Showing 93001 words to 96000 words out of 287295 words

Chapter 32 - KURA A RUMBU COMPLETE

tana kallo na tace

"Su yan uwan nasa da suka cika gidan duk cikin su babu wanda yasan hanyar kasuwa ko da zasu siyo cefanen?"

Shiru na mata na ci gaba da kuka na. Duk yanda na ringa roƙon su

akan su tafi da ni gida amma basu saurare ni ba, ƙarshe ma fasa jiran zuwan Mu'azzam

ɗ

in suka yi da zasu tafi Mama Fauziyya ta ce mai aikin ta Baba Jummai zata dawo gobe zuwa jibi idan yaso se tazo ta ringa mana wanka Zainab kuma ta taya ni raino da gyaran

gida tun da yanzu Yayar Bilal tana nan base ita

ɗ

in ta rin ga zuwa ta mana kamar yanda ta yi niyya a farko ba.

Bayan sun fito Hajja ta tsayar dasu kamar gaske tana cewa

"Har kun fito kenan?" Mama Fauziyya ce ta amsa mata da

"Eh, mun fito".

"Allah

sarki, abu dai duk yazo ba yanda aka tsammace shi ba. Banda ma dai Allah ya taƙaita ƙila da wata maganar ake yi yanzu ba wannan ba, daga zangar fa wai ya fita yabi sahun Halima shiru shiru tun da tace zata je gida da rana har gurin sha

ɗ

aya bata dawo ba sh

i kuma wayar sa wai ta mutu taƙi

ɗ

aukar caji kwata-kwata. Ni nayi mamaki ace a unguwa kamar wannan me cike da tsaro har a iya buge mutum a masa ƙwace; su kuma wanda suka tsince shi da rashin azanci maimaikon ko a masallaci ne su bayar da sanarwa se kawai s

uka kai shi asibiti suka yasar wai ashe suma ba yan unguwa bane hanya ce kawai ta biyo da su, mun dai shiga tashin hankali matuƙa amma dai mun godewa Allah tun da ya bayya na babu dai mashin babu waya, ku

ɗ

in akawut

ɗ

in sa ma se jiya daya tura Habubakar ya

ciro aka ce an kwashe komai; wa

ɗ

annan azzaluman mutane dai se dai kawai mu bar su da Allah" ta ƙarasa tana share hawaye.

"Toh fa subhanallahi ashe abin da ya faru kenan" Mama Fauziyya ta fa

ɗ

a cikin jimami, Hajja tace

"Wlh Hajiya. Abun dai ba da

ɗ

i, duk

hankulan mu sun tashi ace mutum magidanci an neme shi a rasa har kwana biyu abun akwai ru

ɗ

ani".

"Ikon Allah, amma Bilal

ɗ

in ya

ɓ

ata har kwana biyu amma ba'a sanarwa da matar sa ba?" Anty Mimi ta fa

ɗ

a, se Hajja tace

"To ai mu ma bamu san abin da ya far

u ba se jiya da safe. Tun dai da ya baro can gidan waccen ranar bamu sake ji daga gare shi ba na san kuma lafiyar Allah Bilalu baze kwashe kwana biyu bai je mana ba, idan kuma tafiya ce ta kamashi dole ze sanar mun kuma ze kira a waya mu gaisa amma dai bam

u

ɗ

auki abun da girma ba tun da ba wani labari muka samu mara da

ɗ

i ba.

Abokin ƙanin sa ne fa can ya gano shi a Asibiti, banda shaƙiyancin kuma irin na yan zamani maimakon kai tsaye ya fa

ɗ

a masa ga Bilal a asibiti kawai se yace masa wai ina yayan su? Ya

kamata ya bincika shi yaji ko yana lafiya. To tun da dama muna ta jimamin kwana biyu mun ji shi shiru shine fa yana fa

ɗ

a mun hankali na ya tashi muka taho nan gidan babu kowa se makwafcin sa yace mana ai yau kwana biyu kenan ba kowa a gidan. A lokacin har

Habubakar

ɗ

in yace a kira Halima muji ko tana da masaniyar in da yake ni kuma nasan in har ita wani abu ya same ta ba zamu kasa ji daga gare ku ba dan haka na ce masa aa kar a tayar mata da hankali ga tsohon ciki mu tafi gurin yan sanda kawai a kamo shi a

bokin nasa daya fara kawo

zancen a tuntu

ɓ

i Bilal aji ko yana lafiya. Shine fa da aka kamo shi ya ce ya ganshi a Asibitin Murtala se likita ne ya mana bayanin yanda aka kawo shi babu waya kuma baya magana shi yasa suka rasa ta yanda zasu nemi yan uwan sa da

ma jiyan suke niyyar kai cigiya gidan radio".

"Toh Allah ya rufa asiri ya kiyaye faruwar na gaba bari muje mu har an fara kiran sallah" Anty Labiba data gaji da sauraron ta ta fa

ɗ

a tana yin gaba se Hajja tayi saurin tare su da cewa

"Nace mai zai hana

ku tafi da Halima gida Hajiya? Tun da kunga shi mijin nata ba lafiya ga

ɗ

anyan jiki kada

ɗ

awainiyar tayi mata yawa dan shi

ɗ

in ma can gida na zamu wuce dashi yanzu".

"Babu damuwa ai Hajiya ku tafi da shi

ɗ

in Allah ya bashi lafiya ita

ɗ

in se tayi zaman t

a za'a kawo mata wa

ɗ

an da zasu taya ta zama" Mama Fauziyya ta fa

ɗ

a. Se Hajja tayi shiru kafin kuma ta tace

"Amma dai haihuwar fari a al'ada ai gida ake tafiya ayi wanka balle ita wannan da ga halin da ake ciki"

"Wace al'ada mu ai tuni muka yada zancen

zuwa wanka gida, gara dai yarinya ta zauna a

ɗ

akin ta. Dama saka ruwa ne wahalar jegon ai kuma za'a kawo wacce zata ringa yi mata ina ganin ai babu wata damuwa" Mama Fauziyyar ta sake bata amsa dan tuni Anty Labiba ta fice Anty Mimi kuma ta zama hoto kallo

n Hajjan kawai takeyi.

"Ai shikenan tun da haka kuka za

ɓ

a se ta zauna, amma kowa na

ɗ

auke

ɗ

an sa ya kula dashi ki zaku bar taku bakwa ko tsoron ya lalla

ɓ

a da

ɗ

anyan jego ya haike mata duk matsalar data sameta ai ku ne da kuka na wani ba" Hajja ta fa

ɗ

a c

ikin fushi fushi.

"Ba abinda ze same ta se alkhairi Hajiya idan ma kuma ya haike mata ai ba haramun bane matar sa ce, Halima dai ba in da zata je a gidan ta zata yi jego" Mama Fauziyyar ta bata amsa itama cikin fushi daga nan suka yi tafiyar su.

Ko

mawa nayi na zauna kan gado na tallafe fuskata naci gaba da share hawaye ina jiyo Hajja na masifa da fa

ɗ

ar maganganu bayan data tabbatar sun fice daga gidan. Ban san ya akayi ba kuma da Hajja ta tashi tafiya basu tafi da Bilal

ɗ

in ba kamar yanda tace. Na z

ata ita ma Anty Aminar ta tafi se bayan tafiyar su Hajjan kuma naga ta dawo tace mun gida taje ta dawo, har da cefanen kayan miya tayo da nama da kaji guda biyu a daren ta dafa mun

ɗ

aya tace na zauna na ci, se da na ƙoshi kafin ta sakawa Bilal sauran yaci.



Da Bilal ya shiga

ɗ

aki ze kwanta ta ce na tashi na je ko akwai abin da ze buƙata na taimaka masa tunda har sannan jikin sa be gama yin karfi ba. Yana zaune akan carpet ya

ɗ

ora kansa jikin gado na shiga, cikin sanyin da muryar sa tayi ya miƙa mun hannu

yana cewa

"Zo Halima". Na isa kusa dashi na zauna ya kwantar da kaina a kafa

ɗ

ar sa yana cewa

"Ki yafe mun Halima" ban san yafiyar me yake nema ba amma kawai naji hawaye sun

ɓ

alle mun. Ya rungumeni yana cewa

"Nasan haƙƙin ku ne ya kama ni amma na godewa

Allah da ban mutu ba tareda na nemi yafiyar ku ba, je ki kar

ɓ

o mun

ɗ

ana na ganshi" ya fa

ɗ

a yana saki

na. Se da na share hawayen kafin na fita na kar

ɓ

o shi, ya ha

ɗ

a ya rungume mu ni da yaron yana cewa

"Kiyi haƙuri da abin da nayi miki ke da Amirah wacc

en ranar wlh sharrin shai

ɗ

an ne ban ma san meya hau kaina har na aikata abin da nayi ba".

"Amma Bilal na haihu ka kasa zuwa, Abba na ya kira ka nima na kira ka kuma na san ko ba'a fa

ɗ

a maka ba ba zaka kasa jin labari a unguwa ba" na fa

ɗ

a cikin shassheƙa

. Ya sake rungume ni yace

"Na ga kiran Abba Halima; nayi zaton ƙarata kika kai akan abin da na yi wa Amirah shi ya sa na kasa

ɗ

agawa. San da naga saƙon sa na kin haihu a lokacin dare yayi sosai, na so na bari se da safe na zo amma na kasa jurewa. Tunanin

halin da kike ciki da kuma taraddadin kin haihu ko akasin haka yasa na kasa jurewa. Ban san me ya faru ba, nayan na fito daga gida wasu suka tare ni daga nan ban sake gane kai na ba kawai na tashi na ganni a asibiti kuma duk ƙoƙarin da na yi akan nayi maga

na na kasa. Se daga baya na samu labarin wasu ne suka tsince ni suka kaini asibitin" yayi maganar ba tare da ya bari mun ha

ɗ

a ido ba.

Wani irin tausayin sa ne ya lullu

ɓ

e ni, ni dama na san Bilal baze wofantar dani haka kawai ba, ashe abin da ya same sh

i kenan. Kuka sosai na fashe dashi da wani tunani ya

ɗ

arsu a raina. Yanzu da ace kuma Bilal ya rasa ransa ne fa ina zan sa kaina a duniyar nan naji sanyi?

Rungume ni yayi ina jin

ɗ

umin hawayen sa a dokin wuya na ya ce

"Ki yafe mun Halima, ba da gayya b

ane".

Mun shafe kusan minti goma muna koke koken har se da yaron ya gaji da matsar da aka masa ya fara kuka kafin ya sake ni na kar

ɓ

e shi daga hannun sa na shiga jijjiga shi yaƙi shiru dole se da na shiga shayar dashi kafin yayi shirun alamar har da yunw

a ta dame shi. Se bayan da ya ƙoshi ya sake kar

ɓ

ar sa yana kallo na yace

"Da ni yake kama, hancin sa ne kawai irin na ki".

Shafa hanci na nayi ina murmushi na ce

"Irin na ka dai, ai ban kai ka hanci ba"

"Amma na so ace dake yayi kama se ya fi kyau" y

a fa

ɗ

a yana kwantar da yaron a jikin sa. Na bu

ɗ

e ido ina dariya na ce "Haba dai, ka fito fili kawai kace da baze ganu ba"

"Allah da gaske na keyi ke kyakkyawa ce Halima. Kina da kyau me sanyi irin wanda a duk kallo yake ƙara ƙawata idanuwan me kallon ki;

babbar ni'imar da ubangiji ya yi miki ita ce kyakkyawar zuciya, kin ga ko kwatantan kyawun ki da nawa ma ai

ɓ

ata baki ne kawai. Ina addu'ar yanda yaron nan yayi kama ta zahiri da ni, ya yi kama dake ta ba

ɗ

ini" Bilal ya fa

ɗ

a yana kafe ni da ido. Murmushi na

ringa yi kamar wawuya. Ina kallon sa ya

ɗ

ago yaron bayan ya tashi zaune sosai ya shiga yi masa kiran sallah a kunnen sa. Se da ya kammala kafin ya kalle ni ya ce

"Wane suna kike so a saka masa?"

Nayi ƙasa da kaina ina murmushi, idan son rai na ne bani

da za

ɓ

in daya wuce sunan Abba na, amma na san ƙila a ransa ze zo ya mayar da sunan mahaifin sa ne tun da ya rasu. Hakan ya sa na ce masa

"Duk sunan da yayi maka shi ne za

ɓ

i na". Murmushi me kyau yayi mun kafin ya kammala masa hu

ɗ

ubar kafin ya miƙo mun s

hi yana cewa

"Allah ya raya Muhammad Al'amin"

"Abba na?" Na fa

ɗ

a cikin tsananin murna. Ya

ɗ

aga mun kai ya ce

"Na da

ɗ

e da sanin burin ki na sakawa yaron ki na fari sunan Abba, ko kin manta kin sha fa

ɗ

a mun kafin mu yi aure?"

Rungume shi na yi ina ce

wa

"Na gode Bilal, na gode ƙwarai da wannan karar da kayi mun"

"Ni ne da godiya Halima kin yi mun abubuwa da dama a rayuwa da bazan iya biyan ki ba. Naji da

ɗ

i da kika yi farin ciki, Allah ya raya mana shi ya sa ya gaji takwaran sa"

Da "Amin" na amsa ina

sake rungume Abba na a jiki na. Badan dare yayi ba da yanzu zan kira Abba na gaya masa ya samu takwara amma Allah ya kaimu safiya.

A

ɗ

akin muka kwana rungume da juna cikin farin cikin da muka kwana biyu bamu samu kamar sa ba. Hatta Abba na be yi koke ko

ken da yake mana kwanaki ukun zuwan sa duniya ba da safe har Anty Amina se da ta ringa masa tsiya wai ya ji

ɗ

umin Dady yayi lif kamar babu jinjiri a gidan.

*******

A hanyar komawa gida Mama Fauziyya ta kalli Anty Labiba ta ce

"Allah sarki Bilal, ashe

abin da ya same shi kenan duk mun

ɗ

auki alhakin sa mun zata wulaƙanta yarinyar nan kawai ya so yi". Anty Mimi ta ce

"Wlh fa Anty, ni ma duk se jiki na yayi sanyi tun da muka shiga, ana kallon sa zaka gane yaji jiki wlh. Kamar fa harda

ɗ

inki na gani a gef

en kan sa, gaskiya ya daku sosai da alama".

"Amma dai kun bani mamaki wlh, ku yanzu har kun kama ƙaryar wa

ɗ

ancan mutanen kenan?" Anty Labiba ta fa

ɗ

a se Mama Fauziyya ta ce

"Aa Labiba, wannan fa ba zancen ƙarya bane. Idan sun yi ƙarya akan ainihin abin

da ya same shi wannan daban amma a zahiri dai duk wanda ya kalle shi yasan wani abu na rashin da

ɗ

i ya faru dashi, gaskiyar me ya faru kuma wannan se Allah. Kuma dama karki kuskura ki ce zaki sake zuga Yaya akan maganar Halima, dan Allah ki bari yarinyar n

an ta dawo gida dan ganin idon ki dai gashi abinci ma babu a gidan yini guda jegon kwana uku amma ace sun kasa samar mata abin da zata ci da jikin ta yake buƙata ina ga an sake kwana biyu? Gara ta taho tayi arba'in se ta koma".

Shiru Anty Labiba tayi b

ata ce komai ba, ita ta san halin Bilal ko da yanayin sa ya nuna da gaske bashi da lafiya amma a yanda ta sanshi ba wani abun mamaki bane ace shirya wa yayi. Duk se da ta sauke su a gida tunda a motar ta suka fita kafin ta wuce nata gidan, a hanya ta kira

Mama taji ko Zainab

ɗ

in ta tafi Maman tace mata aa, Haliman tace mata Yayar Bilal da mahaifiyar sa suna gidan shi yasa ta dakata da tura Zainab

ɗ

in kar kuma suyi yawa. Idan sun tafi se taje in ma kuma su zasu zauna mata shikenan daga nan sukayi sallama aka

n se washe gari zata je gidan su ƙarasa magana akan yanda za'ayi da kayan barka.

[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*

*WOMEN

OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*

*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*

*Wattpad @MaryamahMrsAm*

*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*

*Ku

ɗ

in karat

u yana wakiltar mutum

ɗ

aya ne, kiji tsoron Allah karki

ɗ

auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*

*KURA A RUMBU littafin ku

ɗ

i ne, a biya naira 800, biya a asusun*

*1840175439*

*Access bank*

*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta

sama*

*PAGE 22*

"Dagaske ne Anty, masu ƙwacen mashin ne suka bige shi; wa

ɗ

an da suka kai shi asibitin ma na san

ɗ

aya daga cikin su tare muka fara Maitama Sule" Mu'azzam ya fa

ɗ

a jin Anty Labiba ta dage akan ƙarya kawai Bilal ya shirga ba wani abu day

a same shi. Zuwan ta kenan ta tarar suna jimamin abun, Na kira Abba na gaya masa an masa takwara sannan na ƙara da fa

ɗ

a masa dalilin da ya saka Bilal be duba mu ba har na bawa Bilal

ɗ

in waya suka gaisa da Abban ya sake bashi haƙuri. Bayan mun gama wayar ne

ya fito yake gaya wa Mama yan da mu ka yi se ga Anty Labiban.

"Ƙarya ya ke yi, saboda maganar ma bata kama kunne na ba shi yasa tun jiyan ban fa

ɗ

a miki ba, na

ɗ

auka ma su Yaya Fauziyya zasu gaya miki tun da naga se jiman ta abun suke yi. Ha

ɗ

in baki ne ka

wai shi da yan uwan sa saboda su goge laifin wofantar da Halima da suka yi" ta fa

ɗ

a sanda Mama ta maimaita mata abin da Abban ya gaya mata.

"Yanzu kai ka san haka ta faru da shi amma shi ne ka yi shiru baka fa

ɗ

awa kowa ba?" Abba ya fa

ɗ

a yana kallon sa,

se ya yi ƙasa da kai ya ce

"Ni ma ai se daga baya na sani Abba. Lokacin da muka mayar da ita gida bayan na dawo aboki na Najib ya kira ni yake gaya mun masu ƙwacen mashin sun bige mai gidan da yaga mota ta a gurin kuma su suka kai shi asibiti ma".

"I

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login