Showing 147001 words to 150000 words out of 287295 words
800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 34*
Kwanaki biyu da suka biyo baya nayi su ne cikin taimakon ubangiji domin a kowacce daƙiƙa ji nakeyi tamkar numfashi na zai iya yankewa. Babu abinda yake shiga c
ikina banda ruwa da paracetamol da nake ta banka saboda azababben ciwon da kaina kama, ikon Allah ka
ɗ
ai yake riƙe dani akan ƙafafuna hatta yaran ma game game kawai nake musu duk abinda hannu ya kai nake ha
ɗ
awa na basu su ci.
Nayi kuka har hawayena sun ƙ
afe ya zama sai na zuci nakeyi, a duk sanda na tuna abinda naji kuma na gani dangane da Bilal sai inji na tsani kaina. Ban san ta inda na gaza ba, ba yabon kai ba na sani ko a cikin mata samun irina mai kula da tsaftar jikinta ciki da waje sai an tona. A k
oda yaushe na kanyi ƙoƙarin na kasance a yanda idonsa ba zai ta
ɓ
a ganin wani abu da bazai so ba a tareda ni. Bana wasa da kyaran jikina a duk sanda na samu ku
ɗ
i kafin nayi komai sai na ware wanda zan siyi duk abubuwan da nake buƙata na amfanin kaina kuma s
aboda shi. Ina
ɗ
aukar last kwabo na na siya abun da
ɗ
i naci saboda jikina ya samar da ni'imar da zata gamsar dashi, ban ta
ɓ
a damuwa da rashin yi biyamun buƙatu na yau da kullum da yakeyi ba ni dai burina a kullum nayi abunda zan faranta masa amma ace ya ras
a abinda zai saka mun da shi sai wannan?
Wai tun yaushe ma yake aikata hakan ba tareda na sani ba? Tun kafin muyi aure dama haka yake ko kuwa daga baya ne ya fara? Bani da mai bani amsa amma abinda nafi ƙarfafawa shine bayan aurenmu ko ma in ce bayan n
a haihu tunda shine lokacin daya fara zaryar zuwa Abuja da sunan aiki ashe abinda yake kai shi kenan. Na tuna lokacin da na tafi gida wankan Al'amin sanda yazo ganinmu bai ko nuna
ɗ
oki ko alamar yayi kewata ba har naji haushi a lokacin ashe dalili kenan. T
un bayan sannan dama ya koma part
ɗ
in sa gaba
ɗ
aya da kwana kuma daga lokacin ya auri chat koda yaushe ya zauna wayarsa na hannu yana danne danne ashe dalilin kenan.
Babban abinda ya sake bani mamaki dashi ta yanda tunda ya fita daga
ɗ
akina wancen dare
n tsayin kwana biyun bai sake tako ko da kan barander ta ba balle ya shigo yayi mun magana ko yayi mun wani bayani da zai kare kansa balle har ya rarrasheni ko ya nuna nadama akan abinda ya aikata
ɗ
in. Ko da yake ni kaina bansan zaman me nakeyi a cikin gid
an ba domin a yanda bake jin zuciyata bai kamata ace na ƙara kwana a ƙarƙashin inuwa
ɗ
aya da shi ba amma kuma na rasa ƙwarin guiwar yin hakan. Allah ya sani ina Son Bilal irin Son da zuwa yanzu na yarda jarabawa ce a tattare dani a kusa ko a nesa kuma bana
fatan wani abu da zai rabani dashi amma a yanzu ban san me nakeji akan sa ba.
Da azahar ina kwance a tsakiyar falo ina juyi saboda azabar ciwon da cikina ya tasar mun da nasan yana da alaƙa da horon yunwar da nake yiwa kaina. Al'amin dana aika ya kiraw
o mun Maman Yusuf suka shigo tare, tana ganina ta ƙaraso da sauri tana salati ha
ɗ
i da cewa
"Na shiga uku mai ya sameki Halima?" Da hannu na nuna mata cikina, ta
ɗ
ago ni zaune sai ta sake
ɗ
aukar salatin daya fi na farko tace
"Innalillahi wa Inna ilaihi
raji'un kin ganki kuwa Halima? Kwananki nawa a kwance? Ina shi Baban nasu da ya barki haka sai kin mutu sannan zai kira iyayenki ya basu gawa ko me?"
Jin ta tsaya kwakwazo ya saka na kamo hannunta daƙyar na
ɗ
ora akan cikina da muryata da bata fita nace
"Cikina mutuwa zanyi". Sai ta miƙe jik na rawa tana cewa
"Ba zaki mutu ba in sha Allahu bari na kira Sadi mu tafi asibiti" ta fita kusan da gudu, ni dai ba zan ga sanda ta dawo ba haka dishi dishi naji sanda aka kwasheni aka fita dani daga lokacin ban s
ake sanin komai ba sai farkawa nayi na ganni a gadon asibiti Bilal na zaune a gefena. Mayar da ido na nayi na runtse bayan dana fahimci a inda nake, ya miƙe tsaye ha
ɗ
i da kamo hannuna yana cewa
"Kin tashi Halima?" Ban amsa ba sai janye hannun da nayi da
ga nasa na yunƙura na gyara kwanciya ta ta hanyar bashi baya, ina jin sa ya sauke ajiyar zuciya kafin ya fita daga
ɗ
akin ba'a da
ɗ
e ba suka dawo tareda likita. Likitan ne ya kira sunana dan haka na gyara kwanciya ta ba tareda na amsa ba ya sake maimaitawa y
ana cewa
"Halima bakya ji nane?"
"Ina jinka" na bashi amsa cikin muryar da bata fita sosai. Yace
"Masha Allah sannu kinji, ina ne yake miki ciwo yanzu?" Sai na girgiza masa kai alamar babu. Matsowa yayi ya saka abun awon bugun zuciya a ƙirji na kafin
ya cire ya
ɗ
auki abun auna Bp ya saka mun a hannu sai da ya gama sannan ya kalli Bilal yace
"Jinin ya sauka sosai yanda ya kamata bata cikin kowanne ha
ɗ
ari yanzu". Bansan sanda na saki tsaki ba jin Bilal
ɗ
in yana cewa
"Alhamdulillah har hankalina ya k
wanta" duk su biyun suka kalleni ni ko dama basu nake kallo ba, likitan ya sake cewa
"Bari naje idan ruwan ya ƙare sai kayiwa Nurse magana tazo ta cire mata ina ganin za'a sallame ku ma ba sai ta kwana ba tunda jikin yayi sauƙi, ni zan shiga wata theate
r yanzu idan mun gama zan sake zagayowa sai kayi mata bayani kuma" ya fa
ɗ
a yana dafa kafa
ɗ
ar Bilal
ɗ
in. Bayan fitar Dr ya koma ya zauna kan kujerar daya tashi cikin lafazin da a baya nake so yake kuma jefani cikin shauƙi da begen sa ya ce
"Fa
ɗ
uwar da kika
yi
ɗ
azu kafin muzo Asibiti kika fara bleeding, toh bayan mun iso da suka gwada suka ce kina da ciki kusan wata uku" sai yayi shiru. Na gyara kwanciya ta na zuba masa ido ina so naji ƙarshen maganar tasa, wai ina da ciki, a yaushe nake da cikin har kusan wa
ta uku amma ban sani ba? Jin yayi shiru ya sunkuyar da kai yasa nayi ƙarfin halin cewa
"Sai me ya faru daga nan toh?" Ya kamo hannun na fizge ha
ɗ
i da jefa masa wani kallo sai ya matsa ya ce
"Dr yace a yanayin da kike barin cikin zai iya zame miki matsa
la shine na saka hannu aka ƙarasa fitar dashi dan dama ya rigada ya lalace". Ban san sanda na yi dariyar da kana ji zaka san ta zallar takaici da baƙin ciki bace na ce
"Ai dama na saba rainon cikin cikin ƙunci da rashin lafiya ko ka manta? Gara dai ka f
a
ɗ
a mun gaskiya baka buƙatar cikin shiyasa kace a cire shi kuma hakan da kayi ba laifi bane domin ko ba'a cire yanzu ba nima idan na sani ba zan barshi ba dan ba zan sake yarda na ha
ɗ
a zuri'a da Maƙaryaciya, Maha'inci kuma Mazinaci mara tsoron Allah irinka
ba" na ƙarasa ina kallon cikin idon sa. Take idanunsa suka canza launi, ya nuna kansa da yatsa ya ce
"Ni kike jifa da kalmar Zina Halima?"
"Karya nayi ba halinka bane?" Na fa
ɗ
a ina kallon sa tar babu alamar tsoro ko nadamar hakan, sai ya miƙe tsaye, d
a fari na
ɗ
auka zai rufeni da duka ne ko kuma ya mareni amma sai naga yaja da baya yana huci kamar wanda kunama ta harba, hakan ya bani damar cigaba da cewa
"Ban ta
ɓ
a zaton haka kake ba Bilal, ka ci amanar So da yarda. Bilal mai nayi maka a rayuwa da ka
za
ɓ
i saka halaccin da na maka ta wannan hanyar? Laifi ne da na So ka na ce sai kai? Laifi ne da na fifita farincikin ka a kan na kowa? Dame na rage ka? Ta ina na gaza daka za
ɓ
i zubar da ƙimarka da mutunchin ka ha
ɗ
i da barin ubangijin ka ta hanyar aikata a
binda yayi hani da? Bilal Zina da aurenka?.... "
"Wlh kika sake cewa tak Halima sai nayi miki abinda baki ta
ɓ
a zato ba" ya katseni cikin hargagin da saida yayan hanjina suka juya. Ya nufoni idanunsa jajir har wani jirkicewa sukayi ya nunani ya ce
"Ki
iya bakinki ki kuma san abinda kike furtawa idan ba haka ba" ya ka
ɗ
a yatsunsa biyu akan fuskata. Na ha
ɗ
e yawu daƙyar saboda har ga Allah na tsorata da yanayin sa, ban kuma sake cewa komai ba kawai na maida kaina gefe hawaye suka shiga ziraro mun. Wannan sh
ine a dake ka kuma a hanaka kuka, wannan na
ɗ
e tabarmar kunyar da yakeyi cikin hauka kuma ya sake tabbatar mun da cewar duk abinda na gani gaskiya ne. To ta yaya ma zai ƙaryata bayan da idona da kuma kunnuwana na ga shaida kuma a wayar sa ba wai wani ne ya
fa
ɗ
a mun ba?
Sai bayan sallar Isha'i likitan ya bamu sallama, dana sakko daga gadon zuciyata ta raya mun in fita na tari Adaidaita na tafi gidan mu sai lokacin na tuna banga yara na ba. Ina tsaye bakin ƙofar reception ya taho bayan yayi settling bill ya
tsaya ba tareda ya kalleni ba yace "muje mana"
"Ina yarana?" Na tambaye shi yayi gaba yana cewa
"Suna gidan Alhaji Sani" (Gidan Maman Yusuf) shine dalilin daya saka na bishi na kwanta a bayan motar ganin ya nufi wata hanyar daban ba wadda zata kaimu
gida ba kamar nayi masa magana sai kuma nayi shiru kawai. Can wani gurin siyar da kayan ciye ciye mukaje, ya fita ya barni ya
ɗ
an jima saboda layi kafin ya dawo yana shigowa motar naji ƙamshin gashi ko Kaza ko Nama ga wata ledar da nake zaton Fura ce ko Yo
ghurt ya aje su a sit
ɗ
in gaba ya tayar da motar. Ko kusan burgeni banji yayi ba, a lokacin Allah Allah kawai nake mu isa gida naga yarana daga nan na zauna nayiwa kaina karatun abinda zai fishsheni.
Ɗ
aki na wuce kai tsaye na fa
ɗ
a wanka dan shi nafi buƙ
ata a lokacin, ina wankan ina kukan daya rigada ya zame mun aboki a kwana biyun. Dana fito na jiyo surutai a falo dan haka na zura Hijab na fita na tarar da Maman Yusuf ce da Anty Amina kishiyarta sai Al'amin da su Kursum da Alina suke guje guje. Sannu suk
a shiga jera mun, na samu guri na zauna ina
ɗ
an murmushi. Maman Yusuf ta ce
"Sannu Halima kinga ki har kin
ɗ
an marmaro fuskarki ta ciki ba kamar
ɗ
azu ba" ni dai nayi murmushi ba tareda nace komai ba sai ta sake cewa
"Ina fita muka ci karo da Baban na
su ai nasan ba lallai kin san ma ya aka fita dake ba dan naga kamar suma kikayi" sai tayi ƙasa da murya kafin ta ce
"Ya kuwa kira yan gidanku naga kun dawo ku ka
ɗ
ai?"
Murmushi nayi nace
"Eh sunje asibitin" ta gyara zama ta ce
"Toh,
ɗ
azun ne naga da
nace ya kira iyayenki ya gaya musu kinga yanda ya hayayyaƙo mun kamar zai rufeni da duka nace toh ko shima irin mazan nan ne da basa son fa
ɗ
a idan wani abu ya faru a gidan su?"
"Yo rashin lafiya kuma menene abun
ɓ
oyewa ai kamata yayi ma ace iyayen su za
'a fara kira a gaya musu idan abu yazo da ƙarar kwana ai dole a kirasu ace an mutu ai" Anty Amina ta fa
ɗ
a suka jigaba da jajanta mun kafin shigowar Bilal ta saka suka miƙe Maman Yusuf na cewa
"Ko dai mu tafi da Sharifa a ƙarasa yayen kawai?" Nayi yar dari
ya tace
"Ai bama ta da damuwa naga taci abincin ta sosai suka sha wasa tayi bacci ko sau
ɗ
aya batayi kuka ba". Har get na raka su ina musu godiya, a kitchen na hango shi yana ƙoƙarin
ɗ
umama kaza a microwave na wuce
ɗ
aki na kimtsa kaina, bana jin yunwa ko
dan ruwan da aka saka mun ne dan haka nayi sallolin da suke kaina bayan na idar na haye gado na kwanta. Bilal ya sake shigowa
ɗ
akin a karo na uku dan sau biyu yana shiga sanda ina sallah, ya kwantar da Sharifa da tayi bacci akan gado kafin ya tsaya a kaina
yana kiran sunana.
Ban amsa ba haka nan ban motsa ba, ya miƙa hannu ya ta
ɓ
a ƙafata na bu
ɗ
e ido da sauri na kalle shi yayi gajeran tsaki ya ce
"Da idonki biyu dan wulaƙanci kina ji na kenan kika yi shiru" ban tanka masa ba ya sake cewa
"Ki taso kic
i abinci ki sha maganinki". Sai lokacin na tashi zaune na kalle shi nace
"Har yaushe ka fara damuwa dani ko lafiya Bilal?"
"Halima kada ki tunzura ni, ina duk iya ƙoƙarin da zanyi naga na biki a hankali amma naga alama magana kike so ki jani da ita. Rash
in kunya da zagina da kika yi basu isheki ba so kike ki ƙara wani" ya fa
ɗ
a yana har
ɗ
e hannayen sa a ƙirji. Sai na tashi zaune da kyau na sauke ƙafafu ƙasa na fuskance shi na ce
"Ƙwarai magana nake so muyi". Ya zuba mun idanunsa da suka canza launi kafin
ya ja stool
ɗ
in gaban mudubi ya zauna ya ce
"Ina sauraronki".
"Ka dubi Allah ka fa
ɗ
a mun gaskiya Bilal dame na rageka a zamantakewarmu?" Na fa
ɗ
a bayan shirun kusan minti biyu da nayi ina ƙoƙarin kamo ta inda zan fara magana, yayi tsaki ya ce
"Idan ki
na da magana mai muhimmanci kiyi"
"Wannan ita tafi komai muhimmanci a gurina domin ina so na san cikin zunubin ka ina da kaso ko babu" nima na katse shi, sai ya kalleni kafin ya
ɗ
auke kai gefe ba tareda yace komai ba. Kukan da ban so zuwan sa a lokacin b
a ya ƙwace mun dukda haka na ce
"Mai ya baka sha'awa a matan bariki Bilal? Mai ka ta
ɓ
a nema nayi maka banyi ba daka gwammace ka fita ka nema a waje?"
"Kina ji ko Halima kowanne mutum da kika gani a rayuwa yana da kuskuren sa kuma da za'a ce kowa a t
ona nasa da ba lallai a samu sauran wanda za'a ringa yiwa kallon mutumin kirki ba a duniyar nan, idan da kina da tunani bai kamata ki bari abinda kika gani ya dameki har ki nemi ki hallaka kanki a banza da damuwa ba, kuma duk maganganun da kike fa
ɗ
a kawai
ina miki uzuri ne kuma ko da kike wannan surutun baki da qata shaida akan abinda kike zargin na aikata. Abinda kika gani kawai normal abu ne tsakanin Saurayi da budurwa amma gaba
ɗ
aya kin wani mayar dashi kamar wacce kika kamani turmi da ta
ɓ
arya da ita, id
an ba ban yafe miki ba sai Allah ya bi mun kadin ƙazafin da kike mun domin baki da hujja" ya fa
ɗ
a ba tareda ya kalleni ba.
Ni ko tunda ya fara magana hawayen da nakeyi suka tsaya, zuciyata ta shiga bugawa da ƙarfi mamakin ƙarfin halinsa da kalaman da ya
ke furtawa suka sumar dani a gurin da nake zaune. Ban san sanda na ce
"Ashe har kana da bakin da zaka iya kare kanka Bilal? Bilal da idona fa na gani na kuma saurari irin fasiƙancin da kakeyi sannan har ka iya bu
ɗ
e baki kace wai da ina da tunani bazan
bari abun ya dameni ba Normal ne, Zina ce ta zama Normal a gurinka? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un Bilal ina iliminka ina saninka na addini da har ka bari duniya ta rufe maka ido kake kiran Zina da Normal abu?" Na ƙarasa ina sakkowa ƙasa kan guiwoyina.
Sai ya miƙe cikin fusata ya ce
"Halima idan kika sake dangantani da Zina wlh sai kin sha mamaki na"
"Ka fa
ɗ
a mun abinda ya kamata na danganta dashi toh Bilal idan ban kiraka da Mazin...." Marin da ya kai mun ya hanani karasa maganar dana fara, sai da
na wuntsila gefe saboda yanda marin ya shige ni na fasa kuka mai tafe da ƙara lokaci
ɗ
aya Sharifa ma ta farka ta fasa mata kukan. Ko a jikin sa ya shiga cewa
"So kike sai kin ƙure haƙuri na, da zaki ringa ce mun Mazinaci da uwarki nayi Zinar?"
Tamkar d
ukan guduma haka naji maganar a kunnuwa, yau Bilal ne yake wannan zagin na rashin mutunchi? Ban dawo daga shock
ɗ
in farko ba yaci gaba da cewa
"Ki
ɗ
auki duk matakin da kike ganin yayi miki Halima idan kinga dama ki tafi gidan Radio ki siyi fili ki fa
ɗ
awa
duniya kinga ina Sex Chat da mace, amma kafin nan ki sani kanki zaki zubarwa