Showing 84001 words to 87000 words out of 287295 words
/>
ɗ
i ya ha
ɗ
a dani da ita rufe mu da duka yana cewa wai ze koya man
a tarbiyyar da ba'a bamu a gida ba" ta ƙarasa tana fashewa da sabon kuka.
Mama dai kamar bata gurin Anty Labiba ko banda ka
ɗ
a ƙafa ba abinda takeyi.
"Kiji tsoron Allah Amirah; yaushe akayi haka?" Na fa
ɗ
a ina kallonta kafin na juya kan Abba nace
"Wal
lahi ƙarya takeyi Abba be doke ta ba kuma ni banji sanda ya zageta ba kawai nasan yayi mata hargagi yace ta taho gida kuma ita ta zage shi ta masa rashin kunya".
"Kinyi asara Halima, namiji ya zagi iyayenki har ya kira ki mara tarbiyya sannan kizo kina
kare shi wallahi kinji
ɓ
utur, namiji dai kika
ɗ
auka uba ko? Zako ki mutu marainiya. In dai Bilal ne gaki gashi nan ko yau be dake ki ba muna nan ranar zata zo Halima zaki san ki fifita son miji akan mutunchin iyayenki" Anty Labiba ta fa
ɗ
a tana miƙewa, sabo
da fushi babbar rigar Abba ta shiga fizga a zaton mayafin ta ne dake ajiye kusa da shi dan duk zaburar data ringa yi
ɗ
azu zata fita babu gyale akanta. Gyalen Abban ya miƙa mata ta fizge ta fita tana sake nanata
"Halima kinyi asara, Halima zaki gane baki d
a wayo a hannun namiji".
Se lokacin Mama ta sauke ajiyar zuciya ta tashi ta bita ba tare da tace komai ba, Abba ya kalle ni yace
"Ina ita ka
ɗ
ai yace t taho gida ko harda ke?" Se na fashe da kuka nace
"Abba ransa ya
ɓ
aci sosai, ina tsoron na zauna kuma
ma ni bani da lafiya, marata ciwo take mun".
"Tashi mu tafi Asibiti" ya fa
ɗ
a yana miƙewa tsaye, sunan Asibitin daya fa
ɗ
a se naji kamar an mun busharar ciwo lokaci
ɗ
aya wani ciwon baya da mara da bansan yanda zan misaltasu ba suka kawo mun ziyara. Hannu
na shiga yarfewa ina cewa
"Bazan iya tashi ba, wayya Allah ina ga ma mutuwa zanyi ni dai". Kiran Mama ya shigayi da ƙarfi se gata, ganin yanda nake dafe ciki ina nanata mutuwa zanyi yasa ta koma da baya se gasu tare da Anty Labiba. Tare suka kamani suka s
ani a mota. Cikin ikon Allah da zuwan mu asibiti ban fi awa
ɗ
aya ba na haifo
ɗ
an ƙaramin
ɗ
ana me tsananin kama da Bilal.
Anty Labiba ce taje ta siyo kayan da aka sakawa yaron da sauran abubuwan da zan buƙata kamar pad da pant, kayan jikina dake dama ri
ga d zani ne muna shiga na yaye zanin dan haka dana gyara jiki na nayi wanka su na mayar duk se nake jin ƙyamar jikina. A hannun Anty Labiba na tarar da yaron bayan na fito daga labor room
ɗ
in, ta mun kallo
ɗ
aya ta watsar dani da alama duk lahaula da salat
in data ringayi tana safa da marwa a bakin labor room duk na lokaci ne ba wai ta manta da fushi na dake ranta bane. Mama kanta a fizge ta mun sannu tareda tambayar badai abinda nake ji nace
mata eh, Abba ne ka
ɗ
ai ya ringa jera mun sannu yana mun addu'a kaf
in ya fita ya bamu guri.
Duk se naji jiki na yayi sanyi, na kwanta akan gado ina satar kallon su biyun Anty Labiba na riƙe da Baby Mama kuma na ƙoƙarin ha
ɗ
a mun shayi ta gama ta miƙo mun se ta
ɗ
auki Hijabin ta ta saka tana kallon Anty Labiba tace
"B
ari naje gida Labiba naga idan Hasana tayi abinda nace mata; kin santa da shirme. Idan suka kawo abincin ita se ta zauna ta kwana dasu ki tafi gida ko?" Bata jira amsar ta ba ta juyo kaina tace
"Se ki kira shi ki gaya masa za'a zo a
ɗ
aukar miki kaya kar k
uma yace an shigar masa gida ba izini".
Anty Labiba dai bata ce komai ba se
ɗ
aukar Babyn hoto da take a wayar ta haka Mama ta fita ta barmu kusan minti biyar a raina na tafi tunanin ko sun gayawa Bilal na haihu?
Anya kuwa? In da ya sani nasan baze kasa
zuwa ba ko wani nasa, ina so na tambayi Anty Labiba aron wayar ta na kirashin amma babu fuska se kawai na kama kaina na kwanta kawai, shi kansa Babyn ina kwa
ɗ
ayin na riƙe shi a hannu na na sake tantance kamannin sa dana hanga daga nesa amma nayi ƙarya nac
e ta bani shi.
Kamar ta shiga zuciyata kuwa se gata ta miƙe ta iso kusa da gadon ta aje mun babyn tare da wayarta kafin tayi ficewarta waje. Nayi murmushi a fili nace
"Antyna ta kaina kenan iyayen daru". Shagala nayi da kallon Babyn da kamar yasan gur
i na aka kawo shi ya fara motsa baki yana wulla yan ƙafafun sa da hannayen sa. Na
ɗ
auke shi na rungume shi, wani farincikin mara misaltuwa ya tsarga rai da ruhi na. Na tuna sanda nake yiwa Hansa'u tsiyar bata da kunya, a hotunan sunan yarta data haifa wata
biyu kenan, ƙiri ƙiri Bilal ya hanani zuwa Abuja sunan bayan har Maman mu se da taje. A kowanne hoto data tura mun tana rungume da yarinyar kamar za'a ƙwace mata ita da nace bata da kunya tace mun bazan gane ba se ranar dana riƙe nawa
ɗ
an zan fahimci ba r
ashin kunya bane.
Motsin ƙofa yasa nayi saurin raba shi da jiki na na zata Anty Labiba ce kafin ta fara mun taratsi ashe nurse ce, ita ta taimakamun tare da koya mun yanda zan shayar dashi. Dake tun kafin na haihu dama ruwan nonon ya fara kawowa dan ha
ka ba
ɓ
ata lokaci ya kama kamar dama a yunwace yake. Tana tsaye har ya ƙoshi kafin ta kar
ɓ
e shi ta sakashi a kafa
ɗ
a tana nuna mun yanda zan sakashi yayi gyatsa. Bacci ya koma ta kwantar dashi tace na shanye shayin da aka ha
ɗ
a mun zata yi mun allura ne. Se
lokacin na tuna ban ma kira Bilal
ɗ
in ba, seda ta gama abun da zata mun ta fita kafin na danna lambobin sa a wayar Anty Labiba takaici da dariya suka kamani lokaci
ɗ
aya ganin sunan data masa saving, wai BILAL BATI. Lallai Anty Labiba ta raina mun miji.
Kira uku nayi masa be amsa ba, dake ana shirin shiga sallar magriba ne se na bashi uzurin ƙila ko yana alwala ko ma ya shiga masallaci ne. Hotunan da tayiwa Babyn na shiga dubawa ina murmushi ni ka
ɗ
ai, shigowar ta tare da su Mama Fauziyya yasa na aje waya
r. Har ƙarfe goma wasu daga cikin yan uwan Mama da suka zo harma dangin Abba basu tafi ba. Ashe har tayi sanarwar haihuwar a group
ɗ
inmu na family ta kuma tura hoton Babyn shi kuma Mu'azzam ya
ɗ
auka ya tura ana
ɓ
angaren Abba. Tunda nace mata ban
samu Bilal
ɗ
in ba se kawai tayi waya gidan ta aka
ɗ
akko mun dogayen riguna dan kiba kawai ta fini da tsayi ka
ɗ
an kowa cewa yake ita na gado a rashin auki to yanzu cikin nan daya hura ni ma mun kusa kai
ɗ
aya. Haka na kwana da zullumin ko Bilal ya san na haihu? Idan y
aji ya ya kar
ɓ
i al'amarin dan nasan abu ne me wahala idan be ji haushi ba ace sedai kawai ya tsinci zancen haihuwa ta a sama bayan yana da haƙƙin daya kamata ace tun muna hanyar asibiti an kirashi an gaya masa. Haka nayi bacci cikin zullumi.
BILAL
Se
da ya fita daga gidan kuma ya ringa jin babu da
ɗ
i kamar abinda yayi ya zarce misali. Can gefe ya nemi guri ya zauna yana tunanin ya koma ne ya bawa Halima haƙuri ko kuwa? Amma daya tuna Haliman da irin son da take masa se ya samu nutsuwa yasan ba zata
ɗ
auk
i abun sa zafin da ze iya zame musu matsala ba amma kuma waccen ƙanwar tata mara kunya ita ce zata iya kai zancen gaba har ya zama wani abu daban. Sau biyu yana miƙewa da niyyar komawa gidan idan ma ta kama ya basu haƙuri ne duk su biyun zancen dai ya wuce
karya koma kunnen yan gidansu amma shigiyar zuciyar sa me yi masa hu
ɗ
ubar tsiya ta zuge shi akan ze siyawa kansa raini ne kawai ai itama Haliman ba zata fara bari zancen yaje gidan ba.
Da haka ya bawa kansa ƙwarin guiwa, da yayi niyyar zama gurin yayi
gadi ko da zata ce zata fita se kuma ya fasa yayi tafiyar sa dan yasan babu in da zata je ita dai Amirah yasan dole zata bar gidan tunda Halima na gudun
ɓ
acin ransa. A masallacin unguwar yayi sallar la'asar yana zaune ya hango gilmawar su, har ya miƙe da
niyyar bin su kuma se ya fasa a ransa ya raya mafita ce ta samu. Yanzu duk inda aka je aka dawo ze juya lefin ne ya koma kanta ta fita daga gidan sa ba tare da ya bata izini ba tunda ai ba ita yace ta tafi ba. Komawa yayi ya
ɗ
auki mashin
ɗ
in sa cikin sa'a
har ya fito bakin titi se lokacin suka samu abun hawa. Se da ya rakasu har gida yaga sun shiga kafin ya wuce gidan su yana ayyana yanda ze canza maganar idan ma ta tashi ance y zagi uban matar sa dukda yayi amanna Halima ba zata ta
ɓ
a bari maganar ta fita b
a yasan ma baze rasa dalilin da ya saka tabi Amiran ba kenan dan kar taje ta fa
ɗ
i abin da ba shikenan ba.
Daya isa gidan suna gaisawa da Hajja abinda ta fara tambayar sa shine
"Wai yaushe matar ka zata tafi wanka ne ko kuwa kana nufin a gidan ka zata
haihu su tatse maka tattalin arziƙi?"
Zancen kenan kullum yaje kamar karatu tun cikin Halima be wuce wata shida ba take surutun se ta tafi goyon ciki ai haka akeyi a al'ada, se kace ita nata yayan da cikin wata shidan suke tahowa kuma ma banda Amina Babb
ar Yayar su shi be sake ganin wata tazo wani wankan gida ba se Fadila itama kuma yasan dan Mijin yaƙi da
ɗ
in azanci ne dama neman tahowa gidan takeyi shi yasa suka fake da haihuwa badan haka ba da Hajjan ce zata je ta zauna mata kamar yanda ta saba yiwa sau
ran shine zata takura se Halima ta tafi tun da wurwuri.
Dukda dai shima yana da ra'ayin ta tafi wankan gida saboda ko babu komai za'a rage masa hidimomi da yawa na yan barka har zuwa suna da abubuwan da zasu biyo baya; duk baya jin yan uwan Halima dan t
un auren su ze iya irga mutum nawa suka zo gidan kuma ko ta haihu ba zasuyi irin zuwan nan na takura ba nasa dangin yake ji dan yana ganin yanda sukeyi a sauran gidajen yan uwansa idan anyi haihuwa wata tun farar safiya zata taho se taci abincin dare sanna
n ta tafi gaskiya baze
ɗ
auki wannan zaryar ba
shiyasa gara ta tafi can gidan su idan tayi arba'in suka gama yawon zaga dangi se ta dawo dukda ma ya gama gane take taken Haliman bata so ta tafi gidan amma hakan ya zame mata dole tunda yana ra'ayi.
Yana
ɗ
akin Hajja suna hira kiran Anty Labiba ya shiga wayar sa, abinda ya fara zuwar masa shine Amirah taje ta ce ya zagi Abban su shine Anty Labiba ta biyo ba'asi hakan yasa ya maida wayar sa aljihu bayan ya sakata a silent a ransa yana raya harka ta lalace mu
samman tunda wannan matar ta shigo ciki ko abun beyi zafi ba se ta ƙara rura wuta. Se da aka kira sallah ya fita, bayan an idar Abdurrashid ya tsayar dashi
ɗ
aya daga cikin Yayan Baba Salahu ne kuma abokin Bilal
ɗ
in dan suna buga ƙwallo tare. Da fara'a ya t
are shi bayan sunyi musabaha yace
"Angon ƙarni ashe an samu ƙaruwa?"
Tunanin da Bilal ya tafi yana magana ne akan Halima nada ciki, se ya gimtse fuska kishi ya motsa wato kalle masa mata ma yake yi yana sa mata ido tsabar kuma bashi da ta ido har ya i
ya tarar sa ya masa barka wai matar sa nada ciki. Shi ko Abdurrashid bema gane sauyin fuskar Bilal
ɗ
in ba yace
"Allah ya raya ya
ɗ
ayyaba, se munzo barka" daga haka ya saki hannun Bilal
ɗ
in ya wuce abun sa. Sakato Bilal yayi a tsaye yana ƙoƙarin ha
ɗ
a magan
ganun Abdurrashid
ɗ
in na ƙarshe, idan ya fahimta barkar haihuwa ya masa ba ta samun ciki ba kenan kuma hakan yana nufin Halima ta haihu ne ko me?
Ƙ
arasa fita yayi daga harabar masallacin kafin ya sake samun guri ya tsaya ya riƙe ƙugu yana ƙoƙarin ha
ɗ
a l
issafin, Nasir ne ya iske shi fuska a washe ya shiga zolayar sa da "Angon ƙarni".
"Ta tabbata kenan" ya raya a ransa, Nasir
ɗ
in yace
"Be kamata ma na kulaka ka ba, ace se dai muji haihuwa a gari ba zaka iya kirana ka gaya mun ba ko da yake yanzu kayi sa
babbin abokai yan GRA naga ai baka yayin irin mu yan ghetto".
"Ka aje maganar wasa Nasir dagaske ne wai Halima ta haihu?" Ya tambaye shi. Se Nasir ya kalle shi yace
"Bana son rainin wayau; matar ka ta haihu ka ringa tambaya ta wasa ne ko gaske? Mutuwa
kayi ka dawo da zaka ce baka san meya faru a duniyar ba ko wani salon wulaƙancin ne haka?"
"Dagaske nakeyi Nasir ban san Halima ta haihu ba. Tsayuwar da kaga nayi a nan yanzu Yayanta Abdurrashid ya gama mun barka shine na tsaya ina jiran wanda ze zo ya
fa
ɗ
a mun gaskiya ko aka sin zancen kuma se gaka, amma lallai mutanen nan sun raina ni. Ace matar tawa ta fara naƙuda har ta haihu babu wanda ya kira ni ya gaya mun? Kenan da mutuwa tayi se dai kawai ace nazo na ga gawarta ko me?" Ya fa
ɗ
a cikin
ɓ
acin rai.
Nasir ya dafa shi yace
"Kar dai kayi saurin yanke hukunci; nima yanzu Fauziyya ta kira ni take gaya mun taga Zubaida ta saka, ƙila yanzu ta haihu kuma kasan sharrin network ta yuwu ma sun kira ka be shigo ba. Tun da dai ta haihu lafiya ai anyi me wahala
r yanzu se ka kirata muji suna wane asibitin ne se muje".
"Zance ma kakeyi wlh, ai har idan an
ɗ
auke ni da muhimmanci tun kafin a fita da ita daga gida ya kamata a kira a nemi izini na kuma a gaya mun.
Idan basu same ni a waya ba bani da dangi ne? Taku
nawa ne tsakanin mu dasu da ba zasu aiko a gayawa mahaifiya ta ko wani
ɗ
an uwana yaje a tafi dashi asibitin ba?. Ashe dai da ake fa
ɗ
ar irin wulaƙancin da masu ku
ɗ
i suke yi su mayar da mazajen yayan su ba komai ba dagaske ne tunda gashi ya biyo ta kaina se
dai ni ba shashasha bane da zan
ɗ
auka wlh se na nuna musu nasan mutunchin kaina" ya ƙarasa a fusace yana zaro wayar sa daga aljihunsa.
Lokaci
ɗ
aya karsashin rashin mutunchin daya hau ya sake shi daya shiga jerin missed calls
ɗ
in daya gani akan wayar sa
. Kafin kiran Anty Labiba da kusan minti talatin Abban su Halima ya kira shi har sau biyu, alamar saƙon daya gani a saman wayar ya duba Abban ne dai ya aje masa saƙo yana sanar dashi Halima tana cikin halin naƙuda ya rubuta masa sunan Asibitin da suke da h
ar da kwatancen inda
ɗ
akin haihuwar yake. Kamar an watsawa kaza ruwa haka yayi laƙwas, Nasir yace
"Ka gani sun kira ka ko?"
Kamar mara gaskiya ya mayar da wayar aljihunsa yana gyara zaman rigar sa yace
"Oho dai koma menene ba'a mutunta ni an bani ƙim
a ta ta mijin ta ba tun farko ma ai ni ya kamata ta kira ta gayawa naƙuda ta kamata ba wai yan gidan su ba ai" ya fa
ɗ
a tamkar bashi da masaniya akan ta fita daga gidan. Nasir dake kallon sa kawai ya girgiza kai yace
"Kaji dashi, yanzu dai idan zamu je a
sibitin bismillah; idan kuma ba zaka je
ɗ
in ba ni in kama gabana ina da abinda zanyi a chemist".
"Babu in da zanje, idan ina da muhimmanci zasu zo har in da nake su buƙace ni" Bilal ya fa
ɗ
a yana wani bu
ɗ
a hannu, hannu biyu Nasir ya
ɗ
aga yana cewa
"Alla
h ya taimaka ya bada sa'a; idan ta dawo gida se ka sanar dani idan ma kuma can gidan su ta wuce duk dai ka gaya mun, ko da yake karka damu zan ji a inda na samu labarin haihuwar kawai ba se ka kira ni ba" daga haka ya juya yayi tafiyar sa Bilal
ɗ
in na tsay
ar dashi be kula shi ba ya shige motar sa daya ajiye gefeb masallacin ya tafi.