Showing 261001 words to 264000 words out of 287295 words
lokutan ta kan yi yunƙurin datse alaƙar amma sai ta kasa, daga ƙarshe ta yaƙi kanta ta kuma tilastawa kanta yarda dashi da amincewa da duk zancen daya zo mata dashi wanda sau da yaw
a ta kan tuhumin kanta akan hakan, abinda ta yarda dashi Bilal
ɗ
in yana da wata baiwa ta iya yaudara da asirce zuciyar mace shiyasa ko da ace tayi niyyar yaƙar zuciyarta ta rabu dashi sai ta kasa.
A karo na biyu ta sake bijiro masa da maganar aure wanda
wani babban dalili ya janyo hakan ta kuma bashi shara
ɗ
in idan har zai aureta toh fa sai dai ya rabu da matarsa wanda bai musa hakan ba kuma ya amince har suka fara shirye-shirye.
Ta siyi gida wanda tayi niyyar mallaka masa ya sakata a ciki idan sunyi a
ure, shagunan da Mamanta ta siya mata su kansu shi taso ta mallakawa domin tana so ya tsaya da ƙafarsa idan sunyi aure bata so ya zamana ita zata cigaba da
ɗ
aukar
ɗ
awainiyarsa.
A hannun Hafiz ta siyi gidan kuma a lokacin ta fa
ɗ
a masa alaƙar da take tsak
aninta da Bilal harda matsayin da suke kai a lokacin, batayi mamaki yanda Hafiz
ɗ
in yace mata ya sani ba domin alaƙarta da Bilal a bayyane take. A lokacin ya ce mata
"Ki kula dai domin KURA A RUMBU, ABAR TSORO CE" bata damu ba dan bata ma san ma'anar kari
n maganar ba, sanda ya bata takardun gidan data shaida masa Bilal ta siyawa, a lokacin ne ya ce mata
"Yanzu bakya tsoron duk bayan kin gama kyautata masa ya guje ki tamkar yanda yayiwa matarsa? Jalilah Bilal ba mutumin kirki bane na shaida hakan, ta sil
ata kika sanshi, daga sanda kika bu
ɗ
e masa ido da ku
ɗ
i na zama mara amfani a gurinsa kamar yanda ya wulaƙanta matarsa, ina baki tabbacin kema haka zai watsar da ke da zarar ya samu wadda ta fiki dan haka kiyiwa kanki tunani. Bance mutum baya canzawa ba, ta
yuwu dagaske yake sonki kuma ba zai butulce miki ba amma kada ki zura jiki domin duk alkhairin da kikayi masa ba zai kai wanda matarsa tayi masa ba kuma daga ƙarshe ya saka ƙafa ya tankwa
ɓ
e"
Ganin da Halima tayi musu a gidansa ya sakw tabbatar mata da
tabbas Bilal
ɗ
in ba mutum bane domin bata tsammaci bayan hakan kunya da nauyin matarsa zai bari ya cigaba da wata alaƙa da ita ba sai gashi a daren ranar ma sai da yaje gurinta, ta ringa hasaso ace ita ce Haliman a lokacin tabbas babu abinda zai hana ta ku
lle ƙofa ta kunna musu wuta sai dai duk abinda zai faru ya faru amma a maimakon haka sai kawai ta juya ta fita tana kuka wannan al'amarin ya saka ta canza niyyarta ta aurensa domin kuwa ta tabbatarwa da kanta Bilal
ɗ
in ba miji bane kamar kuma yanda Hafiz y
a sha fa
ɗ
a zai iya aikata komai akan ku
ɗ
i.
Da wannan ta wuce Dubai a lokacin kuma har ranta ta yanke rabuwa dashi ta gaske. Ita sam bata ma ankare da yayi blocking
ɗ
inta ba dan bata nemeshi ba sai da aka kwana biyu kawai Hafiz ya kirata yana gaya mata w
ai Bilal ya siyar da gida. A lokacin ta sake tsinkewa da lamarinsa, dukda kafin ta taho dama ta fara zargin wani abu akan zancen renovation data bashi ku
ɗ
i ayi amma da yake ta mata hanya-hanya tunaninta sai ya tafi akan ya kashe ku
ɗ
in ne kawai ba'ayi aikin
ba ashe shi mai
ɗ
ungurungun yayi ya siyar da gidan.
Ta jinjinawa basirar Hafiz daya shaida mata takardun hannun Bilal fake ne, yayi zargin haka kuma ya sani idan ya gaya mata ba zata yarda ba shiyasa yayi shiru ya barta taga abinda yake haska mata da
kanta.
A lokacin dukda Hafiz ya ce karta nuna masa komai amma ta kasa, ta ringa nemansa ta duk wata kafa amma ta gagara samunsa, ya rufe layinta kuma idan ta kira da wata number suma basa shiga alamar nan ma ya toshe kira ba zai shiga wayarsa da lambar
da bai yi saving ba.
A haka labarin sakin Halima da auren da yayi tun tana Nigeria ya sake riskarta. Da ku
ɗ
inta ya auro wata ya siyi gida da ku
ɗ
in gidanta zai sakata a ciki, bata gama warkewa daga wannan shock
ɗ
in ba Hafiz ya sake kiranta wai Bilal ya
kai masa tallan shagunanta, ta shiga tambayar kanta a ina ya samu takardun shagunan? Domin dai bata bashi ba. Ta birkice ƙaramar akwatinta wacce takaddun suke ciki nan suka ce ta
ɗ
auke su in da ta ajiye hakan kuma ya ankarar da ita tabbas
ɗ
auka yayi, yanz
u da ba Hafiz
ɗ
in ya kaiwa ba shikenan ya dirata da ka bata ci ba bata sha ba.
Ta da
ɗ
e tana lissafa ta inda ya kamata ta rama, yana
ɗ
aukar kansa mai wayau ya kamata ta koya masa hankali ta muna masa wayon banza gareshi lissafinsa kuma ba daidai yake taf
iya ba. Akan haka ta shirya dawowa, ta hillaceshi da abinda ta san ba zai kaucewa ba wato ku
ɗ
i sai gashi kuwa yayi unblocking
ɗ
inta da kansa.
Abu na farko data farayi shine siyar da gidan daya rigada ya ci ku
ɗ
insa ga tsohon abokin harkarta Ahlan. Abind
a ya rabasu shi
ɗ
in ya fiya tsalle-tsalle sannan kuma yana shan giya, ita kuma duk namijin da zata kula ta fi so ya zama ita take da iko dashi shiyasa tafi harka da wa
ɗ
anda tafi ku
ɗ
i a yanda zata ringa juyasu yanda take so. Ahlan matashi ne da yake cikin l
ate thirties
ɗ
in sa, yana da ku
ɗ
i sosai yana kuma kashewa mata su tamkar a bishiya yake tsinkosu. Tantiri ne na gaske, ko bunsuru albarka a neman mata.
A hanyar dawowa suka ha
ɗ
u a jirgi hira tayi hira yake bata labarin wata yarinya mai shegen taurin kai
daya ha
ɗ
u da ita yayi yayi taƙi bashi ha
ɗ
in kai shi kuma ya rantse tunda yawunsa ya tsinke sai ya
ɗ
an
ɗ
ana dan haka yanzu ya yanke shawara zai aureta daya samu biyan buƙatarsa ya saita mata hanya. Tana jin haka tace masa ai kuwa tana da gida na siyarwa, da
farko ya ce mata Aa, auren da ba zai wuce na kwana
ɗ
aya ba da an
ɗ
aura zai fanshe ku
ɗ
insa ya saita mata hanya sai kuma bayan kwana biyu da yin haka ya kira wai yana son gidan ba wani ja in ja ya tura mata ku
ɗ
inta ya kar
ɓ
i Original takardu a hannun Hafiz.
Wani abin al'ajabi kuma bayan sun bar gidan Bilal
ɗ
in tana duba status taci karo dana
ɗ
aurin auren Ahlan, kawai ta fashe da dariya ba shiri ganin wacece Amaryar, Fadila fa ƙanwar Bilal lallai sata ta saci sata.
*KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MAR
YAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wak
iltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 5
8*
HALIMA
Cike da haushin Dr Salman na koma gida ranar Juma'ar, haka nan ya san banda mu zasuyi meeting
ɗ
in amma ba'a gaya mana ba saida muka rigada muka je tukunna sannan babu damar tafiya haka mukayi zaman banza har sha biyu kafin muka tashi. Dama-da
ma da na ji na samu nayi clearance
ɗ
ina kafin na wuce gida.
Bayan sallahr magriba Anty Labiba tace mu shirya muje gidan Uncle Mudassir yaronsa na biyu Khalil ya fa
ɗ
i
ɗ
azu da safe ya samu karaya, muna shirin fita Mama ta kirata tana tambayarta yaushe zam
uje duba Khalil
ɗ
in tace mata yanzu sai tace toh mu biya mata mu tafi tare kawai.
Mun tarar da yan uwan Anty Ummi matarsa sunzo su da yawa dubiyar sun cika falon dan haka tace mu shiga can falon Uncle Mudassir yana nan dama, tun daga bakin ƙofa na fara
jin ƙamshin turarensa, ina son turare shiyasa duk inda naji wanda yayi mun da
ɗ
e nake riƙe ƙamshin duk kuma idan na ji irinsa a wani guri sai na tuna da asalin inda na fara saninsa.
Suna zaune kan two sitter dining dake gefe a cikin falon da farantan ab
inci a gabansu, Uncle Mudassir har ya ci fin rabin nasa amma shi bai ko ta
ɓ
a ba yana danna waya sallamarmu ta saka ya
ɗ
ago kai caraf muka ha
ɗ
a ido. Sake ƙanƙance ƙananun idanuwansa yayi yana kallona nayi ƙasa da kaina na wuce ina gyara riƙon Sharifa a jiki
na har kuma na zauna ina jin alamun har sannan kallona yakeyi. Ba tareda na bari mun sake ha
ɗ
a ido ba na yi musu gaisuwar ha
ɗ
aka shida Uncle Mudassir
ɗ
in daya taso ya dawo cikin falon yana mana sannu da zuwa.
Na saci kallonsa ganin shima ya taso, ya za
una a gefena kan 1 sitter kafin ya
ɗ
an zame ya shiga gaida Mama cikin girmamawa, bayan sun gama gaisawa ya juya kan Anty Labiba Uncle Mudassir yayi saurin dakatar dashi yana cewa
"Karkaga ta kusa cika two sitter ka
ɗ
auka wata babbace ƙanwarka ce itace au
tarmu" duk sukayi dariya banda ni da nake kallonsa ya wani shafa kai yana murmushi kafin suka shiga gaisawa. Har gurin goma muna gidan sunata hira, ni dai zaman Dr Salman ne ya takurani na kasa sakewa ƙarshe ma jin baƙin cikin gidan sun ragu yasa na koma c
an tareda Inayah da Sharifa da suka fara bacci.
Anty Ummi ce ta leƙo tace na fito mu tafi, na tada Inayah kafin na
ɗ
auki Sharifa muka fita, nayi tsaye ina kallon Dr Salman a raina ina mamakin zaman me yakeyi da har sannan bai tafi gida ba? Tare muka fi
ta muna gaba yana binmu a baya har muka hau babban titi kafin kowa ya kama hanyarsa. Bayan mun sauke Mama Anty Labiba ta fara mun taratsi wai dama mutumin nan Oga na ne shine na masa wata gaisuwar jeka ka mutu?
"A hakan kike so su baki aiki idan kin ga
ma service
ɗ
in alhalin bakya mutunta Oga? Wlh daga yanda naga yana kallonki na san yaji haushi tun wuri ma ki san ta yanda zaki fara bashi haƙuri". Ni dai ban ce mata komai ba har muka isa gida, Amir da baiyi bacci bane ya ke gaya mana Uncle Faisal ya zo g
a saƙo can ma daya bayar a ajiye mun.
Sai da nayi wanka nayi shirin bacci dan munci abinci a gidan Uncle Mudassir kafin na bu
ɗ
e saƙon da Faisal
ɗ
in ya kawo mun, customized pouch ne na wayata, sai water bottle mai kyau shima da sunana a jiki da kuma jot
ter mai kama da diary. Na cire asalin pouch
ɗ
in wayar na saka sabon ina murmushi. Shi da ya ce yanda yake jin Khadija a zuciyarsa (Matarsa) ba zai iya yi mata kishiya ba amma kuma na rasa dalilin zuwan da yakeyi da ƙananan kyaututtukan da yake yi mun, duk
sanda zai zo gidan sai ya taho mun da wani abu amma kuma ya ce shi ba zawarci na yakeyi ba.
Gyara kwanciya nayi bayan na kashe filila na rufe ido na amma bacci ya gagara
ɗ
aukata, tunanin ha
ɗ
uwarmu da Bilal jiya ya shiga dawo mun. Tashi nayi zaune na jin
gina bayana da allon gadon ha
ɗ
i da rungume ƙafafuwana na zubawa wardrobe
ɗ
in dake kallona ido ta cikin duhun daya mamaye
ɗ
akin.
Babu wata alama data nuna kewa ko damuwa a tattare da Bilal, dukda na sani shi
ɗ
in gwani ne gurin iya
ɓ
oye labarin zuciyarsa
ta yanda yake matuƙar wahala ka iya karantar yanayinsa ta cikin ƙwayar ido ko a kan fuskarsa amma nayi tsammanin na tsinci wani abu musamman da nake yawan jin ana fa
ɗ
ar Maza sukan shiga wani hali idan suka rabu da matansu musamman idan ya kasance su suka
zalinci matan amma ya akayi ni a kaina abin ya zama akasin haka?
Babu wata damuwa a tattare da Bilal, idan ma ba idanuwa na bane sai naga kamar har haske ya ƙara da kyau alamar bashi da wata matsala a rayuwarsa. Idanuwana suka kawo ruwa nayi saurin sha
re su kafin su fara
ɗ
iga sannan na koma na kwanta ina jan numfashi ta baki a ƙoƙarin kwantar da zuciyata. To wai ma mai zai dame shi ne bayan yana tareda Duniyarsa? Abar ƙaunar sa ya kuma rabu da kaskar da liƙe masa ai dole.
Cusa kaina nayi cikin pillo
w na saki kukan dana kasa ha
ɗ
iyewa. Na yarda shi dai Bilal bai ta
ɓ
a so na ba kawai ni nayi ta cusa kaina na kuma kasa gane hakan tuntuni. Nasha ji da karanta labaran mazaje sa suke cin amanar matayensu da wasu a waje amma ban ta
ɓ
a cin karo da irin Bilal ba
, yanzu nake ganin kamar ma da gayya ya bada ƙofar da zan fahimci abinda yake aikatawa har ma kuma ya barmun shaidar da ko na ci gaba da zama dashi to fa ba zan sake samun kwanciyar hankali ko nutsuwa a tareda shi ba.
Idan na tuna musayar kalamansu da
Jalilah da kuma ganin da nayi musu a cikin gidana sai in kasa gane dalilin daya saka har yanzu nake jinsa a zuciyata. Ya kamata ace tun da da
ɗ
ewa ya fita a raina irin azabar daya ganawa zuciyata har ma da gangar jikina amma dukda haka amma a koda yaushe ci
kin yi masa uzuri nake. Rabuwa da hawayen nayi sukayi ta shatata tsayin lokaci kafin na tashi na
ɗ
auro alwala na shiga jera raka'oi har saida naji nauyi da ƙuncin daya tasarma mamaye zuciyata ya sauka. Na da
ɗ
e a zaune ina tasbihi da yiwa annabi salati har
saida idanuwana suka fara rufewa kafin na shafa addu'a na haye gado ban ko ƙara ko minti biyu ba bacci mai cike da nutsuwa yayi awon gaba dani.
Alhamdulillah, tunda ubangiji ya lamunce mun na durfafi kai masa kokena koda ace guguwar ƙaunar dana rasa ya
nda zanyi da ita akan Bilal ta taso mun dana kalli gabas zanji komai ya wuce tunanina ya saitu na dawo kan hanya.
Washe gari ta kama asabar kusan wuni nayi ina aikin yiwa Al'amin da Inaayah snacks da zasu kai makaranta a gobe Lahadi zasuyi picnic shine
kowanne
ɗ
alibi zai kai wani abu daga gidan Anty Labiba tace nayi musu cake da samosa. Sai yamma lis na gama nayi wanka, bayan sallar magriba ina azkar na kunna Data dan yinin ranar gaba
ɗ
aya ban hau online ba, ina kallon saƙonnin da suke ta shigowa, numbe
r da na gani ta saka na
ɗ
auki wayar da sauri ina dubawa.
Na goge duka numbobinsa amma haddarsu bata goge a ƙwaƙwalwata ba dan haka ina gani na gane shine dukda wannan layin ba sosai yake amfani dashi ba a lokutan da yake yawan tafiya Abuja ne yake kira
na dashi dukda banyi saving ba amma na haddace number.
Kife wayar nayi ba tareda na karanta abinda saƙon ya ƙunsa ba, na san ba zai wuce shirmen daya fara yi mun waccen ranar da muka ha
ɗ
u ba ne zai cigaba ni kuma banida lokacinsa a yanzu.
Sai da nay
i sallar isha'i kafin na tashi daga gurin na zuba abinci na fara ci kenan Anty Labiba tace mun wai Abba yana ta kirana bana
ɗ
auka in kirashi yanzu hakan ya sa na tashi na
ɗ
akko wayar.
Abban na fara kira bayan mun gama maganar da zamuyi har zan ajiye wa
yar zuciya ta ƙwadaita mun son ganin saƙon daya turo dan haka na shiga Whatsapp
ɗ
in na bu
ɗ
e.
"Na san ko duk duniya zasu juya mun baya ke ka
ɗ
ai ce ba zaki gujeni ba My Halims, ina cikin wani mawuyacin hali ina kuma buƙatar taimakonki. Idan kin amince zaki
taimakamun ki dawo mun da amsa cikin gaggawa ki kuma shirya zan tura miki da address
ɗ
in in da zaki sameni, na tanadar miki da amsoshin da kika da
ɗ
e kina bukatar jin su daga gareni, duk abinda ya faru shiri ne na tabbatar kuma zaki fahimci haka idan kika
saurari bayani na. Bilal
ɗ
inki." abinda ya rubuta a saƙon kenan.
Guri na samu na zauna ina sake nanata karanta saƙon,
"Ni da kika ganni ina tarayya ne da mutanen dana san zasu mun amfani a rayuwa, da zarar amfanin mutum ya ƙare kuma zan ajiye shi dan
ni bana son liability" maganganunsa na wani lokaci suka shiga dawo mun. A fili na furta
"Tabbas na shaida hakan, ya watsar dani a lokacin da yake ganin amfanina ya ƙare a gurinsa ashe kuma da saura". Blocking