Showing 174001 words to 177000 words out of 287295 words

Chapter 59 - KURA A RUMBU COMPLETE

nuna alama

r hakan wannan tasa ya koma cikin mota ya zauna ya tura mata saƙo, jiran minti goma sha biyar yayi kafin ya sake kiran layin amma rashin sa'a ya ji shi a kashe. Ba yanda ya iya yaja mota ya tafi a zuwan gobe zai dawo.

A karo na babu adadi Zulaiha ta sak

e kiransa, guri ya samu ya gangare ya kashe motar kafin ya kirata dan tun da yamma da sukayi waya ya ce mata idan ya fito zaije amma ya manta dalilin hankalinsa da gaba

ɗ

aya ya tafi gurin Halima.

Kukan kissa ta fashe masa dashi bayan data amsa wayar nan

da nan kuwa hankalinsa ya tashi ya shiga rarrashinta, sai da yayi kamar zai yi yaya kafin tayi shiru ta shiga jero masa ƙorafin shikenan daga an

ɗ

aura musu aure yana ganin ta zama mallakinsa zai fara wulaƙanta ta dama ashe duk alƙawarin da ya mata a baya

ba gaskiya bane yanzu ne zai bayyana mata asalin halinsa. Ya ringa rantse rantse akan ba haka bane tun safe yana office da garga

ɗ

in da aka masa akan rashin zuwa aikin da bayayi.

"Amma na

ɗ

auka kace can Headquartern ku na Abuja aka mayar da kai meye kuma

ha

ɗ

in ka da nan da har zasu baka query?" Ta fa

ɗ

a, sai yayi shiru dan ya manta abinda ya gaya mata kenan ya koma Abuja da aiki data tambaye shi yawan zuwan da yakeyi. Sai ya ce

"Kin san wani aiki ne daban na samu a can

ɗ

in kawai bana fa

ɗ

a ne saboda ba n

a gomnati bane ba zanyi saurin sakin wannan aikin ba sai naga wancan

ɗ

in ya gama dai dai ta shiyasa kawai nake cewa headquarter aka mayar dani". Hira suka cigaba bayan ya bata uzurin ba zai samu zuwa yau

ɗ

in ba kamar yanda ya mata alƙawari da farko.

"Am

ma wlh banji da

ɗ

i ba na gama saka ran zan kwanta a jikinka na

ɗ

an yi bacci irin na jiya" ta fa

ɗ

a kai tsaye bayan da ta gama zagaye zagaye taga yana ta kaucew irin hirar da take so suyi. Shiru yayi kafin ya ce

"Nima na so haka amma na fa

ɗ

a miki uzuri na".

Shikenan ta

ɓ

allo hira, ta kuma sake goge masa hadda domin yau ya gane ashe jiya ba komai ya gani ba. Duk yanda ya ringa danne maganar a ransa sai da ya amayar ya ce mata

"Wai Zully ina kika koyi wa

ɗ

annan abubuwan?" Kuma wai sai a lokacin ne taji kunya

ta ce masa

"Gurin ƙanwar Umma Anty Sadiya tunda Baba ya tsayar da ranar

ɗ

aurin aurenmu ba na gaya maka na koma can gidan ba ita ce ta ringa koya mana".

Ji yayi maganar bata kama masa hankali ba amma kuma ta wani

ɓ

angaren ya

ɗ

an samu nutsuwa akan abund

a yake masa yawo a rai sai ya ce

"Tayi ƙoƙari amma a

ɗ

an lokacin nan Zullyn da na sani ko ido bata iya ha

ɗ

awa dani tayi wannan gogewar lallai wannan Antyn tamu ba ƙaramar Malama bace"

"To kuma kunyar me zanji yanzu bayan na rigada na zama mallakinka k

o so kake na tsaya wasa Maman Al'amin ta ƙwace mun kai?" Ta bashi amsa, a ransa ya ayyana

"Halima baiwar Allah ita kam bata wannan rashin kunyar a sunnance take tata". A fili kuma sai ya ce

"Kin san kuwa gwana ce a wannan fannin"

"Ai kuwa duk ƙwarew

ar ta zan nuna maka na fita" ta fa

ɗ

a ya ce

"Anya kuwa?"

"Idan kana musu yanzu kazo ka

ɗ

auke ni mu tafi gida wlh yau sai na goge maka hadda dama ni a matse nake".

Zuwa yanzu kam ko yaƙi Allah dole tsoron Zulaihan ya

ɗ

arsu a ransa, budurqa fa wacce bata

ta

ɓ

a sanin namiji ba take irin wannan sakin zancen, tattara nutsuwar sa yayi guri guda zuciyarsa na bugawa ya ce

"Kina da hankali kuwa Zulaiha? Duk ina kunyarki da na sanki da ita a da zaki iya ringa furta wa

ɗ

annan maganganun? Ko da an

ɗ

aura mana aure ha

r yanzu ba banbancin dake tsakanin da da yanzu fa ka

ɗ

an ne domin bamu rigada mun zama

ɗ

aya ba ya kamata ace har yanzu kina jin nauyina"

"Yanzu saboda ina ƙoƙarin faranta maka shine har kake nema ka fa

ɗ

a mun magana? A fakaice ba so kake kace mun yar iska

ko mara tarbiyya kenan" ta fa

ɗ

a cikin hasalar da bai ta

ɓ

a saninta da ita ba, dake shima zuciyar sa a kusa take sai ya ce

"Ki bawa kanki amsa ya kamata budurwar da bata ta

ɓ

a sanin namiji ba ta ringa irin wannan abinda kikeyi?"

"Zargina kake yi Bilal?

Ƙazafin zina kake so kayi mun?" Ta fa

ɗ

a cikin

ɗ

aga murya kamar yana gabanta, sai kawai ya zare wayar daga kunennsa ya katse kiran ha

ɗ

i da kasheta gaba

ɗ

aya dan ya lura idan ya biye mata zasu iya yin

ɓ

atacciya. Mamaki ya rufeshi yanda lokaci

ɗ

aya halayen d

a bai santa da su ba suke fitowa

ɗ

aya bayan

ɗ

aya. Zulaihar da ko ha

ɗ

a ido batayi dashi ko zai yi me kuwa kanta na ƙasa duk maganar da zasuyi har gara gara a waya ta kan

ɗ

an sake dashi suyi hira har ta fa

ɗ

a masa kalaman soyayya amma ko tsareta yayi a zahiri

yace ta maimaita sai dai tayi kamar zata saka masa kuka ya haƙura ya ƙyaleta ladabi da biyya kuwa kamar zata kwanta masa idan ya fa

ɗ

a mata magana ba zata tsallake ba yanda take gudun

ɓ

acin ransa kuwa wani lokacin har ji yakeyi kamar abun yayi yawa ya zama

kamar tsoronsa takeji amma yau ita ce ta kama sunan sa katsal abinda bata ta

ɓ

a yi ba tana

ɗ

aga masa murya kamar zata rufeshi da duka?

"Gaskiya akwai matsala" ya furta a fili kafin ya tayar da mota ya nufi gidan Hajja.

[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A

RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*

*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*

*Wattpad @MaryamahMrsAm*

*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini

na ba*

*Ku

ɗ

in karatu yana wakiltar mutum

ɗ

aya ne, kiji tsoron Allah karki

ɗ

auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*

*KURA A RUMBU littafin ku

ɗ

i ne, a biya naira 800, biya a asusun*

*1840175439*

*Access bank*

*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya

a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 40*

Tunda yaga babur

ɗ

in Kawu Sani a ƙofar gidan gabansa ya shiga fa

ɗ

uwa domin ya san abinda akw

ɓ

oyewa ya rigada ya bayyana. Sai dai kuma shima yana buƙatar hakan ko dan ya samu a wuce gurin Zulaiha ta tare amma kum

a ya san da wahala su kwasheta da da

ɗ

i da Hajja. Tun daga tsakar gida yake jiyo maganganun Hajjan tamkar zata ari baki tsabar masifar da take zazzagawa, yana

ɗ

aga labule suka ha

ɗ

a ido kallon data jefa masa sai da yaji yan cikin sa sun juya, ta ce

"Yawwa

gara da kazo, dama Bilal idan har ni na haifeka ba canza mun kai akayi a Asibiti ba, bana buƙatar jin kowacce magana daga bakinka a yanzu har sai bayan ka rubuta takardar saki yanzu an kaiwa waccen kaskar da kuka munafurceni aka

ɗ

aura maka aure da ita." S

ai kuma ta fashe da kuka tana cewa

"Allah ya isa tsakanina da kai Sani dan nasan wannan abun shirinka ne Bilal ba zai ta

ɓ

a mun haka ba, dama shi

ɗ

an uba duk in da yake ai ba zai ta

ɓ

a sonka tsakani da Allah ba sai in yana da wata manufa, to ka sani haƙƙi

n marigayi ba zai barka ba wlh tallahi domin ya ƙaunace ka tsakani da Allah in ba an fa

ɗ

a ba ma waye zai ce ba ciki

ɗ

aya kuka fito dashi ba amma shine saboda zuciyarka cike take da mugun abu ka rasa kuma akan wa zaka juye shi sai akan

ɗ

an da yafi so tir da

kai Sani" ta sake rushewa da kuka harda fyace hanci.

Daƙyar ya ƙarasa cikin ya samu guri kusa da Kawu Sani da ya zabga tagumi yana kallon Hajja, murya a dace kamar wanda ya tashi daga ciwo ya ce

"Kiyi haƙuri Hajja amma babul laifin Kawu Sani a ciki

n maganar nan domin ni na saka shi ya nema mun aure ba wai gaban kansa yayi ba". Kamar an yi ruwan sama an

ɗ

auke kuwa ta dakata da kukan da takeyi ta kafe shi da ido alamun sauraron ƙarin bayani, ƙasa yayi da kai kafin ya cigaba da cewa

"Hajja kin fi ko

wa sanin irin son da nake yiwa Zulaiha amma a haka na haƙura da ita saboda kin nuna bakya so a wancan lokacin, Hajja kin san yarinyar nan bakay buƙatar na sake gaya miki komai akanta aurenta tamkar jahadi ne zanyi saboda na taimaketa kuma idan kika duba ts

ahon lokacin da muka

ɗ

auka tare tana jira na tun banyi aure ba har kuma nayi auren bata haƙura ba kuma yanzu nace na zan aureta ba ai zai zama kamar na yaudareta ne kuma dama ai Hajja munyi yarjejeniya dake na fa

ɗ

a miki duk idan na samu dama a gaba zan aur

eta kuma baki ce ba haka ba".

Kukan da ya fi na farko Hajjan ta sake fashewa dashi shi kuma ya sake laƙwashe murya ya ce

"Hajja kin san bana miki musu duk abinda kika ce ko bana so ina yinsa, dan Allah zan roƙe ki ki mun wannan alfarmar ki barni da Zu

laiha, ina sonta nayi miki alƙawari ko me kike so zanyi amma kiyi haƙuri dan Allah kada ki rabani da Zulaiha" ya ƙarasa yana zamowa gabanta ya dafa guiwarta hawayen da yake kokawa dasu suka gangaro akan kuncinsa.

Cikin kuka Hajjan ta shiga cewa

"Yanzu

ita wannan yarinyar ya zakayi da ita?"

"Kada ki damu kanki da batun Jalilah Hajja"

"Ba maganar karna damu ba, wlh a kanta zan iya

ɓ

ata maka rai Bilal wlh" ta katseshi, sakw marairaicewa yayi ya ruƙo hannunta ya ce

"Haba Hajja yanzu har kin fi son wata

bare a kaina kenan?"

"Kai da ka nuna mun iyakata Bilal da raina ban mutu ba ka zagaya ka

ɗ

aura aure har kana da bakin cewa na fifita wani a kanka? Ai ko da bana so har idan dagaske kana martabani a matsayin uwarka ya kamata ka gaya mun, amma shikenan, d

ama gashinan ƙanin ubanka ya fara cewa ni mai son zuciya ce na saka ka auro waccen yarinyar ga yanda ake ciki yanzu ina so na sake turaka ka auro wata ba'a son ranka ba shiyasa ka zagaya kayi aure baka gaya mun ba, shikenan kaje ba zan hanaka ba amma ba'a

son raina ba" ta miƙe tana kuka wiwiwi ta wuce

ɗ

aki.

Gaba

ɗ

aya ji yayi kansa ya kulle dan ko maganar da Kawu Sani ya shiga yi masa sauraronsa kawai yake amma baya gane komai cikin abinda yake fa

ɗ

a, ƙarshe kawai ya miƙe ya fice daga falon. Auren da take

so ta saka albarka a ciki ma ya ya ƙare balle wannan da tace bata so?

Kwanakin da suka biyo baya gaba

ɗ

aya Hajja ta

ɗ

auke masa wuta ko gidan yaje daga sallama bata sake ce masa komai duk kuma magiyar da zaiyi da bata haƙuri ba zata tanka masa ba abin

sai ya zame masa goma da ashirin dan yanda ya tsammaci lamarin Halima zai zo masa da sauƙi sai kuma abun ya sha banban. Washe garin daya sake komawa da yamma haka nan ya ƙara ci kiranta a waya amma bata amsa ba daga ƙarshe ma ta kashe layin gaba

ɗ

aya, ya t

ura mata text duka babu amsa haka ya haƙura ya tafi ga ta

ɓ

angaren Zulaihan itama ba wani sauƙi, fushi ta

ɗ

auka dashi tun akan zancen waccen daren shi ya ƙwafe yana jira ta kira ta bashi haƙuri irin yanda ya saba da Halima amma har aka kwana aka kusan wuni

shiru bai ji ta ba.

Haka nan sonta dake azalzalar zuciyarsa ya tilasta masa kiranta kuma ko kafin su shirya sai da ta masa tatas ta amayar da duk abinda yake cikin ta kafin ta kammala da garga

ɗ

i akan karya sake mata irin haka wai kuma abin takaici ba y

anda ya iya ya bita da ban haƙuri shikenan suka shirya har a daren yaje gidansu kuma kamar yanda tace tunda ba'a masa gwaninta ta daina nuna masa kulawar hakan ce ta faru dan ƙin yarda ma tayi su zauna a mota sai a soro sukayi zancen.

HALIMA

Ba ƙaramin

ƙarfin hali nayi gurin danne zuciyata naƙi amsa Bilal ba, so nakeyi na tabbatar da matsayina a gurin sa, ko da ya tafi zuwansa na farko na ringa ji kamar na kirawo shi na ce ya dawo amma da naga har dare ya tsala safiya tayi bai sake kirana ko tura mun sa

saƙo ba sai ba raina kaina na kuma fara tausayin kaina akan igiyar zaton dana ƙulla na cewar Bilal

ɗ

in dagaske yana ta tawa mutane kawai suke ganin ba haka ba. Na ji sanyi har raina daya sake dawowa sai dai kuma ban biyewa zuciyar da ta ringa azalzata aka

n na kar

ɓ

i uzurin sa ba. Na tambayi kaina wane uzuri zan masa ne ma tunda shi dai bai furta ko nunawa a aikace cewa ya yarda yayi mun laifi ya kuma nemi da nayi haƙuri ba maimakon haka a kalaman da yake turo mun sunfi kama da wanda yake jaddada mun cewar y

a san ba zan iya rayuwa babu shi ba dan haka dole nayi haƙuri na koma masa kuma ko kusa bai ma nemi cewar na bashi dama mu zauna ko zai wanke kansa ba aa kawai cewa yakeyi nazo mu koma gida tabbacin ko a jikinsa ma shi ya manta da duk abinda ya faru.

B

a tareda kowa ya bani shawara ba na yankewa kaina shawarar

ɗ

ibar masa lokaci, zanyi ta jansa in ga iya gudun ruwansa. Shin zai fahimci kuskuren sa ya biyo ta sigar daya kamata ko kuwa zai cigaba da yi mun kallon ba zan iya rayuwa babu shi bane?

Na kwan

aki hu

ɗ

uya jera kullum yaje gidanmu daga zarar kuma yayi mun kira

ɗ

aya ba zan bari yayi na biyu ba zan kashe wayar. Na zuba ido naga gudun ruwansa tunda har aka kwana hu

ɗ

un dai salo

ɗ

aya yake maimaitawa na kirana ha

ɗ

i da tura mun text yana tunasar dani yan

da yake a raina ba wai yanda ni nake a nasa ran ba in dubi wannan nazo mu koma gida. Nasan Mama ta san yana zuwa amma ko da wasa

ɓ

ata ce mun komai ba nima kuma ban ce mata ba a haka muka kwana hu

ɗ

un a yini na biyar shiru tun Magriba nake tsammacin naga kir

ansa amma har sha biyun dare ta gota shiru babu shi babu labarinsa tils na cire rai sai kuma damuwa da ƙuncin da ban tsammata ba suka lullu

ɓ

e ni.

Washe gari haka na tashi sam babu walwala ba fara'a, komai ma baya mun da

ɗ

i dan ko abinci

ɗ

an ka

ɗ

an na tsak

ura na ture saboda yanda nakejin komai yana mun

ɗ

aci a bakina. Bini bini zan

ɗ

auki waya in duba ko zan ga saƙon sa ko makamancin haka amma shiru har azahar tayi, bayan na idar da sallah ina zaune kan sallaya ina lazumi wayata ta shiga ƙara, tun da gari ya

waye ko message bai shigo mun ba ina jin ƙarar wayar kuwa na zabura zuciyata tana raya mun Bilal ne dai dai lokacin kuma Mama ta shigo

ɗ

akin. Wayar na duba ganin baƙuwar number ya saka zumu

ɗ

i na raguwa dukda haka bam cire tsammanin shi bane sai bayan dana

kai wayar kunnena bayan na amsa naji murya daban ba tashi ba.

Zare wayar nayi na kashe ba tareda na amsa sallamar da wanda ya kira yayi ba, na saci kallon Mama jin tana cewa

"Iska dai tana wahalar da mai kayan kara" kafin tayi ƙaramin tsaki ta nufi ƙof

a tana cewa

"Ga Mudassir can a falo yana jiranki". Jiki ba ƙwari na biyo bayanta, bayan mun gaisa da Uncle Mudassir ya tambayeni jiki na ya ce

"Na

ɗ

auka kin kar

ɓ

o posting letter ki Halima tuntuni ashe baki je ba". Ɗan ya mutsa fuska nayi na ce

"Uncle

ba fa ni da lafiya, kuma ni ban ma san an fito daga camp

ɗ

in ba". Daƙuwa yayi mun yana cewa

"Dan gidanku ni kike gayawa baki da lafiya tun yaushe kika samu sauƙi yau kwananki nawa da aka sallamoki daga Asibiti? Naga alamar har yanzu baki san inda yake mik

i ciwo ba Halima, satinki nawa a gidan nan? Ke ko ji bakiyi zaman ya isheki ba kina buƙatar samun abun da zai

ɗ

ebe miki kewa ko kuwa dai saboda kanki aka fara mutuwar aure shikenan sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login