Showing 66001 words to 69000 words out of 287295 words
me ciki ba so kike ki saka abin da yake cikin ki a damuwa shima? Bana son sakarci, ya kamata dai yanzu ace kin girma tunda nan da
ɗ
an lokaci uwa kike shirin zama kina wa yar rashin lafiya kuka yanzu idan ranar haihu
wa tazo kuma se yaya kenan?" Ta fa
ɗ
a. Se na tsagaita da kukan taci gaba da cewa
"Yanzu da su Amir suka dawo yace mun baki da lafiya, toh kun je asibiti dai ko?"
"Eh mun je ba wani abu bane dama marata ce kawai take ciwo kuma nasha magani ta rage" na ba
ta amsa, se ta
ɗ
an yi shiru kamar bata yarda ba kafin tace
"Shikenan Allah ya ƙara lafiya. Ki ringa kula da kanki duk abin da kika san ze jigata ki kar kiyi, na ma yiwa Mama magana tuntuni ko za'a sama miki me aiki tace a bari tunda baki nema ba amma ya k
amata gaskiya saboda ba laifi aikin gidan naki da
ɗ
an yawa kuma yanzu hutu kike buƙata musamman tunda cikin yazo miki da ciwon mara".
"Aa fa yau ne kawai shima nasan saboda aikin da nayi jiya ne amma ba wani abu nake yi da yawa ba duk su shara da moppin
g shi yakeyi da kansa" na fa
ɗ
a dan na ta
ɓ
a yiwa Bilal zancen yar aiki yace baya so, yanzu idan ta kawo ta ya koreta sabuwar gaba ce zata ƙullu tsakanin su. Shiru ta sake yi kafin tace
"Shikenan, Allah y sauwaƙe ya bata lafiya me amfani" daga haka mukayi s
allama. Jin an fara kiran sallah yasa na koma
ɗ
aki nayi, se da na idar da isha'i na sake fitowa har sannan kuma Bilal be dawo ba. Ina tsaka da cin abincin dana saka ka
ɗ
an naji ana buga get. Bilal ya fita da key dan haka nasan bashi bane, nayi mamakin ganin
Anty Labiba da Uncle Saleh bayan dana bu
ɗ
e ƙofar, ban san sanda na rungume ta ina dariya ba. Rabon
ta da gidan tun ranar da aka kawo mun gara, Uncle Saleh be shiga ba a wajen muka gaisa yace ze je ya dawo muka shiga tare da Anty. Na rasa me ma zan bata, h
ar ga Allah naji da
ɗ
in zuwan ta over ma. Ganin ina ta kwaso ruwa da lemo na kinkimo kular abinci yasa ta dakatar dani tana cewa
"Ke bafa zama zanyi ba. Nan bayan ku zamu je gaisuwa gidan wani abokin sa maman sa ta rasu a UK suke to sunyi waya yace yazo
Kano amma gobe ze wuce Abuja shine muka taho yanzu fa se da muka kuje kuma ashe shi ka
ɗ
ai ne yazo banda matar sa, naga zasu
ɓ
ata lokaci da hira shine fa nace ya kawo ni nan na dubaki kafin su gama mu wuce, su Halima matar Bilal, irin wannan mulmul da kika
yi lallai Bilal ya iya kiwo" ta ƙarasa tana kallo na. Na rufe fuska cikin jin kunya ina cewa
"Kai Anty, kamar kin shekara baki ganni ba"
"A shekarar ka
ɗ
an ne babu ai, ha
ɗ
uwa tayi wuya se dai mu gamu a hanya nan kuma ai ba wani ganin ki nakeyi sosai ba
kamar yanzu ko?" Ta fa
ɗ
a, nasan magana ta gaya mun dan haka nayi murmushi kawai na shiga tambayar ta su Inayah.
"Dama suna gidan Mama
ɗ
azu shine su Amirah basu taho da su ba?" Na fa
ɗ
a, se tace
"Aa, se gobe zamu je. Amir ne kawai yaje su je kallon hawa t
are da su Mu'azzam". Hira muka shiga yi gwanin da
ɗ
i, har tara da rabi sannan Uncle Saleh ya kirata yace gashi nan ya taho. Se sannan ta tambaye ni Bilal, tambayar da nake ta addu'ar kar Allah ya bu
ɗ
i bakinta ta mun dan ban san me zan ce mata ba sanin tun k
afin muyi aure da Bilal duk wanda ya sanshi ze bada shaidar baya yawon dare. Duk in da akayi sallar isha'i ya shiga gida in dai ba guri na ze je ba.
Ce mata nayi yana can gidan su ai be jima da fita ba suka zo, kallon da ta mun yasa na fahimci bata kama
zancen ba. Ta ƙare mun kallo tace
"Wannan kayan ma tun na kwalliyar safe ne da kikayi baki sake wasu ba". Zan kwaso rantsuwa ta dakatar dani tace
"Idan kika zauna shashanci kanki zakiwa sagegeduwa. Ba yanzu zaki takaicin barin sa ya koyi yawon dare ba
se nan gaba dan haka tun lokaci be ƙure miki ba ki gyara. Duk irin hirar da zeje yayi a wajen ki tanade ta ki ringa yi masa a gida ya fiye miki alkhairi idan ba haka ba ke kika sani kina zaune can wasu zasu ringa cusa masa wasu ra'ayoyi na banza a lalata m
iki miji".
Tunani maganar ta ta jefa ni, anya babu saka hannun abokai cikin baƙin halayen Bilal da nake cin karo dasu? Waya sani kam ko a yawon da yake tafiya ake yo masa wasu karatu na banza suna gurbata masa tunani dan dai ni shaida ce ba haka Bilal
ɗ
in dana sani yake ba tabbas. Bu
ɗ
e ƙofar da akayi ya dawo dani daga tunanin da na tafi. Muka ha
ɗ
a ido da Bilal ya galla mun harara ba tare da yayi ko da sallama ba ya wuce kitchen yana sakin ƙaramin tsaki. Se da naji ina ma da damar da ƙasa zata tsage na s
hige ciki na
ɓ
uya ko kuma ace abin da ya farun yanzu mafarki ne zan tashi naga zuwan Anty Labiba be faru ba. Kamar me ciwon wuya daƙyar na waiga na kalli Anty Labiba dake danna wayarta se ka rantse bata ji shigowar Bilal
ɗ
in ba. Nayi ƙasa da kai kamar muna
fuka ina jan yatsun hannu na, daga kitchen
ɗ
in ya ƙwalo mun kira. Ƙafafu na sun yi sanyin da bazan iya miƙewa ba, sake kiran yayi se lokacin Anty Labiba ta
ɗ
aga kai ta kalle ni tace
"Ba kiran ki yake yi ba?"
Ina zaton baƙuwar muryar da yaji se gashi y
a fito kamar an jefo shi, yayi turus a bakin ƙofa yana raba ido kafin yayi ƙasa da kai yana shafa ƙeya kamar mara gaskiya lokaci
ɗ
aya ya lalubo murmushi ya
ɗ
ora a fuskar sa ya nufo in da muke yana cewa
"Kune a gidan namu yau Anty"
"Mun same mu lafiya?
Ya sallah?" Ta fa
ɗ
a tana miƙewa saboda wayar ta data
ɗ
auki ƙarar shigowar kira. Bata amsa gaisuwar da ya shiga yi mata ba ta nufi ƙofa tana ce mun
"Allah ya ƙara sauƙi Halima na wuce se da safe" ta fice daga falon. Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki ha
ka na bi bayan ta. Yanzu Allah ka
ɗ
ai yasan tunanin da zata yi kuma. Dubu goma Uncle Saleh ya bani barka da sallah, Anty Labiba dai tunda ta zauna a motar ko kallo na bata sake yi ba yaja suka tafi.
A kan kujera na tarar da Bilal ya dafe kai da hannu bi
yu yana jin motsi na ya miƙe fuska ba yabo ba fallasa yana kallo na yace
"Me yasa baki kira ni kin ce mun ta zo ba?"
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA
MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga
ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a t
ura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 15*
Ban tanka masa ba na shiga tattare kayan dake ajiye dana gama kuma na wuce
ɗ
akina na kwanta, nayi mamakin ganin ya biyo ni, nayi lamo a kan gado ina sauraren sa har ya gama uzure uzurensa na bacci k
afin ya kwanta a baya na tare da jana jikin sa yana cewa
"Nasan ba bacci kike yi ba juyo na baki barka da sallah" nayi masa banza duk yanda yake ya mutsani da son se na biye masa na dake daya gaji ya sake ni ina jin sa yana tsaki har baccin gaske ya
ɗ
auke
ni. Washe gari nayi zaton ze cigaba da fushin amma naga akasin haka dan tun asuba daya tashi be zauna ba seda ya share gidan tas yayi mopping ya wanke ban
ɗ
akuna harda na tsakar gida.
Ina kwance a falo kan carpet in da nayi sallah ya shigo bayan ya gam
a gyara tsakar gidan, zazza
ɓ
i ne a jiki na sosai, na lullu
ɓ
e har kaina ga iskar hadari dake ka
ɗ
awa tasa har karkarwar sanyi nake yi. Sama sama nake jin sa yana kiran suna na, jin ban amsa ba yasa ya ƙaraso in da nake ya duƙa yana kirana tare da
ɗ
an bubbuga
gefen pillow da nake kwance.
"Dame zaki karya?" Ya tambaye ni, nayi shiru dan baki na yayi mun nauyi kuma kusancin da mukayi ƙamshin turaren sa dake bugun hanci na duk se ya sake hautsinamun kai baki na har ya fara tara yawu alamar amai na son taso mun.
Miƙewa yayi yana cewa
"Shikenan ai, tun jiya nake binki kina mun wulaƙanci. Fitina kike nema ni kuma ba zakiyi da ni ba" ya shige kitchen. Se maganar sa ta ma bani dariya, wai yana bina ina masa wulaƙanci Bilal kenan me abin mamaki. Ƙarfe tara na farka
daga baccin da ban san sanda ya
ɗ
auke ni ba, zazza
ɓ
in ya saukar mun dan haka na miƙe ina kallon falon dake ta tashin ƙamshin turaren wuta da roomfreshener. Zancen gaskiya iya gyaran gidan Bilal ba duk mace ba. Haka nan idan ya bushi iska har canza jeren k
ujeru ya keyi. Se da nayi wanka nayi kwalliya cikin sababbin
ɗ
inkin sallar da nayi kafin na shiga kitchen neman abinci. Doya ya dafa da sauce
ɗ
in ƙwai. Dake akwai wuta se nayi microwaving na ha
ɗ
a baƙin shayi na dawo falo na zauna kan carpet na shiga karyaw
a. Bilal ya shigo falon da sallama, kan kujerar dake kallo na ya zauna yana murmushi yace
"Ranki ya da
ɗ
e an tashi kenan". Kallon sa nayi ba yabo ba fallasa na gaishe shi. Surutu ya fara mun ina bin sa da eh da aa har na ƙare cin abincin na yunƙura zan m
aida kwanon kitchen ya kar
ɓ
a se gashi ya dawo harda ruwa me sanyi ya ajiye mun.
"Yanzu Hajja ta kira ni kin ji kuma wai taron suna suke so suyi, na zata tun da aka wuce satin ga kuma daga ita har yaron ba wata lafiya ta ishe su ba ai se su haƙura ko?" Ya
fa
ɗ
a yana kallo na. Na gyara kwanciya ta nace
"Eh, dama Fadilan tace mun zatayi taron suna ai, kuma haihuwar fari ai ya kamata tayi dama kuma yawanci in dai C's ne se sati biyu akeyin taro ba ranar kwana bakwai ba"
"Amma dai ƙarawa mutane
ɗ
awainiya n
e, baki ga jiya nayi dare ba? Wai fa
ɗ
an iskan mijin nan nata se jiya sannan suka zo da yayyen sa biyu wai bada haƙuri suka kawo wasu shegun kayan su a leda wai na barka. Wlh badan Hajja tace nayi shiru ba niyya nayi nace su tafi da tsiyar su tunda da basu
kawo ba
ɗ
in ma babu abin da aka fasa yi mata da
ɗ
an nasu har suna cewa a musu lissafin abin da aka kashe na asibiti zasu biya kamar gaske" ya sake fa
ɗ
a. Tun da ya fara maganar na zuba masa ido ina kallon sa, so nake nace masa kawo kaya a leda ai ba kansu
aka fara ba ƙarewar kayan barka naga har lefe sun kai a leda me yasa dan an musu yanzu abin ze yi musu zafi amma na kasa fa
ɗ
a saboda nasan ƙarshe ze iya juyawa maganar manufa yace na masa gori ko wani abu se kawai na datse zancen da cewa
"Allah ya rufa a
siri kawai".
"Wallahi kawai in na tuna zumunchin da Fadila ta mun shiyasa nake tsaye akan sabgoginta. Yarinyar nan bata ji ƙyashin bani rabon ta na gado nayi sabgogin karatu ba shiyasa ko miliyan nawa zan samu a rayuwa ta nima ba zan ji takaicin kashe
mata ba dan ta mun abinda kowa be mun ba cikin yan uwana" Bilal ya sake fa
ɗ
a, a raina na raya
"Ashe dai kasan me maka" yawan zancen Fadila da irin yanda ya
ɗ
aukaki halaccin da ta masa yasa a kullum nake kyautata masa zaton baze ta
ɓ
a wofantar dani ko ya ma
nta tawa sadaukarwar a rayuwar sa ba kamar yanda da yawa suke tunanin ze bani kunya.
"Kinga a duniya bayan Hajja, ke da Fadila kune mata biyu da suke da ƙima da daraja a ido na. Har gaban abada ba zan manta hallacin ku ba a kullum kuma ina roƙon Allah
daya hore mun abin da zan kamanta muku dan nasan bazan biya ku ba" ya sake fa
ɗ
a yana matso ni jikin sa. Kaina ya fasu, ban san sanda na fara murmushi ba kamar gaula. Ban ta
ɓ
a wa Bilal wani abu da fatan ya biya ni wata rana ba. Komai ina masa ne saboda son
sa da nakeyi tsakani da Allah amma bazanyi ƙarya ba ina jin matuƙar da
ɗ
i a duk sanda ya nuna mun jin da
ɗ
in sa kan wani abu da nake masa irin wannan tunasarwar kuma tana sakawa na cire kokonton dake damun zuciya ta na Bilal ya canza daga bigiren dana san sh
i saboda sababbin
ɗ
abi'un da yake gwada mun a yanzu.
Tuni na watsar da ƙudurin motsa kambu na nuna masa
ɓ
acin raina akan rikicin gangan
ɗ
in da yake mun na biye masa muka shiga filin baje kolin ƙauna. Bayan la'asar ina kwance a falo zazza
ɓ
i na namen daw
o mun, Bilal ya shigo daga masallaci gani na a kwance yace
"Ya haka kuma ke da nace ki shirya da an idar da sallah zamu tafi?"
Na yunƙura na zauna ina dafe kaina dake sara mun nace
"Gaskiya ba yau ba, jiya fa cewa Mama nayi bani da lafiya shiyasa muk
a fasa zuwa kaga ma ƙaryar da nayi ciwon gaske na neman kwantar dani". Zama yayi a gefe na ya
ɗ
ora hannun sa a wuya na yace
"Jikin ki yayi zafi, dubaki Anty Labiba tazo yi jiya kenan? Dama nayi mamakin ganin ta haka kawai ita da tun da mukayi aure bata ta
ɓ
a zuwa ba"
"Allah ne be kawo dalilin zuwan bane ba" na fa
ɗ
a ina gyara zamana. Ya
ɗ
an
ɓ
ata fuska yace
"Ba wani nan nine bata so kika aura ba shiyasa ba zata zo gida na ba" se nayi saurin katse shi da cewa
"Kaima da kake hanani zuwa gidan ta saboda bak
a son ta ne kenan?"
Ya mun kallo me kama da harara kafin yace
"Ya zanyi nace bana son ƙanwar mahaifiyar ki? Kawai bana jin da
ɗ
in yanda bata mun kara ƙarara take nuna bata ra'ayin kasancewar mu tare tun ina neman auren ki. Sannan nasan har yanzu bata ya
da makamanta ba, zuga ki zata cigaba dayi idan kika je gidan".
"Lallai Bilal, ita kuma Anty Labiba saboda bata da abinyi se ta zauna tana zugani. To ta zugani na kashe aure na ko me? Ribar me zata ci?"
"Ita kuwa zata ci riba tun da wannan solo
ɓ
iyon ƙan
in mijin nata na sonki kinga burin ta se ya cika ki aure shi" ya fa
ɗ
a yana wani zare ido. Kallon sa kawai nayi na koma na kwanta dan maganar ta fara hawar mun kai. Beyi shiru ba yaci gaba da cewa
"Yanzu Allah ka
ɗ
ai yasan me zata je ta fa
ɗ
a jiya, tun da n
a gaishe ta naga bata amsa ba nasan ta ƙudurce wani abun ne a ranta". Jin na masa banza ban tanka yasa ya miƙe yana cewa
"Ni bari na tafi toh dan na kira Nasir nace ya shirya ze raka ni mu gaida su Mama zuwa gobe idan kinga zaki iya daga gidan sunan se k
ije".
Ban amsa ba na da naji shiru ma na zata ya fita duk da banji motsin bu
ɗ
e ƙofa ba,
"Halims" ya kira ni, na juya ba tare da na amsa ba. Irin kallon daya yaudare ni dashi nayi kaca kaca a ƙaunar sa ya watso mun kafin ya tsugunna gaba na ya ruƙo han
nu na yace
"In nemi wata alfarma mana"
"Ta me?" Na fa
ɗ
a a ƙasan maƙoshi saboda kallon da yake mun duk yasa naji wani iri se yace
"Kin san rigimar Hajja, wai dubu hamsin take nema a hannu na daga yanzu zuwa dare ni kuma wlh account
ɗ
ina kaf babu dubu as
hirin ma balle ashirin. Gurin Nasir ka
ɗ
ai nake iya zuwa rancen ku
ɗ
i shima kuma cikin buƙatar su yake. Nace mata bani da