Showing 240001 words to 243000 words out of 287295 words
ci sa'a yana ta gurin dan haka ba'a wani
ɗ
auki lokac
i ba ya je ya same su.
"Gaskiya wa
ɗ
annan takardun ba namu bane" Lawyer ya fa
ɗ
a bayan daya gama dubasu. Alhaji ya tashi ya
ɗ
akko wata folder ya ringa fitar da original takardu na sauran shagunan da ba'a siyar ba yana miƙewa Bilal da Kamalu suna dubawa, ya
kwashe su ya mayar sannan ya
ɗ
akko photocopy ya ware su ya cire masa na ainihin shagonsu ya bashi yana cewa
"Kaga photocopy
ɗ
in original
ɗ
in da muka baka nan" ba wani dogon bincike Bilal da kansa ya gane banbanci ƙarara na takardun hannunsa da photocopy
wa
ɗ
anda akace sune wanda aka bashi. Duk kansa sai ya ƙulle, ya kuma tuna tabbas irin wa
ɗ
ancan aka bashi domin bai manta stamp
ɗ
in su da yake a kai ba wanda sai yanzu ya lura babu shi a na hannun nasa.
Alhaji Balarabe ya ce ya tafi da photocopy
ɗ
in san
nan a shirye suke domin su taimaka masa t duk inda zasu iya idan buƙatar hakan ta taso.
"Kayi tunani ko takardun sun shiga hannun wani bayan kai kar ka ce cire kowa walau ya uwa ko Amini muddin sun je hannunsa toh abin zargi ne domin babu yanda za'ayi a t
ashi rana
ɗ
aya ace takaddu sun canza daga yanda suke zuwa wani abu na daban dole wani ne ya canza su" cewar Lawyer Alhaji Balarabe.
Haka ya bar gurin cikin damuwa duk kuma yanda zaiyi ya gano abinda ya faru ya kasa, to wa ma zai zarga bayan daga shi sa
i Jalilah da wa
ɗ
anda suka siya a hannunsu ne ka
ɗ
ai suka san da maganar ita kuma a hoto kawai ya tura mata su bata gansu a zahiri ba. Haka yayi ta kame kame daga ƙarshe ya watsar ya kama sabgoginsa tunda lissafin sa na farko ya wargatse ya sake dawo da Jali
lar rayuwarsa sai dai ya jira kuma ya sake shiri.
BAYAN WATA BIYU
HALIMA
Na fara Bautar ƙasa na gadan-gadan, wani Private Research Center aka kai ni, mai gurin Abokin Uncle Mudassir ne na sha mamakin lokacin da naje gurin dan ban ta
ɓ
a sanin wanzuwa
rsa a Kano ba. Guri ne mai
ɗ
auke da Laboratories babu adadi ga kayayyakin aiki yyanda kasan a irin fina finan Turawan nan na Scientist haka da yawan ma'aikatan gurin duk fararen fata ne ka
ɗ
an ne baƙaƙe iri na.
Fara aiki na ya sa na yarda dagaske da aka
ce zaman banza ne yake kashe zuciya har mutum yayi ta tunane-tunanen banza da wofi mai abunyi sau tari ya kan manta da duk wata matsala idan ba wacce ta shafi aiki ko sana'arsa ba. Toh nima hakan ce ta kasance dani domin ban rufa sati ba na fara
ɗ
aukar sa
iti, na tattara duk wata damuwa na watsar na kama aiki na domin gani nayi tamkar ban ta
ɓ
a zama a aji ba komai sai ya zamar mun baƙo a lab
ɗ
in da aka kaini, da yake kuma har raina a shirye nake da na mayar da hankali na koyi abin sosai sai na ware duk wani
test da akayi idan na koma gida zan zauna nayi Reserch a waya har sai na samu cikakkiyar fahimta akan abun, na ƙulla abota da ChatGPT, duk abinda ya shige mun dubu shi zan tambaya ya warware mun musamman da na gano yana jin hausa shikenan na samu abinyi ko
Whatsapp sai in wuni na kwana ban leƙa ba ina can ina kwasar romon ilimi har na fara hasaso kaina na koma makaranta nan da wani
ɗ
an lokaci nima na zama babbar Scientist tamkar mamallakin gurinmu dukda a hoto kawai na ta
ɓ
a ganinsa sai dai ya burgeni, matas
hi don bai kai shekarun Uncle Mudassir
ɗ
in ba ma idan kuma ba hoton ne ya mayar dashi yaro ba amma har mamakin irin abubuwan da yayi nayi wanda suke rubuce cikin tarihinsa da akayi bango guda a cikin reception
ɗ
in gurin.
A cikin satin daya mutu na kamm
ala iddar Bilal, mun rabu kenan ko in ce na cire duk wani sauran fata da nake dashi akan al'amura zasu iya canzawa ko da ace akwai sauran zama a tsakaninmu toh fa sabon lale ne, sabon nema, sabon
ɗ
aurin aure wanda na tabbatar abu ne mai matuƙar wahala ace
waliyyai na su sake kar
ɓ
ar maganar auren Bilal, sai dai ƙaddara mai girma irin wacce ta ha
ɗ
a mu a baya wadda a yanzu ni da kaina bana fatan ta sake giftawa.
Aurensa ya zame mun darasi a rayuwa, banyi nadamar kasancewa tareda shi ba domin za
ɓ
i na ne ba
dole aka mun ba amma kuma na godewa Allah daya farkar dani a dai-dai lokacin da rayuwara take da sauran ma'anar da zan iya canza gobe na.
Tun ranar daya bani takardata ban sake ha
ɗ
uwa da shi ba ko da a hanya haka bai sake nemana ba in banda text message
daya turamun sau biyu akan cewar zai ƙwace yaransa shikenan bai kuma waiwayata ba ya tare da amaryarsa ya manta da ni da yaran da muka haifa tare.
Ko kusa ban ta
ɓ
a kawo cewar ko da cewar baya sona na kuma yarda da hakan babu haufi amma kuma na
ɗ
auka al
barkacin zaman da mukayi na shekaru zan samu gurbin da zai ringa tunawa da ni a zuciyarsa har ya tuntu
ɓ
e ni, kai ko bai nemeni ba ya kamata ace ya nemi yaransa, ko da yake tun kafin ya sakeni ma zaman da mukayi bai ta
ɓ
a waiwayarsu ba har gara ni a sanda ya
so ya yaudareni ya sake mayar da rayuwata cikin uƙuba ya bibiyeni amma bai ta
ɓ
a tambayar yaransa ba, bai san cin su ba, bai san shan su balle suturar su ba shi ba hatta da yan uwansa babu wanda har kawo yau yayi tunani ko karar dai dai da rana
ɗ
aya yazo y
a gansu ko ya kira yaji lafiyarsu sai Abubakar.
Shi ka
ɗ
ai yake tuntu
ɓ
ata duk kuma sanda ya zo Weekend sai yazo ya gansu ba kuma zai zo hannu haka ba idan ma bai kawo komai ba zai basu ku
ɗ
i ya ce a siya musu bayan shi hatta Anty Amina da nake zaton tana
so na tun ranar da suka zo biko suka tafi ban sake jin
ɗ
uriyarta ba balle kuma uwar gayyar Hajja a taƙaice dai sun barmun yaran kawai na kuma yi murna da hakan a kullum kuma ina addu'ar Allah ya raya min su suyi tsahon rai su kai lokacin moro naga yan uwan
Bilal
ɗ
in zasu zama ire iren marasa kunyar mutanen da nake samun labari da sai a lokacin da yara suka zama abin moro ne sannan zasu gwada iko akansu matsayin dangin mahaifinsu ko kuwa sun barsu har abada?
*KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAR
OUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wakiltar m
utum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 54*
J
inyar stitches
ɗ
in Zulaiha ta saka Bilal baya fita ko ina idan ba masallaci ba, duk ayyukan gidan shi yakeyi, sannan ya kula da ita a
ɗ
an taƙin lokacin kuma ya
ɗ
an fara samun nutsuwa daga tsoron sababbin halayen da ya ringa gani a gurinta tun bayan da aka
ɗ
aura musu aure. Ranar data kwana uku ƙanwar Ummansu Anty Habi taje gidan ta kai mata gamje gamjen magunguna da ta ce na Aljanun da suke shafarta ne. Shi ya ringa jigilar dafa mata na wanka safe yamma kuma ya hura mata coal tayi turare, maganin na sati
ɗ
ay
a ne ranar data cika satin tana yi kuwa Aljanun suka tashi.
Lokacin ya fita siyo kayan miya ya dawo ya tarar da ita su Suby sun daddanneta tana wasu abubuwa suka ce masa wai a haka suka tarar da ita suma. Dukda dai yayi mamakin ta inda suka shiga gidan
tunda ya rufe daya fita ita kuma sun ce sun sameta ta hau iskoki to waya bu
ɗ
e musu ƙofar?
Haka ya fita can masallaci ya samo wanda zaiyi mata ruƙiyya, suka ringa kafa masa Sharu
ɗ
an kar a ringa
ɓ
ata mata rai, kar ayi mata fa
ɗ
a da sauransu in ba haka ba
zasu dawo daga haka dai suka fice sai kuma suka riƙe mata ƙafa, sati biyu taci tana jinya kafin ta ware gaba
ɗ
aya suka durfafi sabuwar rayuwar amarci tunda
ɗ
inki ma ya warke, duk yanda take ƙoƙarin dannewa kar tayi abinda zai sake jefa zargin wani abu a z
uciyar Bilal
ɗ
in ta kasa.
Ranar da suka sake gamuwa dukda shi ya fara nuna buƙatar abun amma tun kafin ayi nisa taga ya canza, karsashin daya fara da shi ya sakeshi sai ƙananan tsaki da ya ringa saki, bata damu ba ta cigaba da shafashi a ƙoƙarin mayar
dashi kan network amma sai kawai ya tureta lokacin da wayar sa tayi ƙara. Abun ya mata ciwo matuƙa, tana sauraron wayar da yakeyi data gane da Hajja ne kuma masifa take masa dan sai bata haƙuri yakeyi kafin ya kashe bayan ya ce mata gashi nan zai zo gidan
yanzu da yake da yamma ne.
Tayi ƙwafa ta bishi da harara sanda ya shiga ban
ɗ
aki, sai kuma ta tashi da sauri ta
ɗ
akko Humrar kiranyenta ta shafa sannan ta
ɗ
ebi maƙale mata a hannunta ta koma ta zauna tana murmushin mugunta, Tunda ba zaiyi dan Allah ba t
oh kuwa zai yi dan dole.
Bilal kuwa daya shiga ban
ɗ
akin sakin ruwa yayi akansa dukda garin da sanyi sanyi amma bai damu ba, duk da ya san gaskiyar abinda ya sameta amma kuma zuciyarsa ta kasa kar
ɓ
ar abun har yanzu. Yana son Zulaiha tamkar rai, amma da
zarar ya tuna cewar bai sameta a Mace ba sai yaji duniya ta masa zafi, duk sanda buƙatuwar ta ta motsa masa kuma da zarar ya tuna abun sai ya ji komai ya mutu kamar dai yanzun a matse yake ya kuma yi ƙoƙari ya kawar da tunanin amma suna farawa abun ya zo m
asa take yaji komai ya mutu duk yanda ya so daya daure ko dan ganin kamar itama tana so
ɗ
in amma ya kasa.
Wani tunanin ne ya sake gifta masa wai me yasa ita bata tsoronsa?
Kashe shower yayi ya zauna akan toilet yayi shiru kamar mai jira wani ya bashi a
msar. Ya tafi tunanin farkon aurensu da Halima daƙyar sai ya matsa take iya kallonsa babu riga amma ita wannan haka take ƙure shi da ido kamar mayya har lashe baki takeyi idan da ya biye mata ma da tuni tun kafin
ɗ
inkin nata ya warke ma zata bashi kanta kw
ata kwata babu kunya ko jin nauyinsa a tareda ita ko da kuwa tayi ƙoƙarin nuna hakan bai san mai yasa yake ganin kamar na ƙarya ne ba.
Ji yayi kansa na nema ya fara ciwo dole ya kore tunanin ya miƙe ya shiga wanka, sanda ya fito tana kwance akan Gadon a
mma ya san ba bacci takeyi ba tunda bai ji munshari ba, ya wuce gaban mirror zai
ɗ
auki wayarsa ya bar mata
ɗ
akin hancinsa ya fara shaƙo masa wani ƙamshi, kansa ya sara, kamar wanda aka ja da igiya haka ya tafi kamar kuma waccen ranar yau
ɗ
in ma haka ya rin
ga aiki tun yana na jin da
ɗ
i har ya koma na wahala sai gashi yana kuka wiwi duk kuma yanda ya so ya bari abu ya gagara sai da ita da kanta ta gaji kafin ta yakiceshi daƙyar ta gudu ban
ɗ
aki ta kulle ƙofa.
Bilal kuwa kwanciya yayi riƙe da ciki yana juyi c
ikin azaba, ya gaji amma kuma so yake yayi abun, daƙyar ya lalla
ɓ
a ya fice daga
ɗ
akin ya koma nasa ya shiga wanka, sai da yayi kusan sa
ɓ
i uku har cikin hancinsa ya wanke kafin ya daina jin ƙamshin turaren a hankali kuma nutsuwa ta fara saukar masa ya fita
ya kwanta akan gado yana sauke ajiyar zuciya a jere. Gaskiya ba haka kawai ba akwai wani abu dan shi dai a rayuwarsa bai ta
ɓ
a gamuwa da irin wannan bala'in ba. Sai gurin ƙarfe tara ya iya tashi yayi sallar magriba da Isha'i, yana zaune ya jiyo tana ƙwanƙwa
sa masa ƙofa ha
ɗ
i da kiran sunansa kamar na zai tashi ba sai kuma ya miƙe yana rangaji yaje ya bu
ɗ
e mata.
Sum sum ta wuce ta ajiye try
ɗ
in data shiryo masa kayan abinci akai, ba tareda ta kalle shi ba ta miƙa masa wayarsa tana cewa
"Tun
ɗ
azu ake kira
" ya kar
ɓ
a yana kallonta sai kuma ya ji tausayinta yana ratsashi babu dalili. Abincin data zuba masa ya jata jikinsa suka shiga ci, jollop
ɗ
in shinkafa taji nama ga kuma peppered chicken daban a gefe da salad sai lemon exotic babban kwali mai sanyi sosai.
Sai da ya kai geji kafin ya shiga tantance abincin. Ɗan
ɗ
anon da ƙamshi harda yanda aka shirya abincin ma bai yi kama da girkinta ba.
Zulaiha bata iya girki ba bai kuma yi mamakin hakan ba domin ya fi kowa sanin daga gidan daya
ɗ
akkota, yayi gyaran murya
ya ce
"Daga ina aka kawo abinci?" Ta kalle shi a shagwa
ɓ
e ta ce
"Ni na girka mana"
ɗ
an murmushi yayi ya ce
"Ai nasan bamu da ingredients
ɗ
in da zakiyi irin wannan girkin, ya kamata ma a samo fridge gaskiya saboda ajiyar nama da kayan miya na gaji da
siyan guntu guntun nan" daga haka ya
ɗ
auki wayarsa ya shiga duba missed calls ita kuma ta kwashe kwanuka ta fita da su ranta ƙal.
Kiran Kamalu ya fara bi dukda yaga missed calls
ɗ
in Hajja kusan guda goma, basu wani ja gaisuwa mai tsayi ba Kamalu ya ce m
asa
"An ce kayi ta zuwa nemana Allah ya sa lafiya dai"
"Eh wlh kuma nayi ta kiran layinka kullum a kashe, dama maganar shagunan nan ce na bawa lawyer na takardun ya duba amma ya ce fake ne" Bilal ya bashi amsa.
"Fake kuma?" Kamalu ya tambaya cikin
mamaki Bilal ya amsa masa da
"Haka ya ce, nima nayi mamaki amma kuma dana ha
ɗ
a su da wasu takardu na ga banbancin da ya ce akwai tsakaninsu da original
ɗ
in".
"Gaskiya toh bansan a inda aka samu matsala ba dan kai shaida ne takardun nan hannu da hannu
yanda aka bani su take na miƙa maka ban ko tafi dasu wani guri ba balle ace ni na canza su" Kamalu ya fa
ɗ
a.
"Ai ba ina zarginka bane Alhaji Kamalu nima abun ya bani mamaki ne kaga kenan daga can gurinsu da suka siyar mana sune macutan, sun kar
ɓ
i ku
ɗ
in
mu ƙila zasu sake siyarwa da wasu kuma"
"Gaskiya a sanin da nayiwa Alhaji Balarabe ba zai ta
ɓ
a yin haka ba, na fi shekara goma sha biyar muna harkar ƙasa da shi ba'a ta
ɓ
a samun sa
ɓ
ani ba, amma abinda zai faru gobe idan Allah ya kaimu kazo office ka same
ni sai muje gurinsa duk ma abinda ya faru sai a warware" Kamalu ya sake fa
ɗ
a daga haka sukayi sallama.
Dukd dare ya farayi haka ya tafi gidan Hajja tareda Zulaiha, sai da ya tsaya a hanya yayi mata siyayyar toshiyar baki kafin suka isa gidan. Fadila na
falo tana kallo ita da Abubakar shi kuma yana cin abinci suka shiga, ta gaishe shi ba tareda ta ko kalli Zulaihan ba Abubakar dai tamkar bai ji shigarsu ba sai da Bilal
ɗ
in yayi masa magana kafin ya
ɗ
aga kai tareda yi masa sannu a taƙaice ya cigaba da cin
abincin sa.
Ɗ
aki ya wuce da Fadila ta ce masa Hajjan ta kwanta, ya zauna daga gefen ƙafarta yana gaisheta dan ba bacci takeyi ba kafin ta miƙe zaune fuska ba yabo ba fallasa ta ce
"Ashe kuma ka saki Halima"
Kai a ƙasa yana shafa ƙeya ya ce
"Kotu
suka ce zasu kai ni Hajja ni kuma naji tsoro kar su fitar da waccen maganar shiyasa kawai na saketa".
"Ai shikenan, yanzu yaushe zaka kar
ɓ
o yaran toh?" Hajja ta sake fa
ɗ
a. Da sauri ya kalleta ya ce
"A kar
ɓ
o yara kuma Hajja?"
"Da bar mata su zakayi
shikenan an rabu kake nufi ko me?"
"Aa ba haka nake nufi ba, da niyyata dai a barsu su ƙara tasawa tunda yanzu idan an
ɗ
akko su nan idan aka kawosu wahala zasu zamar miki" ya sake fa
ɗ
a kai a ƙasa. Hajja dake kallonsa ta ce
"Au, ni kake zaton zan ri
ƙ