Showing 27001 words to 30000 words out of 287295 words

Chapter 10 - KURA A RUMBU COMPLETE

barta, in kuma Allah ya ƙaddara an yi aure ayi ta tsallen tsiya ana jeka ka dawo akan me?

Tun da suka ce zasu zo neman auren me yasa baku dakatar dasu ba ku ce kun wa yar ku miji se yanzu za

ki zauna kina tagumi da maganganun banza da ba zasu miki amfani ba to wlh tun wuri ki tashi tsaye ki ƙwato yar ki tun ba a kai ki an baro ba, ke Salamatu da zaki ce aure saura sati biyu mutane zasu yi surutu idan aka fasa in yar ta shiga garari uban waye z

e taimaka musu balle a guji maganar da zasu yi? Allah ya tsinewa duk wanda be yi surutu ba, dama ai mugun hali irin na mutanen yau yasa suka yi shiru kaf maƙwaftan ku ace an rasa wanda ze bugi ƙirji ya fa

ɗ

awa Aminun gaskiya idan duk su yan uwansa maza yan

ubanci yasa sun yi shiru suna kallo yar sa zata shiga gararin rayuwa su sauran da za a ha

ɗ

a auren su tare idan da haka nasu maneman suka shuka rashin arziƙi ai ba zasu ja baki su kulle ba se shi za a masa mugunta a bar shi son ya ya rufe masa ido to ba a i

sa ba se kuma naga uban da ze ƙulla auran nan" Goggo Habi ta fa

ɗ

a.

Mama dai juya kai kawai take yi ta kasa cewa komai, tun da Anty Labiba ta kira ta ta gaya mata ta yiwa Bilal magana da kanta be ce komai ba daga nan ta ƙarasa cire ranta akan al'amarin

auren sa da Halima ta kuma godewa

Allah daya sa matsalar ta

ɓ

ullo daga gurin sa ko hakan ze sa Halima ta hankalta ta Kuma haƙura se dai ko da ta yiwa Abban zancen cewa yayi kar ayi saurin yanke hukunci a jira aji ta bakin su tun da akwai sauran lokaci.

"Amma Hajiya na ke ganin abi komai a sannu ya fi, shi lamarin aure sirri ne ba'a san abin da Allah ya

ɓ

oye ba be kamata ace muyi katsalandan a ciki ba. Aure nawa akayi a cikin irin haka daga baya kuma se kiga Allah ya warware komai ya wuce kamar be faru b

a balle yaron nan ba wai zauna gari banza bane yanda kike tuna ni. Da aikin sa, a gwamnatin tarayya yake aiki bama state ba kin ga ko ai yana da albashin da ze riƙe aure mace biyu ma ba

ɗ

aya ba, shi shirin aure kowa ya sani Allah ke yi ba mutum ba duk ku

ɗ

i

n ka duk tana din ka se kiga abu ya zo maka ba a yanda kayi tsammani ba musamman ace aure ya taso ga gini abin duk se a hankali fatan mu dai Allah yasa ha

ɗ

in ya zama alkhairi duk wani ƙyale ƙyale da bidi'a ba shi ne ba".

Kallon ta Goggo Habi tayi tsaf

tace

"Lallai Salamatu dole ki ce haka, tone tone babu kyau amma da se in ce ai ba zaki ga aibun abun ba tun da irin auren da aka miki kenan da Mijin ki na Farko Haladu me kifi har yamma tayi za'a tafi kaiki

ɗ

akin da aka bashi aro a cikin gidansu ba'a kwas

he hatsin da aka ajiye a ciki ba. Haka muka raka ki aka ajiye ki a

ɗ

akin uwar sa, ina kwananki uku Allah jiƙan rai Halima taje ta

ɗ

akko ki aka kashe auren irin haka kike so a maimaita to ba da mu ba wallahi ba a ta

ɓ

a ba ba kuma za a fara akan Halima ba"

"Haba Goggo dan Allah ki de na fa

ɗ

ar haka" Mama ta fa

ɗ

a se ta juya kan ta kafin tayi magana Abba da Baba Salahu suka yi sallama hakan yasa tayi shiru. Sama sama ta amsa gaisuwar da suka mata dan tun jiyan tace komai daya faru laifin Abba ne shi kuma Baba

Salahu ta ce yan ubanci yasa yaƙi gayawa Abban gaskiya. A tsanake Abba ya sanar musu da abin da Halima ta gaya musu ya rufe da cewa

"Da nasan ze zo da wannan maganar da ban fara rabon katin

ɗ

aurin auren nan jiya ba. Gashi jar abokanai na na wasu garuruwa

n duk jiya na aika musu dan kar ya zama a ƙurarren lokaci har an fara turo mun da gudumma yanzu se dai na maida musu na bawa kowa haƙuri kenan".

"Aa wace irin magana kake yi haka ai ba cewa yayi ya fasa ba uzurin sa ya bayar be kammala gini ba, abun du

k me sauƙi ne kiran sa ya kamata ayi aji ta bakin sa ko a kira su waliyyan nasa, idan lokacin ne baze ishe shi ba se a

ɗ

aura auren a bar biki zuwa sanda ze kammala se su tare idan kuma haya ze nema duk ba wani abu bane suyi zaman su wata rana se kaga komai

ya wuce kamar ba ayi ba" Inna Salamatu ta fa

ɗ

a se Goggo Habi ta miƙe tana cewa

"Da ba cikin ku dayayda Aminu ba se in ce kema hassada kike masa Salamatu ko da yake dama ai duniyar nan ta lala ce kai dai kayi ta kanka kawai to in ga dan bantan uban da z

e zauna dashi ko iyayen nasa maza azo a ha

ɗ

a duk tsiyar da suka kawo a maida musu yanzun nan ba se an jima ba gara da akayi haka Allah ya ha

ɗ

a kowa da rabon sa ma alkhairi kan ta farau fasa aure ko a kanta za'a ƙare balle ace? Maza Amina taso muje ki tatta

ro komai da kika san ya kawo gidan nan a fitar dashi".

Mama ta sauke tagumin data zabga tun da Abba ya fara maganar tace

"Ai babu wani abu nasu a gidan nan Goggo"

"Mantawa nayi, to bari in

ɗ

auko hijabi na ke Salamatu ki tashi ki raka ni can gidan nasu

muje mu zage su dan ba zamu bar su haka ba ladan

ɓ

atawa jikata lokaci da yayi dan uban sa" Goggo Habi ta sake fa

ɗ

a, se Abba yayi saurin cewa

"Duk abin be kai na haka ba Goggo ayi haƙuri" ta musu banza ta shige

ɗ

aki. Daga ciki ta ƙwalawa Mama kira ta tash

i ta tafi. Bayan barin su gurin Inna Salamatu ta kalli Abba tace

"Kada ka biyewa zancen Habiba kasan ta da rikici tun zamanin ƙuruciya balle yanzu da girma ya cimmata, maganar yaron nan uzuri ne babba yazo dashi tun da dai muhalli a aure yana gaba da koma

i. A gani na kar a biyewa shai

ɗ

an ace za'a fasa auren nan akan wannan, arziƙi da babu duk daga Allah ne nan duk daga babun muka taso gashi yanzu ubangiji ya bawa kowa bakin rabon sa. Ni dai shawarata Aminu ku kira iyayen yaron nan kuji ta bakin su, in har

ba su suka ce a bar maganar auren nan gaba

ɗ

aya ba karku bari ace daga gefen ku matsala ta

ɓ

ullo ba".

"Amma Yaya maganar gaskiya fa lamarin nan abin dubawa ne. Yau da ace yaron nan ya nuna iya ƙoƙarin sa a sabgar nan za'a fi samun ƙwarin guiwar kyautata

masa zato amma fa ki duba tun da aka fara maganar nan wane yunƙuri yayi ko iyayen sa suka yi, ko sadaka za'a basu auren yarinyar nan ai yaci su nuna yabawa amma yau har saura kwana goma sha hu

ɗ

u ba kira ba aike kuma jiya fa ko jiya naga katin auren ƙanwar

sa Alhaji Malam ya raba a kasuwa kuma sunan ta ita ka

ɗ

ai aka buga ban da nasa" Baba Salahu ya fa

ɗ

a, Abba dai be ce komai ba ya har

ɗ

e hannu biyu yana sauraron yan uwan nasa. Shi ka

ɗ

ai yasan yana yin da yake ciki a zuciyar sa ga irin kukan da Halima takeyi

gaba

ɗ

aya komai ya dagule masa.

Sallama Baba Salahu ya musu yace Abba suyi magana da Mama, duk abin da suka yanke ya sanar masa, bayan fitarsa Inna Salamatu tace su je can falon sa suyi magana saboda Goggo, bayan sun nutsu tace masa

"Kar ka bari shai

ɗ

an ya shiga zuciyarka kamar yanda ya samu guri a zukatan sauran. Ba se na tuna maka ba ka fini sanin a yanayin daka auri uwar yarin yar nan ba, idan ban manta ba se da

ɗ

aurin auren ku ya rage saura kwana uku kafin nayi

ɗ

aukar adashi na baka ka biya ku

ɗ

in h

ayar gidan da kuka fara zama. A shekara goma na farkon auran ku se da kuka zauna a gida bakwai, da da

ɗ

i babu haka Amina tayi haƙuri da kai daicdai da rana

ɗ

aya bata gaza ba har Allah ya yanke ya kawo ku in da kuke yau, yanzu idan ba wanda ya sani ba wa za'

a fa

ɗ

awa irin wahalar da kuka sha a rayuwa ya yarda? Baka zaton gwaji ne ubangiji yake yi maka yaga ta yanda zaka godewa ni'imar da yayi maka. A sanda Amina ta aure ka dai dai da kayan sakawar ka irgaggu ne Aminu amma yanzu fa? Ko cewa kayi ba zaka maimait

a kaya ba kana da sararin da kullum zaka saka sabo.

Yanda Allah yayi maka bakayi zato ba wata rana shima zeyi masa, a aure nagartar ma'auri ita ce abu ta farko da ake dubawa. Yaron nan bashi da laifi an san shi an san iyayen sa ubansa mutumin kirki ne

har ya fa

ɗ

i ya mutu ban ta

ɓ

a jin an ce ga wani halin sa mara kyau ba badan ma mutuwa me tonon asiri ba ta yaya za'ayi ace kamar

ɗ

an Alhaji Mansur ya rasa muhallin da ze shiga ya zauna da iyalansa? Kasan sanda ya rasu basu tasa sosai ba yan uwansu suka hau

kan komai suka bar musu abin da suka ga dama shi da ƙannen sa da suke ciki

ɗ

aya, yayyen sa na sama uku duk mata ne shi

ɗ

in dai shi ya tashi yake ta fafutuka da nemo abin da ze rufawa uwarsa da

yan uwansa asiri yanda ka gan ka

ɗ

in nan hake yake me zumunchi

abin sa na yan uwan sa ne har irin wannan Mijin ne za'a ce ba za'a bashi aure ba?

Karka kuskura ka biyewa mutane dan idan abun kuka ya same ka dariya zasu maka idan na farin ciki kuma yazo se sun san yanda suka yi suka ture ko shi Salahun da yake wanna

n maganar naga Maryam haka ya aurar da ita ba lefen yanzu ka gaya mun duk cikin yayan dangi wa cece take jin da

ɗ

i a gidan aure kamarta? Ka ci gaba da addu'a kawai ka barwa Allah komai shi yasan sirrin daya lullu

ɓ

e a cikin auran nan dama kuma duk wani abun

alkhairi ai baya samuwa ta da

ɗ

i mu ci gaba da addu'a kawai tun da dai yarinya tana son sa babu abin da za'a fasa in Allah ya yarda za'a yi komai arziƙin kenan, ubangiji ya hore maka ka kira shi kaji, idan har aikin gidan nasa ba me yawa bane da za'a iya ƙa

rasa wa a masa in ma kuma baze gamu ba a nemi haya ko ka basu gida su zauna arziƙin kenan amma zancen a fasa aure be taso ba sharrin da za'a bibiye mu dashi ka

ɗ

ai ma se ka rasa in da zaka tsoma ranka to ina dalili tun da dai Allah be hana yanda za'ayi ba"

maganganun da Inna Salamatu ta fa

ɗ

a masa kenan da suka bar shi cikin kogin tuna ni zuciyar sa ta kasu biyu.

*******************

Se yamma lis na koma gidan Anty Labiba, ko da naje gidan su Hansa'u dama ban gaya mata komai ba data tambaye ni me ya same ni

fuskata ta kumbura se kawai nace mata kuka nayi yan uwan Abba ne suka zo yi mun nasihar aure ta ringa tsokana ta daga nan muka

ɗ

an ta

ɓ

a zancen biki ƙawayen mu nata ƙorafin ba'a gani na naƙi nazo a fara shirye shirye nace mata gobe tazo muyi maganar a gida

n Anty Labiba kawai. Ban iya runtsawa ba cikin dare, Bilal be kira ni ba na kira shi kuma wayar sa a kashe ga Abba ma nayi zaton yanda baya son damuwata kafin wucewar yinin ranar ze aiwatar da abinda ya kamata ya share mun hawaye na se dai har dare shiru w

annan ya

ɗ

aga mun hankali na ringa tunanin ko dai su Baba Salahu sun zuge shi ne tun da naga alamar daga shi har Baba Hashim

ɗ

in ba son auren suke ba wannan tunanin ya ninka tashin hankali na tsabar damuwa har ji na ringayi numfashi na yana sarƙewa, rabuwa

ta da Bilal is the last thing i could ever imagine in my life. Ina son Bilal irin wanda ban san adadin sa ba ba kuma na fatan ace wani abu ya shiga tsaka ni na dashi.

Washe gari da wani irin ciwon kai na farka bana ko iya bu

ɗ

e ido na da kyau ga ciki n

a daya

ɗ

auki ciwo shima dan rabo na da abinci tun na safiyar jiya haka na wuni na kwana. Daƙyar na iya fita kitchen ina dafa bango na ha

ɗ

a shayi, a ƙasan kitchen

ɗ

in na zauna na shanye kafin na jingina jikin bango ma rufe ido na ina jin kaina na bugawa kam

ar me. Anty Labiba ta shiga, kallo

ɗ

aya ta mun ta wuce yin abin da ya kai ta kitchen

ɗ

in se da ta gama zaryar fitar musu da abin karyawa ganin har sannan ban motsa ba kafin tace mun

"Ki tashi ki mun wanke wanke yau wadda zata miki gyaran jiki zata fara z

uwa, kalli yanda kikayi firkai firkai dake a banza zaki kashe kanki saboda wani banza da be san mutunchin ki ba". Se da ta maimaita sau biyu ban amsa ba a fusa ce tayo kaina tasa ƙafa ta haure ni, ina jin duk abun da take fa

ɗ

a se dai bani da ƙarfin amsa ma

ta a zaunen da nake jiki na ya saki gaba

ɗ

aya duniyar ma juyawa takeyi a ido na. Haurin da ta mun yasa na zame daga bangon dana jingina na sulale a ƙasa ganin haka yasa ta fasa ihu babu shiri daga nan kuma ban sake tuna komai ba kawai na farka na ganni a g

adon Asibiti Bilal na zaune a gefe na.

[5/18, 13:09] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*

*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*

*What

sapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*

*Wattpad @MaryamahMrsAm*

*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*

*Ku

ɗ

in karatu yana wakiltar mutum

ɗ

aya ne, kiji tsoron

Allah karki

ɗ

auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*

*KURA A RUMBU littafin ku

ɗ

i ne, a biya naira 800, biya a asusun*

*1840175439*

*Access bank*

*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 8*

"Sannu Halims, kin tas

hi" Bilal ya fa

ɗ

a yana nufo ni se dai shigowar Anty Labiba

ɗ

akin ta katse masa hanzari se ya ja gefe yana shafa kansa ita kuma ta balla masa harara kafin ta nufo ni ta kamani ganin ina ƙoƙarin tashi zaune.

"Sannu" ta fa

ɗ

a tana gyara mun

ɗ

ankwali na daya

zame. Bilal ne ya fita ya kira wo likita suka dawo

ɗ

akin tare da Abba. Bin su kawai nakeyi da kallo har likitan ya gama dubani yace babu komai jiki na ya dai dai ta amma a barni na sake hutawa. Abba yayi mana sallama akan ze je wani guri Bilal na raku

ɓ

e a

bango kamar wani maraya a idon sa na hango tarin damuwa wadda nasan tana da nasaba da halin da nake ciki se dai wanzuwar Anty Labiba tsakanin mu tasa ya kasa yin motsi me ƙarfi balle yayi mun magana.

Ita ta kai ni toilet da nace mata ina jin fitsari se

kawai taci na daure nayi wanka gaba

ɗ

aya ko zan ji da

ɗ

in jiki na. Tana cu

ɗ

a mun baya na tambaye ta me ya same ni? Kuma tun yaushe nake asibitin? Ta mun banza bata amsa ba har muka gama ta ruƙo ni se kuma ta dakata tace na jira ta fita, ina jiyo muryar ta

ta cewa Bilal ya bamu guri, se da ta rufo ƙofa kafin ta dawo ta fito dani cikin kaya na da na gani a ƙaramar jaka na shirya, bana jin ciwon komai ban da kaina da yayi mun nauyi se jiki na da babu ƙwari dan haka a zaune nayi sallolin da Anty Labiban tace su

n same ni a kwance. Ina idarwa ta miƙa mun cup data ha

ɗ

a tea na girgiza mata kai ina cewa

"Bana jin yunwa Anty". Se ta mayar ta ajiye akan drawer ta nemi guri ta zauna tare da ciro wayar ta daga aljihun rigar ta ta shiga dannawa. Kusan minti goma muka yi

shiru, so nake yi na tambaye ta ko Bilal ya tafi ne amma yanda ta tsare gida yasa na ji shakkar yi mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login