Showing 186001 words to 189000 words out of 287295 words
bata amsa a tsaye,
ɗ
auke kai yayi ganin ta juyo ta kalle shi ta
ɗ
an yi murmushi ta ce
"Akan Hafiz har Malamai na shiga amma shegen guy
ɗ
in nan yanda kasan aljani na kasa samunsa"
"Bafa zan
ɗ
auki wannan wulaƙancin ba ta yaya a gabana zaki ringa gaya mun kina son wani daban a hakan kike so na aureki?" Ya taso mata, wani shegen kallo ta masa tace
"In aureka dai, ai nice mijin kaine mata
r ko kai a haka da kake kana zaton ka isa ka aureni?
Banda ma so banzan abu ne Bee ai ka san ni ba tsararka bace ko shi ubangidan naka nafi ƙarfinsa kawai dai zuciya da baka da iko da ita tayi ta kwaso maka tarkace tana saka ka son su" ta ƙarasa tana sok
a earpiece a kunneta. Ya kusa minti biyar yana kallonta yama rasa mai zaiyi ko mai zaice, tunda yake ba'a ta
ɓ
a masa zagi irin wanan ba, wato shine tarkace? Lallai Jalilah taga gadon baccin sa.
Ha
ɗ
iye zuciya yayi ya tada motar, sai da suka fita daga Ai
rport
ɗ
in kafin a ƙufule ya sake tambayarta in da zai kaita
"Nace maka gidana ko kunnuwanka sun toshe ne kuma baka ji da kyau?" Ta bashi amsa, wlh ba dan ba sai ya gaggaya mata maganganu kuma ta fice masa a mota amma kuma yanzun dai bai isa ba amma lokaci
na zuwa, daya tuna abinda ya shuka dole ya sauke fushi ya gyara murya ya ce
"Kin manta ana aiki a gidan ne?"
"Aikin da akeyi a waje meya shafi ciki kuma ina kace an gama fentin cikin tun last week?" Ta tambaya tana tsare shi da ido, titi ya mayar da i
donsa kafin ya ce
"An gama amma ai kin san an kwashe kayan ni kuma da naji kince sababbi za'a zuba shiyasa ba'a mayar ba dan wasu abubuwan ma na kyautar dasu"
"Su kuma kayana ka kaimun su ina?" Ta fa
ɗ
a tana tsare shi da ido, kashe mata ido
ɗ
aya yayi ya c
e
"Na kaiwa Matata ta ringa sakawa kinga se na ringa ganinta kamar ke"
"Har ta mutu ba zatayi kyauna ba" ta fa
ɗ
a tana juya ido, ya ruƙo hannunta yace
"Ni shaida ne yar balarabiyata, yanzu dai ina zamuje kinga idanuwanki sun nuna a gajiye kike ki samu
ki huta kar kiyi missing flight kuma goben"
"Muje gidanka toh tunda kace can babu gurin kwanciya" ta fa
ɗ
a tana kallonsa.
"Gida na kuma?" Ya fa
ɗ
a da sauri har yana sakin stirring, ta ta
ɓ
e baki tace
"Eh mana ko ba zaka kaini ba?"
"Zan so in kaiki mana
amma kin manta na gaya miki matar gidan bata nan kuma kinga dai unguwarmu ba kamar in da can gidan yake bane akwai yan sa ido yanzu a ganni na shiga gida da Mace ai na shiga uku a garin nan bama unguwar ba"
"Ai kuwa ko dubu zaka shiga yau sai dai ka sh
iga dan wlh ba zan kwana a hotel ba a gida na yi niyyar kwana tunda kuma ka kyautar mun da kayan gida ba tareda izini na ba sai ka kaini naka gidan ba wai matarka bata nan ba ko tana nan wlh ba abinda ya mun zafi a nan zan kwana dan dama da baka zo ba sai
dai ka ganni a ƙofar gida kuma ko yanzu ka direni a nan ƙila sai na rigaka zuwa so baki alaikum ka wuce mu tafi dan ni a gajiye nake wanka nake so nayi na kwanta nayi bacci" ta bashi amsa itama.
Duk yanda ya so ya fahimtar da ita ta masa banza ƙarshe m
ayafinta taja ta rufe fuskarta kamar me bacci, ganin har
ɗ
aya ta kusa suna gararanba akan titi bai kuma ga alamar zata canza ra'ayi ba ya saka kawai ya kama hanyar gida a ransa yana addu'ar Allah ya sa kowa yayi bacci har masu gadin layin. Ya da sauri ya k
alli mirror jin ta ce
"Ga wata mota nan ma tun
ɗ
azu take binka ƙila ma matar taka ce ko wani daya sanka" ta ƙarasa tana dariya. Kallon motar yayi dakyau, sai tayi masa kama da motar Suhaila matar Hafiz amma kuma number ta banbanta tata kamar ABJ wannan ku
ma ABC dukda dai bai tabbatar ba amma ya ƙarfafawa kansa hakan ne dan ba zai iya hasaso cewa Matar Hafiz
ɗ
in ce ko kuma ma shine da kansa ba iya tashin hankalin da yake ciki yanzu ya ishe shi. Kamar me motar ya san me suke cewa kuwa yazo ya wuce su dama a
junction suke ya
ɗ
auki wata hanyar daban Bilal ya sauke ajiyar zuciya kafin ya balla mata harara ya cigaba da tuƙi.
Roƙonta ya ringayi akan ta rufe fuskarta sanda suka isa unguwar, duk wanda ya kalle shi dakyau sai ya fahimci bashi da gaskiya haka ya la
lla
ɓ
a ya shige Allah ya taimake shi mutum
ɗ
aya ne zaune sauran masu gadin duk sunyi bacci get
ɗ
in kuma a bu
ɗ
e yake dan haka bai ma taso ba tunda ya gane motar daga zaune ya masa sannu da zuwa ya wuce dama kuma windows
ɗ
in motar tint ne ta gaba ne za'a iya
ganin wanda yake ciki. Sai da ya shige da motar ya dawo ya kulle get kafin ya tsaya ya riƙe ƙugu yana sauke numfashi. Ta fashe da dariya bayan da ta fito daga motar tana cewa
"Wai yanzu duk tsoron kar yan unguwa su ganka ne yasa ka birkice haka amma bak
a tsoron Allah kake bajekolinka a hotel ko?"
"Dan Allah ki wuce ciki kum wlh tun kafin gari yayi haske zamu fita ba zaki zubar mun da mutunchi a unguwa ba dama duk sun tsaneni tunda Halima ta bar gidan nan" ya fa
ɗ
a yana wucewa gaba bayan daya shiga
ɗ
akin
tsakar gida ya kunno Solar dan babu wuta tunda sha biyu ta wuce kuma ya san ba dawo da ita zasuyi ba. Bayan tafiyar Halima da aka fara rashin wuta ya ha
ɗ
a ta babba har Ac take
ɗ
auka. Kan kujera ta fa
ɗ
a tana cewa
"Wash Allah, da
ɗ
i na da matar nan taka a
kwai tsafta ba wanda zaice falon me yara ne kamar na sabuwar amarya komai na nan da sabuntarsa"
"Basu da
ɗ
e ba ai bayan haihuwar Sharifa ta canza su" ya bata amsa yana
ɗ
aukar remote
ɗ
in Ac ya kunna. Ta miƙe tana ƙoƙarin cire doguwar rigar jikinta tace
"D
ukda haka dai tana da tsafta gaskiya" sai ya wuce
ɗ
aki yana cewa
"Ba laifi amma dai ni nake shara da mopping har wankin toilet duka" ta kuwa fashe da dariya tace
"Ashe boyi boyi ta mayar da kai sannu mijin tace".
Indomie ya dafa mata bayan tayi wanka
ya
ɗ
umama Shawarmar daya siyo
ɗ
azu a microwave dama guda biyu ce ya dafa tea suka ci kafin ta kwanta a Asalin
ɗ
akin Halima da tace gadon irin nata ne na gida dan haka nan zata kwanta kafin ma ya gama wanke kwanukan da suka
ɓ
ata ya tattare falon har tayi b
acci. A falo ya kwanta bayan daya leƙa ta ya tarar tana bacci dan dama cike yake da taraddadin karta nemi suyi wani abu dan gaskiya ba zai iya ba gaba
ɗ
aya yanzu haka ma a mugun tsorace yake ji yakeyi kamar wani zai iya shigowa ya tarar dasu yayi mamakin y
anda yake ji
ɗ
in dan ko ka
ɗ
an bayajin komai idan suka je can gidan ta ko da yake yan unguwar kallon ma'aurata suke musu irin kamar a wani garin suke zama sai hutu suke zuwa nan
ɗ
in. Daƙyar bacci ya
ɗ
auke shi yana yi yana farkawa gudun karsu makara gari yay
i haske bai fita da ita daga unguwar ba.
HALIMA
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir No
vels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800,
biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 43*
HALIMA
Yanda naga rana haka naga dare, sai naji ashe ma jiya baccin da
ɗ
i nayi yaune nake ganin asalin baƙin dare. Sai da aka idar da
sallar asuba kafin na samu bacci ya fizgeni, sai dai ban wani yi nisa ba na farka sakamakon kiran suna na da nake ta ji anayi.
Na tashi zaune daƙyar ina matse ido ha
ɗ
i da dafe gefen kaina da nake ji kamar zai fa
ɗ
o saboda ciwo. Mama na tsaye ta ce
"Ha
la kin manta abinda Abbanku ya fa
ɗ
a miki shiyasa kika shantake kina bacci har ƙarfe tara".
Gabana ya yanke ya fa
ɗ
i, mai take nufi? Takardar ya turo ta kar
ɓ
a ko me?
Muryata bata ko fita sosai saboda uban kukan da nasha jiya ga bacci da ciwon kan da
suka mun rubdugu na ce
"Dan girman Allah Mama ki bashi haƙuri"
"Kin yafe ba zakiyi bautar ƙasar ba kenan in je na gaya masa?" Ta katse ni. Na tabbatar har kunnuwanta ƙarar ajiyar zuciyar da nayi ya isa jin ba abinda nake tunani bane, ta ja tsaki ta
fice daga
ɗ
akin tana cewa
"Ki tashi ki shirya tun ranki bai sakw
ɓ
aci ba dan wlh a cike yake dake kin kuma san dai bai iya fushi ba".
Ina wanka ina hasaso ta inda zan samu mafita cikin wannan tsaka mai wuya da Abba yake ƙoƙarin jefa ni. Yanzu shi ba
bu ruwansa a ringa cewa aure na ya mutu kenan? Na tafi tunani dangi na uwa da uba babu wata bazawara kamata, yawanci ma har manyan mutuwa ce ta rabasu da mazajensu ba sakin aure na shikenan ni zan zama abar buga misali a dangi da unguwa, fatan da aka ring
a mun zai tabbata na san ƙila labari na babu inda ba zai kai ba har Facebook da Whatsapp groups.
Kan toilet na zauna na sha kuka na godewa Allah kafin na fito na sake zama kan gado na rafka tagumi. Allah ya sani ina son Bilal, rabuwa dashi abu ne da ba
n ta
ɓ
a hasasowa a nan kusa ba duk da abinda ya faru yayi silar zabtarewar sama da kaso hamsin na yanda nake jin sa a zuciyata amma in ce na dena son sa wannan ƙarya kawai nakeyi.
Hannu biyu na saka ina goge sababbin hawayen da suka
ɓ
alle mun, da kaina
kuma na shiga tugumar kaina anya kuwa nayiwa kaina adalci idan na cigaba da son Bilal?
Babu wani abu da zan
ɗ
orar a zamana dashi wanda zan dogara akansa har ya bani ƙwarin guiwar sake bashi dama a karo na biyu bayan abinda ya faru. Ya gwada mun halayen
ni da kaina na yarda zuciyar dake cike da so ba zata aikata irin su ba abu mafi muni ya ci amanata a bayan ido na yana mu'amala da macen banza sannan ya tozartani akan hakan har mahaifiyata yayiwa zagi mafi muni kuma dukda haka nake jin zan iya yafe masa
na cigaba da rayuwa dashi.
Ƙ
asa na durƙushe na sake fashewa da kuka ina nanata "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Tabbas ina cikin masifa ni kaina na sani ta yaya wanda ya aikata mun irin wa
ɗ
annan zunuban zan cigaba da dakon soyayyar sa a raina?
Muryar Mama naji a kaina tana cewa
"Halima wai ba zaki ko duba ƙananun yayanki kiyi tunanin halin da zasu shiga idan babu ke ba kin dage lallai sai kin ja wa kanki ciwon da zai kashe ki ko?" Ta fa
ɗ
a tana kallo na, ban
ɗ
ago ba sai kukan da na cigaba da yi
, tayi ƙaramin tsaki ta ce
"Mu'azzam yana da uzuri kin zaka ya tsayar dashi ya ce ya kaiki idan ba zakije ba ki fita ki gayawa Abba ya sallame shi ya tafi sabgar sa dan Allah"
"Mama kin dena so na, kwata kwata yanzu kin dena damuwa da abinda ya shafe
ni kenan idan ma na mutu yarana ne ka
ɗ
ai suka rasa banda ke" na fa
ɗ
a cikin kuka. Tayi ƙaramar dariya tana nufar ƙofa tace
"Mutum kuwa ya ta
ɓ
a haifar
ɗ
a a cikin sa yace ya dena sonsa Halima? Ke
ɗ
in ce ai kin zama gomnati ba'a miki kutse yanda aka dama d
a nace yaranki kuma kinga ai su ke ka
ɗ
ai gare su ni kuwa Alhamdulillahi ku hu
ɗ
u Allah ya bani dama kuma da
ɗ
in haihuwar da yawa kenan idan wani bai faranta maka ba wani zai saka ka farinciki. Ni dai idan ba zakije ba kije ki fa
ɗ
a masa dan Allah ya sallamar
mun yaro ya tafi dan shi yana da abubuwan yi da zasu taimaki rayuwar sa".
Wato ni ce wadda bata da abinyi da zai taimaki rayuwata? Haka nan na haƙurtar da kaina na saka kaya ban ko nemi mai ba balle aje ga batun turare ko in yi kwalliya, sai sa na gama
shiryawa kuma sannan na tuna ai Khaki ya kamata na saka kuma ban taho dasu ba suna can gidan Bilal.
Har raina naji da
ɗ
i dan dole ai yanzu a fasa fitar, falon na fito, ina bu
ɗ
e ƙofa muka ha
ɗ
a ido da Abba dake tsaye da alama kuma ni yake jira. Kamar muna
fuka sum sum na zube a ƙasa murya ba amo na shiga gaishe shi, bai amsa ba sai cewa da yayi cikin dakewa
"Tashi ku tafi".
Nayi diriri a tsugunne ina ji Mama na cewa
"Da dai ta karya ko?"
"Idan sun dawo sai ta karya yanzu Mudassir ya kirani mutumin y
ana ta masa waya".
"Sai ku wuce ku tafi ai" Mama ta fa
ɗ
a, na miƙe kamar kazar da aka tsamo daga ruwan zafi na nufi ƙofa Abban ya dakatar dani yana cewa
"Ina uniform
ɗ
in?"
"Suna can gidan ai" na bashi amsa ina kallon ƙasa. Da hannu ya mun alamar mu
je, Mu'azzam yayi caraf ya ce
"Bafa zasu barta ta shiga a haka ba yanzu doka na aiki ko colored hijan ba'a shiga dashi secretariat balle taje musu da kayan gida, kalli shigar da ta yi ga fuskar ta duk a kumbure
ɗ
auka za suyi ma mabaraciya ce".
"Kuma da
i? To sai ku bari sai gobe ai a cigita ko a cikin unguwa ai ba za'a rasa masu service
ɗ
in ba su bata aron uniform
ɗ
in kan ta
ɗ
inka wani" Mama t fa
ɗ
a, sanyi na ji har raina sai dai kuma murnata ta koma ciki jin Abba ya ce
"Tunda uniform
ɗ
in makaranta ne
da zaki ce ta aro? Su biya ta can gidan ta
ɗ
akko ko babu muƙulli a hannunki?" Ya ƙarasa yana kallona. Yau
ɗ
in ganinsa nake wani daban kamar ba Abba na mai yawan fara'a da wasa da dariya ba, da sauri na
ɗ
aga masa kai alamar akwai kafin na juya cikin
ɗ
aki n
a
ɗ
akko muƙullin dan yana ajiye dama a kan mudubi.
Har muka isa layin gidan ci kanki Mu'azzam bai ce mun ba nima kuma tawa ta ishe ni tunda na ha
ɗ
a kai da window ban ko motsa ba sai da naji ya tsaya na duba na ganmu a ƙofar gidan.
Karki
ɓ
ata mun lok
aci Malama" ya fa
ɗ
a yana wani
ɓ
ata rai kamar shine gaba dani, haka nan na ringa jin wani iri a jikina. Na kalli layin daga farko har ƙarshe ina tuna ranar da na bar gidan. Sammani mai gadin gidan Maman Yusuf ya taso da sauri gani na, dole na ƙago murmuyna
ɗ
ora akan fuskata sanda muke gaisawa ya ce
"Kin dawo Hajiya?"
"Abu nazo
ɗ
auka dai amma dan Allah karka gayawa su Maman Yusuf na zo dan sauri nakeyi ba zan samu damar shigar musu ba" na bashi amsa. Yana shafa kai ya ce
"Ai bata nan ma Hajiyar tana Umar
ah, Amarya kuma ai ta bar gidan kin san Alhaji ya ƙara aure shine ta tayar da rigima har dai sai da ya saketa yau kwanata hu
ɗ
u da tafiya ita Hajiya tana can Saudiyya ma duk bata san meya faru ba".
"Allah ya rufa asiri" na fa
ɗ
a ina zura key a jikin ƙofa
har cikin raina kuma banji da
ɗ
in sakin Maman Khadija da ya ce anyi ba, na tuna yanda suka ringa kirana a waya suna bani baki akan nayi haƙuri na dawo aure duk zaman haƙuri akeyi dan duk a zaton su da sauran yan unguwa sakina Bilal yayi ashe itama nata saki
n na tafe.
Ganin motar sa ajiye ya saka nayi turus dan ban zaci zamu iya samunsa a gidan ba musamman tunda yau
ɗ
in akwai aiki kuma lokaci ya fara ja dan sha
ɗ
aya har ta gota. Ji nayi