Showing 279001 words to 282000 words out of 287295 words

Chapter 94 - KURA A RUMBU COMPLETE

ba. Ta shanye baƙin ciki, ta

ɓ

oye damuwa, ta jure tozarci da wulaƙanci amma daga ƙ

arshe ya biyewa shai

ɗ

an ya barta.

Tabbas, yanzu da bulalar nutsuwa ta sameshi ya fahimci kura-kuren daya tafka a zamantakewatarsa da Halima ya kuma yarda da cewar da mutane da yawa sukeyi haƙƙinta sai ya bibiyeshi.

Duk abinda ya samu ta silarta ya rasa

shi, wa

ɗ

anda sukayi saura ma ya sani yana dab da rasa su uwa uba ya rasa mutunchi da ƙimarsa.

Ya ringa tafka kuskure a koda yaushe yana raya cewa nan da lokaci ka

ɗ

an zai daina, zai gyara kura-kurensa sai dai a duk sanda ya yi yunƙurin dainawar sai zuciy

a ta sake angizashi ta sake kwa

ɗ

aita masa wani abun ya sake ƙudurce idan ya same shi zai tuba a haka yayi ta zurmawa har aka kawo wannan lokacin daya fa

ɗ

a cikin rijiya mai gaba dubu. Bai fahimci talala ubangiji ya ringa masa ba sai yanzu daya kama shi dumu

-dumu.

A haka ma kuma ya godewa Allah domin ya masa gata da bai barshi ya mutu a kan

ɓ

arna ba, yana addu'a da fatan abinda ya faru ya zame masa ishara da sauran masu hali irin nasa.

A haka ya shafe sati biyu a kurkuku cikin yanayin da shi ka

ɗ

ai zai

iya fasaltawa. Sai ya kwana ya yini bai saka komai a cikinsa ba dan hatta da ruwan gurin baya iya sha. Shopping sosai Zulaiha tayi masa harda miya da soyayyen nama ta kai masa amma yana shiga ciki wasu suka ƙwace bai kuma iya yin ko tari ba domin fuskokin

su ka

ɗ

ai daya kalla ya san babu abinda suke jin tsoro, zasu iya yi masa komai tunda dama ba barin gidan zasuyi ba da yawansu

ɗ

aurin rai da rai aka yi musu. Haka ya shafe kwanakin cikin wahala da ciwo, ga zazza

ɓ

i ga damuwa da tashin hankali kafin cikar loka

cin idan ka ganshi sai ka

ɗ

auka shekara goma yayi ba wai sati biyu ba.

Yayi baƙiƙƙirin, tunda yaje sau uku yayi wanka shima ba soso ba sabulu haka kayan jikinsa sai da wani da suke cell

ɗ

aya ya taimaka ya wanke masa. Abu ne ya ha

ɗ

u da mai son jiki wand

a bai saba da wahala ba shiyasa abin ya masa yawa, yan uwansa babu wanda bai zubar da hawaye ba lokacin da aka kawoshi za'a shiga dashi kotun.

Hajja data dage sai an je da ita haka ta kware baki ta fashe da kuka tana cewa

"Sai kace wanda yayi kisan ka

i kalli yanda suka mayar mun dashi?"

"Koma menene shi ya janyowa kan sa ai Hajja, kuma babu wanda ya masa komai, Abubakar ya ce baya cin abinci baya wanka ai dole ki ga ya zama haka. Kawai kici gaba da addu'a Allah yasa shari'ar ta zo a yanda muke fata

kawai" Anty Ladidi ta fa

ɗ

a mata.

Sai da akayi Shari'a biyu kafin aka zo tasu, bayan maganganu daga kowanne

ɓ

angare, Lawyer Alhaji Lawan ya tabbatarwa da kotu an mayarwa da Client

ɗ

insa ku

ɗ

a

ɗ

en daya bayar na siyan gida ciff ba tareda ko naira biyar tay

i ciwon kai ba. Shima lawyer Jalilah ya fa

ɗ

i an mayar musu da wani kaso na daga jumullar ku

ɗ

in kayan da aka

ɗ

iba, kuma client

ɗ

insa ta amince da roƙon da yan uwan wanda ake ƙara sukayi na cewa za'a ringa biyanta ku

ɗ

in a hankali har a warware. Abinda yayi s

aura tsakaninsa da kotu ne domin jin matsayin laifukan daya aikata a matakin dokar ƙasa.

Alƙali Yakubu Bechi daya gama sauraron jawabi daga bakin lawyoyi yayi rubuce rubuce kafin ya fara karanto hukunci kamar haka.

"Bayan sauraron kowanne

ɓ

angare, an

gabatar da hujjoji masu ƙarfi da suka tabbatar da cewa Bilal Saleh ya fasa store da Jalilah Muhammad ta ajiye kaya in da ya

ɗ

ebi kayan da ku

ɗ

insu ya kai kimanin naira miliyan talatin (₦30,000,000)."

A firgice Bilal ya

ɗ

aga kai ya kalli inda Jalilah tak

e zaune, ta kuwa sakar masa murmushi harda kashe masa ido

ɗ

aya. A ina ya

ɗ

ebi kayan miliyan talatin? Amma ya zaiyi? Bai isa ya musa ba ko na miliyan dubu tace ya

ɗ

iba haka nan zai amsa tunda shi ya jawa kansa.

Mayar da kai yayi ya cigaba da sauraron Alƙ

ali dake cewa

"An samu shaidar hoto mai motsi daga CCTV camera da kuma shaidu na gani da ido wanda suka ga lokacin da aka fita da kayan.

Haka kuma, an tabbatar da cewa ka damfari Alhaji Lawan Isiyaku in da ka siyar masa da gidan da Jalilah Muhammad ta b

aka kake kula mata dashi bayan ka gabatar da bogi, ka kar

ɓ

i naira miliyan hamsin da biyar (₦55,000,000)".

Alƙali Yakubu yaja fasali kafin ya ci gaba da cewa

"Duk da haka, kotu ta lura da wasu abubuwa masu muhimmanci:

Ka amsa laifinka tun farko ba tare

da wasa da hankalin kotu ba. Sannan kotu ta samu tabbaci da shaidar mayarwa da Alhaji Lawan ku

ɗ

insa da kuma wani

ɓ

angare na ku

ɗ

in kayan Jalilah Muhammad bayan kotu ta fara sauraren shari’ar.

Sannan, a zamanka a kurkuku ka nuna cikakkiyar nadama da bayy

anannen yunkurin gyara ta hanyar ayyukanka wa

ɗ

anda ma'aikata suke lura da shi.

Wannan kotu ba ta tsaya kan hukunci ba kawai, tana kuma la'akari da gyara da dama ha

ɗ

i da niyyar shiriyar wanda ya aikata laifi. Saboda haka, kotu ta yanke hukunci kamar haka:

1-A kan laifin fasa store da sata, kotu ta yanke maka hukuncin shekara biyar (5) a gidan gyaran hali, amma za a dakatar da aiwatar da hukuncin zuwa nan gaba idan aka sake samunka da aikata wani laifin (suspended sentence) a tsawon shekara biyu.

2-A k

an laifin damfara, kotu ta yanke maka hukuncin shekara bakwai (7), sai dai saboda ka mayar da ku

ɗ

in da kuma nadamar da ka nuna, kotu ta sauya hukuncin zuwa shekara uku (3) ko kuma tarar naira miliyan goma a matsayin diyya ga wanda aka damfara, sannan da ai

kin taimakon al'umma (community service) na tsayin shekara

ɗ

aya a ƙarƙashin kulawar hukumar gyaran hali. Sannan ba zaka tsaya takarar siyasa ko samun wani promotion na aiki ba a tsakanin shekaru biyar masu zuwa.

3-Zaka biya gomnati tarar naira miliyan 5

diyya ga gwamnati a matsayin horo da kuma darasi akan laifukan daka aikata. Karya

ɗ

aya daga cikin Sharu

ɗ

a ko sa

ɓ

awa doka yana nufin kotu zata dawo da cikakken hukunci ha

ɗ

i da ƙari a kai.Ina fatan hakan ya zame maka darasi a rayuwarka da sauran masu aikata

laifuka irin naka." Daga haka ya buga guduma wacce take nuna tabbatuwar kammala hukunci.

Bilal dake jingine da katakon box

ɗ

in da yake ciki ya

ɗ

ago idanuwansa cike da hawaye, tsananin nauyi da kunyar da yakeji ta saka ya kasa

ɗ

aga ido ya kalli

ɓ

angaren

da masu sauraron Shari'a suke. Yana jin nauyin idanuwa akansa amma bashi da ƙarfin guiwar da zai iya ha

ɗ

a ido da kowa a yanzu. A hankali ya zame a gurin, ya fashe da kukan da bai shirya yin sa ba.

Bai san inda aka shiga aka fita har aka nema masa yanci,

sau

ɗ

aya lawyer da aka

ɗ

aukar masa yaje gurinsa a prison shima basu wani yi magana mai tsayi ba ƙorafi yayi masa akan amsa laifinsa da yayi a kotu bayan ya tsara masa duk abinda zai fa

ɗ

a idan anje.

Abubakar da Nasir ne a duk sanda sukaje suke bashi tab

bacin ya kwantar da hankalinsa Insha Allahu komai zai dai-daita. Koma dai mai akayi ya godewa Allah ya kuma godewa

ɗ

anuwansa da Amininsa Nasir da basu dubi halinsa sun wofantar dashi ba.

Kamar an ce ya sake

ɗ

aga kansa karaf suka ha

ɗ

a ido da Halima dake

zaune a row

ɗ

in dake kusa da ƙofa. Ji yayi gabansa ya fa

ɗ

i, tayi masa wani irin kwarjini, kallon da takeyi masa daya fassara na baƙin ciki da jin kunyar abinda ya aikata. Kasa daina kallonta yayi kamar yanda itama take kallonsa kafin ta miƙe a hankali ta f

ice daga

ɗ

akin kotun wani wanda bai san ko wanene ba da sai lokacin ya lura dashi ya bi bayanta riƙe da jakarta data bari akan table.

Sam bai ji maganar da

ɗ

ansandan dake kusa dashi yakeyi masa ba sai da Barr Sajid ya ƙaraso gurin yana murmushi da yi ma

sa barka. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi yana amsawa dukda hankalinsa gaba

ɗ

aya yana kan Halima da tunaninsa ya tafi akan sanin wanene wancan daya bi bayanta?

A wajen kotun bayan murna da jaje daga yan uwa, Hajja dake riƙe da hannunsa kamar wani zai ƙ

waceshi ta kalli Barr Sajid da yace zasu tafi da Bilal

ɗ

in a ƙarasa cike takardu. Kamar zata fashe da wani kukan tace

"Ɗannan ba an sallame shi ba?"

"An sallame shi Hajiya, amma dole sai munje anyi cike-ciken takardu tukunna. Ganin harda Abubakar suka t

afi ya saka hankalinta ya

ɗ

an kwanta suka wuce gida tareda su Anty Amina da sauran yan uwa da suka halarci zaman kotun.

Dab da magriba su Bilal suka isa gidan Hajja a motar Nasir shi da Nasir

ɗ

in sai Abubakar. Yanda yake jin jikinsa tamkar wanda aka haƙ

o daga rami ya so ace kai tsaye gida suka fara kai shi yayi wanka tukunna ko Asibiti ma dan shi ka

ɗ

ai ya san abinda yake ji amma dai yayi shiru har suka isa gidan Hajjan. Nasir ya musu sallama da addu'ar Allah ya ƙara kiyayewa. Abubakar na kallon Bilal ya

ce

"Yaya Nasir yayi maka ƙoƙari, duk tarin abokananka shi ka

ɗ

ai ya tsaya da jikinsa da aljihunsa har Allah ya ƙwatoka. Ka gode masa kuma kada kayi wasa da abotarku dan shi

ɗ

in mai sonka tsakani da Allah ne"

"Haba Abubakar ai babu zancen godiya tsaka

ninmu duk abinda nayi saboda Allah ne ba dan a gode mun ko wani abu ba. Ni dai fatana ya kiyaye Allah kuma ya sake tsare mu baki

ɗ

aya" Nasir ya fa

ɗ

a daga haka yaja motarsa ya wuce su kuma suka shige ciki ganin unguwa da yara sun fara taruwa suna kallonsu.

Falon Hajjan cike da yayanta da yan uwanta da suke jiran dawowarsu, gida ya sakw cika da murna da kuma jaje. A ƙofar

ɗ

akin da Abubakar yake ya hangi Zulaiha tsaye yana masa murmushi, bai ganta

ɗ

azu a kotu ba, ko kuma bai lura bane oho haka dai suka shig

e falon Hajja bayan ya

ɗ

aga mata hannu. Abubakar ne yace yaje ya huta suma matan kowa ta wuce gidanta haka kuma abun ya isa.

A tsakar gida ya kalli Abubakar ya ce

"Ka samo mana Adaidaita na gaji wlh kamar zan fa

ɗ

i nakeji"

"Ga ruwa can ai naga ta k

ai maka ka samu kayi wanka bari naje na samo maka abu mai

ɗ

an ruwa ko yoghurt ne, ga magungunan da Yaya Nasir ya taho maka dasu yace idan kasha zaka samu sauƙin ciwon jikin kafin safiya sai muje Asibiti" Abubakar ya bashi amsa yana nuna masa Zulaiha dake t

saye ƙofar ban

ɗ

akin tsakar gida, ya kalleta ya kalli Abubakar

ɗ

in, bai dai yi magana ba ya wuce

ɗ

akin da ta shiga zuciyarsa cike da tambayoyi.

Ɗ

akin na nan yanda yake Katifa ce Gado huta a ciki sai ƙaramin carpet a tsakiyar

ɗ

akin daga gefe kuma ga alwat

una da yake zaton kayansa ne dana Zulaihan a ciki. Towel

ɗ

in data fitar ta bashi ya cire kaya ya

ɗ

aura ya yafa wani ƙarami kafin ya fita yana sunkuyar da kai ya shiga wankan. Bokiti uku ta ajiye masa sai da ya gamsu dan kansa da wankan da yayi kafin ya fit

o yana jinsa kamar wanda aka sake haihuwa. Bai san inda zai tsoma ransa ba da ta tabbata zai yi zaman kurkuku na shekarun da yaji ana ambatowa. Ko a ina aka samu ku

ɗ

a

ɗ

en da aka ce an biya masa bashin ma sai Allah domin dai bashi da su bai kuma bawa wani aj

iya ba.

Ka

ɗ

an ya ci abincin da Zulaiha ta shirya masa bayan yayi sallar magriba da aka kira yana wanka. Yana jingine da bango yayi shiru Abubakar ya ƙwanƙwasa ƙofa ya bashi izinin shiga dan Zulaiha bata

ɗ

akin. Ledar Rufaida yoghurt ya ajiye masa da magu

nguna yana masa sannu.

"Na san dai da takura amma ba yanda za'ayi da nayi tunanin ko nemi haya toh ga wani sabon lissafin kuma ya sake tasowa. A haka ma Allah ya rufa asiri kaga gidajen da aka siyar duka sunyi daraja sosai shiyasa har aka samu aka rage

ku

ɗ

a

ɗ

en" Abubakar ya fa

ɗ

a. Bilal dake kallonsa ya ce

"Wai a ina aka samu ku

ɗ

a

ɗ

en da aka biyasu kuwa?"

"Shine maganar da nake yi maka, an siyar da gidanka na Goran dutse da kuma wancan na Rijiyar Zaki sai filaye guda biyu, takardun uku na gani amma bi

yu ne suka siyu

ɗ

ayan dillalan sunce hanya ce kaima kayi ganganci daka siya".

Shiru yayi kafin a hankali abin tausayi yace

"Toh yanzu saura nawa a gama biyanta ita?"

"Miliyan goma aka bata" ya bashi amsa, ya

ɗ

ago kamar a firgice ya zaro ido ya ce

"

Goma? Saura Ashirin fa kenan, a ina zan nemo miliyan ashirin banda yanzu waccen tarar? Na shiga uku da wahala dai idan ban yi zaman kurkuku ba dan ban san in da zan samo ku

ɗ

in nan ba" ya fa

ɗ

a gwanin tausayi kamar zai fashe da kuka.

Abubakar ya kalle sh

i cike da tausayawa ya ce

"Alhaji Hafiz ya biya duka tarar, yanzu ina hanya Barr Sajid ya kirani yake cewa ya kirashi yace ya tura da account number da za'a saka ku

ɗ

in, ya tura masa na san kuma ya saka dukda bai sake kirana ba".

Cike da rashin yarda Bi

lal ya ce

"Hafiz? Hafiz dai dana sani ko wani daban?"

"Shi dai Hafiz abokinka. Badan shi ba ai da wahala wannan yarinyar ta haƙura. Na fahimci ba wai ku

ɗ

in ne a gabanta ba burinta ta wulaƙanta ka dan shi kansa Alhaji Lawan

ɗ

in ita ta ringa zugashi sai

da Hafiz

ɗ

in ya shiga maganar kafin suka haƙura."

Shiru sukayi na kusan minti biyar kafin a hankali Bilal ya ce

" Ɗazu naga Halima amma kafin mu fito ta tafi ita da wani Namiji"

"Eh taje nima bamuyi sallama ba gaskiya ta wuce" Abubakar daya miƙe ya

bashi amsa. Sai ya sake karyar da murya ya ce

"Shi wanene wanda na gansu tare toh?"

"Wanda zata aura ne" ya bashi amsa cikin halin ko in kula. Yanda ka san dirar mashi haka yaji maganar, ya gwale ido yana kallon Abubakar ya ce

"Wanda zata aura?"

"H

aka tace mun" Abubakar ya sake bashi amsa. Sai ya koma laƙwas ba tareda ya sake cewa komai ba Abubakar kuma ya fice daga

ɗ

akin.

Kwana yayi a zaune, dukda ya tsammaci rasa sauran abubuwan daya mallaka domin dai babu mai biya masa bashin daya ci wa kansa

amma kuma bai zaci abin zai dame shi haka ba. Shikenan yanzu ko gidan da zai zauna bashi da shi ya dawo

ɗ

akin ƙaninsa da zama dan asalin nasa

ɗ

akin samartaka a soro yake shi aka shigowa Hajja dashi aka ƙara mata a falo bayan da aka raba asalin

ɗ

akin ya ko

ma ciki da rumfa sannan aka mata ban

ɗ

aki da sauran a cikin

ɗ

aki. Shi gashi yanzu

ɗ

akin ma falle

ɗ

aya suka samu ban

ɗ

aki sai sun fita tsakar gida, hatta da kayan gadon sa da na Zulaihan duka dasu akayi gwanjon gidan kayan kitchen

ɗ

inta da sauran abubuwanta k

awai ta fita dasu.

Abu

ɗ

aya da ya saka ya

ɗ

an ji dama-dama yanda bai ga damuwa sosai akan canjin muhallin a tattare da Zulaiha ba. Ba yabo ba fallasa take sabgoginta, daya gama cin abinci ta tattare kwanuka ta fita dasu ta dawo ta tambaye shi ko akwai

abinda yake buƙata yace babu shikenan tayi kwanciyarta.

A haka ya kwashe kwana uku yana jinyar malaria daya kwaso a prison, ba inda yake fita yana

ɗ

aki ko falon Hajja sai ta fito tana ta ƙwala masa kira musamman idan yan jaje da yace munafunci suke zuwa

suka zo kafin zai shiga yafi ganewa ya zauna a

ɗ

aki kawai yayi shiru yana Istigfari da tunanin duniya.

Ranar daya kwana hu

ɗ

u da yamma yana kwance a

ɗ

aki ranar an samu sauƙin yan jaje dan tun safe babu wanda yayi sallama, yana kwancen yana jiyo Hajja n

ata sababi wanda kuma ya san ba zai wuce da Zulaiha take ba. Tun washe garin daya dawo ya fahimci za'a samu gagarunar matsala tsakanin Hajja da Zulaihan a zamansu.

Hajja tamkar shi take, gurinta ya gado shegiyar tsafta da rashin son ganin shirgi a guri

. Idan ka shiga gidanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login