Showing 51001 words to 54000 words out of 287295 words
tambayar menene, ban iya ce masa komai ba se ciki na dana nuna masa. Ɗaki ya wuce ina jin sa yana cewa
"Kin c
i rabon ki da ba naki ba ai dole kiyi ciwon ciki" hawayen azaba ha
ɗ
i da takaici suka zubo mun lokaci
ɗ
aya. Saboda na ci nama shine ze zama sanadin ciwon ciki se kace wadda ta ci na sata ko Allah ya isa?
Farin magani ya dawo dashi a hannun sa ya durƙusa
gaba na ya bu
ɗ
e bayan ya jijjiga ya tsiyaya mun a murfi. Cikin ikon Allah ina shan maganin ciwon ya fara lafamun, a nan ƙasan tiles
ɗ
in bacci ya kwashe ni, ban san ya Bilal ya ƙare da sahur ba ni dai na farka naga ga gari ya waye tangarau. Se da na watsa r
uwa nayi sallah ina ji na duk ba yanda na saba ba. Jiki na ba ƙarfi sam ga marata dake mur
ɗ
a lokaci lokaci se na kawo ko period ne yake shirin zuwar mun. Dana shiga wanka ma se da nayi amai dan haka na haƙura da zancen azumin ranar kawai. Har na shirya na
sake fitowa falon banji motsin Bilal ba hakan yasa na fita na leƙa part
ɗ
in sa, ta window falo na hango shi yana bacci akan kujera se na koma cikin gida kawai. Ina jin yunwa amma sam bana jin cin komai, a haka na ja Carpet
ɗ
in dana na
ɗ
e na fita dashi na sh
are wajen nayi mopping sannan na kwanta ina jin duniyar na hautsina mun.
Bilal be fito ba se gurin sha biyu saura lokacin har na gama murƙususun ciwo har ya sake ni na miƙe na shiga kitchen ina tafasa indomie da dafaffen ƙwai. Ina tsaye jikin cabinet i
na jiran indomin ta ƙarasa na sauke ya shiga kitchen
ɗ
in, muka ha
ɗ
a ido se naga kamar harara ta yayi kafin ya mayar da idon sa kan bowl
ɗ
in dana saka ƙwai biyun dana dafa ina jira su huce na
ɓ
are. Gaban deep freezer ya wuce ya bu
ɗ
e ya shiga
ɗ
aga kayan ciki
ni dai na wuce na kashe gas ganin indomin ta mun yanda nake so. A fusace ya
ɗ
ago ya kalle ni yace
"Ina kifin dana siyo jiya?"
Nayi kamar banji ba ina
ɓ
are ƙwai na se da ya maimaita da lafazin daya fi na farko kauri kafin na dakata na juya gaba
ɗ
aya ina
kallon sa nace
"Na zuba shi a sink zan wanke ƙarnin sa ya tayar mun da zuciya kafin na kar ga matsawa amai ya ƙwace kuma babu yanda za ayi ya ciyu shi yasa na zubar dashi"
"Kika zubar saboda kin yi hauka ko me? Ce miki nayi sato shi nayi ko a ƙasa n
a tsunto da zaki yi amai akai ki zubar saboda baki san zafin ku
ɗ
i ba Halima?" Ya fa
ɗ
a fuskar sa na amayar da fushin dake cikin zuciyar sa. Yaci gaba da cewa
"Tsabar baki da mutunchi baki san darajar ku
ɗ
i ba shine zakiyi amai akan abin da za a ci kuma b
a kunya ba tsoron Allah kike gaya mun kin zubar kifin dubu biyun kina zuba mun a shara, to wlh idan kin saba
ɓ
arnatar da abinci a gidan ku saboda sangarta ba a ce miki komai ni a nan ba zan
ɗ
auka ba dan ba sato ku
ɗ
in nake ba da gumi na nake neman su. Kin h
aramta kifi kin zubar sannan kin mun asarar hypo roba guda da abun wanke wanke to wlh bazan
ɗ
auka ba ki kuma kwana da sanin se kinyi nadamar abin da kika yi" ya ja tsaki kamar ze katse harshen sa kafin ya buga murfin freezer ya wuce ni yana cewa
"Aikin ba
nza kawai mace babu abinda ta sani se taci ta kwanta ta
ɓ
arnatar maka da abinci".
[5/18, 14:39] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN
OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in kara
tu yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp t
a sama*
*Page 13*
Kasaƙe nayi ina kallon sa har ya fice daga kitchen
ɗ
in lokaci
ɗ
aya jiki na yayi sanyi lanƙwas kamar an watsa mun ruwan sanyi. A hankali na ajiye bowl
ɗ
in hannu na na dafe drawer baya na da hannu biyu jin jiri na neman
ɗ
iba ta. "Sam
wannan ba Bilal bane, ba halin sa bane akwai wani abu da yake damun sa tabbas" abin da na furta a fili kenan cikin son ƙarfafawa kaina guiwa da kuma bawa kaina tabbacin ba cikin sani Bilal yayi mun wannan tozarcin ba. Nafi minti biyar kafin na tattara ƙarf
in daya rage mun na bi bayansa zuciyata na ƙarfafa ni da naje naji me ya same shi? A bakin ƙofar
ɗ
akin na ci burki na kasa shiga saboda yanda zuciya ta take bugawa fat fat. Ba zan iya jurewa ya sake gaya mun wasu maganganun ba zuciya ta zata iya bugawa amm
a kuma ina da buƙatar sanin me yake damun sa? Waye ya tunzuro shi haka ko ma im ce wasu shai
ɗ
anu ne suka shafe shi?.
Ina kama hannun ƙofar aka bu
ɗ
e daga ciki, mukayi ido hu
ɗ
u ya jefe ni da kallon da na kasa mantawa kafin ya ja tsaki kamar ze ture ni ya
fice, daga in da nake na jiyo yanda ya buga ƙofar get. A nan gurin na sulale na zura kaina cikin cinyoyi na se dai hawaye ko
ɗ
is be zubo mun ba zuciyata ce ka
ɗ
ai take suya wani abu me
ɗ
aci da maƙaƙi na yawo cikin maƙoshi na. Nafi minti ashirin a zaune a g
urin kamar ma ba a duniyar nake ba, kalaman Bilal na mun amsa kuwwa tamkar a lokacin yake fa
ɗ
a mun su. Jin ana kiran wayata a karo na uku yasa na yunƙura daƙyar na tashi, Mama ce take kira na, na san har idan na amsa tilas zata fahimci halin da nake ciki h
akan yasa na mayar da wayar na ajiye na kwanta akan kujera.
A nan na wuni sur sallah ka
ɗ
ai ke tayar dani gaba
ɗ
aya ji nayi duniyar tayi mun duhu komai ya ha
ɗ
e mun na kuma rasa ta ina zan fara gyarota, wa zan kira na fa
ɗ
a masa matsala ta? Ban san me yas
a sam naji na kasa kiran Anty Labiba ba dukda ita ta fara zuwar mun se kuma Hansa'u amma duk su biyu dana tuna basa son Bilal se naji be kamata na kai kuka na kan abin da ya shafe su gurin sa ba daga ƙarshe na yanke shawarar na shanye
ɓ
acin raina ni ka
ɗ
ai
tun da dama cikin nasihohin da aka mun an jaddada mun muhimmancin riƙe sirrin gidan aure na.
Rashin cin abinci da
ɓ
acin ran da nake ciki suka haifar mun da ciwon kai da ciwon ciki me tsanani. Shida saura Bilal ya dawo, sama sama nake jiyo muryar sa da
alama waya yakeyi yana ta raha amma dana
ɗ
aga kai bayan daya turo ƙofa ya shigo gani nayi ya ha
ɗ
e rai tamkar be ta
ɓ
a dariya a rayuwar sa ba. Tsayuwa yayi a kaina yana kallo na, nayi kamar bacci nakeyi ina jin sa ya saki tsaki kafin ya wuce yana ƙunƙuni se
na bishi da kallo hawaye na gangarowa ta gefen ido na, kitchen ya shige, daga can naji ya fara kiran suna na ban amsa ba se gyara kwanciya da nayi na bada baya ina goge hawayen da suka
ɓ
alle mun.
"Wato baki ma
ɗ
ora mun abin shan ruwa ba ko? Na lura nem
a na kike yi da fiti na Halima. Iya asarar da kika mun bata ishe ki ha yanzu kuma hora ni kike so kiyi da yunwa ko? shikenan kiyi yanda kika so" ya fa
ɗ
a ni dai ban juyo ba ya wuce
ɗ
aki be
ɗ
auki lokaci ba ya fito ya sake shiga kitchen ina jin sa yana ha
ɗ
a t
ukwane yana gwarawa ƙarar tana shigar mun har tsakiyar kai. Ina kwance a gurin aka kira sallah na yunƙura na tashi da ƙyar ina dafe da kaina ga ciki na daya fara yamutsawa dalilin ƙamshin suyar ƙwai daya fara tasowa daga kitchen
ɗ
in.
A hankali na kalli
Bilal ya fito daga kitchen da plate me
ɗ
auke da ƙwai da cup
ɗ
in shayi. Kan center table ya ajiye su ya wuce cikin
ɗ
aki, ganin ƙwan da ƙamshin daya sake kusanto ni ya hautsina mun zuciya. Da ƙarfin da ban san in da na same shi ba na miƙe muka ci karo a bak
in ƙofa yana shirin fitowa ni kuma zan shiga ganin yanda na tafi zan kifa ya ruƙoni kafin na ƙwace aman da nake dannewa ya fi ƙarfi na na shiga kwarara masa a jiki. Irin kallon da yake mun ka
ɗ
ai naji gara ya rufe ni da masifa ko ya doke ni yafi wannan kall
on. A ƙasa na kwanta ina juyi cikin aman saboda wani irin yanayi da nake ji da bazan iya fasaltawa ba. Bansan ko imani ne ya shige shi tausayi na ya kama shi ba ya tsugunna dukda kallon da yake mun wanda daga baya na fahimci na ƙyamar ƙazantar aman da nayi
ne be bar fuskar sa ba ya shiga kiran sunana yana tambayata menene. Da hannu na nuna masa kaina da ciki na, tashi yayi ya cire rigar jikin sa ya ajiye a gurin sannan ya
ɗ
auke ni, se da ya
ɗ
auraye mun jiki da ruwan
ɗ
umin da nake jin kamar ruwan dalma yake
watsamun take zazza
ɓ
i ya rufe ni.
Yana tsaki kamar ze katse harshen sa ya gyara gurin aman tsaf ya goge ya fesa room freshener sannan ya
ɗ
auraye kayan sa da nawa da suka
ɓ
aci kafin ya gama bacci ya kwashe ni ban zan ya ya ƙare ba se cikin dare na farka
yunwa na neman yin ajali na. A kan center table na samu sauran jallop
ɗ
in shinkafa daya ci ya rage na cinye na ha
ɗ
a da sauran wacce na gani a tukunya sannan na fara gane kaina. Ƙarfe uku da kwata lokacin, a falo nayi sallar magriba da isha'i da banyi ba i
na lazumi Bilal ya fito daga
ɗ
aya
ɗ
akin. Kallo
ɗ
aya ya mun ya wuce kitchen, zuciya ta ta shigan bugawa ina jira na ji ya fara masifar abincin da naci amma naji shiru se gashi ya fito da cup da ruwan zafi ya ha
ɗ
a tea a kan dining ya zauna yasha da ƙaton bre
ad
ɗ
in sa bayan ya gama ya koma
ɗ
aki ya canzo kayan jikin sa ba tare da yayi mun magana ba ya tayar da sallah nan kusa da in da nake.
Ina zaune gurin ya dawo daga sallar asuba, kan kujera ya kwanta ya har
ɗ
e hannunsa biyu bayan kansa yana kallon sama, n
a shafa addu'a na gyara zama ina kallon sa kamar me tsoro na shiga gaishe shi. Nayi mamakin yanda ya amsa ba yabo ba fallasa har ya tambaye ni jiki na na sanar masa babu abunda yake damu na a lokacin.
"Naga dankali da doya da wasu kaya a
ɗ
akin can" ya fa
ɗ
a bayan daya tashi zaune, kaina na ƙasa na ce
"Eh, Abba ne ya aiko da su shekaran jiya"
"Shine baki fa
ɗ
a mun ba?" Ya fa
ɗ
a cikin sautin daya fi na farko taushi. Se na
ɗ
aga kai na kalle shi maganganun daya ya
ɓ
a mun jiya suka shiga dawo mun take ido na ya
ciko da hawaye na sadda kaina ƙasa ba tare da nace komai ba.
"Zan kwanta, idan ƙarfe bakwai tayi ban farka ba ki tashe ni" ya fa
ɗ
a yana komawa cikin kujerar ya kwanta. Hakan da yayi ya nuna mun ya huce daga fushin jiyan, amma ni kuma cin mutunchin da
ya mun fa? Shikenan a ganin sa komai ya wuce?
"Amma Bilal abinda ka mun jiya kana ganin ka kyauta?" Na fa
ɗ
a murya ta na karyewa. Se ya tashi zaune yana kallo na yace
"Kin sani bana son dawo da abinda ya wuce karki
ɓ
ata mun rai Halima" daga haka ya miƙe
ya shige
ɗ
aki ya barni a zaune na rakashi da ido. Duk yanda naso na ƙarfafi kaina na nunawa Bilal jin zafin abin da ya mun na kasa, ganin ya sakko kawai se na lallashi zuciyata nima na haƙura. A haka azumi ya fara ja har an kai na goma. Daƙyar nayi guda h
u
ɗ
u saboda yanda lafiya tayi mun ƙaranci. Ciwon mara da ciwon kai suke damuna ga amai ba dama na shaƙi ƙamshin abinci ko banyi aman ba nayi ta kakari kenan. Munje chemist da Bilal suka rubutamun magungunan malaria harda allura ta kwana uku an mun amma banj
i sauƙi ba. Ganin lokacin al'ada ta ya wuce yasa na fara zargin ko ciki ne dani.
Ranar da aka kai azumi na goma tun yamma dama yace mun idan an sha ruwa zamu je gidan su mu gaishe su haka yasa dana tashi yin abin shan ruwa nayi da
ɗ
an yawa zan
ɗ
ibar wa
Hajjansu. A raina na raya se yayi magana dan kullum ne se yayi mitar ina dafa abinci yana yin yawa da zarar yaga kwanuka ze fara bu
ɗ
e bu
ɗ
e yana mitar duk cikin mu zamu cinye wannan a hakan ma ba wani abin kirki nakeyi ba saboda bana jin da
ɗ
i baya wuce abu
biyu me dan sauƙin saraffawa na bu
ɗ
a baki se kuma abinci da za'a sake ci da kuma lokacin sahur amma haka ze yi ta surutun nayi da yawa kuma a hakan ze cinye tas har ya ringa cewa beyi sahur me kyau ba. Dama ƙiri ƙiri ya hanani yin kunu da ƙosai na sadakar
da nayi niyya wai da me zanji?
A kwando na jera kwanukan abincin dana zuba, ina jin kamar zazza
ɓ
i ze rufe ni amma na daure, a sabon mashin
ɗ
in daya bu
ɗ
e shekaran jiya muka fita. Tun lokacin biki yace mun ya siyar da mashin
ɗ
in sa se yanzu ya sake siya
n wani. Muna tafe muna hira gwanin sha'awa har muka isa gidan a raina nayi gulmar yanda bece komai ba daya ga basket
ɗ
in abincin,
kamar Hajiyar su zata goya ni haka ta ringa nan nan da ni. Taji da
ɗ
in abincin dana kai mata, ina zaune ta soya mun ƙosai tac
e tasan da yawan mutane sun fi son ƙosai da an sauke daga mai shiyasa da yace zamu zo ta ajiye ƙullin. Sosai kuwa naci ƙosan da kunun tsakiya a nan take gaya mun ai geron da waken ma daga gidan mu aka kawo musu harda buhun shinkafa dana sugar da pastar man
gya
ɗ
a. Se gurin goma saura muka bar gidan, a hanya naga gurin gasa tsire tun daga nesa naji raina ya biya dan haka nace masa dan Allah ya tsaya ya mu siya ba musu kuwa ya tsaya ya siya muka wuce gida.
A haka aka ƙara azumi biyar, tun washe garin da muk
a je gidan su nake jira naji yace na shirya muje gaida nawa iyayen amma shiru. Har Mama se da ta gaji ta mun magana akan yaushe zamu zo? Na ce mata bani da lafiya ne amma zamu zo, Allah sarki uwa washe garin da mukayi maganar kuwa se ga Imam da Amira da Na
bila yar ƙanwar Abbanmu Anty Surayya da tazo hutu gidan Mama tace su zo su dubani. Ran da aka kai azumi na sha biyar
ɗ
in tun asuba na masa zancen se yaushe zamu je gidan mu ne?
"Akwai abin da nake jira ne kin ga ai ba da
ɗ
i muje musu hannu haka babu wat
a tsaraba" amsar daya bani kenan. Se nace masa
"Yanzu ita Hajja ba haka muka je muka gaishe ta ba bamu kai mata komai ba suma gaisuwa ce ai ba wani abu aka ce dole se an kawo ba". Kamar baze yarda ba har na fitar da rai kuma bayan la'asar ina ƙoƙarin
ɗ
ora
abin shan ruwa yace na shirya kawai ya kaini gidan. Sosai naji da
ɗ
i, da muka je be shiga ba ya ce mun se ya dawo
ɗ
auka ta tukunna yanzu sauri yake ana jiran sa a wani guri. Mama na kitchen da Nabila suna aiki ta ringa kallo na da mamaki na rungumeta cikin
jin da
ɗ
in ganin ta dan rabo na da gidan tun zuwan da nayi