Showing 138001 words to 141000 words out of 287295 words
Ai sai yanda kace ayi. Soyawa za'ay
i da ƙwai ko sauce za'ayi mata?"
"Ki soya ki dama kunun gya
ɗ
a ga gasara nan a ciki" ya fa
ɗ
a. Kamar na ce masa gya
ɗ
ar bata da yawa ta kuma ta Al'amin ce amma dai nayi shiru kawai na
ɗ
auki tukunya na rage doyar kamar yanda ya ce yana tsaye. Tare suka fit
a da Fadila bayan na gama ha
ɗ
a abin karyawar. Na fashe da kuka ina kallon doya ƙwara ukun da suka bar mun a matsayin rabona. Ganin ina kukan ya saka Sharifa ma ta saka kuka dole na rarrashi kaina dan tayi shiru.
Kafin a sha biyu na kammala abincin rana
na zuba na asibiti a zatona zai dawo ya
ɗ
auka ko zai turo amma har aka fara shiga masallaci bai dawo ba na kira wayar sa har sau biyu kuma bai amsa ba sai kawai na shirya na tafi. Gidan Mama na fara biyawa na ajiye Sharifa, dama shinkafa da wake da mai da
yaji na dafa ganin sun gama abincin rana na canza fulasai na zuba miya a maimaikon Mai na ha
ɗ
a komai. Mama ce ta ce na jira Abba ya dawo daga masallaci sai muje tare da ita ta duba Hajjan, sai uku da wani abu Abban ya dawo sannan muka tafi. Muna shiga asib
itin zuciyata ta fara bugawa, na san da wahala idan Bilal bai yi fushi ba ko da yake dole ma yayi fushi har ƙarfe uku da wani abu amma ba'a kawo musu abincin rana.
Ina ga ganin Mama ya saka kai tsaye aka bar mu muka shiga sai dai kuma ban gansu a gadon
jiyan ba. Wata Nurse da jiyan naga ta zo ta duba jinin da aka saka mata na tambaya tace sun koma Retainer ship. Ba yabo babu fallasa suka kar
ɓ
e mu, ganin kwanukan abinci yasa hankali na ya kwanta tunda dai basu zauna da yunwa ba. Mama bata jima ba ta musu
sallama ta tafi bayan ta ajiye wa Hajja dubu ashirin ku
ɗ
in dubiya. Har ga Allah banji da
ɗ
in yanda ko a fuska basu nuna jin da
ɗ
i ba balle su gode mata. Tare muka fita na rakata mota muka ci karo da Anty Amina wadda da alama itama zuwan ta kenan suka gaisa
muka wuce.
"Amma dai ki dawo da wuri saboda waccen rigimammiyar da kika baro karta ishe mu da kukan ta na rashin dalili" Mama ta fa
ɗ
a bayan da ta shiga mota. Ina tsaye har suka tafi kafin na koma. A
ɗ
akin na tarar da Bilal na tabbatar kuma ya gammu tar
e da Mama tunda yanzu ya dawo amma bai tsaya ya gaishe ta ba ya wuce ciki abunsa. Na samu gefe na zauna dan
ɗ
akin yana da girma akwai kuma wadatar gurin zama, bai ce mun ƙala ba nima ban ce masa ba suna ta hirar su har da Hajjan kace gidan biki ne na wai A
sibiti ba. Sai da aka kira La'asar ya fita, nima fita nayi na tafi in da naga an shimfi
ɗ
a kafet nayi sallah ta acan. Ina gurin a zaune na hango Bilal yana tahowa da wasu mata biyu a bayan sa sai Namiji da kaya riƙi riƙi.
Da farko ban zata tare suke da
matan ba tunda mutane nata shige da fice a gurin sai da naga sun shiga gurin da
ɗ
akuna suke. Mayar da hankali nayi kan wayata da nake dubawa amma haka kawai zuciyata ta ringa ka
ɗ
aita mun son sanin su waye baƙin. Ɗaya da facemask a fuskarta dan haka ban gan
e ta ba wacce fuskarta take a bu
ɗ
e kuma ban santa ba. Ƙoƙarin cire tunanin su nayi a raina amma na kasa, dole na tashi na koma
ɗ
akin ina tafe zuciyata na bugun da ban san dalilin sa ba.
Ina tura ƙofar ido na ya sauka cikin n mai facemask
ɗ
in. Gaba na y
a yanke ya fa
ɗ
i nayi saurin yin a'uziyya a zuciya ta. Ta zubo mun idanuwan ta masu girma haka nima na ringa kallonta dukda yanda kallon nata yake sake assasa gudun zuciya ta. Farace tas farin gaske kuma ba na bleaching ba, tana da kyau wanda ko mai hassada
r mutum ba zai ƙarya ta hakan ba a shekaru kuma zata iya haura talatin dukda jikinta bai nuna shekarun ba amma aka ce ido ba mudu ba amma ya san ƙima.
A hankali nayi sallama dukkan yan
ɗ
akin suka zubo mun ido sai lokacin ita kuma ta
ɗ
auke nata idon dag
a kallo na. Na wuce gurin da na tashi na zauna ba tareda na kalli kowa a cikin su ba. Muryar Hajja na ji tana cewa
"Halima baki ga baƙi a
ɗ
akin bane?" Sai lokacin na
ɗ
aga kai muka sake ha
ɗ
a ido da ita ta sakar mun murmushin da ya sake fa
ɗ
ar mun da gaba ka
fin cikin muryar ta da naji kamar na ta
ɓ
a jin ta a wani guri ta ce
"Halima ce?"
"Ita ce" Bilal dake tsaye kusa da ƙafafun Hajja ya fa
ɗ
a yana kallo na. Na mayar da kaina ƙasa kafin na ce
"Ina wunin ku?"
Ban san sanda ta taso ba ƙamshin turaren da
na ji dab da hanci na ya saka na
ɗ
ago kai ta kuma sakar mun murmushi ha
ɗ
i da miƙo mun hannun ta ta sigar musabaha tana cewa
"Sannu Maman Al'amin". Murmushi na ƙirƙira na miƙa mata hannun, hannuna na da laushi amma sai na jishi tamkar na namiji a cikin nat
a. Ta dafa ni ta ce
"Ina yara na?"
Maimakon na bata amsa sai na kalli Bilal da ya zubo mana ido fuskar sa
ɗ
auke da yanayin da na kasa fassarawa.
"Ki dawo ki zauna mana JALILA ku da kuka sha hanya zaki tsaya surutu kuma" Hajja ta fa
ɗ
a, sai na
ɗ
aga
kai da sauri na kalleta bugun zuciya ta yana ƙaruwa. JALILA na ji ta ambata, JALILA abokiyar aikin Bilal ta can Headquarter su ko kuwa wata daban?
Dama haka JALILAR take budurwa ce ba matar aure ba yanda nake tunani?
Haka kawai na ji zufa na tsatstsaf
omun dukda a
ɗ
azu sanyin Ac har takura mun yayi shine ma dalilin da ya saka na tafi waje nayi sallah. Ta sake sakar mun murmushi kafin ta koma in da ta taso tana kallon Bilal ta ce
"Yau naga Maman Al'amin". Murmushin yaƙe yayi ya ce
"Ai kuwa dai yau king
a Halima"
"Babu wanda zai ce ta haifi su Al'amin tafi kama da yayar su" ta sake fa
ɗ
a tana yar dariyar da ta saka na ji kamar numfashi na zai tsaya. A hankali na miƙe ba tare da na kalli kowa ba na nufi ƙofa na ci sa'a kuma har na fita babu wanda ya dakata
r da ni.
Na zauna kan bencin da ke ƙofar
ɗ
akin ha
ɗ
i da dafe ƙirji na da hannu biyu ina sauke numfashi. Ina nan zaune suka fito gaba
ɗ
ayan su da suke cikin
ɗ
akin banda Anty Amina ina jiyo muryar Hajja ma musu Allah ya tsare hanya babu wanda ya lura da n
i a cikin su suka wuce. Tashi na yi na bi bayan su, na tsaya daga can gefe ina hango su jikin wata mota, gaba wacce suka zo taren ta shiga ita da Bilal suka shiga ba, ji na ringayi kamar mafarki ne ba wai gaske abin yake faruwa ba. Na shiga laluba jiki na
ina neman wayata dan na kira shi na tabbatar da gaske shi ne suka shiga bayan mota da wata Mace ba ni ba ko kuma dai idanuwa ne kawai suke hasashen gaibu?
Banji waya ta a tareda ni ba na tuna sanda na koma
ɗ
akin a gefe na na ajiye ta ba cikin aljihu ba
dan haka na koma da sauri ina waigen motar da ta tashi har sun fice daga harabar gurin ajiye motocin. Yanda kasan anyi ruwan sama an
ɗ
auke haka sukayi shiru ina shiga
ɗ
akin, ni ba ta su nakeyi dan ko sunyi maganar ba bana zaton zan fahimci abinda suke cew
a. Na
ɗ
auki waya ta na fita ina jiyo yanda Fadila da Hadiza suka sheƙe da dariya kamar wasu ta
ɓ
a
ɓɓ
u harda tafawa. Ina kiran layin sa aka ce mun a kashe yake ba tareda na koma nayi musu sallama ba kawai na fice daga Asibitin na wuce gida.
I wanted to sum
marize it in one or 2 chapters but i was overruled
Nagode da masoya na haƙiƙa wa
ɗ
anda ko sunyi fushi basu manta tunanin su, wa
ɗ
anda suke yiwa Marubuci kallon Mutum ba wai Bawa da suka siya da ku
ɗ
i ba.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*LABARI/RUB
UTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 08142548705* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu
yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta
sama*
*PAGE 32*
*Barkanmu da Sallah yan uwa*
🙏🏽
Sai da na fita kofar asibitin kafin na tsaya ina raba ido, ina zan nufa ne ma? Gida zan tafi ko kuwa gari zan shiga cigiyar inda Bilal ya tafi? Na kai hannu na share laimar da naji akan fuskata wad
da ban tantance hawaye bane ko zufa kafin na shiga tare abin hawa, gidanmu na wuce, ban ko kar
ɓ
i canji ba bayan na sauka na shige gidan a bakin ƙofa na zauna kamar wata zararriya na fasa kukan da ya saka Mama ta fito daga falo kamar zata hantsila da Sharif
a a hannunta ta shiga tambayata mai ya faru?
"Mutuwa Hajjan tayi?" Ta fa
ɗ
a tana kallona sai na girgiza kai ina turza ƙafa kamar ƙaramar yarinya na sake gyara zama ina cigaba da kukan. Sai ta buga mun tsawa tace
"Bana son iskanci Halima haka nan zakizo
ki fa
ɗ
ar mun da gaba na tambaye ki menene kuma kinƙi fa
ɗ
a to tashi ki fita tun ban rufeki da duka ba". Ganin ta ajiye Sharifa na san zata iya dukan nawa kamar yanda ta fa
ɗ
a hakan yasa na miƙe na shige falon da sauri ina cigaba da kukan. Bata sake bi ta ka
ina ba, sai da nayi mai isata kafin na kama hanyar gida ba tareda nayiwa Mama sallama ko na
ɗ
auki su Sharifa ba na tafi.
Ina ƙoƙarin bu
ɗ
e gida naji muryar Maman Yusuf tana kirana, na waiga ganin ta nufoni yasa na tura ƙofar na shiga itama ta biyo bayan
a.
"Kin dawo kenan" ta fa
ɗ
a tana kallona ba tareda mun ha
ɗ
a ido ba dan bana son ta fara tuhumata mai ya sameni na bata amsa da "eh na dawo".
"Ai har zan shigo
ɗ
azun sai kuma naga kina da baƙi sai kawai na wuce dama can gidan Hajiya Zainab zan ce miki
ko zamu leƙa ta gamu da tsautsayi ta karye a hannu" ta sake fa
ɗ
a, sai nayi jimm dalilin cewar da tayi wai
ɗ
azu taga nayi baƙi, su wa ta gani ko in ce suwaye suka zo gidan tunda no dai nasan kafin na fita babu wanda yazo mun amma saboda bana son dogon suru
tu sai kawai nace mata
"Allah sarki Allah ya bata lafiya nima surukata ce bata da lafiya tana Aminu Kano a kwance". Jajantawa tayi ha
ɗ
i da yiwa Hajjan fatan samun sauƙi kafin tace zata yiwa su Amina magana in zasu samu dama ko zuwa gobe su leƙa su dubat
a. A raina Allah Allah nake ta wuce shiyasa ma na tsaya ban bari mun shiga falo ba, ganin bani da niyyar bata gurin zama ya saka tayi mun sallama akan in zasu samu zuwa dubiyar gobe zata kirani nace mata toh.
Na ringa kallon tarkacen dana tarar cikin f
alona, daga kan kofunan da aka sha lemo da robobi har zuwa disposable packs wanda ke
ɗ
auke da sauran abinci ga kaza da aka yiwa cin wulaƙanci duk anyi mun kaca kaca da gurin dana gyara tsaf na saka turare kafin na fita daga gidan. Ko ba'a fa
ɗ
a mun ba nasan
Bilal ne, wani abu ya taso daga ƙasan zuciyata ya tokare mun maƙogaro. Kenan nan ya kawo su ya bu
ɗ
e musu
ɗ
akina suka shiga ba tareda izinina ba? A hankali na ringa takawa saboda yanda nakejin tamkar zan fa
ɗ
i saboda ƙuncin daya mamayemun zuciya. Ɗaki na wu
ce na samu gefen gado ma zauna lokaci
ɗ
aya hawaye masu tsananin zafi suka
ɓ
alle mun. Bansan adadin lokacin dana
ɗ
auka zaune ba saida na jiyo ana kiran sallar magriba lokacin kuma naji ana bugun ƙofa kamar za'a
ɓ
alla ta.
Tun daga ƙofar falo na fara jiyo
ihun kukan Sharifa, na ƙarasa da sauri na bu
ɗ
e naci karo da Mu'azzam fuskar nan kamar zeyi aman wuta yana ganin na bu
ɗ
e ya direta a ƙasa ya juya ba tareda ya ce mun komai ba haka na jasu muka shige cikin gidan Al'amin na gaya mun sun da
ɗ
e a tsaye suna ta
buga ƙofa ba'a bu
ɗ
e ba.
"Mami me akayi miki kike kuka ko baki da lafiya?" Ya fa
ɗ
a yana kallona dan guri na sake nema na zauna ina shayar da Sharifan ina hawaye. Maganar sa ta saka na shiga goge fuskata can ƙasan zuciyata wani
ɓ
angare yana tunasar dani cew
a
"Kuka ba zai miki maganin damuwarki ba Halima".
Sai ƙarfe sha
ɗ
aya da mintuna Bilal ya dawo gidan ina zaune a falon da ban
ɗ
aga ko tsinke daga abinda na dawo na tarar ba naji motsin bu
ɗ
e ƙofa, ban motsa ba saida naji an cire kwa
ɗ
on dake jikin get an
a ƙoƙarin zugeshi kafin na miƙe a tsorace saboda tun da aka ƙwace Mashin
ɗ
in Bilal ba'a bu
ɗ
e get
ɗ
in amma dana hangoshi ta window sai hankalina ya kwanta na koma na zauna, gunjin mota da naji ana ƙoƙarin shigowa da ita gidan ya saka na sake miƙewa da sauri
na tafi bakin ƙofa. Ina tsaye har ya gama daidaita parking ya fita ya kulle get ua sake komawa cikin motar, motar da suka tafi daga Asibitin a ciki ce
ɗ
azu.
Sai da ya kwashi kusan minti biyar a ciki kafin ya fito waya kare a kunnensa ya wuce part
ɗ
in
sa ba tareda ya nuna koda alamar yaga tsayuwata ba dukda nasan cewar ya ganni dan ƙofa a bu
ɗ
e take. Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka na koma na zauna ƙwaƙwalwata da zuciyata cunkushe har na rasa wane tunani ya kamata nayi a lokacin, ina nan zaune
ya sake fitowa ina jiyo takunsa kan barander nayi saurin kwanciya kan kujera ha
ɗ
i da lumshe idanuwana tamkar me bacci. Har raina naji tsakin daya ja bayan daya shigo falon ya tsaya a kaina kafin ya shiga jijjiga ƙafata yana kiran sunana.
Na tashi na z
auna ina kare idona tamkar daga baccin gaske na farka, da ido ya nuna mun tsakiyar falon kafin ya ce
"Menene haka? Amma dai kin san na tsani kwana da datti a cikin gida ko?"
Na bi gurin da kallo nima kafin cikin zafin ran da ban ta
ɓ
a sanin ina da shi
ba na ce
"Mai ya hana ka fa
ɗ
awa wa
ɗ
anda suka
ɓ
ata gurin su gyara ko kuwa haka suka zo suka tarar dashi?"
Ga mamakina sai gani nayi ya saki murmushin dake narkar da zuciyata a duk sanda nayi katarin arba dashi kafin ya zaune gefena harda
ɗ
ora ƙafafu aka
n cinyarsa cikin murya mai cike da annashuwa ya ce
"Kuma kin san saida tace in bari ta gyara amma na hana".
Ji nayi tamkar ya da
ɓ
a mun wuƙa a ƙahon zuci, na janye ƙafafu na daga jikinsa ha
ɗ
i da gyara zamana ina kallonsa, sau biyu ina bu
ɗ
e baki amma sau
tin muryata yaƙi bani ha
ɗ
in kai gurin furta kalaman dake kan harshe na sai kawai na fashe da kuka, abinda ya sake karyar mun da zuciya yanda ya miƙe tamkar baiga hawayen da nakeyi ba ya wuce kitchen ya
ɗ
akko tsintsiya da dustbin ya shiga tattare gurin, sai
da ya share tas ya gyara gurin sannan ya dawo kusa dani ya zauna ha
ɗ
i da jana jikinsa. Duk yanda na so na ƙwaci kaina yaƙi bani dama.
Ban ta
ɓ
a jin na tsani tarayya da Bilal ba irin na wannan daren, nayi kuka tamkar raina zai fita shi kuwa ko a jikinsa
daga ƙarshe da yaga zan
ɓ
ata masa lokaci ma ƙarfi ya sakamun yayi yanda yaga dama dani kafin ya tsallake ya barni a nan falon ya koma part
ɗ
insa. Saida idanuwana suka daina kawo ruwa suka fara mun ra
ɗ
a