Showing 108001 words to 111000 words out of 287295 words

Chapter 37 - KURA A RUMBU COMPLETE

a kawo mun kuma a haka dan bani da kunya na cigaba da

yi musu kankanba ni me miji kuma yana so na ai ko auren ha

ɗ

i ba za'a kwata abinda aka mun ba.

Ni dai abin da na ke raya wa a zuciya ta Bilal na so na, duk kuma abin da a ke ganin ba ya mun da ma ce ba shi da ita ina kuma da yaƙinin wata rana zai mun ni

nkin abin da ma ba'a ta

ɓ

a tsammata ba gashi kuwa ya fara tabbatar da hasashe na. Bacci ma kusan rabi da rabi na yi, bini bini zan farka na ja waya na duna dan in tabbatar ku

ɗ

in na nan ba su gudu ba.

GIDAN HAJJA

Tun safe suka ta shi da kacaniyar taron

sunan da suka shirya zasu yi a can gidan. Ita ta ƙarfafawa Bilal akan ba wani taron suna da Halima za tayi in dai ba can gidan su zata tafi suyi a can ba, daga baya kuma ta riki

ɗ

a ta ce ita zata yi taro a nan gidan ta, jikan ta na farko na

ɗ

a namiji bai ka

mata ace ba a yi taron suna ba. Da Anty Amina ta ce mata in dai ba Halima za'a bawa ku

ɗ

i ta yi taro ba se dai a haƙura haka ta ringa fa

ɗ

a ta na cewa ita ta kasa ganewa Amina, gaba

ɗ

aya ta canza yi ta ke ma yanzu kamar Halima ce yar uwar ta ba Bilal ba to b

a za'a bata

ɗ

in ba idan ta na so ta fitar da ku

ɗ

in ta tayi taron nan itama da Fadila ta haihu ai babu ƙwandalar kowa su suka yi taron sunan su.

Da Bilal

ɗ

in ya ce mata ba shi da ku

ɗ

i yanzu na Rago ya ke ƙoƙarin ha

ɗ

awa ma ce masa ta yi ita ba damuwar ta

ba ne wannan idan ya so ma ya bari se ranar sati biyu sannan ya yi musu yankan. Haka nan se da ya basu ku

ɗ

in kafin ya samu lafiya a hannun Hajjan. Da safe kuma bayan an gama ra

ɗ

in suna bayan da ya je banki ya tarar da Hafiz ya aika masa saƙon da ya girgiz

a masa lissafi. Ya san tabbas ze yi masa abu na bajinta domin Hafiz akwai harkar girma amma be zata abun ze kai har haka ba. Babu bata lokaci ya Abubakar ya ce ya zo ya kar

ɓ

i ku

ɗ

i ya siyo Ragon shi kuma ya wuce wani uzuri.

A gurin da ya siya ya yanka ak

a fe

ɗ

e masa kamar yan da Bilal

ɗ

in ya ce ayi sannan ya wuce ya kai can gidan ya na komawa gida marin sa ne kawai Hajja ba ta yi ba dan a yanda ta ce ta

ɗ

auka yana da hankali idan ya siyo zai yi tunanin ya fara kaiwa gidan ta ba wai ya wuce ya kaiwa Halima

ba. Ta ringa sababi, se kace wacce aka kai musu garke guda hatta da yayan ta

sai da abin ya ba su haushi ga mutane duk suna zaune suna jin ta take wannan abun. Suna tsaka da sabgogin su Fainusa ta je ta ke basu labarin yanzu aka kira ta ana can ana bidiri

a gidan Bilal, kuma wai duk se ransu ya

ɓ

aci akan me ba'a gaya musu Halima za ta yi taro ba, har Bilal

ɗ

in Hajja ta kira ya ce shi bai san zata yi ba dan be bata ko sisi ba se dai idan yan gidan su ne suka shirya abun su, haka suka zari jiki suka tafi har

Hajjan da ta ce zata bisu suka hana ta ta ringa jaddada musu akan duk abin da aka yi su taho mata da shi se gasu yanda suka je haka suka dawo hannu na dukan cinye se ma asarar ku

ɗ

in mota da suka yi dan dai ko ruwa ba'a basu ba a yanda suka ce. Suka ringa z

agin Halima da yan uwan ta suna wassafawa Hajja irin liyafar da suka tarar ana yi tun daga kwanukan almajiran da suke ƙofar gidan zaka san ana harkar girma a ciki amma tsabar an raina su ba'a kuma daraja su ba haka nan aka bar su kamar wasu almajirai babu

wanda ya bi ta kan su suka gaji da zama suka taho.

Saboda yan da abin ya harzuƙa Hajja bata iya cewa komai ba, ta ringa kiran layin Bilal wayar na ringing amma yaƙi ya amsa wannan ya sake

ɓ

ata mata rai, duk yan da aka yi da sanin sa shi ya sa ya zagaye y

a sa aka kai musu Rago ba tareda ya yi shawara da ita ba.

WASHE GARI

Tun da na yi wankan safe na ci abinci na sake komawa bacci ban farka ba se azahar lokacin har Baba Jummai ta gama soya naman tas ta gyara gidan, ban yi mamakin ganin babu wanda ya zo

taya ta suyar naman ba. Se da na sake watsa ruwa sannan na fito, tambayar ta na yi ko Bilal ya shigo ina bacci ta ce be fito ba ba ta ji motsin sa ba. Abinci na fara ha

ɗ

a masa, sauran sinasir da waina na

ɗ

umama na

ɗ

ibi nawa na ha

ɗ

a komai a try na faki ido

n Baba Jummai na tafi

ɗ

akin. Sallah na tarar ya na yi, bayan ya idar ya kalle ni da murmushi ya ce

"Kin ta shi kenan?"

Murmushin na mayar masa na ce

"Ashe ka leƙa na tambayi Baba ta ce bata ji motsin ka ba"

"Sanda na shiga tana can tana soya nama, da

kamar na yi mata magana na ga ta goya Al'amin ga hayaƙi ga kuma zafin wuta kar su dame shi". Na zare ido ina dariya na ce

"Lallai, ka ce ka so ka siya mana magana ta ce ka mata rashin kunya. Ka san mitar Baba kuwa? Ɗazu fa daga ta masa wanka ta ajiye shi

taje zubar da ruwan naga towel

ɗ

in ya bu

ɗ

e ga farka a kunne na gyara masa ta na zuwa ta fara mun taratsi wai me na ke dubawa a jikin sa kar na mata sharri na ce ta masa wani abun" muka yi dariya tare kafin ya ce

"Amma tana da kirki sosai ga aiki, na lu

ra sam bata son ƙazanta itama ko ina fes fes

ɗ

akin ku yana ƙamshi kamar ba na masu jego ba gaki kema ta na kula mun da ke sosai" ya fa

ɗ

a ya na jana jikin sa. Ban musa ba na je, yana shafa fuska ta ya ce

"Jegon nan ya kar

ɓ

e ki My Halims, wani kyau kullum k

ike ƙarawa haƙuri na fa ya fara ƙarewa". Zabura na yi na bar jikin sa da sauri ya fashe da dariya kafin ya ja try

ɗ

in gaban sa ya bu

ɗ

e ya na cewa

"Kamar kin san yunwa na ke ji sosai,

ɗ

an

ɗ

ebo mun naman nan na ta

ɓ

a. Idan kuma akwai sauran peppered chicken

ɗ

in jiya ki kawo mun". Zuwa na yi na

ɗ

ebo masa naman na ha

ɗ

o da kazar da ya ce na ji da

ɗ

i da na tarar Baba Jummai a garin lalla

ɓ

a Al'amin ta bi shi sun yi baccin tare se na

ɗ

auki abinci na na wuce da shi muka ci tare muna hira kamar lokacin ya dawwama.

"Akwai tafiya da zan yi, zamu je wani aiki Abuja daga office. Tun shekaran jiya wa

ɗ

an da zamu tafi tare suka yi gaba na bari ne dama se an yi suna nima jiki na ya sake warwarewa kafin na bi bayan su cikin ku

ɗ

in aikin da aka bamu ne ma na tura miki wani abu

daga ciki jiya" Bilal ya fa

ɗ

a bayan da muka gama cin abinci,

"Toh, yaushe kenan kuma zaka tafi?" Na tambaye shi. Ya

ɗ

an

ɓ

ata fuska ya ce

"Gobe nake tunani dan suna ta mun waya akan na taho ni suke jira mu fara aikin".

"Amma fa har yanzu jikin ka da sa

ura, na fa lura da kana sallah ƙafar ka daƙyar ka ke lanƙwasata a haka kuma zaka tafi wani aiki ba zasu canza ka da wani ba?" Na fa

ɗ

a cikin marairaicewa. Se ya miƙe ƙafar yana cewa

"No na samu sauƙi fa, rashin yawan motsa jikin ne ma ya sa har yanzu nak

e

ɗ

an jin ciwo amma babu wata damuwa zan iya. Kuma ban da abin ki bayan har an bani ku

ɗ

i na kashe se na ce kuma ba zani ba kenan zan mayar musu da ku

ɗ

in su".

"Kuma aikin na menene?"

"Bari na zo na je gidan Hajja, naga ta kira ni tun jiya ashe ban lura

ba se

ɗ

azu tukunna" ya fa

ɗ

a ba tare da ya bani amsar tambayar da na masa ba. Tattare kwanukan na shiga yi ina cewa

"Bari to na yiwa Baba magana ta raba naman se ka tafi musu da nasu kawai" na fice daga

ɗ

akin. Ina shiga kitchen na jiyo ana buga get, shi

ya fita ya bu

ɗ

e, gaba na ya fa

ɗ

i jin muryar Hajja ta na cewa

"Bacci kuke ko me da za'a yi ta bugu ba zaku bu

ɗ

e ba". Sauri na yi na kashe famfo na bar

ɗ

auraye kwanukan da na yi niyya da gudu gudu na wuce

ɗ

aki na na shige ban

ɗ

aki.

Kamar na fasa kuka sa

nda ya zo ya na ƙwanƙwasawa wai na fito ga su Hajja sun zo, se da na kwashi kusan minti biyar kafin na fita falon kaina a ƙasa ba tare da na bari mun ha

ɗ

a ido ba na samu gefe can na zauna na shiga gaishe su. Bata amsa ba ta fara zazzage mun asalin abin da

ya kawo ta wato bin ba'asin wulaƙanta yayanta da yan uwanta da aka yi jiya.

"Har su zo miki taro a hana su abinci, ban da tsiya me akai aka yi abinci da har kuke rowar sa? Ko da yake dama shi taka hayen arziƙi in be nuna halin sa ba ta ya za'a gane shi?

Duk wata fuffukar da kuke yi kallon ku kawai muke yi wlh har yaushe Aminun ya zama wata tsiya da har kuke ƙafafa, ai wanda bai san asalin ungulu ba ne za'a ce masa daga masar take ya yarda. Ke ba dan mutuwa me tonin asiri ba har Aminu za'a saka shi a jerin

masu arziƙi ne balle ya haife ki kamar Bilal ya kalle ki ya aura ai ƙaryar ki" cewar Hajja.

Na rasa dalilin da ya saka a koda yaushe take ƙoƙarin cin mutunchin iyaye na. Idan ma laifi na mata me yasa ba zata zageni ni ka

ɗ

ai ba dole se ta ha

ɗ

o da iyaye

na da basu mata komai ba ta zage su ta yi musu cin mutunchi? A karo na biyu Bilal na zaune akan idon sa da kunnuwan sa Hajja ta ke aibata ni da iyaye na Lanti da suka zo tare tana taya ta amma be iya ce musu komai ba.

Baba Jummai ta fito daga

ɗ

aki, na

tabbata kuma hayaniyar su Hajjan ce ta tashe ta daga bacci tayi mici mici da ido tana kallon ta ta ce

"Amma dai ko wacece ke baki da

ɗ

a'a ba kuma ki da mutunchi. Ki shigo har

ɗ

akin yarinya ki sakata a gaba kina zagin iyayen ta da basu ji ba basu gani ba

"

"Ni a uwar Bilal" Hajja ta bata amsa, hakan be saka Baba Jumman ta tausasa lafazi ba sai ma Kara harzuƙa da ta yi ta ce

"Eh lallai ba shakka ashe rashin arziƙin na ku gado ne. Yanzu dai ban da bakya tsoron Allah har ke zaki cewa wani bai gaji arziƙi

ba alhalin ga tsiya nan har ta yi kuka a jikin ku tana neman a kawo mata

ɗ

auki. Ai wlh Halimatu ce da kaico domin ba tayi miji ba, banda ƙaddara ina ita ina ita ina ha

ɗ

a hanya da kwa

ɗ

ayayyu irin ku? Da zaki ce sun zo suna an hana su abinci gayyar su aka yi

ko kuma shi mara zuciyar

ɗ

an na ki ya bada ƙwayar shinkafa ya ce a dafa balle har ki tada jijiyar wuya saboda an hana su abinci? Se ka ce dai ana yunwa zaki taho ƙafa da ƙafa kiyi rashin arziƙi saboda an hana abinci ba'a bayar ba ki

ɗ

auki matakin".

Nem

ar hawayen da na ke yi na yi na rasa, na zabura na miƙe tsaye tare da

ɗ

ora hannu biyu a kai ina juya wuya kamar wacce aka tsare da bindiga tsabar yanda jini na ya daskare na ma kasa furta komai balle na hana Baba Jummai cigaba da wannna

ɓ

arin bakin da take

kamar wacce aka kwancewa kai.

Hankali na ya sake dugunzuma jin Hajja ta fashe da kuka ta na kallon Bilal ta ce

"Kana ji Bilal? A gaban ka Halima take zagi na?" Mamaki da tsoro suka dirar mun lokaci

ɗ

aya, wai Halima ta zage ta ni? Yaushe?

Bilal na

kalla, fuskar sa ta yi jajir kamar an watsa masa barkono jijiyoyin goshin sa sun fito kamar an zana su, cikin murya kamar wanda aka shaƙewa wuya ya ce

"Jummai dai ta zage ki Hajja ba Halima ba" se ta ƙarawa kukan ta ƙaimi tana cewa

"Wlh Halima ce ta zage

ni, kalaman bakin ta ne saboda ba zata iya fa

ɗ

a ba ne ta karanta mata idan ba haka ba me ya ha

ɗ

a ni da wannan matar? a ina ta sanni balle ta zage ni haka? Wlh duk Halima ce ta shirya mata tun da dama ai ta san dole zan zo gidan" ta ƙarasa tana sake rushew

a da wani irin kuka irin wanda yake nuna zafin dake cikin zuciyar me yin sa.

"Ashe bayan tsiya har da sharri kuka iya" Baba Jummai ta sake fa

ɗ

a se kawai na fashe da kukan da ya fi na Hajjan tashin hankali, murya ta bata ko fita na ce

"Dan girman Allah

kiyi shiru, ki tafi babu ruwanki wa ma ya kira wo ki haka kawai yanzu kin ga abinda kika jawo mun"

"Haka kika kawo Amirah gidan nan ta zage ni yanzu kuma kin sake kawo wata ta zagi mahaifiya ta. Ni Bilal ban yi lalacewar da zan

ɗ

auki haka ba Halima, i

dan ni kin zage ni na shanye baki isa ki zagi mahaifiya ta ba ko ki wulaƙanta dangi na na

ɗ

aga miki ƙafa. Ki tafi gidan ku Halima ki tafi gidan ku.

[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up th

e story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*

*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*

*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*

*Wattpad @MaryamahMrsAm*

*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya ju

ya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*

*Ku

ɗ

in karatu yana wakiltar mutum

ɗ

aya ne, kiji tsoron Allah karki

ɗ

auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*

*KURA A RUMBU littafin ku

ɗ

i ne, a biya naira 800, biya a asusun*

*1840175439*

*Access

bank*

*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 25*

Ina zaune a falon har Baba Jummai ta gama ha

ɗ

a kayan ta tana kukan da nake ji kamar na tashi na shaƙe mata wuya idan ya so ta yi mai dalili. Ni da ta ke neman ta kash

ewa aure ai ni ce da kuka ba ita ba, akan na ce ta tafi tun da ita ta janyo ni ma aka ce na tafin shi ne ta fasa kuka wai na mata rashin kunya tana ƙoƙarin kare mun mutunchi na watsa mata ƙasa a ido. Ta shi na yi na goya Al'amin bayan da ta fito da jakar t

a daga

ɗ

aki ina kallon ta na ce

"Kuma wlh karki gayawa kowa abin da ya faru, kawai ki ce musu kin gaji da zama a nan ne kika koma gidan Mama".

"Allah ya shirya ki Halimatu Allah ya bu

ɗ

e miki idanuwan ki tun kina da sauran lokaci kafin ki ƙarasa maka

ncewa, kuma baki isa ki saka na yi ƙarya ba, tun da baki da zuciya har namiji ya ce ki bar masa gida ki share guri ki zaune zan je na fa

ɗ

awa Hajiya Amina duk irin cin mutunchi da tijarar da ya ke miki ki ke zaune da shi, kuma zaki san idan zamana yana da a

mfani ko ba shi da shi, zaki gane baki da wayo yarinya ga ki ga Mijin nan ga kuma

ɗ

anyan jego" Baba Jumman ta fa

ɗ

a tana goge fuska.

Na zum

ɓ

uri baki ba tare da na sake ce mata komai na ta fice daga falon. Bin bayan ta na yi, se da ta fita ta bugu kofar

get

ɗ

in da ƙarfi kafin na ta

ɓ

e baki na koma cikin falon a fili ina cewa

"Haka kawai mata babu dangin iya babu na Baba zaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login