Showing 24001 words to 27000 words out of 287295 words
juya maganar a raina, abin da Anty Labiba ta fa
ɗ
a mun yanzu akan na godewa Allah da be lalata mun rayuwa ba ya fa
ɗ
o mun a rai se nayi saurin korar maganar daga raina ina bawa kaina tabbacin Bilal ba z
e ta
ɓ
a yaudara ta ba ba kuma wannan niyyar ta kawo shi guri na ba.
"Karki takura kanki idan ba zaki iya ba babu damuwa dama magana ce akan abinda ya shafe mu mu biyu da nake ganin ya kamata mu tattauna amma zamu iya barin ta kawai idan baki da lokaci"
ya katse mun shirun da nayi. Ban san sanda harshe na ya furta
"A ina zan zo na same ka toh?"
"Ina shagon Sani" ya bani amsa. Se na sauke ajiyar zuciya jin ba wani guri daban ya ce na same shi ba har na tsinewa shai
ɗ
an
ɗ
in daya fara kawo mun wasi wasi ak
an Bilal
ɗ
in. Aje wayar nayi na shiga toilet da sauri na canza pad
ɗ
in jiki na tare da wanke fuskata na fito na canza kaya. Dogon Hijab na saka da niƙab saboda munafukan unguwan mu. Dana fito ban tarar da Anty Labiba a falo ba se Amir ne ya tare ni yana ta
mbayata me ya samu Momy ya shiga
ɗ
akin ta ya tarar da ita tana kuka nace masa ban sani ba sauri nakeyi kuma ana jira na ne yaje ya bata haƙuri.
A bayan gidan mu Chemist
ɗ
in Abokin sa Sani yake, haka na ringa gyara niƙab
ɗ
in fuskata harda canza tafiya d
an kar a gane ni ce, na tarar da shi da Bilal zaune suna hira. Kallo
ɗ
aya na masa na hango ramar da yayi idanunsa sun sake fitowa haka dogon hancin sa ya ƙara tsayi hatta da lips
ɗ
in sa se naga sun bushe sun ƙara jaa alamar yana cikin damuwa ko bashi da la
fiya. A taƙaice muka gaisa da Sani kafin ya fita ya bamu guri. Na sauke kaina ƙasa saboda yanda Bilal ya kafe ni da nasa idon da nake jin sun ƙara kaifi yau, sama da minti biyar muna zaune kafin a hankali ya fara magana yace
"Kiyi haƙuri Halims be kamat
a ace na
ɗ
auki fushi akan abin da ya faru ba. Bayan na dawo gida na nutsu na gane kun fini gaskiya se dai ina cikin wani yanayi da ni ka
ɗ
ai na san wane hali nake ciki duk kuma wanda zan yiwa bayani be zama lallai ya fuskan ce ni ba". Kallon sa nayi jin yay
i shiru se yayi murmushi ya ci gaba da cewa
"Tun farko shiyasa ban so aka saka bikin nan wata shida ba kuma kema na gaya miki, dalilin da ya saka bana
ɓ
oye miki komai da nake ciki kenan Halims saboya tunani na duk abin da ya taso za kiyi mun uzuri" se na
ɗ
aga kai na kalle shi yayi saurin cewa
"Ban ce baki mun ba, wlh na sani kin yi ƙoƙari. Kin mun abin da ba kowacce mace ba kuma na yaba and i will for ever be grateful for that Halima. Ke
ɗ
in kin nunawa duniya true love still exist, se dai har yanzu
ban ka
i ba Halima. Nayi tunanin a wata shidan nan zan iya yin ƙoƙarin ganin ban baki kunya ba amma se yanzu na fahimci wautar da nayi gashi kuma lokaci ya ƙure mun balle na juya da baya".
Gaba na ya yanke ya fa
ɗ
i baki ja har yana rawa na kalle shi nace
"Ban
gane ba, what are you trying to tell me Bilal what do you mean by lokaci ya ƙure balle ka juya baya?"
"Relax Halima ba wani abu nake nufi ba" ya fa
ɗ
a yana kama hannu na, se na fizge ina kallon sa se dai na kasa ci gaba da magana saboda yanda zuciya ta
take wani irin bugu kamar zata huda ƙirjina ta fito. Wayar sa ya ciro daga aljihun sa yayi danne danne kafin ya miƙa mun, hannuna na rawa na kar
ɓ
a na kalli screen
ɗ
in. Video gidan daya kai ni a matsayin nasa wanda zamu zauna a ciki ne yake playing, seda n
a kalla daga farko har ƙarshe kafin na kalle shi muka ha
ɗ
a ido dan shima ni yake kallo se ya kar
ɓ
i wayar ya mayar da ita aljihunsa kafin ya ha
ɗ
e hannu biyu ya dafe ha
ɓ
arsa ya furzar da iska daga bakin sa kafin yace
"Bayan da aka saka ranar auren mu muny
i magana da Baba Liman ya kuma kira gidan su yaron da ze auri Fadila akan suyi haƙuri a ƙara ranar auren su zuwa wata goma amma suka ƙi yarda akan in dai ba wata shidan da suka yanke ba se dai a mayar musu da ku
ɗ
in su kawai ya haƙura ya fasa auren ta. Na g
aya miki Halima ni zan yi mata komai na aure, babu abin da baki sani ba a kaina tun da mahaifin mu ya rasu duk wata ragama ta yan
ɗ
akin mu ta dawo kaina. Yayyenmu tun da muka samu sa
ɓ
ani dasu lokacin rabon gado shike nan suka zare hannun su daga komai daya
shafe mu ko sanda nace babu damuwa a bar zancen auren mu a wata shidan na
ɗ
auka su Yaya Alhaji ze yiwa Fadila kayan
ɗ
aki ne se da kuma biki ya taho da Hajja tayi musu magana suka ce ai an raba gado an bawa kowa nasa dan haka ba abin da zasu mana.."
"Bi
lal ka fa
ɗ
a mun kai tsaye me kake nufi ko me kake so ayi yanzu dan Allah tun baka janyo zuciya ta ta buga ba" na katse dogon sharhin daya
ɗ
akko wanda babu abin da nake fahimta a ciki. Shiru yayi ina kallon yan da abin wuyan sa ke sama da ƙasa alamar magana
na cikin sa ya kasa furtata kafin ya sake riƙe hannaye na biyu duk yanda naso na ƙwace be bani dama ba haka ya kafe idon sa cikin nawa yana murza zoben dake hannu na yace
"Ina son ki Halima bana fatan na rasa ki amma a yanzu bani da halin auren ki".
"Dagaske Bilal dama yaudara ta kake yi ba aure na zaka yi ba?" Na fa
ɗ
a cikin karyewar sauti. Se ya ƙara ƙarfin ruƙon da yayiwa hannaye na yace
"Allah shine shaida ina son ki Halima dai dai da rana
ɗ
aya ban ta
ɓ
a niyyar yaudarar ki ba"
"Amma da bakin ka y
anzu kace ba zaka iya aure na ba, me yasa tun farko baka fa
ɗ
a mun ba se da ka bari auren mu ya rage sati biyu?" Na fa
ɗ
a ina fashe wa da kuka.
"Nayi zaton zan iya Halima, na
ɗ
auka zan samu yanda nake so kafin lokacin amma hakan yaci tura. Ta yaya kike zat
on iyayenki zasu bani ke bayan ba ni da ko muhallin da zan ajiye ki?" Ya fa
ɗ
a tamkar shi ma ze fashe da kukan. Kamar zan shi
ɗ
e nace
"Shi kuma wannan gidan fa? Ko dama ba naka bane ƙarya kayi mun kace na ka ne?"
"Gida na ne Halima amma wannan shi da kan
go ai basu da maraba ta yaya mutum ze shiga ya zauna a gurin da ko da
ɓ
e babu? Ki aje maganar wannan gidan a gefe kawai dan dashi da babu banbancin su ka
ɗ
an ne. Da ace ina da sararin da zan kama miki haya ma da wlh bazan damu ba amam bani dashi, a yanzu ban
i da wasu ku
ɗ
i a tare dani se wanda za a siyawa Fadila kujera su kansu basu gama ha
ɗ
uwa ba dama sadakin ta ne na cika kuma na ranci wani abu ciki dashi na ƙarasa aikin fulasta ai kin gani sanda muka je iya waje ne da fulasta ba ayi a waje ba ko? Za
ɓ
i biyu
ne ka
ɗ
ai ya rage mana Halima, ko dai a
ɗ
aga auren mu wanda bana zaton iyayenki zasu amince tun da har sun ambata dama akwai wanda suke so su ha
ɗ
a ki dashi a familyn ku kenan se dai na haƙura dake tun da bani da halin auren ki shikenan rayuwa ta tazo ƙarshe
ban san wace alƙibla zan kalla ba idan babu ke a tare da ni".
[5/18, 13:09] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS
ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wakiltar
mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE
7*
Page 7
Na fi minti goma tsaye a ƙofar gidan mu ni ban shiga ba kuma ban bar gurin ba. Maganganun da mu kayi da Bilal ne suke mun amsa kuwwa a kunnuwa na da ƙwaƙwalwata bana kin ko wanne sauti dake zagaye dani banda muryar sa.
"Ba ni da ku
ɗ
in da za
n ƙarasa gini Halima, ba kuma ni da sararin da zan kama haya a yanzu. Abu biyu ya rage, ko dai iyayen ki su
ɗ
aga auren mu ko kuma mu haƙura gaba
ɗ
aya, ƙila a gaba idan muna da rabon kasancewa tare se muyi aure. Ina son ki Halima amma bani da halin mallakar
ki a yanzu" kalaman ƙarshe daya gaya mun kenan. Bana ko gani sosai na shiga bubbuga ƙofa, se da na buga sau uku kafin aka bu
ɗ
e. Musa ne, jikan Goggo Habi Ƙanwar Mahaifin Mamanmu. Ɗan ta
ɗ
aya Baba Sulaiman kuma shine mahaifin Musan accident suka yi dashi d
a matar sa duk suka rasu. A Birnin gwari take da zama dama naji Anty Labiba tana fa
ɗ
ar tace tun biki na saura sati biyu zata zo ashe har ta zo
ɗ
in kuwa.
Kallo na ya tsaya yi saboda niƙab
ɗ
in dake fuska na ra
ɓ
e shi na wuce ina ha
ɗ
a hanya, motar Abba da
na gani a ajiye yasa na gane yana gida dan haka
kai tsaye na wuce falon sa. Tare da Aminin sa Baba Hashim na same su suna magana daga kuma yana yin fuskokin su na fahimci ko ma me suke tattauna ba magana me da
ɗ
i bace. A tare suka amsa sallama ta suna kallo
na, ka ƙarasa gaban Abba, tamkar wadda tazo isar da saƙon rasuwa haka na fashe da kuka irin me gigitar nan har jiki na yana jijjiga. Abba ya miƙe hankali tashe ya ruƙo ni yana cewa
"Lafiya Halima? Me ya samu su Labibar?" Haka Baba Hashimu ma cikin ka
ɗ
uwa
suka ringa tambaya ta me nene amma na ƙi cewa komai har se da nayi kuka iya kar yi na se da naga Baba Hashimu ya nufi ƙofa yana cewa
"Bari na kira Amina" se lokacin na bu
ɗ
e baki daƙyar nace
"Ba se ka kira ta ba". Se da na sake kwashe kusan minti biyar i
na kokawa da kukan dake taho mun da zarar na bu
ɗ
e baki kafin daƙyar na iya cewa
"Abba Bilal ne"
"Me ya same shi?" Abban ya tambaye ni. Ina kuka tamkar raina ze fita na tsara musu duk yanda mukayi da Bilal da abin da ya gaya mun ban rage komai ba. Su kayi
shiru kamar ruwa ya cinye su banda sautin kuka na da ƙarar fanka baka jin komai har kusan minti goma da alama duk su biyun bakin su ya mutu sun rasa abin da zasu fa
ɗ
a ne. Daƙyar Baba Hashimu ya katse shirun yace mun
"Ki bar kukan haka Halima kiyi shiru m
uyi magana". Se da na sake shafe wasu mintunan kafin na iya tsagaitawa da kukan, yace
"Zaman nan da muka yi zancen ki muke yi Halima. Mahaifinki ya kira ni yana cike da damuwa akan lamarin auran ki. Yau saura kwana goma sha hu
ɗ
u amma babu wata magana me
ƙarfi daga gidan maza su basu zo akan suna sane da lokaci ba kuma basu ce wani abu dangane da shirun da suka yi ba. Yanzu Alhaji Salahu muke ji yazo mu ji ta bakin sa akan abin da ya kama muyi se kuma gashi kin zo da wannan maganar. Ina ganin ai ba abin k
uka da tayar da hankali bane ba, dama kullum cikin yi muku addu'a muke akan Allah ya za
ɓ
a muku mazaje na gari. Irin haka babu da
ɗ
i, amma sha'anin aure da ace ayi azo ana dana sani daga baya gara a haƙura se kiga ubangiji ya musanya miki da wanda ya fishi z
ama alkhairi a gare ki".
Kukan dana sake fashewa dashi se ka rantse da Allah irin marin nan na shammata ya zabga mun, ko da yake ai gara ya dake ni naji zafin a kan fata ta da ciwon da yake neman haifar wa zuciya ta. Na rabu da Bilal fa yake cewa. Daga
shi har Abban Kallo na suka ringa yi cikin mamaki za a ko ace
ɗ
imuwa tamkar dai basu fahimci dalilin sabon kukan dana dasa ba. Ban ji nauyin Baba Hashim ba domin dama Abba babu batun jin kunya tsakani na dashi nace
"Wallahi ina son sa Abba, idan na rasa B
ilal ban san ya zanyi da rayuwa ta ba ni dai a nemi wata mafitar amma kar ma a fara cewa in rabu dashi" na ha
ɗ
e kai na da kujera na ci gaba da rera kuka. Baba Hashim ya ringa salati yana tafa hannu Abba dai yayi shiru ya tallafe ha
ɓ
ar sa da hannu biyu yana
kallo na. A haka Baba Salahu ya shigo ya same mu, a taƙaice Baba Hashim ya yi masa bayanin abin da nazo musu dashi yayi shiru kawai yana jimanta abun a ransa yana kallo na, jin kukan nawa bana ƙare bane yasa ya fara magana cikin lallashi yana cewa
"Yi
shiru Halimatu kwantar da hankalin ki babu wanda ze raba ku amma ki fara amsa mun tambayar nan tsakani da Allah kar ki mun ƙarya ni kuma zan yi iya ƙoƙari na ganin na samar miki muradin ki". Na tsagaita kukan ina share hawaye ha
ɗ
i da face maji na da hijabi
na, shiry ya
ɗ
an yi cikin jin nauyin maganar da take bakin sa kafin daƙyar ya iya cewa
"Halimatu, kar kiji nauyi ko kunyar mu ki gaya mun tsakanin ki da Allah wani abu na rashin dacewa ya ta
ɓ
a shiga tsakanin ki da Bilal ne?"
Da sauri Abba ya kalle shi
se Baba Hashim ya masa alama da ido akan kar yace komai ni kuwa a yanayin da nake ciki ban ma ji tambayar tasa a wani daban ba kai tsaye na ce masa
"Wallahi Baba Bilal ba
ɗ
an iska bane ni yake so tsakani da Allah ba wai wani abu nawa ba. Ni ko hannu be t
a
ɓ
a riƙewa da gangan ba aure na yake so kawai ba wani abu ba".
"Alhamdulillah" suka ha
ɗ
a baki su ukun suka fa
ɗ
a Abba har seda ya gyara zama ya koma cikin kujera ya kwanta ha
ɗ
i da rufe idanun sa. Nasiha Baba Hashim da Baba Salahu suka shiga yi mun se da
i jin su kawai nakeyi badan ina
ɗ
auka ba, sanyin da naji da duk su biyun suke jaddada na kwantar da hankali na babu abin da ze faru zasu kira Bilal suyi magana dashi. Dana fito daga falon nasan in na shiga gurin Mama ƙarshe raina ne ze sake
ɓ
aci se kawai n
a maida niƙab
ɗ
ina na fice na tafi gidan su Hansa'u.
Hajiya Amina na zaune ta zabga tagumi tana sauraron Goggo Habi dake zuba tijara, tun yammacin jiya data sauka gidan ta ce a fito mata da kayan lefe ta gani aka ce babu shi kenan ta dasa tijara in tay
i ta gaji ta huta an jima ta ci gaba, yanzu ma zuwan Inna Salamatu Yayar su Alhaji Aminu ta biyu yasa aka sake maido da zancen sabo.
"Ni tun da uwata ta haife ni ban ta
ɓ
a jin labari ko ganin neman aure irin wannan ba, ni fa tun ga ni na da yaron sau
ɗ
aya
ban ga miji a nan ba yana yawo da wata shegiyar suma kamar zakaran da yake tashen balaga na
ɗ
auka shiritar yarinta tasa ta biye masa da zarar ta samu nutsatstse me hankali zata rabu dashi ashe abu dai bana ƙare bane. Ban da ma sakaci irin naku na iyayen y
anzu ke Amina kina ina har kika bari har tayi sabo da wannan lalata mogal
ɗ
in?
Irin wa
ɗ
annan samarin dama kowa yasan basu aje ba basu bawa kowa ajiya ba se dai suyi wanka su ringa yawo kwararo kwararo duk in da suka ga yarinya me
ɗ
an gwa
ɓ
i gwa
ɓ
i su shig
a jikin ta su hanata kula mazan arziƙi daga ƙarshe su gudu su