Showing 270001 words to 273000 words out of 287295 words
nayi"
"Mantawa kikayi?" Y
a fa
ɗ
a cike da mamaki, nayi saurin rufe baki na kamar yana gabana nace
"Aa ba haka zan fa
ɗ
a ba cewa zanyi inata aiki ne ban san dare yayi haka ba so nakeyi idan na gama sai na kiraka"
"Amma kika ce bacci kikeyi? Ko dai Bilal ne ya
ɗ
auke miki hankali?"
Ya jefo mun wata tambayar, nayi narai-narai da fuska kamar ina gabansa kafin nace
"Aa wlh dagaske zan kiraka aiki ne ya
ɗ
auke mun hankali"
"Shikenan na yarda, toh ya kike ya dare?" Ya fa
ɗ
a daga haka muka shiga hira wacce zancen tafiyarsa gobe ne. Dam
a shi hirarsa kenan aiki da sabgoginsa na rayuwar yau da kullum ni kuma sai dai nayita binsa da Eh ko Aa dan a gurina wannan ba hira bace, a matsayinsa na mai neman gurin zama a ganina ya kamata hirar sa ta kasance ta ƙoƙarin kafa kansa a gurina amma shi s
am ba haka yake ba. Sha biyu na bugawa yayi mun sallama, kashe wayar nayi gaba
ɗ
aya dan tun muna magana nake ta jin shigowar kiran Bilal.
Tunanin fara maganarmu da Dr Salman na tafi, washe garin ranar da muka ha
ɗ
u dashi a gidan Uncle Mudassir mun fita
tareda su Al'amin da yamma siyo Popsicles muka ha
ɗ
u dashi a gurin. Har ga Allah ban so kulashi ba dukda mun ha
ɗ
a ido musamman da na ganshi tareda wata mace da wani abokinsa ina tsaye gurin biyan ku
ɗ
i ya tarar dani sai jin muryarsa nayi a bayana yana cewa
"Barka da yamma Malama Leemah". Da farko dukda naga tsayuwarsa ban
ɗ
auka dani yake ba musamman sunan daya kira wai Leemah dan haka ban amsa ba, sai da ya sake matsoni sosai yana kallona ya maimaita maganar kafin kuma kunya ta kamani na shiga gaishe shi
kai a ƙasa. Shi ya biya ku
ɗ
in abinda muka siya ya rakamu har mota kawai ya miƙa mun wayarsa wai na saka masa number na. Haka na koma gida cike da mamakinsa bai kirani ba sai washe gari Monday lokacin mun fita break, tsarin number dama gani kawai jikina ya
bani shine, ilai kuwa bayan na amsa yace naje na sameshi a office, tareda Uncle Mudassir na tarar dasu babu kuma jeka ka dawo a gaban Uncle Mudassir
ɗ
in ya ce wai nayi masa tun ranar daya fara ganina a lokacin ma bai san nice Niece
ɗ
in Mudassir ba kawai ya
ji yana so na dagaske kuma idan na amince aurena yake so yayi.
Uncle Mudassir yace masa babu ruwansa shima yace bai sakashi a ciki ba abinda ya saka ya fa
ɗ
a a gabansa kawai saboda ya san dagaske yakeyi koda yaji labarin wani zai masa shige ya fa
ɗ
a cewar
yana ciki, ni dai na tafi na barsu kawai, shikenan ya fara kirana a waya, ban kuma
ɓ
oye masa ba na fa
ɗ
a masa na ta
ɓ
a aure har ina da yara biyu, nayi mamakin jin wai bai sani ba dan na fa
ɗ
a masa ne saboda ya ji daga bakina dukda ina da yaƙinin ya sani Uncl
e Mudassir ba zai ƙi ya gaya masa ba amma yace mun bai sani ba.
"Bakiyi kama da wacce ta ta
ɓ
a aure ba har kuma ace kin haifi yara biyu amma ke nake so, aure ko haihuwa ba zasu canza hakan ba" abinda ya fa
ɗ
a mun kenan. Soyayyar sa a bayyane take kuma da
zafi yake yinta.
Dukda cewar baya fa
ɗ
arta da baki amma a bayyane take a duk ayyukansa ba kuma ya shakka ko jin nauyin wani ya sani kamar yanda nake jin tsoron fallasuwar alaƙarmu a office
ɗ
in, ya mutane zasu kalli abun ace daga zuwansa kawai soyayya ta
ƙullu tsakaninmu? Ba yan office ba hatta da mutanen gidanmu bana bana so maganar ta fita su ji ban kuma san dalilin haka ba.
Ban sani ba ko kulawar da yake bani ce ta saka zuciyata ƙoƙarin kware masa, yanda yake mun idan yana tareda ni yana sakani ina
jina tamkar sarauniya, abu
ɗ
aya ne cikas
ɗ
in, baya mun kalaman soyayya irin wa
ɗ
anda kunnuwana suke da muradin sauraro, amma dukda hakan zan gwada.
HAJJA.
Cikin yanayin damuwa ta kalli su Anty Amina tace
"Kunji wai bata da lambar sai dai a tambayi N
asir"
"Toh ki kira Nasir
ɗ
in aji, ni bari na wuce duk yanda zake ciki sai muyi waya" Amina ta sake fa
ɗ
a tana miƙewa daga haka tayi musu sallama Anty Habiba ma ta miƙe suka bar Hajjan ita ka
ɗ
ai.
Abubakar ta kira tace ya kirawo mata Nasir
ɗ
in a waya,
"Kana kallo duk sunyi tafiyarsu kamar ma halin da
ɗ
anuwanku yake ciki bai damesu ba" ta fa
ɗ
awa Abubakar. Yana danna waya ya ce mata
"Toh Hajja me kike so suyi? Shi fa ya jefa kansa a koma menene idan sun zauna mai hakan zai canza?"
"Amma ai sa
ɗ
eb
e mun kewa su kwantar mun da hankali ko?" Ta sake fa
ɗ
a, ya miƙa mata waya ganin Nasir ya amsa kiran ya fice ba tareda ya sake cewa komai ba. Nasir
ɗ
in ma kamar Halima ce mata yayi ya kwana biyu rabonsa da Bilal yana ta kiran layukansa kuma baya samu sai da
yaje can gidan matarsa tace ai yayi tafiya. Ya ce mata
"Na san dai kin san mai yake faruwa Hajja, ki fa
ɗ
a masa duk ma inda ya tafi ya dawo dan wannan ba mafita bace gara yazo kawai ayi abunda za'ayi asiri ya rufu".
"Wai har dubu nawa ne ku
ɗ
in da zai
saka ya gudu?" Hajja ta tambayi Abubakar bayan data gama wayar, ya watsa hannu kafin ya ce
"Ni ban sani ba Hajja idan ya dawo sai ki tambayeshi"
"Ai shikenan" Hajjan ta fa
ɗ
a kamar abar tausayi, har ya miƙe sai kuma ya koma ya zauna ganin tayi tagumi l
okaci
ɗ
aya fuskarta harta wani rame damuwa ta cikata.
WASHE GARI
HALIMA
Ƙ
arar waya ta ce ta tayar dani daga baccin da ban jima da komawa ba dan tun asuba bayan na idar da sallah Dr Salman ya kirani bai kuma barni ba har sai da aka fara sanarwar jirgi
nsu zai tashi zuwa Abuja wayar sama da awa biyu kunnuwana har ciwo naji suna neman kamawa daga ƙarshe a speaker na sakata na kwanta ina amsa shi da Eh da Aa. Ban jima da komawa baccin ba aka sake kira, na tashi zaune daƙyar, har wani yaji-yaji kaina yake m
un, na
ɗ
aga nayi sallama cikin muryar bacci, sai daya amsa sannan na fahimci wanene mai kiran dan banga sunan da kyau ba.
"Na tashe ki daga bacci Anty Halima na
ɗ
auka ai kina gurin aiki ma" ya fa
ɗ
a, nace
"Yau banida aiki shiyasa" daga haka muka gaisa y
a
ɗ
an yi jimm kafin ya ce
"Jiya Hajja ta kiraki ko?"
"Eh ta kira tana tambayar ko ina da wata number Abbansu Al'amin" na bashi amsa, ya sakeyin shiru kafin ya ce
"Na san ko ba zai kira kowa ba zai kiraki ta yuwu ma ya fa
ɗ
a miki in da yake, dan Alla
h ki bani number da ake samunsa Anty Halima idan kuma ba haka ba nazo ki kirashi sai ki ha
ɗ
a mu a wayarki"
"Ni bamuyi magana dashi ba amma akwai wata number sa da nake tunanin zaka iya samunsa a ita bari na tura maka". Sallama mukayi na aika masa da num
ber kafin na kashe wayata na koma bacci.
Abubakar kuwa tana tura masa number ya dannawa Bilal kira, sau uku ya kira bai amsa ba sai ya tura masa message cewar Hajja tana kwance a Asibiti kuma tace a kirawo mata shi dan jikin yayi tsanani ya zo idan ba y
ana so ya mutu da nadamar ƙin zuwan ba.
Yana turawa ya kashe wayarsa ya tafi uzurinsa, ya sani Bilal
ɗ
in yana girmama lamarin Hajja da wahala kuma ya share alhalin an ce tana kwance a gadon Asibiti.
Tunaninsa kuwa ya zama gaskiya dan lokacin daya ki
rashi yana zaune yana karyawa ne kuma cikin shiri yake dan yana so yaje gurin Yusuf da yake ta kira tun daren jiya baya
ɗ
auka bayan sunyi magana ya gaya masa an sauke kaya ya sauraresu a kowanne lokaci zai iya jin alert tunda sun kar
ɓ
i details
ɗ
in sa da ko
mai dama, yana ganin kiran Abubakar ya san tabbas Halima ce ta bashi number.
Niyyar kashe wayar yayi gaba
ɗ
aya ganin yana ta kira sai ga saƙonsa ya shigo take kuwa hankalinsa ya tashi ba shiri ya kama hanyar Kano. Yana tafe a hanya yana sake gwada kira
n Yusuf
ɗ
in shiru har sannan tana ringing amma ba'a
ɗ
auka, yana guraren Yankaba ya same shi, haƙuri ya bashi wai wayar ce yara suka saka masa a silent bai lura ba sai yanzu daya
ɗ
akkota yaga tarin missed calls yace ya sameshi a office yanzu dan haka ya kar
ya akalar motar daga hanyar asibitin da suke zuwa in da yayi tunanin an kai Hajja zuwa gurin Yusuf
ɗ
in.
Ji ya ringayi kamar ana jijjigashi tsakanin sama da ƙasa, dukda sanyin Ac daya cika office
ɗ
in amma zufa ta shiga keto masa ya ringa kallon Yusuf
ɗ
in
yana sake kallon Tablet
ɗ
in daya kunna masa video.
"Kayi haƙuri Alhaji Bilal, shiyasa na ringa maka magana akan ka rage yawan ku
ɗ
in nan amma kaƙi ji, yanzu ka shiga harkar nan mu mun da
ɗ
e da yin wayo a cikinta. Yanda ake samun riba kamar hauka haka ida
n Allah ya juyo abun asara ta afku nan ma sai kaji kamar zaka haukace amma kuma idan ka tuna a baya Allah ya baka dan ya jarabceka yanzu dole kayi haƙuri. Toh yanzu ma haƙurin zakayi mu kumayi addu'ar Allah ya kawo ninkinsu a gaba, amma gaskiya nafi zargin
canza kayan nan sukayi dan irin packing
ɗ
in da akayi da wahala ace wai ruwa ne ya tarar dasu har yayi wannan
ɓ
arnar sai dai idan dama can lalatattun ne" Alhaji Yusuf ya fa
ɗ
a yana dafa kafa
ɗ
arsa.
Cike da ƙarfin hali kawai Bilal yake
ɗ
aga masa kai, gaba
ɗ
aya basu fi buhu goma sha zuwa ashirin bane aka bu
ɗ
e su lafiya lau sauran komai ya lalace ba ga Zo
ɓ
on ba ba cittar ba sun yi funfuna cittar kuwa da yawan buhunhunan har ta siƙe kamar yanda sukace ta zama kamar ƙurar katako.
"Kaga lissafin iya abinda ak
a samu nan, sai ka sake turawa da Abu Amar details
ɗ
in sai ku ƙarasa magana, yanzu bari naje ana jirana idan kuma yanzu zaka wuce sai mu tafi tare ka saukeni dan ba da mota na fito ba" Alhaji Yusuf
ɗ
in ya sake fa
ɗ
a, yanda yake magana ba zaka
ɗ
auka da wanda
ya tafka asarar Miliyoyin ku
ɗ
a
ɗ
e yakeyi ba kamar ma ba komai. Da laluben bango Bilal ya fita daga office
ɗ
in, Yusuf
ɗ
in ne yaja motar dan ce masa yayi baya gani sosai ya taimaka ya kaishi gida kawai.
"Haba Alhajin Allah kada ka bada maza mana, ni idan
na fa
ɗ
a maka irin ibtila'in daya ringa saukar mun bi da bi sai kayi mamaki amma dana mayar da komai gurin Allah ba gashi ya wuce ba? Ita rayuwa dama akwai samu akwai rashi ai, kuma sau tari jarabta tana zama matakin nasara idan kayi haƙuri sai kaga Allah y
a maido maka da dubunsu" Alhaji Yusuf
ɗ
in ya fa
ɗ
a Bilal sai jin sa kawai yakeyi ba dan yana gane komai ba.
Har ƙofar gida ya kaishi kafin ya masa sallama ya wuce yana sake jaddada masa kada fa ya sakawa kansa damuwar da zata haifar masa da wata rashin
lafiyar yayi biyu babu, dukiya dai ta tafi ba dawowa zatayi ba, a waya ya shiga kiran Zulaiha dan baya jin zai iya fita daga motar da kansa. Ƙirjinsa ya masa nauyi haka kansa sara masa yakeyi sosai tamkar wanda ale ki
ɗ
an gangi a cikinsa.
Ya kira Zulaih
an yafi sau biyar bata amsa ba daga ƙarshe haka ya lalla
ɓ
a baya ko ganin gabansa ya fita daƙyar bai ko kashe motar ba balle ya kulleta ya fita yana bin bango har ya tsaya jikin get
ɗ
in kafin ya shiga bugawa da duka ƙarfin daya rage masa.
ZULAIHA
Tan
a kwance tana baccin huce gajiyar da Ahlan ya tara mata a ha
ɗ
uwar da sukayi jiya. Tunda suka fara mu'amala babu wani abu daya ta
ɓ
a shiga tsakaninsu, zai
ɗ
auketa su fita yawo gari ko suje Hotel amma ba abinda yake mata sai dai suyi hira duk shaye-shayen da
yake ƙoƙarin koya mata sai jiyan tukunna ta kasa riƙe kanta dan tunda Bilal
ɗ
in ya tafi ita ka
ɗ
ai ta san a halin da take ko da ba wani samun yanda take so takeyi sosai a gurin nasa ba amma yafi babu, yanzun da baya nan ga hirarraki da wasannin banzan da s
ukeyi da Ahlan
ɗ
in kullum idan ta koma gida har kuka takeyi kafin ta samu tayi bacci, jiyan ji tayi kamar ya zuba mata wani abu a lemon da suka sha dan sai bayan komai ya lafa kuma ta shiga jin haushin kanta ha
ɗ
i da nadamar abinda ya faru ƙarshe bata ko ji
ra shi ba ta hawo Adaidaita sahu ta koma gida.
Tun bayan tafiyar Bilal ta samu free get, gari na wayewa zata yi wanka ta fice sai dare zata dawo, hankalinta kwance take al'amuranta. Ɗaki Ahlan
ɗ
in ya kama musu ko bai kirata ba zata tafi tayi kwanciyarta
ta wuni a can irin yanda ta saba a lokacin da take gida sau da yawa zata fita da sunan makaranta amma hotel zata wuce can zata wuni sai magriba ta koma gida abunta.
Duk yawon makarantar data ringayi asar ku
ɗ
i kawai ta ringa yiwa Bilal amma ba karatun
takeyi ba, canjin department
ɗ
in ta na uku kenan yanzu ita daya kamata ace tayi graduation kamar yanda Bilal
ɗ
in yake zato amma maganar gaskiya 200L take shima da taimakon wani saurayinta da yake HOD a wani department shi ya shiga ya fita idan ba dan haka
da tuni an koreta tareda su Suwaiba. Toh yanzun ma dai bata da banbanci da korarriyar dan tuni semester tayi nisa har ana shirin fara exams amma bata san ta yanda zata fara sanarwa da Bilal
ɗ
in zata koma makatanta ba.
Ƙ
arar bugun da yakeyi tamkar zai
ɓ
a
lle ƙofar ya farkar da ita, a gigice ta rarumi zani ta
ɗ
aura ta fita tana murza ido, sai data tareshi ganin yana shirin fa
ɗ
owa. Jiki na rawa ta kamashi suka shiga ciki ya zube akan carpet yana sauke numfashi kamar mai cutar Asthma. Yanayin da yake ciki ya
saka ta wartsake babu shiri ta rarumo wayarta ta shiga kiran layin Hajja.
Hajja na zaune tareda Anty Ladidi tana bata labarin halin da ake ciki, Ladidin tayi tagumi tana cewa
"Tun jiya Yaya Habiba ta kirani ai ta gaya mun harda yanda suka tarar da Fadi
la itama. Ashe
ɗ
an abu ta kazan uba mijin nata mayaudari ne, ya zo ya yiwa mutane lam
ɓ
o an bashi yarinya yaje yana gana mata azaba kamar wanda dama yayi auren
ɗ
aukar fansa? Ai nace mai yasa suka barota a gidan basu tasota a gaba sun taho ba? Ko sai ya kash
eta tukunna sai ya bugo waya yace azo a
ɗ
auki gawarta ko me?"
Cike da mamaki Hajja ta ce
"Wace Fadilar kike magana akai?"
"Auta mana ko muna da wata Fadilar ne bayan ita?" Ladidin ta bata amsa, kafin ta sake magana wayarta dake kan cinyarta tana jiran
kiran Bilal tunda Abubakar ya gaya mata ya tura masa saƙo ta shiga ringing,
ɗ
agawa tayi kawai ganin number daga can muryar Zulaiha ta cika mata kunne cikin tashin hankali take sanar mata ga Bilal ya zo ita dai bata gane kansa ba gashi nan numfashinsa yana
sarƙewa.
Miƙewa Hajjan tayi da sauri kafin kuma ta koma kamar wacce aka ja tayi zaman yan bori, cikin tsananin azabar data ziyarci bayanta zuwa ƙugunta ta saki wayar hannunta tana wayyo Allah dai-dai nan Abubakar ya shigo, ganin yanayin Hajjan bai ko t
saya jin ba'asi ba ya kinkimeta daƙyar, tare suke da Abokinsa Isma'l ya shigo ya gayawa Hajja abokin zai shiga su gaisa kenan dan haka ya sakata a motar Isma'l
ɗ
in suka wuce Asibiti da sauri.
A hanya yake tambayar Anty Ladidi mai ya faru tace masa bata
sani ba an dai kirata a waya ne ta miƙe tsaye kuma ta koma ta zauna gashi sun baro wayar a gida balle subi ba'asin kiran ko na menene?
Aminu Kano suka kaita sun ci sa'a babu
ɓ
ata lokaci aka kar
ɓ
eta emergency, a ransa ya ringa jin babu da
ɗ
i, ƙaryar da y
ayi saboda Bilal ya zo gashi Allah ya tabbatar da abun. Layin Bilal
ɗ
in ya shiga