah ya saka mun kasance
cikin wa
ɗ
anda zasu gani.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 070618384
88* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 30*
Watan Al'amin goma sha takwas na
yaye shi a kuma watan na samu wani cikin wanda ko kusa Bilal bai yi maraba da samuwar sa ba.
"Wai dama bakiyi komai na tsarin Iyali ba? Ni na zata hankalin ki zai baki da kiyi ba sai an tuna miki ba, kina kallon yanda abubuwa duke tafiya kuma kawai zaki k
ama ki wani sake yin ciki. To ni dai gaskiya ban so haka ba" Abun da ya fa
ɗ
a kenan lokacin da na shaida masa ina da cikin.
Gaba
ɗ
aya sai na rasa yanda zan fassara maganganun sa. Fassara ta kai tsaye dai na san yana nufin baya son cikin kenan sai dai na
yi ƙoƙarin kyautata masa zato da bashi damar gyara maganar sa ta hanyar cewa
"Yanzu mai kake nufi kenan?"
"Duk yanda kika
ɗ
auka haka nake nufi ni dai na fa
ɗ
a miki ban so kika sake samun wani ciki yanzu ba. Kina sane tun ba yanzu ba na gaya miki a tsar
i na gaba
ɗ
aya bana so yayana su haura guda uku, yanzu ƙasa da shekara hu
ɗ
u kina shirin yin