Showing 231001 words to 234000 words out of 287295 words
/>
aya suka sheƙe da dariyar sha
ƙ
iyanci suna tafawa. A wani shegen tea flask iya ta da ta zuba masa ruwan zafin data taro a ban
ɗ
aki ta ha
ɗ
a da guntun bread
ɗ
in da suka rage da sauran Milo dan sun shanye ledar Peak 500g daya siyo, a hannu ta riƙe kayan Suby na cewa ta
ɗ
ora a try mana tay
i wucewarta.
BILAL
Kallon sama zuwa ƙasa yayi mata kafin ya tsayar da idonsa kan hannunta yana duban abinda ta ruƙo harta dungurar dasu a gabansa tana cika tana batsewa ko me ta tuna kuma sai ta saki fuska ka
ɗ
an ta zauna a gefensa ta shiga gaishe s
hi tana ƙoƙarin shiga jikinsa cike da kissa. Janyeta yayi ya miƙe zaune daƙyar dan kwanciyar da yayi zazza
ɓ
i ya rufe shi, ya dafw kansa dake bugawa yana kallon kayan dake gabansa kafin ya ce
"Menene wannan?"
"Breakfast mana" ta fa
ɗ
a tana sake matsawa
kusa da shi dan ganinsa da tayi babu riga ya saka ta fara jin muradin kasancewa dashi dan abubuwan data sha jiya basu gama sakinta ba dukda taga alama shi nasa ya sake shi.
"Ni zanci wannan sauran biredin sai kace wani almajiri kuma ina madarar?" Ya fa
ɗ
a, ta yamutsa fuska ta ce
"Ai dai kana kallo baƙi nayi ka godewa Allah ma daka samu sauran madara kuma sun shanye"ta ƙarasa tana harararsa. Da mamaki ya ce
"Ita madarar suka shanye duka?"
"Dan Allah ji yanda kake magana sai kace wanda suka shanye
bugu
ɗ
aya, su hu
ɗ
u fa, ko ni ka
ɗ
ai waccen yar madarar da ƙalau nake ai zama
ɗ
aya zan shanyeta".
Kasa ce mata komai yayi ya tsaya kawai yana kallonta kafin ya sauke ajiyar zuciya ya koma ya kwanta saboda yanda zazza
ɓ
in yake nuƙurƙusar jikinsa ya ce
"Ki
soya mun ƙwai toh".
Haka ya ringa tura ƙwan daya ga kamar da gayya aka ƙone shi ga ga uban ƙarni daƙyar ya iya ha
ɗ
a Milon a kofin robar data ha
ɗ
o masa da shi. Safiyarsu ta farko da Halima ta shiga dawo masa, dukda yanda ta ke a wani yanayi na shiga sab
uwar rayuwa haka ta ringa kai da kawowa bata nutsu ba saida ta cika masa dining da lafiyayyun breakfast bayan dankali da ƙwai nama kansu kusan kala uku ga sauran kazar amarci ga wanda aka taho mata da su daga gida komai cikin kwanuka na alfarma suna ci sun
a annashuwa amma yau shine aka bawa sauran biredi a gidansa da shayi a flask
ɗ
in roba da kofin roba kuma babu yanda ya iya ya ci.
Baccin wahala ya sake komawa bayan ya sha paracetamol Zulaiha kuwa dama tunda ta dangwarar masa da ƙwan ta koma gurin ƙawa
yenta suka cigaba da sabgarsu.
HALIMA
Dole ta saka nake ƙarfafa jikina domin na yiwa kaina alƙawarin ƙaryata Bilal da yake cewa dole ya san zan neme shi. Ina son sa ba zan ƙaryata hakan ba amma kuma ni da kaina dana nutsu na fahimci cewar rabuwata d
a shi shine alkhairi a tare da ni.
Daga kalaman daya kalli idona ya fa
ɗ
a mun na tabbatar dagaske yakeyi baya so na, albarkacin soyayyar da nakeyi masa ta saka ya aureni idan ma kuma yana so na
ɗ
in tunda ya fahimci so na ya fi nasa yawa ya sakawa ransa
zan zauna dashi komai wahala zan jure shine dalilin daya saka ya ringa azabtar dani a fili da ba
ɗ
ini har kuma da yake gargadar rasani bai yi nadamar hakan ba sai ma ƙara tabbatar mun da yakeyi ya sani ba zan iya rayuwa da waninsa ba.
Tsayin wata biyu d
a nayi tun barowata daga gidansa bai biyo ni ba ko a waya bai kirani ba sai yanzu haka wani nasa bai zo ba duk sai bayan da iyayena suka
ɗ
auki matakin da suke ganin shi zai kawo mun maslaha a rayuwata.
Abu uku ne dama fargabata idan na rabu da shi, Soya
yyata, makomar yarana sai kuma yanda mutane zasu kar
ɓ
e ni.
Soyayyar da nake masa batayi mun rana ba, bata amfana mun komai a zamantakewata da shi ba face wahala, baƙin ciki, ƙasƙanci da zubewar mutunchi. Na bashi zuciyata, rayuwata da komai nawa. Na za
ɓ
i
kasancewawa dashi sama da farin cikin dangina amma abin da ya mayar min da shi? Cin amana, ƙarya da yaudara.
A yanzu na fahimci wata soyayyar ba rahama ba ce kamar dai soyayyata da Bilal azaba ce.
Da ace Bilal ya mutuntani ko da baya so na ya kare
martabata ya kuma riƙeni amana ƙila ba zan ta
ɓ
a fahimtar komai ba Soyayyata zata cigaba da riƙe aurenmu har zuwa lokacin da ubangiji ya
ɗ
iba mana amma sai ya kasance mai butulci, a sanda ya gama cin moriyar ganga kamar yanda Anty Labiba da Hansa'u sukayi n
asarar haska mun gaskiyar abinda na rintse ido a baya naƙi yarda dashi. Ya mayar da ni daddawar
ɓ
urma, ya
ɗ
ana tarko dani. Ta yuwu ya samu iya abinda yake farauta shiyasa amfanina ya ƙare a gurinsa ko kuma na gaza samar masa da abinda yake muradi shiyasa y
a watsar dani.
Bana son tuna ƙazantar da kunnuwana suka jiye mun da wanda idanuwana suka gane mun yana aikatawa shi da Jalilah, a yanzu dana tabbatar da ba ita ya aura ba, buri na na ƙarshe shine sanin da me wacce ya aura
ɗ
in ta fini? Ta ina na gaza? M
e take da shi wanda ya
ɗ
auki hankalinsa da ni bai samu a tattare da ni ba? Ta yaya tayi nasarar cafkar soyayyarsa? Domin na tabbatar tunda ba Jalilah bace toh wannan da yayiwa laka
ɓ
i da DUNIYARSA ya aura ita ce kuma ya kaini gidansu a unguwarsu Anty Labiba
.
Da hannu biyu na share hawayen da tunanin da na tafi mai zurfi yayi mun sanadin zubarsu, zan daina kuka na sani amma ba yanzu ba domin ciwon da yake danƙare a zuciyata bai ko kama hanyar warkewa ba balle na dena kukan zugi da ra
ɗ
a
ɗ
in da yake mun.
Wayata dake aje saman kaina ta shiga ƙara, agogo na fara dubawa karfe tara da rabi lokacin, duk da naga mai kiran Maman Yusuf ce maƙwafciyata amma sai na mayar da wayar na ajiye dan bani da sukunin da zan iya amsata a lokacin na san kuma ba zai wuce zance
n kwashe kaya zatayi mun ba tunda Anty Labiba ta ce ta shiga gidan neman guduma dukda bata tarar da ita ba sai yara amma na san sun bata labari.
Ganin tana ta kira ya saka na
ɗ
aga ba'a son raina ba, murya can ƙasa na mata sallama ta amsa cikin yanayin
dayayi kama da wacce take cikin damuwa tace
"Yanzu Maman Al'amin ashe dagaske kike ba zaki dawo ba?"
Nayi murmushi na ce
"Gashi kuwa kin gani har an kwashe kaya"
"Wlh ko da aka ce mun an kwashe kaya ban kawo dagaske ba zaki dawo ba tunda nawa
akayi irin hakan kuma aka koma? Ga Amina (Ƙishiyarta da aka saka) itama cikin satin nan zata dawo kuma har kayan ta kwashe. Sai da naji hayaniyar mata da gu
ɗ
a kafin da Ummi ta dawo take ce mun wai amarya aka kawo gidanki, wlh na
ɗ
auka ko haya ya bayar sai
da Abbansu ya ce wai ai dama yayi aure tuntuni tariyarce sai yanzu. Kiyi haƙuri amma Baban Al'amin
ɗ
an abu ta kazan uba ne" ta kora masa ashar.
Murmushin na sakeyi kamar tana gabana ban kuma iya sake ce mata komai ba har ta gaji da surutu ta mun sallam
a akan zata samu lokaci tazo dukda tayi nauyi abinda ya saka ban ganta ba kenan ma tuntuni amma sun so suzo biko. Bayan da mukayi sallama kamar in kashe wayar sai kuma na fasa na kunna Data na shiga Whatsapp.
Cewar da tayi an saka amarya a gidan sai ya
nemi ya hargitsa mun lissafi. Wato dama jira yakeyi a kwashe kaya kenan ya saka amaryarsa? Lallai ta tabbata bana gaban Bilal yaudarar kaina kawai nakeyi amma ya da
ɗ
e da kulle shafina.
Kenan da ya ce ba zai sakeni bama so yayi ya cigaba da azabtar dan
i ta hanyar barina da igiyoyin aurensa ba wai saboda yana buƙatar mu sasanta bane. Status
ɗ
in Fadila na lalubo dan idan har dagaske amaryar Bilal ta tare na san ko kowa bai saka abinda ya shafi bikin ba ita zata saka ilai kuwa ina kunnowa naha write up
'A
llah ya sanya alkhairi bro' ga kuma sauran status nan da suka biyo baya hannu na rawa na shiga bu
ɗ
e su ina fatan in ga fuskar amarya cikin sa'a hoto na biyu kuwa na ci karo da ita, a falon Hajja aka
ɗ
auketa tana durƙushe tsakiyar wa
ɗ
anda suka kawota amma f
uskarta ta fito tar da yake da Iphone aka
ɗ
auki hoton.
Hutun wucin gadi na tafi ina kallon amaryar Bilal. Baƙa ce kuma mummuna domin ko da nima ba farar bace amma akanta balarabiya ce ni ba kuma sai an gaya mun ba na san ta girmeni kuma tana da jiki duk
da dai da gani ƙibar tata ta sama da ƙasa ce ba duka jiki ba.
Ji nayi wani kaso na abinda nakeji ya yaye, ko da aka ce yabon kai jahilci amma dole in yabi kaina wlh na mata zarra a ajiyeni a ajiyeta sai na fita yin kasuwa.
"A hakan kuma ta ƙwace miki m
iji" zuciya ta raya mun nayi fatali da tunanin a fili na ce
"Ba ƙwace ta mun ba, ya raina ni'imar da Allah yayi masa shiyasa aka ha
ɗ
a shi da daidai halinsa yanzu".
Cigaba da kallon hotunan nayi sauran a can gidan a
ɗ
akunana a da amma akayi su, sai na r
inga jin kamar ma na san fuskarta a wani guri, a hoto na ƙarshe naga Suwaiba, cousin sister Hansa'u ce ina ganinta kuma na tabbatar da tabbas na san fuskar amaryar Bilal
ɗ
in tareda Suwaibar na ta
ɓ
a ganinsu kenan amma me cece alaƙarsu? Itama yar uwarsu ce k
o kuwa ƙawar Suwaibar ce kenan?
Ba yar uwarsu bace gaskiya domin da ƙila Hansa'u zata san ita ce ya aura ta yuwu dai ƙawarta ce. Haka kawai na shiga zullumin son sanin alaƙar Suwaiba da Amaryar Bilal, har na kashe wayarna sake kunnawa nayi screenshot
ɗ
i
n hoton da Suwaibar ta fito na turawa Hansa'u.
*KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko
wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*706183848
8*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 53*
"Lallai su Bilal anyi Amarya, toh Allah ya zaunar lafiya" amsar da Hansa'u ta bani kenan duk kuma yanda na so da naji ƙarin bayani bata sake cewa komai ba, Da na
isheta da tambaya ma balbaleni tayi da fa
ɗ
a tana cewa
"Wai menene ha
ɗ
in ki da matarsa ne Halima? Mutum ya rabu dake tuni ma shi ya manta ya ta
ɓ
a rayuwa da wata Halima har yana shirin fara rayuwa da wata amma ke ashe kina nan kina dakon wahala sai anyi m
agana ki fara rantsuwar kin cireshi a ranki gashi kina bibiyarsa".
Tilas na bar maganar amma kuma na gaza hana zuciyata tunani da hasashen Bilal da amaryarsa a wannan dare. Zuciyata ta ringa zafi, ina kwance lamo akan gado har sha biyu bacci ya gagara
ɗ
aukata, daren mu na farko na ringa tunawa, a hankali na saki kukan da nake ta ƙoƙarin dannewa na cusa kaina a cikin pillow na shiga yin sa a hankali. Na da
ɗ
e ina kukan sai da naji sauƙin abinda ya tsaya mun a rai kafin na tashi na
ɗ
auro alwala na shiga yi
n Nafila har sai da bacci ya fara fizgata kafin na kwanta.
Washe gari da safe ina ha
ɗ
awa su Amir abincin da zasu tafi Tahfiz da shi Anty Labiba ta shigo kitchen
ɗ
in, ganin tana kallona da wani murmushi na sha jinin jikina ilai kuwa sai ji nayi ta ce
"Ke ashe amaryar Bilal ta tare jiya". Nayi kamar ban jita ba, bata damu ba ta cigaba da cewa
"Sadiyar Shehu ce ta koma tana bawa su Nasiba labari wai sai suka ga gidan kamar kango ba kamar sanda aka kai ki ba, a hakan ma wai an ce shi ya mata kayan
ɗ
aki".
Ni dai ta tafasa sauke ban ce mata ba na cigaba da abinda nakeyi amma cewar da tayi wai Bilal ne yayiwa Amaryarsa kayan
ɗ
aki ya tsaya mun a rai. Bilal da yayi mun lefe a leda kuma a tsayin zamana dashi cokali bai ta
ɓ
a siyowa ko ya
ɗ
auki ku
ɗ
i ya bani n
a siya ba shine yanzu yayiwa mace kayan
ɗ
aki
ɗ
ungurungum? Ko da yake ba abin mamaki bane tunda an ce shi ya siya musu gidan da suke zaune ma. Tambayar kaina na shiga yi wane irin So yake yiwa yarinyar haka?
"Irin soyayyar da kike masa" na bawa kaina am
sa. A fili can ƙasa na ce
"Ya Allah na roƙeka, yanda ka jarabceni akan mutumin nan shima ka
ɗ
an
ɗ
ana masa kwatankwacin wahalar da na ci akan soyayyar sa"
"Iska na wahalar da mai kayan kara" Anty Labiba ta fa
ɗ
a tana ficewa daga kitchen
ɗ
in na rakata da h
arara dan haushinta ne ya kamani. Ko menene manufarta na gaya mun ma oho? Haka nayi yinin ranar sukuku gaba
ɗ
aya tunani na yana can yanda take kasancewa da Bilal da sabuwar amaryarsa. Dagaske fa ya gama da babina tunda gashi har ya samu madadina, ko da yak
e dama ko a sanda nake tareda shi ina gurin ne kawai amma ni da babu duk
ɗ
aya. Da naga ina nema na sake mayar da kaina ruwa bayan duk alƙawarin dana
ɗ
aukar wa kaina dole na yaƙi tunanin na kwaso Khaki na na shiga wankewa bayan ya bushe na hau guga sannan n
a fitar da duk abinda zan buƙata dan washe gari litinan zan je nayi reporting a PPA na.
BILAL
Sai bayan Azahar ya farka dalilin surutai da ya ringa ji a tsakiyar kansa. Ya tashi zaune yana matse fuska, zazza
ɓ
in daya kwanta dashi ya sauka amma kuma jiki
nsa sam babu ƙarfi ga hayaniyar data cika gidan daya rasa ta mecece, tashi yayi a hankali ya fita falo, yayi turus a tsaye ganin mata sun bararraje kamar a
ɗ
akunansu suna cin abinci suna hayaniya sai kace masu cin kasuwa.
Wacce take saitin ƙofa ce ta a
nkara da tsayuwarsa tayiwa sauran alama duk suka juya suna kallon sa, kallon sa kafin wa
ɗ
anda da
ɗ
in hira ya saka suka cire kallabinsu suka shiga
ɗ
auka suna yafawa. Shi dai tsaye yayi yama rasa abinda zaiyi, yanzu ace duk girman falonta da
ɗ
akuna biyu ga ts
akar gida bai ishe su suyi didimarsu ba sai sun dangana da
ɗ
akinsa? Tukunna ma mai suka zo yi?
"Baby ka tashi ashe" Zulaiha data shigo falon da ƙaramar kula a hannunta ta fa
ɗ
a tana masa murmushi. Kallo
ɗ
aya ya mata ya juya ciki ha
ɗ
i da rufo ƙofa sai ta
ajiye kular hannunta ta bi bayansa
ɗ
aya daga cikin ƙawayenta ta ce
"Amma Zully baki da M, dama yana ciki shine kika kawo mu nan gashi mun saki baki muna ta zuba har Billy tana cewa zata shiga tayi kashi ashe Allah ya rufa mata asiri"
Dakatawa tayi ta
na ware ido ta ce
"Hirar me kukayi?"
"Ke labarin duniya ne kawai ba wani abu ba" wata mai kama da yan sholisho ta fa
ɗ
a. Sai ta sauke numfashi ba tareda ta sake cewa komai ba ta shiga
ɗ
akin.
Ƙ
arar ruwan da taji yasa ta zauna tana jira ya fito, ya mata
kallo
ɗ
aya ya wuce gaban mirror bayan daya fito daga
ɗ
akin baƙin ciki goma da ashirin, shigen atamar jiya ce a jikinta, ashe ba leda bace kawai munin da atamfar tayi a idonsa ne ya sa ya ganta kamar ledar. Tashi tayi ta matsa kusa dashi ta rungume shi ta
baya tana cewa
"Wai me ya faru ne kake ta
ɓ
acin rai Baby?"
Ya tureta, bata haƙura ba ta ƙanƙameshi tana shinshinar jikinsa kamar wata mayya tana cewa
"Baby haba mana, kasan dai babu gurbin fushi a fuskar sabon ango"
Janyeta ta sakeyi bayan daya j
uya ya fuskanceta, so yake ya tuhumeta akan daren jiya. Ya zura mata ido, tabbas shi shaida ne Zulaihar dake gabansa a yanzu ba Zulaihar daya sani a baya bace akwai sauye-sauye da yawa a tattare da ita amma bai ta
ɓ
a zaton bayan sababbin
ɗ
abi'u da halaye da
ya fuskanta a tareda ita ba harda na mutunchi da