Showing 102001 words to 105000 words out of 287295 words
duk yan da aka yi sun so ne su mayar da ke daddawar
ɓ
urma, ke kuma So da ƙuruc
iya ya rufe miki ido kika kasa gane hakan".
"Kallon rashin fahimta nayi mata dan ban ta
ɓ
a ji ba balle na san ma'anar kalmar da ta fa
ɗ
a daga ƙarshe; ta ci gaba da cewa
"Ko a ƙauye ban ta
ɓ
a ganin in da ake haka ba. Haihuwar fari dai ko mutum shi ya yanke
wa talauci cibiya yana ho
ɓɓ
asa da taimakon dangin sa ya yi abu na bajinta balle wannan yaron da duk wanda ya kalle shi ya san babu rashi a tattare da shi sai dai mugunta kawai ta hana ya yi miki abin da ya kamata. So ya ke yan da ya aure ki ki zame masa ha
nnun jari komai iyayen ki su ringa
ɗ
akkowa suna baki toh ni dai ba zuga ki na ke yi ba amma tun da sauran hasken rana duhu bai cimmiki ba ki ki farka ki kuma ƙwatarwa kan ki yan ci domin har idan kuka miƙe a haka tabbas ke zaki sha wahala musamman da ya ka
san ce ya riga da ya gane son da kike masa ya fi na sa".
Mayar da kai na nayi ƙasa kawai ina sauraron ta, zuciya ta na so ta kama abin da take fa
ɗ
a amma kuma wani
ɓ
angaren ya kore maganganun nata. Kullum haka suke cewa Bilal ba ya so na ni kuma ba zan t
a
ɓ
a yarda da hakan ba. Abin da na jaddadawa zuciya ta shine Bilal ba shi da ku
ɗ
i sannan ya na da matsalar rashin iya tantance kalmomin da ya kamata ya yi amfani da su a magana shi ya sa yake fa
ɗ
ar kowacce irin magana ta zo bakin sa ba tare da ya taunata ba
, wannan kuma
ɗ
abi'ar mutane da yawa ce ba shi ka
ɗ
ai ne haka ba. Wannan tabbacin na bawa kai na ya kuma kore tasirin da maganganun Baba Jummai suka so suyi a ƙwaƙwalwa ta.
"Bilal ya na so na, kuma na san ba shi da shi ne shi ya sa amma babu abin da ba
ze yi mun ba Baba Jummai" na bata amsa ina murmushin da be kai zuci ba, ta ƙura mun ido kafin ta ce
"Yanda ki ke kyautata masa zato Allah ya bawa mara
ɗ
a kunya a sanda zai samu wadatar yi mikin" daga haka ta miƙe tana gyara goyon Al'amin kamar yanda Abba y
a ce ba za'a saka masa wani sunan iyayi ba a kira shi da hakan. Tana rufe mun ƙofar na sake fashe wa da kuka, ni ya ke cewa ba ni da tunani kuma ba ni da tsoron Allah na
ɓ
oye ku
ɗ
i ban ba shi ba.
Ƙ
arar waya ta ta sa na tashi na
ɗ
akko ta, Anty Labiba ce.
Sai da kirab ya katse wani ya sake shigowa lokacin na dai dai ta kaina kafin na
ɗ
aga.
"Bacci kika fara ne?" Ta tambaya nasan kuma murya ta da ta ji ne dalili, na samu gangara dan haka na ce mata
"Eh wlh, na ga ji ne; na
ɗ
an kishingi
ɗ
a ban ma san ashe b
acci ya
ɗ
auke ni ba"
"Sannu, toh ya kuka yi da Bilal
ɗ
in?" Ta sake fa
ɗ
a. Sabon kuka ne ya kusa ƙwace mun amma na danne shi da ƙyar na ce mata
"Ni fa ban yi masa magana ba Anty saboda kin ga fa wayar sa da aka ƙwace sun yi amfani da ita sun kwashe masa k
u
ɗ
in account duka, kuma ba'a yi albashi ba ai se yaga rashin hankali na ma idan na yi masa maganar wasu ku
ɗ
i yanzu, sannan gashi ba shi da lafiya ko fita ba ya yi a zo a tara masa hayaniya a kai a babu da
ɗ
i".
"Kuma haka ne" ta fa
ɗ
a amma se na rasa har
ran ta tayi maganar ko kuma baƙar magana ta fa
ɗ
a mun tunda na san halin ta sarai, a sanyaye na sa ke cewa
"Kawai a bar taron ko Anty tun da dama yawancin duk wa
ɗ
an da zasu zo sun je tun muna asibiti wa su kuma sun zo nan gidan".
"Shikenan se ayi hakan,
amma dai kin san yan Galadanci ko an ce babu taron suna ba zasu fasa zuwa ba kuma jiya Mama duk ta sake aika musu da yaji wanda ya manta ma kin ga an tuna masa, amma dai shikenan tun da mai gida ya ce ba za'a yi taro ba ai ba a zo masa gida ba bari na kir
a ta yanzu se a gaya musu a can gidan ku za'a yi sunan dama ai ba wani abu bane taron sunan a ha
ɗ
u ne kawai a ci abinci ba lalali sai kina gurin ba".
"Aa fa Anty shi ba cewa yayi kar ayi ba" na yi saurin katseta kafin ta ƙulla wata maganar, ba ta ja zan
cen da tsayi ba ta mun sallama bayan da ta ce itama ai ba cewa tayi shi ya hana ba ta fahimci maganata kawai zasu yi taron su a gidan Mama shikenan. Ranar kasa bacci na yi har guraren ƙarfe uku sannan, maganganun Bilal suka yi ta mun yawo a zuciya, se da n
a ji kaina yana neman tarwatsewa saboda ciwo kafin na rarrashi kai na nayi bacci.
BILAL
A fusace ya fice daga
ɗ
akin ya koma
ɓ
angaren sa. A falo ya kwanta ya tada kansa da hannu biyu ya tafi tunani,
Waccen ranar da ya gamu da tsautsayi bayan sun rabu
da Nasir ya koma gidan Hajja ya tarar da ita ta na shirin tafiya dubo Halima ya hanata, bayan sun koma
ɗ
aki ta ke ce masa
"Amma yanzu idan ba mu je ba kar ace mun yi rashin kyautawa, musamman da Balarabiya ce matar ƙanin uban ta ta shigo har nan ta gaya
mun kaga ai ko da kai ba'a kira ka ba ni ai an gaya mun ka bari kawai na je dai". Zama yayi ya kalallame ta da zance yana nuna mata ai matsayin su ya fi ace can wata za'a aiko ta fa
ɗ
a musu kawai ta ƙyale su idan ma za'a je
ɗ
in se gobe da safe tukunna tun d
a yanzu dare yayi. Har ƙarfe tara yana gidan Hajjan sai da ya ci abinci kafin yayi mata sallama ya tafi gida a bakin titi suka sake ha
ɗ
uwa da Nasir ya ringa masa masifa da ya ce masa bai je asibitin ba har sannan amma ko a kwalar rigar sa ya ce shifa sai d
a safe sannan zai je. Sai da ya koma gida kuma gaba
ɗ
aya ya kasa tsaye ya kasa zaune. Har ya kwanta ya ringa jin kamar hakan da ya aikata ganganci ne musamman da bai san me suka fa
ɗ
a da suka je gidan ba kar wannan ƙin zuwan da zai yi ya sa a gasgata magana
r su. Sha
ɗ
aya tayi amma haka ya zura jallabiya ya fita. Bai kuma yi nisa da fita daga layin su ba wasu da bai san ko su waye ba suka tare shi, kafin ya yi ihu suka rufe masa baki su uku ne, mutum biyu suka masa dukan tsiya
ɗ
ayan ya haye mashin suna gama j
ibgar sa suka zare wayar sa suma suka hau mashin
ɗ
in su ka arce.
San da aka maida shi gida a lokacin da ya ha
ɗ
a ido da Halima se ya godewa Allah da abin da ya faru da shi domin da bai san da wane irin ido ze kalle ta ko ya kalli yan uwan ta ba dan haka
nan ya yarda haƙƙin barin ta
da wahalar naƙuda ne ya jefashi halin da ya samu kan sa a yanzun amma kuma sanadin haka ya shafe laifin sa a idon dangin ta babu wanda ze tayar da maganar ƙin zuwan sa asibiti. Amma kuma bai zata za'a dawo da Halima gida ba, ya
ɗ
auka daga haka zata wuce gida wanka amma kuma sai gashi an maido da ita, wannan tabbas be yi masa da
ɗ
i ba saboda shi dai yana so ta tafi gida wanka ko babu komai zai samu sauƙin wasu hidimomin amma ita ya rasa dalilin ta na son dole se ta zauna a gidan b
a zata tafi gidan su ba. Shi ya cewa Hajja ta yiwa su Anty Labiba magana akan su maida Halima gida shima can gidan Hajjan zai tafi amma suka ƙi, zaman kwana biyar
ɗ
in nan tabbas ba dan Anty Amina ba da bai san yanda ze yi ba saboda shi dai bai yi wani tana
di ba.
Shi ya sa ya ci gaba da langwa
ɓ
ewa yaƙi ƙarfafa jikin sa, ba ƙaramin da
ɗ
i ya ji ba ganin sun ha
ɗ
o kayan barka, ko da bai kama ƙafar wanda aka kawo daga gidan su Haliman ba amma dai sun fitar da shi kunya dan da ace shi suka bari ya yi ko ya baya
r da ku
ɗ
in ayi da tabbas ko rabin hakan babu lallai ya samu. Yanzu ragon suna ka
ɗ
ai ya rage masa, da yayi zaton tun da Abba ya yiwa takwara ƙila cikin halin dattako irin nasa ya bashi rago kyauta a yankawa takwaran sa, amma sa
ɓ
anin da suka samu da Halima a
kan zancen sunan ya tabbatar masa da ko da ace Abban ya ambata ze bada tabbas ba zata bari ba domin ya lura hu
ɗ
ubar Anty Labiba ta fara tasiri a ƙwaƙwalwarta tun da har zata iya
ɓ
oye abu a
ɗ
aki ta ringa ci ita ka
ɗ
ai yana kwance bashi da lafiya amma bata ba
shi ba; ya san kuma hu
ɗ
ubar Anty Labiba ce.
Already kayan abincin su dama saura ne ya san kuma kafin yan barka su janye zuwa ma sun ƙarasa cinye komai sannan azo batun cefane da sauran kunji kunji, gaskiya shi ba shi da sukunin da zai iya kulawa da mai
jego a yanayin da ake ciki, ya mata hannun ka mai sanda taƙi ta fahimta shi yasa kawai ya yanke shawarar biyo mata ta wata sigar ya rutsata a
ɗ
aki ko zata ji tsoro ta tafi amma duk da haka shi bai ga alamar zata tafi ba tunda ma maganar taron suna ta ke yi
.
Ko naman ƙaurin da aka kai gidan su da farko ya ji da
ɗ
in abun amma da ya je gidan Hajja se abub ya juye masa zuwa
ɓ
acin rai. Hajja ta ce masa wulaƙanci ne ya sa zasu aika musu da
ɗ
anye nama saboda su ja a zage su a gari bayan kowa ya san yanzu an den
a wani ƙauri se su sarakan iyayi, idan dan Allah ne kuma ai da gidan Bilal
ɗ
in ya kamata a kai San a yanka idan so ake a siya masa mutunchi ba wai a wani sako musu ƙafar baya
ɗ
aya da rabin ƙirji a buhu a kai musu gida ba. Ta ringa masifa, hatta da kayan ba
rka sai da tayi ƙorafin saboda nan ma a nuna musu iyakar su ya sa zasu ha
ɗ
o kaya kamar zasu bu
ɗ
e kanti, ai ba gwaninta suka yi ba, taƙamar mace ai ta gidan miji ce ba ta gidan uba ba idan so suke suyi bajin ta se su bu
ɗ
a masa Abba ya saka shi a harkokin sa
shima ya samu ku
ɗ
i ta yanda ze ringa musu abu na bajin ta yanda suke so. Maganganu dai ba kai ba ƙafa wanda shi kuma ya ji su kamar fami a ran sa dan daman abinda ya da
ɗ
e yana ci masa tuwo a ƙwarya ne ya dai rasa da wa zai tattauna da zai fahimce shi shi
yasa yake yin shiru.
Yanzu tunanin ta in da ragon suna zai fito ya ke dan dagaske ba shi da wasu ku
ɗ
i a hannun sa kuma bai yi yunkurin nema ba. Hafiz ya saka ran ze iya masa wannan rufin asirin tun da ya iya bashi na layya ma balle wannan da ya jefi ts
untsu biyu da dutse
ɗ
aya ya ce masa Dad
ɗ
in sa ya yiwa takwara, to kuma tafiyar gaggawa ta kama shi ranar da ya ce masa zasu
dawo Kano se dare ya sake kira a wayar Haliman ya ce masa ba ze samu shigowa Kano ba tafiya ta kama su zasu tafi Finland amma ze tu
ra masa da saƙo har yanzu kuma saƙon bai iso ba bai kuma san ta yanda zai same shi ya tuna masa ba. Ku
ɗ
a
ɗ
e da suke ha
ɗ
awa na abokanan su na unguwa ko kar
ɓ
ar su a hannu bai yi ba ya ce a bawa Kabir dama akwai shaddojin da ya siya a gurin sa har an
ɗ
inka bai
ƙarasa biyan ku
ɗ
in ba da ya san Hafiz zai masa haka da ragon ya siya da su idan ya so in akayi albashi sai ya cikawa Kabir
ɗ
in. Da wannan fushin ya komada niyyar kar
ɓ
ar wayar ta ya duba Hafiz
ɗ
in ko ta Whatsapp ne amma ta tare shi da zancen shirme ta sake
ɓ
ata masa rai.
Haka ya kwana yana juyi da tunanin ta in da rago zai fito, wani tunani ya yi, ya tashi da sauri ya shiga laluba rigar da ya cire. Shaf ya manta da ya yo swapping na layukan sa. Rashin azanci ya sa ya manta bai siyi ko ƙaramar waya me to
uch light ba, ta yuwu ma Hafiz
ɗ
in ya tura masa ku
ɗ
i ta account bai sani ba. Ɗan dama dama ya ji, duk da dai ko ya tura
ɗ
in dole se ya je banki saboda ba asalin account
ɗ
in sa wanda aka ya she shi ya tura masa ba wanda ya ke saving a ciki ya bashi shi kuma
dama bai yi activating USSD transafer ba dole se ya je banki rufin asirin da Allah ya masa kenan da tuni nan ma sun yashe shi. Da wannan murnar ya yi bacci, washe gari kuwa daga sallar asuba bai dawo gidan ba ya wuce gidan su in da za'a ra
ɗ
in suna daga ca
n kuma bayan gari ya waye sosai ya wuce banki.
HALIMA
A makare na tashi saboda baccin da ban samu na yi da wuri ba. Kallo
ɗ
aya za'a mun a karanci damuwar da ke cunkushe cikin zuciya ta wadda fuskata ta gaza
ɓ
oyewa. Ko da na yi wanka gado na sake komaw
a na kwanta dan bani da kuzarin da zan iya yin wata kwalliya. Ina kallon Baba Jummai har ta gama shirya Alameen ya yi kyau sosai ta ringa masa rawa kafin ta saka shi cikin gadon sa ta fita ta bar mu bayan da ta sake jaddadamun akan na tashi na shirya kafin
mutane su fara zuwa.
Ina saka kayan ina tunanin yanzu idan muka yi baƙin me zan basu? Sai lokacin na jinjinawa wautata, da na sani kawai na cewa Anty Labiba ya bani ku
ɗ
in, har ga Allah ba zan so aga gazawar Bilal ba musamman a irin wannan lokacin.
T
unani na yi ko na bawa Baba Jummai ta je tayi cefane idan ya so na kira maƙwafta na su Maman Yusuf su yi abincin tun da ko jiya da rana sai da ta aiko ta tambaye ni akwai aikin da za'a yi na ce mata babu, ni duk na manta ma ko ba'ayi abinci dan kowa ba ai
na yi saboda maƙwafta na tun da dai ban gaya musu ba zanyi taro ba kuma a cikim layin ko ba zasuyi taron suna ba su kan yi wani abu a aika gida gida.
"To ko snacks zan yi order?" Wata zuciyar ta raya mun, na zauna gefe gado ha
ɗ
i da rafka tagumi. Ko ban b
awa Anty Labiba komai ba na san da na fa
ɗ
a mata gaskiyar Bilal ya ce bashi da ku
ɗ
i ƙarƙari ta zage shi amma za'a yi komai a kawo mun daga gida amma yanzu na ce mata ni ce bana son yin taron sunan ko dai kawai na ha
ɗ
a kaya na na tafi can gidan tun da su zas
u yi taron a can? Amma kuma Bilal zai yarda? Duk na ringa jerwa kaina tambayar da bani da mai amsa mun. Sanda na fito daga
ɗ
aki tara har ta gota amma kamar ba gidan suna ba babu wanda ya ƙwanƙwasawa mana ƙofa balle mutane su fara taruwa. Har raina na ji ba
bu da
ɗ
i na tabbatar kuma Mama ta fa
ɗ
awa yan Galadanci kar su zo saboda bada haka ba tun sassafe nasan tsofafin gidan mu zasu zo kar
ɓ
ar suna su kuma yan gidan su Bilal ba na ce ga abinda ya hana su zuwa ba.
Da ƙyar na tura shayi da ƙwan da Baba Jummai ta
soya mun, ina zaune zugui ni ka
ɗ
ai dan Baba Jumman ta shiga wanka, get na ji ana bugawa. Se da na dan zabura a raina na shiga addu'ar Allah ya sa kona wanene ba daga
ɓ
angare na bane. Mayafi na
ɗ
akko