Showing 135001 words to 138000 words out of 287295 words

Chapter 46 - KURA A RUMBU COMPLETE

sai cewa yayi wai motar da ta

ɗ

akko kayan daga ƙauyen da aka siyo su yan kidnapping sun ƙwace ta shikenan maganar ta wuce.

Haka na sake komawa a karo na biyu akan a ƙara mun jarin sai Abba ya bani za

ɓ

i saboda ya ce ku

ɗ

in da ya ware a lokacin wanda zai biya mun aikin Hajji ne. Idan na

yarda ya bani rance a ciki tunda akwai sauran lokaci da Shara

ɗ

in zan maido da su kuma na kar

ɓ

a tunda na san zance ne kawai yake yi in dai Allah ya nufa tunda yayi niyya zai biya mun na je na san kuma ko da na mayar da ku

ɗ

in ba zai kar

ɓ

a ba. Wannan karon A

nty Labiban na bawa aka kawo mun kayan yaran kuma Allah ya bu

ɗ

a mun kasuwar kafin kace me suka ƙare sai dai kafin na ha

ɗ

a ku

ɗ

in na sake bata a kawo wasu na cinye rabi, da aka sake kawowa dab da sallah ƙarshe ya saka na bawa yaran yayyen sa akan zai siya ha

r yau kuma bai bani ku

ɗ

in ba shikenan jarin ya karye ido da kunya kuma na sake komawa.

Sai da Abba ya kira sau biyu kafin nayi ƙarfin halin

ɗ

agawa. Muak gaisa kafin ya ce

"Ina kan hanya ne sai da ma sauka yanzu naga kiran ki, kuma

ɗ

azu na shigo unguwar

taku wata gaisuwa kamar na leƙo naga wannan maƙuyaciyar matar tawa da ake mun rowar ta sai kuma na wuce"

"Lah Abba da ka zo ai bata da lafiya ma shiyasa kwana biyu kuka ji mu shiru" na fa

ɗ

a. Ya tambaye ni mai ya sameta na gaya masa harda sunan magungun

an da aka rubuta mata kafin ya mata addu'ar samun sauƙi. Jin yana ƙoƙarin kashe wayar ya saka na ce

"Dama Abba likitan ya rubuta mana wani test ne yace idan ta sha maganin na kwana uku bata samu sauƙi ba muyi kuma yau kwana ukun da sauƙi jikin amma ba y

anda na zata ba shine nake tunanin ko zan mayar da ita ayi"

"Ya kamata dai ayi test

ɗ

in na

ɗ

auka ma ai sai da sukayi kafin aka bata maganin, amma dai ba Dr Bashir kuka gani ba dan na san shi baya rubuta magani kai tsaye in dai symptoms yana buƙatar ayi

test sai ya tabbatar da abunda yake damun mutum kafin nan" cewar Abba. Shiru nayi ya sake cewa

"Ki tabbata gobe kun koma anyi test

ɗ

in Allah ya sa ba Pneumonia ba ce ba"

"Ai ku

ɗ

i ne bani da shi ma shiyasa da yau

ɗ

in zan mayar da ita" nayi ƙarfin hali

n fa

ɗ

a. Ya

ɗ

an yi shiru kafin ya ce

"Babanta baya nan ne?"

"Aa yana nan Abba, cewa yayi na bari cikin wanin satin ayi salary tukunna"

"Wace irin magana ce ita rashin lafiyar yarinyar za'a ce a jira har wani lokaci? Zan tura miki ku

ɗ

i yanzu ki kama h

anya ki mayar da ita Asibiti duk kuma yanda akayi ki sanar da ni" Abban ya fa

ɗ

a kamar cikin fushi dai dai lokacin Bilal ya shigo

ɗ

akin nayi masa kallo

ɗ

aya na cigaba da yiwa Abba godiya.

"Halimatu" Abba ya sake kira sunana, kafin na amsa ya cigaba da ce

wa

"Ya kamata kiyi ƙoƙari ki samu certificate

ɗ

in NYSC a nema miki aiki idan ya so ki ha

ɗ

a da business

ɗ

in gaba daya zai fi, duk da dai na ce ba zan sake magana akan hakan ba amma hakan ya kamata ayi".

"Shikenan Abba zan masa magana duk shawarar da ya

yanke sai na fa

ɗ

a maka" na fa

ɗ

a murya ta na karyewa, ya ce

"Ba zancen shawara bane Halima umarni nake baki, ya isa haka ya kamata ki san in da kika dosa a rayuwa zuwa yanzu". Haka nan naji zuciya ta ta karye kuka ya taho mun amma na daure na ce

"In sha

Allah Abba".

"Ko akwai wata matsala ne Halima?" Na toshe baki na da hannu dan kar sautin kukan da ya taho mun lokaci

ɗ

aya ya isa kunnuwan sa daƙyar na iya saita kaina na ce

"Babu komai Abba, nima dama zama hakan ya isheni dama ina so na fara aikin na

ha

ɗ

a da business

ɗ

in duka"

"Ya dai fi kam, Allah yayi miki albarka ki gaida maigidan naki" ya sake fa

ɗ

a na amsa da " Amin" kafin na kashe wayar na kife kaina akan pillow na fashe da kukan tausayin kaina.

[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*(Based

on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*

*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*

*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*

*Wattpad @MaryamahMrsAm*

*TikTok @Marya

mfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*

*Ku

ɗ

in karatu yana wakiltar mutum

ɗ

aya ne, kiji tsoron Allah karki

ɗ

auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*

*KURA A RUMBU littafin ku

ɗ

i

ne, a biya naira 800, biya a asusun*

*1840175439*

*Access bank*

*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 31*

Nayi mamakin yanda Bilal bai musa ba lokacin da nayi masa maganar service. Nayi sa'a a lokacin ana dab da f

ara registration dama, ranar da aka bu

ɗ

e kuwa banyi wasa ba na je na yi a matsayin mara aure saboda ko da na gaya masan ya ce toh nayi zaton zai je ya fitar da certificate of marriage da domicile letter wa

ɗ

anda zan buƙata amma har ranar ta zo bai ce mun ko

mai ba nima kuma banyi masa magana ba dan ina gudun kada ya canza ra'ayi.

Posting ya fito aka kaini, ban wani damu ba tunda ba nesa bane nasan zan iya zuwa nayi registration a ranar na dawo ba daga nan na nemi relocation dan ba zai yuwu nayi service

ɗ

i

n a can ba. Sai ana gobe shiga camp

ɗ

in sannan na fa

ɗ

a masa Jigawa fa aka turani kuma gobe zan je.

"To me kike so na ce yanzu? Ai ba yau kika san Jigawa aka kaiki ba ko da yake yanzu sai kin gama yanke shawarar ki kike gaya mun kinga wata magana tawa ba

ta da amfani sai ki je ai" amsar da ya bani kenan. Washe gari kuwa na kama hanyar Jigawa da sassafe, saboda ban san sanda zan dawo ba Al'amin bai je makaranta ba na kaishi gidan Mama. Cikin sa'a dake ranar farko ce kuwa kafin ƙarfe uku na gama komai na kar

ɓ

i exit, a Kano shida ta mun dan ma mota ta

ɗ

an tsaya mana a hanya na wuce gida kawai ba tare da na

ɗ

akko Al'amin ba dan na gaji kuma goben Juma'a ce ya ƙara hutawa Monday sai ya koma makarantar.

Ina tayar da sallar magriba wayata ta fara ƙara, yanda k

ira ya ringa shigowa daga wani ya katse ya

ɗ

aga mun hankali, daƙyar na kammala ina yin sallama na

ɗ

auki wayar gaba na ya yanke ya fa

ɗ

i ganin Bilal ne. Ina shirin bin bayan kiran wani ya sake shigowa na

ɗ

aga, cikin muryar dake nuna yana cikin tashin hankali

ya ce

"Halima kina ina?"

"Ina gida na dawo mai ya faru?" Na fa

ɗ

a cikin sauri.

"Hajja ce sukayi accident gamu nan a Emergency na Aminu Kano" ya fa

ɗ

a lokaci

ɗ

aya kuma ya kashe wayar.

A fili na shiga nanata Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Hajja k

uma Accident? A garin yaya? Ina suka je?

Bani da mai bani wannan amsar sai kawai na saka wayar a ajihun rigar dake jiki na na

ɗ

auki Sharifa muka fita. Sai da na je get na tuna ban

ɗ

auki ku

ɗ

in da zan hau mota ba na sake komawa na

ɗ

auka. Daƙyar na samu abu

n hawa duk wanda na tare sai ya ce ba can ya yi ba, a hanya nayi ta sake gwada kiran Bilal amma wayar taƙi shiga. Yanda na ji muryar sa na san da alama yanayin babu da

ɗ

i a raina na ringa addu'ar koma menene Allah ya taƙaita wahala.

Hanani shiga securit

ies sukayi duk yanda na roƙe su daga ƙarshe na koma gefe na cigaba da kiran Bilal har sannan kuma wayar taƙi shiga. Ga gajiya ga yunwa dake damuna ga sauron bala'i a gurin haka nan na tsaya a bakin ƙofa ina addu'ar Allah ya fito da shi ko wani da na sani k

o zan samu su bar ni na shiga. Har ƙarfe tara muna tsaye kafin mai gadin yaga dama ya bari muka shiga. Ido na shiga warewa ina laluben ta inda zan hango su Hajjan amma ban dace ba. Wata Nurse na tambaya tace bata gane wa nake nufi ba, haka na ringa bi gado

gado a can ciki na same su.



Hajja na kwace kanta da hannunta

ɗ

aya na

ɗ

e da bandeji sai ledar jini da aka saka mata amma idon ta biyu. Ajiyar zuciya na sauke dan har ga Allah ban zaci haka zan ganta ba, irin yanda na ji muryar Bilal na

ɗ

auka zanzo na ta

rar da ita a halin rai da mutuwa ne. Muna ha

ɗ

a ido ta

ɗ

auke kai gefe, na kalli sauran Anty Amina, Yaya Saude sai Fadila da Hadiza yar ƙanwar Hajja. Anty Amina ce ka

ɗ

ai ta amsa sallamar da na yi musu, na jingina da gadon dan har jiri nake ji saboda yunwa da

gajiya kafin na shiga gaishe su da tambayar mai jiki.

"Tun bayan magriba nake a waje maigadin ya hanamu shigowa ina ta kiran wayar sa kuma tun ina hanya bata shiga" na fa

ɗ

a. Ina rufe baki Fadila tayi tsaki ta ce

"Ƙaryar banza"

"Ke Fadila meye haka?"

Anty Aminan ta tsawatar mata. Murmushi kawai na yi kaina a ƙasa, kusan minti biyar duk munyi shiru sai ga Bilal da Hafiz sun ƙaraso gurin. A mutunce muka gaisa Bilal kuwa muna ha

ɗ

a ido ya mun kallon da na fassara da harara. Hafiz ya kar

ɓ

i Sharifa dake bacc

i a hannu na yana tambayar ina Dady na ce masa yana can gidan mu.

"Jikin nata ai da sauƙi ba kamar yanda na yi tunani ba" ya fa

ɗ

a, a raina na ce

"Munyi biyu". Bilal ya ce

"Da sauƙi kam amma baka ga a yanda muka kawota asibitin bane Allah ya taimaka ta

samu kulawa da wuri ne kawai amma da an ja wani lokaci irin jinin da ta zubar da ba wannan maganar akeyi ba".

"Toh Allah ya ƙara kiyaye gaba Allah kuma ya sa ya zame mata kaffara" cewar Hafiz gaba

ɗ

aya muka amsa da "Amin".

Fita suka sakeyi da Bilal,

na gyara tsayuwa ta dan ƙiris ya rage na fa

ɗ

i babu kuma wanda ya mun tayin gurin zama a cikin su bayan wani lokaci suka sake dawowa. Sallama yayi musu bayan ya aje musu ku

ɗ

in da ban san ko nawa bane ba. Hajja ta ringa saka masa albarka haka su Yaya Saude k

amar maroƙa sai faman zabga masa godiya suke. Ina lura da Anty Amina dake ta faman cika tana batsewa bani da tabbacin mai aka mata da alama kuma kamar bata ji da

ɗ

in rawar jikin da suke ta yi ba.

Sharifa ya miƙo mun ya na cewa Bilal

"Ba yanzu zaku wuce

gida ba? Dare fa ya fara ga gurin da sauro kada a

ɗ

ibar ma Sharifa malaria". Naji da

ɗ

i har raina da Bilal

ɗ

in ya ce tafiya zamuyi Fadila da Hadiza ma suka ce tafiyar zasuyi muka fita gaba

ɗ

aya ya rage Anty Amina da Yaya Saude wadda zata kwana da Hajjan. A

hanya Hadiza ta sauka Bilal ya tare mata Adaidaita da zau ƙarasa da ita muka wuce tare da Fadila ban so kwanan da ta ce zata yi a gidan mu ba. Har gida ya sauke mu, a hanya ya cewa Bilal

"Ya dai kamata fa ka samu mota ko ƙarama ce saboda irin haka" shi k

uma yayi dariya ya ce

"Tukunna dai ai har yanzu ban isa riƙe mota ba, yanda rayuwa ta ƙara tsada mota ai sai irin ku dai manya mu dai barmu mu cigaba da hawa Adaidaita sahun da muka fi ganewa". Hafiz

ɗ

in ya yi dariya ya ce

"Gara ma kace baka da ra'ayin

siyan mota zan fi yarda idan kuma haka ne ai ita Madam na san ba zata ƙi ba sai ka siya mata ko dan saboda hidimar yara ko kema kin fi ganewa hawa Adaidaita sahun?" Ya jefo mun tambayar, murmushi kawai nayi na ce

Hawa Adaidaita ai sai dole gara dai ya ta

imaka ya siya mana motar mu huta"

"To ka dai ji abinda Madam ta fa

ɗ

a" Cewar Hafiz

ɗ

in. Zancen motar suka cigaba dayi har muka isa. Ua zaro ku

ɗ

i daga aljihun sa ya sakawa Sharifa a hannu sanda zamu sauka nayi masa godiya muka wuce.

Muna ƙoƙarin shiga

falo Fadila ta ce mun

"Yanzu ko kunya bakya ji da auren ki a gaban mijin ki kike washe baki kina magana da wani namijin daban? To tun wuri idan ma zaki shiga hankalinki ki shiga dan Yaya Hafiz da iri na ya dace" ta fa

ɗ

a tana wani watsa hannu da juya ido.

Kallonta nayi cike da mamakin kalamanta na ce

"Da alama kinyi hauka ko Fadila? Ban gane na washe baki ina masa dariya ba? kin san me kike cewa?"

"Tsaki ta yi ta shige ciki kamar gidan ta. Na bita da kallo kafin na bi bayan ta zuciya ta na tafarfasa n

a ce

"A zaton ki kowa shashasha ce irin? Ko zamanin yammatanci na ban banzatar da kaina nayi alaƙar banza da maza ba balle yanzu da nake da aure kuma wai da abokin miji na. Kije ke da Allah ƙazafin da kika mun" na nufi

ɗ

aki dai dai lokacin Bilal ya shigo,

tana ganin sa ta shiga matsar hawayen ƙarya tana cewa

"Ni kike cewa karuwa Halima?"

"Da Allah malama dakata duk naji abinda kowaccen ku ta fa

ɗ

a, ki shiga hankalin ki ba kowanne iskanci zan

ɗ

auka ba yanzu" ya fa

ɗ

a yana nuna ta da yatsa. Murmushi na sa

ki raina fes da yanda karo na farko ya tsaya mun na kalleta na ce

"Ba a koda yaushe ƙarya da munafunci suke cin nasara ba nan gaba kin san me zaki fa

ɗ

a" na wuce

ɗ

aki Bilal ya biyo baya na.

"Saboda ba mahaifiyar ki bace a Asibitin shiyasa sai da kika g

a dama sannan kika je ko? Ai da kinyi zamanki kawai ma baki je ba dan banga amfanin da zuwan naki ya yi ba" ya fa

ɗ

a take murmushi kan fuskata ya gimtse. A hankali na ce

"Wace irin magana kakeyi haka Bilal? Wlh kana kashe waya na tafi, na fi awa guda a w

aje kafin security ya barni na shiga kai kuma nayi ta kiran wayarka tun ina hanya amma bata shiga ba.."

"Dalla malama rufe mun baki maƙaryaciya kawai" ya dakatar da ni cikin tsawa. Wani sanyi na ji tun daga kaina har ƙafafu na, na bishi da ido ganin ya

nufi kan gado ina da na zube ku

ɗ

in da Hafiz ya bawa Sharifa ya kwashe su ya fita daga

ɗ

akin. A hankali na sulale a ƙasan in da nake tsaye saboda yanda ƙafafu na sukayi matuƙar sanyi. Har ta fara kai mu ga zagi kenan? Kullum gaba abun yake yi a maimakon ya

yi baya.

Daƙyar na ƙarfafi jiki na na canzawa Sharifa diaper na fita na dama mata abinci Fadila na kwance kan kujera tana waya na wuce kitchen na ha

ɗ

o abinci na koma

ɗ

aki, duk yanda nake jin yunwa haka ma kwanta wani irin abu nake ji da ban san yanda z

an misalta shi ba. Da asuba ina jiyo shi yana sharar tsakar gida, sai da gari yayi haske kafin na fito ina takawa a hankali saboda yanda yunwa ta gama rarake mun ciki. Sai da na fara ha

ɗ

a baƙin shayi na sha yan hanji na suka warware kafin na shiga fere doy

ar da na gani a kitchen

ɗ

in. Ban san ya yake so ayi da ita ba dafawa za'ayi ko soyawa ko fate?

Na gama na kwashe

ɓ

awon kafin na fita daga kitchen

ɗ

in da niyyar zuwa na tambaye shi yanda za'ayi da doyar sai gashi ya shigo muka ci karo a bakin ƙofa. Mats

a masa nayi ya shiga, ya aje ledar ya matsa gaban sink in da na ajiye robar da doyar take ciki ni dai ina tsaye ina kallon sa kafin murya kamar wanda aka cusawa tsumma a baki ya ce

"Ki rabata biyu tayi yawa idan ya so kiyi mata fate da sauran da daddare.

Murmushi na yi ma ce

"Soyawa za'a yi yanzu?"

"Ke baki san abinda ya kamata kiyi ba?" Ya hayayyaƙo mun, sai na wuce in da ya ajiye leda ina cewa

"Har yaushe na fara yanke hukunci akan abinda ka kawo cikin gidan nan?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login