Showing 180001 words to 183000 words out of 287295 words
ta shigo bayan da na tashi zaune na jingina da Gado. Ganin Abba ya saka zuciyata ta shiga bugawa da sauri da sauri, haka nan ban tuna sanda Abba ya shigo
ɗ
akina ba tun ma zamanin yammatanci balle yanzun na san dole abu ne me muhimmanci ya kawo shi. K
an bedside drawer ya zauna ba yabo ba fallasa yana amsa gaisuwar da nake masa, muka yi shiru kafin can ya ce
"Kin san me yasa na biyo ki har
ɗ
aki?" Na girgiza kai alamar aa, ya ce
"Saboda ki gane muhimmancin maganar da nake so mu tattauna dake". Bugun
da zuciyata keyi ya saka tsananta har wani
ɗ
umi numfashina ya
ɗ
auka gaba
ɗ
aya a tsorace nake ban san wace magana zai mun ba dukda bana raba
ɗ
aya biyu akan Bilal ce amma me zai ce mun?
"Nasan baki manta ba ni nayi tsaye na goya miki baya kika auri yaron
nan dukda yanda mahaifiyarki da yan uwanta har ma da nawa yan uwan suke ganin rashin dacewarki dashi. Ki sani, abu biyu zuwa uku na duba da har na amince da aurenku. Na farko, a iya binciken da nayi akansa ba'a same shi da wani mugun hali wanda zai saka a
ƙ
i bashi aure ba, dai dai gwargwado ya samu shaida ta mu'amala kuma ana kyautata masa zato akan addininsa. Abu na biyu soyayyarki gare shi, yanda kike mu'amalantar sa ya tuna mun yanda muka rayu da mahaifiyarki a lokacin da ban ma kai shi ba domin ni sanda
na aureta banida da ko tartibiyar sana'a amma a hakan ta ƙaunace ni har kuma Allah ya kawo mu matsayin da muke kai a yanzu.
Na kyautata masa zato kuma son da nake miki da burin ganin na samar miki da farinciki a rayuwarki ya saka na amince na bashi au
renki bisa kyakkyawan yaƙinin zai riƙe mun ke amana amma baki
ɗ
auki dogon lokaci a gidan aurenki ba na fara dana sanin biyewa zuciya, a ƙoƙarin son samuwar farin cikinki har hakan ya rufe mun ido na kasa hasaso idan aka samu akasi wani hali rayuwarki zata
shiga?
Duk da haka ban sare ba, na cigaba da yi muku addu'a na kuma ringa tallafa miki a ganina raguwar
ɗ
awainiyar zata taimaka gurin samun dai daito a zamantakewarku musamman tunda na fahimci halayya da kuma
ɗ
abi'ar mijin da kika za
ɓ
i rayuwa dashi. Ko
da baki ta
ɓ
a zuwa kin fa
ɗ
i laifin sa ba amma komai a bayyane yake, kuma wannan hujjar na riƙe a duk sanda mahaifiyarki ta so yin bore ko kawo hargitsi cikin zamanki da shi na kan nusassheta da cewar a gurinta ne take ganin gazawa ko matsi a zaman da kikeyi
amma ni a guri na lafiya kike zaune domin baki ta
ɓ
a zuwa kin kawo ƙara ko kin fa
ɗ
awa wani damuwarki ba na kuma san ba dan baki da damuwar bane sai dan halin zurfin ciki da kuma soyayyar dake wahalar dake kin kuma yarda zaki rayuwa dashi cikin kowanne irin
yanayi sa'annan akwai nauyi da gudun kar ayi miki dariya sanin kowa sai da ya ce miki kar kiyi kikace kinji kin gani.
Duk da dai da fari na
ɗ
auka rashin wadata ne sanadin abubuwan da suke wakana a tsakaninku shiyasa ban ta
ɓ
a cewa komai ba nake kuma iy
a bakin ƙoƙari na gurin ganin na samar miki da abinda ya gagara baki sannan kuma na hana mahaifiyar ki ko wani nata duk sanda sukayi yunƙurin
ɗ
aukar wani mataki akan zamantakewarku amma daga baya idona ya bu
ɗ
e na kuma fahimci komai, tsantsar son kai da mug
unta ce kawai take damun sa ba wai babu bace.
Ina so san cewa ke kike son Bilal Halimatu kuma ko da ace yana sonki to ki sani bai kai ko kwatan soyayyarki gare shi ba. Iya zamanki a gidan nan daga zuwanki zuwa rashin lafiyar da kikayi kawo yanzu ta isa
hujjar da zakiyiwa kanki Hisabi ba tareda wani ya ce miki komai ba, idan ba dan na samu tabbaci daga wanda ba zai mun ƙarya ba da banzan ta
ɓ
a yarda da cewar da igiyar aurensa akanki yayi miki irin wannan tozarcin ba".
Sai lokacin na
ɗ
aga kaina na kalle
shi jin kalmar tozarci daya fa
ɗ
a idanuwana basa ko gani da kyau saboda hawayen da suke cikinsu, ya gya
ɗ
a mun kai cikin tabbatarwa ya ce
"Babu wani namiji da yake ganin matarsa da ƙima da zaiyi kwatankwacin abinda Bilal ya aikata miki. Da kansa ya
ɗ
akko
ki ya kawoki gidan nan saboda ya nuna miki cewar ke bakya gabansa, a sanadin sa kika kusa rasa rayuwarki kuma har kikayi jinya kika gama shi ki wani nasa babu wanda ya tako yazo yaga ya kike sai surutu da maganganun da suka ringa yawo da su suna fa
ɗ
an abu
buwa marasa da
ɗ
i akanki, duk wannan bai isa ba tunda ya fahimci har yanzun kina yawo cikin duniyar mafarkinki shiyasa ya
ɗ
aura aure abunsa da wata.
Kin san duk me yasa na tsaya ina miki wannan dogon bayanin kafin na fa
ɗ
a miki ainihin abinda ya kawo ni?"
Cikin kuka na ce
"Aa Abba" ya gyara zama ya ce
"Saboda na lura baki da tunanin kanki ba kuma kya gane komai sai abinda zuciyarki ta aminta dashi. Tuntuni na tsammaci ganin sauyi tattare dake amma akasin haka na lura a maimakon sauƙi kullum al'amuranki
ƙ
ara lalacewa sukeyi. A cikin zuciyarki nan na tabbatar duk lokacin nan kina jiran Bilal ya zo ya lallasheki ya fa
ɗ
a miki maganganu dai dai da wa
ɗ
anda kike so kiji daga nan ku shirya ku koma shiyasa kika za
ɓ
i ha
ɗ
iye baƙin cikinki ke ka
ɗ
ai kika ƙi gayawa ko
wa dan kar hakan ya saka a baki shawarar ki haƙura dashi ko?"
Kai na girgiza masa alamar Aa, ya sake cewa
"Eh mana, Tunaninki kenan saboda har yanzu ƙwaƙwalwarki bata hasko miki illar rayuwar da kike ciki ba. Halima babu iyayen da zasu so yar su tayi a
ure ta dawo sai dai idan abun yafi ƙarfin su domin burin kowanne iyaye ne yayansu suyi aure a inda zasu rayu cikin aminci da walwala da kuma mutuntaka wanda gaba
ɗ
aya kika rasa. Ko wanda bai sanki ba kuka ha
ɗ
u a hanya ya kalle ki in dai maganar nutsuwa ake
yi ta bayyana ƙarara baki da ita. Ko shekara talatin baki cika ba kin
ɗ
orawa kanki hawan jini harda kumburin zuciya akan namijin da kina raye ma ya wofantar dake ya auri wata balle kuma ki kashe kanki saboda dashi bana zaton ko a addu'a zai ringa tunaki.
Ba shawara nazo baki ba, kamar yanda na tsaya tsayin daka na ha
ɗ
a ki da shi haka yanzu nake so ki rama mun nima ki faranta mun zuciya ta hanyar rabuwa dashi. Da na so na kira shi da kaina ya bani takardar sakin sai dai kuma na tuna bani da sauran mutunc
hi a idon sa ko na kira shi ma ba zuwa zai yi ba tunda mun sha ha
ɗ
uwa a ƙofar gidana ma ya kalle ni na kalle shi ya wuce ba tareda ko ci kanka ya ce mun ba balle kuma in
ɗ
aga waya na kirashi ai sai abunda kuma na gani. Dan haka ko ki kirashi ko ma duk ta y
anda kika san saƙo zai fi saurin isa ki gaya masa kada ki kurkura satin nan ya ƙare kina cigaba da amsa sunan matar sa a cikin gidan nan".
Tunda ya fara maganar kuka na ya tsaya tsak, yanda kasan zuciyata zatayi tsalle ta fito haka naji sanda ya ce wai
Bilal ya rubuto takardar saki ya kawo mun, ganin ya miƙe tsaye alamar ya gama magana daƙyar na lalubo yawu na jiƙa maƙoshi na kafin na samu na fizgo maganar data tsaya mun a wuya na ce
"Abba amma da wasa kake yi?" Murmushin takaici yayi kafin ya ce
"Dama
ina wasa dake ne Halima?" Daga haka ya saka kai ya fita ba tareda ya sake ce mun komai ba.
Zumbur na miƙe kamar wacce aka tsikarawa Allura na shiga zagaye
ɗ
akin ina nanata Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, nayi zagaye ya kai hamsin kafin na zube gef
en gado lokaci
ɗ
aya na fashe da kukan rashin mafita. Ya Abba zaiyi mun haka? Na
ɗ
auki tsayin lokaci ina kukan kafin na fahimci hakan ba zai sama mun mafita ba, falo na fito, Mama, Mu'azzam da Imam suna zaune gabansu ƙaton tray da gasasshen kifi suna ci sun
a hira cikin nisha
ɗ
i irin su basu da wata matsala a rayuwarsu. A gaban Maman na zube na kama guiwarta lokaci
ɗ
aya na fashe da kuka har jikina yana jijjiga tsabar yanda nake janyo kukan tun daga can ƙasan raina, ta sauke Sharifa daga kan cinyarta jiki na ts
uma itama ta kamoni tana cewa
"Menene?" Ban iya ce mata komai ba in banda kukan dana ƙara ta hanyar
ɗ
aga murya, Mu'azzam ya ce
"Wlh sai Allah ya saka mata wannan fa
ɗ
uwar gaban da kike sakata, banda tsabar iskanci kawai idan kika bushi iska sai ki hau
kuka duk ki
ɗ
agawa mutane hankali ke ko shekarunsu bakya dubawa? Ai gasu nan kema kin haifa idan da da
ɗ
i abinda kikeyi zaki ji wata rana" yayi tsaki ya miƙe zai bar gurin dai dai nan Abba ya shigo falon, ban yarda na kalle shi ba ina jin sa yana cewa Mu'az
zam
ɗ
in
"In sha Allahu yaranta ba zasu mata haka ba ita ma
ɗ
in da takeyi mun yafe". Ya ƙarasa ya zauna kan kujera ban saki Mama ba haka ban daina kukan ba sai da ya daka mun tsawar da tunda nake ban ta
ɓ
a jin ko wani can a waje yayiwa ba balle mu
ɗ
in, cik
in tsawa yace
"Saketa ki tashi daga nan sakaryar banza kawai wacce bata san ciwon kanta ba" ba shiri na saketa na mataa gefe na ha
ɗ
e kai da guiwa kamar marainiya na cigaba da kuka, Mama ta ce
"Wai me ya faru ne Abba wlh duk ta tsinkar mun da zuciya".
"Saboda na ce ta kar
ɓ
o takardar sakinta gurin wancan yaron ko?" Ya bata amsa, sai ta dafe ƙirji ta ce
"Kai wa ya aike ka?" Ya bita da kallon mamaki da kuma rashin fahimta sai ta ce
"So kake ta saka ka a bakin duniya tace kai ka kashe mata aure? Ai da
kayi shawara dani da baka fara wannan
ɗ
anyan aikin ba". Tsaki yayi ya miƙe yana cewa
"Ni dai na fa
ɗ
a mata, kuma dama gobe in Allah ya kaimu ta wuce ta kar
ɓ
o posting letter ta idan ba haka ba wlh Halima zakiga other side of me wanda baki sani ba tunda naga
alamar sako sakon da ake miki ya saka yanda kika mayar da kanki shashasha kowa ma kike so ki mayar dashi haka" ya wuce
ɓ
angarensa. Mama ma miƙewa tayi bayan da tace
"Allah ya rufa asiri toh" Imam ko yanda ka san baya falon kifin sa kawai yake ci yana b
awa Sharifa, da yaga kukana zai cika masa kunne ma remote ya
ɗ
auka ya ƙara volume
ɗ
in Tv, haka na ja jiki na sake komawa
ɗ
aki na cigaba da kuka kamar wacce aka ce za'a fillewa kai gobe. Sai da na gaji kafin nayi shiru ina jan ajiya zuciya, ciwon da kaina y
ake mun kuwa ba zai mislatu ba har wani
ɗ
in
ɗ
in nake jin ƙara kamar ta agogo a cikin kan nawa.
Dare ya tsala kowanne mai rai dake da nutsuwar zuciya yana kwance yana bacci amma banda ni ina dai kwance akan gadon ina juyi daga wannan kusurwa zuwa waccen
na gagara bacci haka nan ƙwaƙwalwata ta kasa bani ha
ɗ
in kan da zanyi tunani mai ma'ana da zai sama mun da mafita gashi, da ina da tsarki ne ma sai inyi sallah ko zan samu nutsuwa. Ina tunanin firgici ne ya matso mun da period dan a lissafi sai nan da kusa
n kwana hu
ɗ
u zai zo amma
ɗ
azu ina shiga ban
ɗ
aki na ganshi.
Bansan me zanyi ba, umarnin Abba yayi mun tsauri, dukda cewar ni a karon kaina har yanzun ban yanke shawara dangane da yuwuwar cigaba ko ƙarewar zamana da Bilal ba na bar hakan ne tukunna har sa
i ni da shi mun zauna munyi magana ta gaskiya daga nan ne zan yanke hukunci akan abinda ya kamata nayi amma shi Abba kai tsaye ya yanke nasa hukuncin yanzu yaya ake so nayi?
Idan kuma ya zama duk abinda Hafiz
ɗ
in ya fa
ɗ
a ƙarya ne ko ma duk abinda ya faru
tsakaninsa da Jalilan setup ne fa tunda ai da bakinsa ya ce basu san ya sani ba toh ta ina ya sani kenan bibiyarsu yakeyi idan kuma haka ne dama akwai abinda yake so ya cimma shiyasa har yake binsu kenan?
"Amma kuma wace riba zai ci idan yayi hakan?" Ni
da kaina na jefawa kaina tambayar da bani da amsarta. A zahirance ma bani da wata hujja da zan jefa masa kowanne irin zargi domin Bilal bashi da wani abu da har zai saka mutum irin Hafiz yayi framing nasa. Kuma ko da ace da gaske shirin ne idan dama ba ha
lin sa bane ko yana so ai babu yanda za'ayi ya biye mata tunda babu inda naga alamar ta masa dole a cikin hirar su duk ba wannan bama ai da ba zai ha
ɗ
a ta da danginsa ba har tazo duba mahaifiyarsa da bata da lafiya.
"Ta yuwu ma ita ya aura tunda tana da
kyau kuma tana da ku
ɗ
i dama kuma ai ya ce shi baya tarayya da mutumin da ba zai ƙaru da shi ba" na fa
ɗ
a a fili. Sababbin hawaye ne suka
ɓ
alle mun na koma na kwanta ina jin ƙuna a ƙirji na, na ringa tuna fuskarta ha
ɗ
uwar mu a asibiti fara kyakkyawa mai diri
duk hassadar mutum bai isa ya kushe halittarta ba. Ji na ringayi tamkar numfashi na zai tsaya har saida na tashi zaune, abunda na tabbatar shi ake kira da kishi ya turnuƙeni, lokaci
ɗ
aya kuma hotunan waccen ranar suka shafe na kyakkyawar fuskar Jalilah da
nake gani, muryoyin da sukayi musaya suka shiga mun amsa kuwwa a kunne, hannu biyu na saka na toshe kunnuwana na fashe da kuka mai sauti.
BILAL
Hankalinsa ya kwanta yanzu saboda ya samu nutsuwa akan kokonton dake neman hargitsa masa lissafi akan Zula
iha. Dukda dama zuciyarsa bata yarda zai samu akasin abinda yake tsammani daga Zukaihan ba sai dai canjin halayyarta na lokaci guda ne ya bashi tsoro, amma zuwan da yayi jiyan da hirar da sukayi ya kwantar masa da hankali dan har haƙuri ta bashi sosai kama
r zatayi kuka akan
ɗ
aga masa muryar da tayi a waya. Sun da
ɗ
e suna hira sosai irin yanda suka saba, da zai tafi ya shiga suka gaisa da Ummansu, har ya miƙe ta dakatar dashi tana cewa
"Dama yan uwana ne sukayi magana akan suna so suje ganin gurin da zata
zauna". Kansa na ƙasa dan bala'in kunyarta yakeji har mamaki yake yanda bayajin nauyin Mamansu Halima irin yanda yakejin ma Umman Zulaihan.
"Dama zuwa wani satin nake so idan an ƙarasa gyaran gurin nayi magana je a gani" ya bata amsa, ta muskuta tana g
yara hijabinta tace
"Toh madallah, kasan da yake sune jikokin ya mace na farko ni a gidanmu da za'a fara aurarwa duk yayyena matan yayayensu maza ne shine fa kowa hankalinsa yana kan bikin nan, ga zancen kawo lefe ma kasan abunka da masu ƙaramin ƙarfi sai
anyi tanadi ya kamata idan za'a zo afa
ɗ
a da wuri saboda a tanadi abun tarbar baƙi, su dai na Nuratu sun ce Asabar ta sama nan da sati biyu kenan da kawo lefen da tariya duk rana
ɗ
aya dan ya
ɗ
auke ta ma sunje gurin tela an gwadata a
ɗ
inke zasu kawo abunsu.
To itan ma ya kamata kaga mu sani in kuma ku
ɗ
in za'a bayar ma duk kaga sai a san shirin da ake ciki" ta ƙarasa tana sosa kai kamar wata mara gaskiya.
Zama yayi sosai dan da a tsugunne yake ya ce
"Ai Umma munyi magana da ita tace kince ba sai anyi lefe
ba kawai ayi mata kayan
ɗ
aki da ku
ɗ
in". Yanda ta zaburo tace
"Inji ubanwa? Yaushe mukayi haka da ita?" Sai da abin ya bashi mamaki domin a iya saninsa da ita kullum muryarta a ƙasa take fuskarta washe da fara'a. Itan ma da sauri ta gyara zama bayan da ta
fahimci abinda tayi ta shiga kame kame tana cewa
"Na rasa yaushe Zulai ta koyi magana biyu, ni bamu ta
ɓ
a zancen lefe da ita ba, Mijin Nuratu dai da ya ce ko yayi mata kayan
ɗ
aki a madadin lefen to kuma yayyina suka ce Aa ai ba'a haka, za'a mata daidai
ƙ
arfin mu duk abinda bai masa ba daga baya ya sake mata toh ni dai iya zancen da nasan anyi kenan shine ta canza magana ashe ta