Showing 105001 words to 108000 words out of 287295 words
a
ɗ
aki kafin na fita na bu
ɗ
e bayan da na tambayi wanene.
Maman Yusuf ce da surukar ta inna da kuma Maman Aliyu. Ina murmushin yaƙe na basu hanya suka shigo, bayan sun zauna muka shiga gaisawa,
"Tun sassafe na cewa Sidi idan ya ga kun bu
ɗ
e ƙofa ya gaya mun shiru shiru dai na ce bari mu shigo yanzu" Maman Yusuf
ta fa
ɗ
a. Na yi murmushi kawai ba tare da na ce mata komai ba kafin na miƙe na shige kitchen na samu jikin cabinet kawai na jingina ina tunanin me zan basu.
To dai ko bamu da dangi daga ni har Bilal
ɗ
in ace yau ana suna a gidan mu ya ci a ce mun tattaro
maƙwafta sun rufa mana asiri balle daga ni har shi babu wanda za'a yiwa gorin yawan zuri'a amma ace ko ƙuda babu da sunan ya zo taya mu murna. Muryar Baba Jummai da na ji ta sa na shiga share hawayen da suka fara saukar mun da sauri, ta wuce ni, tukunyar d
a ke kan gas ta bu
ɗ
e bayan ta
ɗ
ebo kwanuka ta shiga zuba miya, na ringa kallon ta da mamaki ita dai bata ko kalle ni ba har ta gama zuba miyar ta jera a try ta fita da su kafin ta dawo ta zuba tuwo shima ta ha
ɗ
a da ruwa ta fitar musu da shi. Tabbas da na f
arka na ji gidan na ƙamshin miya amma ban gasgata ba. Bayan tafiyar su Maman Yusuf dan basu ci tuwon ba juye musu tayi suka tafi da shi ta ce na lissafa mata gidajen da za'a aika da tuwon. Baki na kamar ze tsage dan farin ciki na ce
"Baba yaushe kika yi
tuwon nan?"
"Ba dai ke sakarya ba ce a garin ki rufawa miji asiri zaki tonawa kanki asiri banda haka a ina kika ta
ɓ
a ganin irin wannan rashin lissafin na ki? Yanzu ba dan nayi dabarar tashi da duku duku na yi tuwon nan ba yanda mutanen nan suka shigo da
me zasu fita su bada labari? Dama salin alin da an gama kai abincin nan ki saka kayanki da na yaron nan a yar jaka mu tafi can gidan in ya so ma dawo da dare dan ni dai tunda uwata ta haife ni ban ta
ɓ
a ganin irin wannan kalan tsiya ba.
[5/19, 22:05] Buha
inat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @
MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 24*
A ƙaramar akwati na zuba mana duk abun da na san zamu buƙata a yinin, Baba Ju
mmai ta goya Al'amin tana tsaye tana jiran na yafa gyale na da na ajiye a gefe. Zama na yi a gefen gado ina rarraba ido kamar wadda ta yiwa sarki ƙarya, ta kalle ni ta ce
"Ya kuma kika zauna? Tun da dai an kaiwa maƙwaftan nan abinci se ki tashi mu tafi ku
ma su ce zasu shigo yinin suna".
"Baba ban gayawa Bilal ba" na fa
ɗ
a ba tare da na kalle ta ba,
"Naga abinda ya ishe ni ni Hasana, yanzu gidan ku
ɗ
in da zaki tafi shine kike cewa baki gaya masa ba? Me ze miki? Naga tun farar asuba ya fice ya bar miki
gidan gashi har sha biyu ta taho ko
ɗ
an tsako be leƙo gidan nan daga dangin sa ba, kar kiyi ta kanki kin ji. Ni dai idan ma ba zaki tafi ba se in yi gaba abu na in ya so ki saka ce gidan duk bugun da za'a yi karki bu
ɗ
e tun da dai baki da abun bawa ma su sh
igo mikin" Cewar Baba Jummai. Se na miƙe na yafa mayafin jiki a sanyaye, ta nufi ƙofa tana cewa
"Jira na taro mana
ɗ
an sahu ba ma fita haka da akwati ana kallon mu ba" ta fita. Komawa na yi na zauna na yi tagumi hannu biyu, ko a waya ba wanda ya kira ni
se kace wata mara galihu. Tunanin in da Bilal ya tafi na shiga yi, gashi ba waya a hannun sa balle na kira shi kuma gaskiya zan so na tafi can gidan nima tun da zamana a nan dai a yau ba shi da wani amfani. Muryar Baba Jummai da na jiyo da wani da ban gan
e ko waye ba ya sa na fita tsakar gida na tarar da ita tare da Abubakar da Saleh suna ƙoƙarin saƙale Rago a jikin window
ɗ
akin tsakar gida.
"Yanzu da ze yi yankan tun farar safiya ba'a yi ba se yanzu da rana ta take?" Na jiyo ta tana fa
ɗ
a, su dai ba su
tanka mata ba suka gama
ɗ
aure shi kafin suka shigo falon muka gaisa a tsatstsaye suka wuce. A falon na zauna Baba Jummai kuma ta kwance Al'amin ta hau aikin gyara kayan ciki tana yi tana mita duk ta cika mun kunne se kawai na koma cikin
ɗ
aki na rufo ƙofa t
a. Har bacci ya fara
ɗ
iba na sama sama hayaniya ta tashe ni, kamar na doka tsallen murna ganin su Amal da sauran cousins
ɗ
ina kusan su goma. Zuwan su ya wartsakar da ni musamman da na gansu da tulin ruwa da lemo katan katan ga wasu kuloli da suka ce saƙon
Anty Labiba ne ta ce kar wanda ya ta
ɓ
a se ta zo. Zuwa la'asar gida ya gama cika taf da dangi na kusa da na nesa ana ta harkokin arziƙi har sannan kuma yan cikin gidan su Bilal babu wanda ya zo.
Babu ce kawai Anty Labiba bata dafo ta kawo ba tun daga ka
n abinci zuwa snacks da abubuwan sha iri iri. Nan gurin dining
ɗ
ina ta sa aka tura shi gefe ta zuba kayan suka ringa serving, daga yanda taƙi matsawa ko nan da can daga kan abincin na fahimci ta shirya wani abu shi yasa har zuciya ta nayi farin ciki da ras
hin zuwan dangin Bilal dan dai na san koma menene saboda su ne. Biyar da wani abu na shiga canza kaya saboda me
ɗ
aukar hoto da ya zo se ga yan gudan su Bilal zuga guda yan
ɗ
akin su da kuma yan uwan Hajja babu dai dangin Baban su ko
ɗ
aya ko matan yayyen sa
a ciki.
Dama tun da Khausar ƙanwar Mijin Fainusa ta zo take tambayar bata ƙaraso ba ne na ce mata eh bata zauna ba kuma ta tafi dama jiki na ya bani sai ta kira Fainusan ilai kuwa se gasu manya da yara Anty Amina ce kawai babu.
Falo na suka fara shig
a suka gaisa da yan uwana da ke zaune kafin Fadila da Fainusa suka iske ni
ɗ
aki, Fadilan ta ce na basu key
ɗ
in can falon
Bilal tun da nan
ɗ
in ya cika da mutane. Ban musa ba na
ɗ
auka na bata dan zan fi so su ware gefen.
A can na same su muka gaisa mai h
oton ya fara shiga can muka yi hotunan kafin na dawo tsakar gida muka cigaba. Na
ɗ
auka za'a samu wanda zai yi tunanin basu abinci shi yasa na cigaba da sabgogina, Ummi yar Anty Sauda yayar su ta biyu tazo tayi kira na wai inji Maman su. Na tarar da su kowa
cce fuska a
ɗ
aure kamar zasu rufe ni da duka. A gadarance ta ce mun
"Da alama kin manta muna zaune a nan ko Halima?"
Duk da na fahimci in da maganar ta ta dosa dan banga ko ledar ruwa an ajiye musu ba amma na ce mata
"Na san kuna nan mana Anty"
"Iska
nci ne wato ya saka aka barmu a gantale ko kuwa jira ake mu fito mu
ɗ
ibi abincin da kanmu?" Anty Hauwa, ƙanwa ce gurin Hajja abokanan wasa suke ta fa
ɗ
a. Se na miƙe ina cewa
"Kuyi haƙuri, ina ga sun shafa'a ne bari na je na musu magana, yanzu za'a kawo m
uku" na fita daga falon ina ji suna bi na da ƙananun maganganu. Rasa ta yanda zan tunkari Anty Labiba na yi dan haka na ja Amal gefe na ce ta
ɗ
auki manyan kuloli a kitchen ta zuzzuba abinci idan Anty Labiba ta tambaye ta ta ce ƙawaye na da zasu zo an jima
za'a ajiyewa se ta kai mun
ɗ
akin Bilal ta ajiye. Shiru shiru kusan minti goma sai gata, da sauri na tare ta ina tambayar ina abincin ta ce mun Anty Labiban ta ce ba ze ƙare ba duk wanda ze zo ma ze samu. Ban ji da
ɗ
i ba, na ringa jele tsakanin falon da
ɗ
aki
amma na kasa yi mata magana. Bana so na yiwa wani babba maganar ta ce na kai ƙarar ta ko wani abu amma kuma a take taken ta naga alamar ta shirya yi musu wulaƙanci ne kawai tun da ai taga zuwan su har gaisawa suka yi kuma ita idan ta haihu naga ai tun ma
kafin a fara rabawa mutane abinci take ware na dangin mijin ta.
Hansa'u na jawo akan ta yiwa Anty Labiban magana ta ce wlh babu ruwanta. Na kasa tsaye na kasa zaune ga Ummi tsaye bakin ƙofa na san kuma ba ze wuce sake aiko ta akayi kar
ɓ
ar abincin ba ku
ma tana ji Anty Labiban na yekuwar idan da me buƙatar ƙarin wani abu ya zo ya kar
ɓ
a, ina kallo ta jinjina kai irin zata je ta kai rahoto ta juya se kawai na yanke shawarar yin shahada na mata magana. Ina matsawa gurin na jiyo Mama Sa'a matar kawun su Mama
tana tambayar ta an kai wa dangin miji na abinci kuwa?
Anty Labiban ta ce
"Aa ba'a kai musu ba, na manta". Na sauke ajiyar zuciya a filiz na san ba ƙaramin mutunchin Mama Sa'ar take gani ba da har ta bata amsa me da
ɗ
i haka, ina ji ta wuce tana ce mata
"To ki zuba a kai musu dan Allah ba da
ɗ
i kusan rabin awa da zuwan su kuma sun shigo sun tarar da mutane na cin abinci"
"Za'a kai yanzu" ta sake bata amsa. Ta ke na ji sanyi a raina na waske na bar gurin ba tare da na ce mata komai ba duk da a ƙasan rai
na na ji kamar na tsaya na
ɗ
ibarwa Bilal ban sani ba ko ze bawa su Nasir da sauran abokanan sa na unguwa amma na san zata iya saka kaina a kular abincin shiyasa na haƙura ban koma ba. Se da aka kira Magriba taro ya fara watsewa, na samu alkhairi ƙwarai da
gaske Abba ma ya yi goshi daga kan riguna ku
ɗ
i da kayan amfani su diaper da omon wanki da su sabulu mun same su babu adadi zamu ja lokaci sosai kafin su ƙare mana.
Tun da naji za'a kaiwa su Fadila abinci ban sake bi ta kan su ba musamman da ƙawaye na d
a mu kayi poly tare suka zo duk hankali na ya tafi ga maƙwafta masu shigowa da sauran yan uwa gaba
ɗ
aya na sha'afa da su sai da su Baby Bashir zasu tafi na fito raka su kafin ido na ya sauka kan ƙofar
ɗ
akin Bilal
ɗ
in da na hango yara na tsere a ciki. Gaba
ɗ
aya se na rasa nutsuwa, get na yi niyar taka musu amma na tsaya daga in da nake na bar su da Hansa'u ta tafi raka su wajen ni kuma na wuce
ɗ
akin Bilal. Babu kowa sai yara dake wasa da wasu yan gidan su Abban mu yammata suna
ɗ
aukar hoto. Ce musi na yi su f
ita na kullo ƙofar dan key
ɗ
in ma a jiki suka bar shi na jefa shi cikin aljihun rigata zuciya ta na bubbugawa dan na san har dai zasu tafi ba tare da sun yi mun sallama ba tabbas da wuya idan ba Anty ta musu wani abun da ya sosa musu rai ba ne. Haushin kai
na ya kama ni, ko me ya sa ban tsaya na ga abincin da ta zuba musu ba ko kuma na sake komawa gurin su na tabbatar an basu komai wadatacce, bana ma zaton ta basu souvenirs
ɗ
in da naga ta bawa ƙawaye na da suka tafi yanzu ƙila ko daga baya aka kawo su.
Haka dai jama'a suka ida watsewa ya rage na jiki wa
ɗ
anda suka tsaya suka gyara mun gida tsaf ba zaka ce anan aka sha didimar biki ba, abincin da yayi saura da yawa masu so sun
ɗ
iba sun tafi da shi, ta zuzzuba mun abinda ze ajiyu na saka a fridge miya kuma
da nama na saka a frizeer haka sauran ruwa da lemo kusan katan goma goma duk na lode su a store, basu bar gidan ba hatta kayayyakin da muka samu na barka se da suka taya ni na ware su komai ya koma muhallin sa kafin kowa ya wuce gidan sa. Ina tsaka da shaf
a mai bayan na watsa ruwa saboda jiki na da ya yi mun tsami sosai Bilal ya dawo.
Da Baba Jummai na jiyo suna gaisawa be shigo
ɗ
aki na ba bayan na gama shiryawa kamar in share shi sai kuma wata zuciyar ta ce na dai je. Dama na ware masa abinci na sake
ɗ
umamawa na ha
ɗ
a komai a try na fito Baba Jummai ta bini da kallo ta na cewa
"Ba dai
ɗ
akin sa zaki kai masa ba" na yi murmushi kaina a ƙasa dan na san baze wuce abin da ya faru jiya ya sa tayi tambayar ba se kawai na wuce na ajiye su tsakiyar falo kan cent
er table ina cewa
"Aa, a nan zan ajiye masa"
"Ya dai fi miki" ta fa
ɗ
a tana wucewa
ɗ
aki. Fita na yi na tafi
ɗ
akin Bilal, a falo na same shi yana waya bakin nan kamar ze tsage saboda farin ciki ina shiga ya yafito ni da hannu, ban matsa kusa da shi sosai
ba na tsaya daga gefe ya miƙo mun wayar na kar
ɓ
a duk da ban san waye ba sai da na kara a kunne na kafin na gane Hafiz ne.
Muka gaisa yana tambayar ina Dadyn sa tare da bani haƙuri akan rashin zuwan su wai uzuri ya taso musu basa ƙasar, ya ce Shahida ta
ce idan ta kira ni bata samu na fa
ɗ
a masa na yi setting layi na private ne idan ba ni da number kiran ba ze shigo ba se dai na ga missed call kuma tabbas na ga an kikkira ni da number waje amma ban san ita ba ce shiyasa ban bi baya ba. Jin muna yin sallam
a Bilal ya ra
ɗ
a mun a kunne wai na yi masa godiya, ban san godiyar ta me ce ce ba amma haka na yi ya ce ba komai daga nan na mayar masa da wayar sa na fita bayan na sanar masa ga abinci can yana jiran sa.
Na zata ba ze zo ya ci ba ganin kusan minti gom
a har na fara gyangya
ɗ
i kafin ya shigo. Farat farat ba zaka ce shi ya gama gasa mun maganganu jiya da daddare ba wai har yana tambaya ta ya taro an ce masa an sha
bidiri a gidan nan. Na yi murmushi kawai ina kallon sa yana cin abincin yana soko mun hira, a
raina na raya kenan su Fadila ba wani abu ya sa suka tafi ba tare da mun yi sallama ba ko kuma dai labarin bai iso kunnen sa ba ne. Da ya gama ci naga alamar yana so ya ja hirar da tsayi na ce masa bacci nake ji, na ringa kallon sa da mamaki jin ya ce na
karanto masa account number na ya samu wasu ku
ɗ
i ni ma zai tura mun wani abu.
Na gama karanta masa ya saka muka yi sallama yana shirin rungume ni na zille na shige
ɗ
aki, na goge ido na ya fi sau nawa a son na tabbatar da gaske ku
ɗ
in da na gani haka suk
e ko kuwa dai ban ga ni da kyau bane ba. Dubu
ɗ
ari Bilal ya aika mun, dubu
ɗ
ari dai a tarihin rayuwa ta da shi tun da muke dunƙulalliyar dubu goma bai ta
ɓ
a
ɗ
auka ya bani ba idan ba ta siyan kayan barka ba.
Duk baccin da nake ji sai na ji na wartsake, na
rasa ma wacce kalar murna zanyi. Screenshot na yi na turawa Anty Labiba, kafin su tafi ba kalar habaicin da bata mun ba ace haihuwar fari amma abincin da za'a ci na suna se dai a dafo daga gidan ubana