Showing 177001 words to 180000 words out of 287295 words

Chapter 60 - KURA A RUMBU COMPLETE

ki zauna ki lalata rayuwarki a banza ba zaki gyara gobenki ba?"

Da s

auri na kalle shi jin abinda ya fa

ɗ

a na ce

"Ni fa Uncle aure na bai mutu ba". Ina kallo Mama ta jijjiga kai irin na zallar takaici shi kuma ya ce

"Oh har kina da bakin cewa aurenki bai mutu ba? Toh zaman uban me takeyi kusan wata biyu a gida?" Ya ƙarasa

yana kallon Mama. Hannu biyu ta watsa ta ce

"Gaka gata ƙila kai tunda tana ganin kanka da gashi ta gaya maka zaman me takeyi tunda mu da ta raina ba yanda bamuyi ta girma da laluma ta fa

ɗ

a mana mai ya faru ta taho gidan ba amma tace babu komai"

"Aa w

annan kuma laifinku ne Anty, ai ƙarya ne wlh yarinya ta taho gida sama da wata ba wani ƙwaƙƙwaran dalili ni duk

ɗ

auka ta ya saketa ne kuma abinda yasa kika ga ban ko yi miki maganar ba saboda naga babu amfani ne ko yanzun LGI

ɗ

in ne ya kirani dan tuni an t

uro da relocation list har anyi posting nasu dake nayi masa maganar ta da in da nake so a kaita ya kirani akan bafa ta je ba har yanzu shiyasa ma kika ganni yanzu. Kuma shi Yaya Aminun ya zuba muku ido take ta zama bai ce komai ba?"

"Toh mai zai ce Muda

n? Ita me auren an tambayeta tace babu komai shi kuma bai biyo baya ba haka babu wani nasa da yazo toh ta ina zamu san meya faru?" Mama ta sake fa

ɗ

a, ni dai kaina yana ƙasa ina jinza ya kira sunana na sake sadda kai ƙasa sai da ya buga mun tsawa kafin na

ɗ

ago da sauri ya nuna ni yana cewa

"Kar kiga kin girma ko kin haihu wlh dukan tsiya zan miki Halima kuma banga uban da zai ce dan me ya saka ba, tun muna shaida juna dake ki fa

ɗ

a mun mai ya saka kika taho gida yanzu ba sai anjima ba". Kuka na fashe dash

i bayan da naja baya daga kusa dashi dan na san dukan daya ambata zai mun tsaf zai aikata dan zuciya ce dashi kamar kuturu duk cikin ƙannen su Mama yafi su zafi ba kuma ya wasa damu dama shiyasa muke shakkar sa sosai. Tsawa ya sake bugamun bayan daya miƙe

tsaye da alama neman madoki yakeyi, dai dai nan Anty Labiba da Mama Fauziyya sukayi sallama da gudu kuwa na nufi Mama Fauziyya na rungume ta ina sake fashewa da kuka ta

ɓ

oye ni a bayanta tana tambayar mai ya faru nan kuwa ya fara zazzaga fa

ɗ

a akan me zan z

o gida tsayin lokacin nan na sakina akayi ba kuma naƙi fa

ɗ

ar zuwan me nayi wlh zai mun dukan tsiya idan ban bu

ɗ

e baki nayi magana ba.

"Kai da

ɗ

i na da kai saurin hasala Mudassir banda haka duk maganar ai bata wuce ayita a zaune ba" Mama Fauziyya ta fa

ɗ

a,

Mama ta ce

"Ai kuwa magana ta wuce ta sulhu dan tuntuni nake bin yarinyar nan akan ta fa

ɗ

a mun mai ya faru tun hankalina yana tashe da lamarin har na haƙura na fawwalawa Allah tunda naga alamar zan

ɗ

orawa kaina damuwa ne a banza alhalin wacce nakeyi akan

ta ita bata damu ba toh wlh nima yanzu na gaji, cikin biyu dole ayi

ɗ

aya. Ko dai idan sakinta yayi ta fa

ɗ

a mu san zaman me takeyi ko kuma ta tattara ta koma amma na gaji da zama da ita a haka kullum ina kallonta ina jin

ɓ

acin rai".

"Hmmm mu dai anayi mu

na jin da

ɗ

i" Anty Labiba ta fa

ɗ

a tana zama akan kujera irin ba abinda ya shafeta

ɗ

in nan, banda kuka ba abinda nakeyi, sai da Uncle Mudassir ya mun tatas kafin ya tafi akan kada na kuskura ya sakw dawowa bai tarar da

ɗ

ayan biyu ba, ko dai in koma ko kuma y

a samu tabbacin zaman yanci nakeyi. Ba abinda ya sake

ɗ

aga mun hankali irin yanda Mama take nanata ita ta gaji Mama Fauziyyar da take kareni sai in tattara na bita amma ba zata cigaba da zama dani alhalin bata san ina ma saka gaba ba. Duk sai suka sake jag

ula mun lissafi ga danuwar da na tashi da ita ga kuma wata sabuwa data

ɓ

ullo na ringa jin inama ban biyewa hu

ɗ

ubar Hansa'u ba na saurari Bilal ƙila da na bashi dama zai zayyana mun nadamar sa ya kuma nemi yafiyar tawa idan yaso sai in yanke hukuncin da nak

e ganin ya fi mun yanzu gashi nan a garin jan aji ya tsinke gidan ma kuma zasu tasoni a gaba in rasa ina zan tsoma raina.

Ɗ

aki na koma na cigaba da kuka sai da nayi mai isata kafin na haƙura na wanko fuskata na koma na zaune bayan na

ɗ

auki wayata zuciy

ata na ayyana mun na kirashi, tarin missed calls na gani da number da aka kirani da ita

ɗ

azu zai text guda

ɗ

aya,

"Hafiz ne abokin Mijinki Bilal, idan kin samu lokaci ki kirani akwai abinda nake so mu tattauna" abinda saƙon ya ƙunsa kenan. Na natata karant

a saƙon yafi sau biyar a raina ina mamakin wace magana ce Hafiz zai tattauna dani kuma mai muhimmanci kamar yanda ya ce?

Tunani na shigayi a zuwan Matarsa ko akwai wani abu dana fa

ɗ

a mata da bai kamata taji ba amma ban tuna ba, ajiye wayar nayi kawai b

a tareda na kira shi

ɗ

in ba kamar yanda ya buƙata dan ni banga dalilin hakan ba. Bacci ne ya kwashe ni ina tsaka da tunanin neman mafita, sanda na farka gari har yayi duhu alamar magriba ma ta wuce na ringa salati in mamakin wane irin bacci nayi haka tun a

zahar kuma ace babu wanda ya tashe ni da akayi la'asar da ga magriba ma lallai dagaske da Mama tace ta gaji da zamana ba wasa takeyi ba tunda gashi ko a jikinta bata ma ko yi tunanin mutuwa nayi ba ba wanda ya leƙo ni. Hawaye suka

ɓ

alle mun ina wanka ina k

uka har na gama sannan nayo alwala ina jin cikina kamar zai ha

ɗ

e da bayana tsabar yanda yunwa ta gama rarakeni, daƙyar nayi sallolin da suka wuce ni kafin na fito kai tsaye na fa

ɗ

a kitchen neman abinda zanci.

Mama da Zainab na aikin ƙarasa abincin dare

ko kallo na batayi ba sai Zainace ta ce

"Kin tashi Yaya Halima? Tun

ɗ

azu nake leƙo ki naga kina jin da

ɗ

in baccin shiyasa ban tashe ki ba". Ban amsa ta ba na

ɗ

ebi abinda na gani na fita, bayan mun gama ci tareda Sharifa ina shirin na koma

ɗ

aki tun kafin Ma

ma ta fito falon Mu'azzam ya shigo, ba yabo ba fallasa ya ce mun

"Kina da baƙo yana falon Abba".

Kallon za nayi kafin cikin

ɗ

aga murya na ce

"Wane irin hauka ne haka ni zaka cewa ina da baƙo ko ka manta matar aure ce ni?"

"Wai matar aure" ya fa

ɗ

a y

ana nuna ni kafin ya tuntsure da dariya harda buga ƙafa ya wuce yana cewa

"Idan zaki tashi kije Malama ki wuce kar ki

ɓ

ata masa lokaci".

Miƙewa nayi da zummar na bishi in ji ba'asin akan me da mutunchi na da kuma aure na har wani zai zo gurina a shigo

dashi har falo saiga Abban ya shigo, ba yabo ba fallasa shima ya kalleni ya ce

"Ibrahim bai gaya miki kina sa baƙo ba ne?"

"Abba ya za'ayi da aure na ace wai wani yazo gurina in fita?" Na fa

ɗ

a ina rau rau da ido kamar zan fasa kuka, sama sama yace

"

Bana son sakarci Halima ki wuce kuma tun kafin ranki ya

ɓ

aci". Sum sum na wuce domin na fi kowa sanin fushi ba

ɗ

abi'ar Abba bace har kuma idan ransa ya

ɓ

aci to fa baya yi da sauƙi.

Turus nayi a bakin ƙofa ganin baƙon, Hafiz ne abokin Bilal. Na ƙarasa c

iki da ƙaramar sallama na samu kujera can nesa na zauna kafin ma shiga gaishe shi ya amsa cikin kulawa yana tambayata yara na gaya masa Al'amin yana can gidan Anty Labiba Sharifa kuma tana ciki.

"Kiyi haƙuri Halima kin ganni ba tareda kinyi mun izini ba

, na yi ta jiran martaninki toh amma gaskiya ina da

ɗ

an uzuri ne wanda kuma ina son mu tattauna kafin na wuce dan ban san ko har zan dawo ba tareda lokacin buƙatar hakan ya wuce ba" ya fa

ɗ

a, ni dai kaina yana ƙasa ya cigaba da cewa

"Kiyi haƙuri Halima,

na san zaki iya cewa menene nawa da shiga cikin maganarki da Bilal amma ki sani ina da dalilin yin hakan, na san kin fi kowa sanin kusancin da yake tsakanina da Bilal. Allah ne ya ha

ɗ

a jinina da shi kuma Allah shine shaida ina jin sa a raina tamkar wanda

alaƙar jini ta ha

ɗ

a mu shiyasa ban ta

ɓ

a ƙyashin nayi masa wani abu ba, a zaman da nayi da Bilal na karanci wasu halayensa wa

ɗ

anda na

ɗ

auka a matsayin tawaya da kowanne

ɗ

an adam yake dashi dole idan ya zamo ya cika ta wani

ɓ

angaren ta wani gefen kuma za'a s

ame shi da kuskure dan haka na kar

ɓ

e shi a yanda yake ina kuma yi masa uzuri a duk in da ya kuskure domin nima na sani dole akwai ta inda nake da gi

ɓ

i sai dai ko kusa ban ta

ɓ

a tsammanin Bilal zai aikata irin abin nan ba.

Kiyi haƙuri Halima ni ne silar d

a har Bilal ya san Jalilah sai dai bani da wata masaniya ta ƙulluwar wata alaƙa a tsakanin su domin daga shi har ita sun rufeni akan haka. Jalilah Ex

ɗ

ina ce kuma dalilin da ya kawo ru

ɗ

ani tsakaninki da Bilal shine silar rabuwar mu da ita har na fasa auren

ta bayan har an yi mana baiko. Yanda kike son Bilal haka Jalilah take so na, albarkacin wannan soyayyar ta saka kuma duk yanda na so na yakice ta daga rayuwata taƙi fita na raga mata har muka cigaba da mu'amalar gaisawa.

Ban

ɓ

oyewa Bilal komai akan Jali

lah ba tun a sanda ya fara ganinta har yake tuhunata akan me yasa naƙi aurenta bayan a nasa ganin tafi Suhaila komai na ya mace, na

ɗ

auka abinda na gaya masa akanta zai saka ya hankalta dukda ban ta

ɓ

a kawo cewar wata mu'amala zata iya shiga tsakaninsu ba s

ai dai abin takaici hakan ya faru kuma ya rufeni har ta kai a silar ta yana shirin rusa rayuwarsa ta hanyar rabuwa da abubuwa masu muhimmanci ciki harda ke da kuma aikin sa.

Bazan cika ki da surutu ba amma Halima ina so ki san da cewa duk wani abu da k

ike tunani akan Bilal da Jalilah na sani, na da

ɗ

e ina masa addu'ar gane gaskiya tun kafin ubangiji ya kawo irin wannan lokacin da asirinsa zai fasu, kada kiyi tunanin shirun da kikayi yana nufin kin rufa masa asiri domin shi da kansa ya

ɗ

aurawa kansa ƙarar

rawar da zata yayata sirrinsa har ya isa ga kunnuwan kowa. Jalilah ba zata ta

ɓ

a yarda da cin amanar da yayi mata ba bayan ta gama

ɓ

ata lokacinta ta kuma kashe ku

ɗ

inta akansa da tunanin zai aureta sannan ya zagaya yayi amfani da ku

ɗ

in ta ya auri wata hakan

ba zai ta

ɓ

a yuwuwa ace ta ƙyale shi ba".

Kusan daga iya in da na dena fahimtar duk wasu maganganu daya cigaba da fa

ɗ

a kenan, da farko na cika da mamakin yanda yace ya san komai dake tsakanin Bilal da Jalilah sai kuma maganar da na tsinta ta ƙarshe ta go

ge mun hadda ta kuma jefani a

ɗ

imuwa ko in ce gushewar hankali na wucin gadi cewar da yayi Bilal yayi amfani da ku

ɗ

in Jalila ya auro wata?

Har idan dagaske ta silar sa Bilal ya san Jalilah kenan sai bayan ya aureni hakan ta faru tunda ina gidan Bilal su

ka ha

ɗ

u da Hafiz hakan yana nufin bani ce wacce aka auro da ku

ɗ

in Jalilah ba kenan to me yake nufi? Aure Bilal ya ƙara ko me?

[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*

*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Mary

amfarouk01*

*Wattpad @MaryamahMrsAm*

*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*

*Ku

ɗ

in karatu yana wakiltar mutum

ɗ

aya ne, kiji tsoron Allah karki

ɗ

auki hakkina ta hanya

r fitar mun da littafi*

*KURA A RUMBU littafin ku

ɗ

i ne, a biya naira 800, biya a asusun*

*1840175439*

*Access bank*

*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 41*

A yayinda muke shirin kammala wannan littafi, idan kin

san kina karantawa ba tareda kin siya ba kiyi ƙoƙari ki sauke nauyi domin babu lallai in yafe haƙƙina. Account details suna sama

🙏🏽🙏🏽

A hankali na bu

ɗ

e ido na jin saukar abu mai sanyi a goshi na, ganin na bu

ɗ

e idon ya saka Mama janye hannunta, gani

n da tayi ina shirin sake komawa baccin ya saka ta ce

"Da dai kin tashi haka nan kuma ki ƙarfafa jikinki tunda dai zazza

ɓ

in ya sauka". Na yunƙura na zauna ina cije baki saboda kaina daya sara, dukda zazza

ɓ

in da rafke ni ya sauka amma har yanzun bana jin

ƙ

warin jikina. Ban

ɗ

aki ta shiga bata jima ba ta fito tana cewa

"Ga ruwa can na tara miki kiyi wankan Zainab zata kawo miki abinci" daga haka ta juya ta fita na rakata da ido ƙauna da kuma tausayinta suna sake ratsani. Allah sarki iyaye masu da

ɗ

i duk ind

a akaje aka dawo su

ɗ

in dai ko sun yi fushi a hakan zasuyi haƙuri su kar

ɓ

e ka. Jiya ta gama nanata ta gaji da zaman da nake gabanta amma hankalinta yafi na kowa tashi da yanayin da na shigo gidan bayan da na baro Hafiz.

Na runtse ido na saboda yanda tu

na Hafiz

ɗ

in ya dawo mun da zantukansa da sukayi matuƙar ki

ɗ

imani ha

ɗ

i da hargitsamun tunani, hawaye suka

ɓ

alle mun, dukda har yanzun na kasa gasgata maganarsa wai Bilal yayi aure amma tunanin hakan ka

ɗ

ai da nakeyi ace da gaske ne ji nake zuciyata kamar za

ta ƙone saboda zafin da takeyi mun, ba zan ta

ɓ

a iya jurar ganin wannan baƙin cikin ba wata mace a rayuwar Bilal sai kawai na ha

ɗ

e kai da guiwa tareda fashewa da kuka mai sauti harda shassheƙa.

Ƙ

arar ruwa dake ta zuba ya saka na tashi daƙyar bayan da na

ha

ɗ

iye kukan nayo wanka ha

ɗ

i da alwala na fito, kan gado na sake komawa na zauna, gaba

ɗ

aya komai ya sake jagulemun na sake komawa yanayin da nasha wahala kafin na samu kaina daga cikin sa. Saƙe saƙe kala kala zuciya ta ringa kawo mun, daga ƙarshe na yaƙi

kaina ta hanyar tashi na

ɗ

ora dogon hijabi kan towel

ɗ

in dake

ɗ

aure jikina na shiga jera nafila duk da cewar bayan la'asar ne magriba ma ta gabato lokacin.

Bayan sallar isha'i ina kwance a ƙasa, duk yanda naso na mayar da hankali na kan lazumin da nake

yi na kasa gaba

ɗ

aya tunani na ya tafi akan son sanin haƙiƙanin gaskiyar abinda Hafiz ya fa

ɗ

a mun. Idan har da gasken ne Bilal yayi aure toh wa ya aura? Ko Jalilan da suka gama sheƙe ayarsu a titi ya aura? ko kuma wata daban?

Zuciya ta raya mun 'ko kuma

duniyar sa ba? Ko wacce ya kaini gidansu gaisuwa. Duk a rana

ɗ

aya na sansu ranar da na banka

ɗ

o sirrinsa da Jalilah ƙila

ɗ

aya daga cikinsu ya aura. Sabbin hawaye suka

ɓ

alle mun, bai ko bani damar yi masa tambayoyi da yawa da suke cunkushe cikin zuciyata ba

kafin na baro gidan sa har a yanzun kuma daya dawo daga yanda ya

ɓ

ullo na fahimci baya buƙatar warware ƙullin baya kawai so yakeyi mu

ɗ

ora sabon babi.

Da hannu biyu na rufe fuskata ina jan kuka, na rasa tunanin daya kamata nayi, mai yasa Bilal zai mun h

aka? Duk haƙurin da nayi duk juriyar da nayi akan lamuransa lokaci

ɗ

aya ya rasa irin sakayyar da zaiyi mun sai wannan?

Jin ana ƙwanƙwasa ƙofa ya saka na shiga goge fuskata da sauri dan zaryar da Zainab take mun na san da wahala idan ba CID Mama ta sakata

ba, kuma daga yanayinta tun jiya da yanda Abba da kansa ya ce na fita gurin Hafiz

ɗ

in na tabbatar ma abinda na jima ina

ɓ

oye musu ya rigada ya bayyana ma'ana ya fa

ɗ

a musu komai akan Bilal da Jalilah ga kuma wata sabuwa data

ɓ

ullo yanzu.

Ɗ

aga murya nayi

na ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login