Showing 75001 words to 78000 words out of 287295 words
/>
ɗ
a a fili ina bin ƙofar daya bugo da kallo, wato in kore ta, ni ze shafawa kashin kaji kenan? banda ma ya raina mun wayo me yasa s
hi da aka gayawa zata zo be ce aa ba se yanzu ni in koreta in yaso a sakani a bakin duniya ace na kore ta daga gidan
ɗ
an uwanta to wlh ba zanyi ba.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up th
e story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya ju
ya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access
bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*Page 17*
Be ko saurari tayin abincin da na masa ba ya fice daga gidan bayan yayi wanka yana sake jaddada mun Fadila ta bar gidan kafin ya dawo, bayan fitar sa na shiga gyara fal
on da tayi mun kaca kaca da shi dan tun shigowar Bilal
ɗ
in ta koma
ɗ
aki na in da na sauketa. Na tabbatar taji banbamin da yakeyi tun da ba a hankali yayi maganar da ze fita ba, na
ɗ
auka daya fitan zata tuntu
ɓ
e ni da zancen amma shiru se ma dawowa falo da t
ayi zata sake tarwatsa gurin na dakatar da ita ta hanyar ce mata ba nisa yayi ba yanzu ze dawo. Ina kallon ta ta harare ni harda murgu
ɗ
a baki ta koma
ɗ
aki.
Ranar raba dare mukayi muna tashin hankali da Bilal tunda ya dawo gurin goma ya tarar Fadila bata
tafi ba ya tasa mun masifa tun ina bashi haƙuri da nuna masa rashin dacewar abinda yake son nayi har na kai bango nace ba zan kore ta ba ai ƙanwar sa ce kuma gidan sa ne idan da gaske baya buƙatar zamanta ya kore ta da kansa mana shikenan fa ina wuta ya s
akani a ciki ya ringa zazzaga da tijara se naga ashe abinda ya mun akan kifi ma somin ta
ɓ
i ne. Dana gaji na kwanta na juya masa baya se dai na kasa bacci ga
ɗ
an Fadila da kamar ma sa gayya yake ta canyara uban kuka duk suka ha
ɗ
u suka cazamun ƙwaƙwalwa.
Daƙyar na iya farkawa nayi sallah bayan dana samu bacci ya
ɗ
auke ni, sosai kaina yake mun ciwo ga zuciya ta da babu da
ɗ
i. Ina idar da sallah na sake komawa na kwanta ban farka ba se ƙarfe tara harda wani abu. Se da nayi wanka sannan na fita daga
ɗ
aki, Fadi
la na har
ɗ
e akan kujera da remote tana canza tasha, yanda ta kalle ni se ka
ɗ
auka kishiyar ta ce ta fito ta wani basar ta maida kai abinda takeyi nima kallo
ɗ
ayan na mata na maida hankali na kan falon dake nan kamar yayi sati bega gyara ba ga kwanukan abin
cin a ajiye har sun bushe alamar ba amfanin safiyar nan bane harda cup dana hango sauran shayi a ciki.
Ji nayi zuciyata ta sake harzuƙa, ni ya kamata nayi jidali an kawo mun baƙuwa ba tare da an sanar da ni ba kuma tazo tana nema ta mayar mun da gida w
ani dandalin yan datti ga wani sabon raini da ban santa da shi ba tana nema ta fara gwada mun. Kitchen na wuce ba tare da na ce mata kanzil ba, ko me tayi tunani kuma se ji nayi tace
"Ina kwana Anty, se yanzu kika tashi kenan?"
Da lafiya na amsa mata na
shige kitchen, nan
ɗ
in ma kaca kaca komai yana zaune da ƙafarsa. Se da na gyara gurin tas kafin na bu
ɗ
e fridge in fito da abincin da Bilal yaƙi ci se in
ɗ
umama mu ha
ɗ
a da baƙin shayi tunda
banga alamar ya siyo abin karyawa ba, banga abincin ba se lokacin
nayi realizing ai nama wanke kwanon cikin kayan dattin dana tarar a kitchen
ɗ
in. Tunanin wanda yaci na tafiyi, nasan ba Bilal bane zuciyata ta raya mun Fadila ce.
Ina tsaka da jimamin irin wannan abu ta shigo kitchen
ɗ
in tana ha
ɗ
a fuska kamar zatayi ku
ka tace
"Kun san da masu jego a gidan saboda Allah se ku kwanta kuyi ta bacci? Ni wlh yunwa nakeji har jiri nake gani asan yanda za'ayi dani".
Ba yabo ba fallasa nace mata
"Wace abinci kuma kike nema bayan wanda kika ci?" Yanda tayi da ido kamae irin
na mata ƙage se kuma ta watsa ido tace
"Wai abincin cikin fridge? Yunwa ce ta hanani bacci tun dare naci wannan na duba ma naga ko da dankali ko doya in soya mana naga babu se wani sauran bread na samu akan dining na ha
ɗ
a shayi nasha amma ji nakeyi ma ka
mar ƙara mun yunwar akayi". Tunda ta fara magana nake kallon ta har ta kai aya, mamakin ƙarfin halinta nayi. Ɗan bread
ɗ
in da take cewa fa ka
ɗ
an ne babu a guda in da dani da Bilal muka ci har saura se yayi mana shine take cewa wai beje mata ko ina ba.
Rufe fridge
ɗ
in nayi ba tare da nave mata komai ba na wuce store, banda shinkafa da ƙwarorin taliya da macaroni babu abin da yayi saura a ciki, taliyar na
ɗ
auka na ha
ɗ
a da papper mix guda
ɗ
aya daya mun saura na dafa mana mukaci ina jinta a wasance tana cew
a wai na bata abinci babu kifi babu nama nayi kamar ban ji ba dan raina a
ɓ
ace yake bana so kuma na furta wani abu da daga baya ze zama abin magana tunda naga su basa raina abin laifi. Bata tayani da ko cangwal ba na aikin gida se hayaniyarta data
ɗ
an ta d
ata cika mun kunne. Ina gamawa na koma
ɗ
aki na kulle ƙofa ta na bari akan tunda akwai sauran taliyar taci da rana.
Tunda na kwanta bacci ya kwashe ni ban tashi farkawa ba se ƙarfe uku harda mintoci na rana. Sallah na farayi kafin na leƙa naga halin da
Fadila suke ciki, falon babu kowa se pillows dake hargitse kamar anyi wasan dambe. Ɗaki na leƙa nan ma bata nan babyn ta ma baya nan balle nayi zaton ko ban
ɗ
aki ta shiga. Tunani na shigayi ina ta tafi? In da akwatin ta ke ajiye na duba nan ma babu hakan ya
tabbatar mun da fitar taje ta dawo tayi ba ƙila gida ta koma amma me yasa zata tafi bata gaya mun ba?
Ji nayi hankali na ya tashi, kar dai Bilal ya dawo ya kore ta, amma kuma da ya dawo gidan dole ze tayar dani ko da yake tunda ba abin ƙwarai zeyi ba
be zama lallai ya tashe ni
ɗ
in ba tunda yasan zan hana.
Duk se naji babu da
ɗ
i, layin ta na shiga kira wayar tayi ta ringing ba'a amsa ba dana sake kira kuma se na jita a kashe. Har na mayar da akalar kiran kaj Bilal se kuma na katse na bari idan ya dawo z
anji dalilin da yasa be haƙura ba ya koreta. Haka na ƙarasa wunin rai babu da
ɗ
i, biyar da rabi ya dawo sallama ma ciki yayi be amsa sannu da zuwan da nake masa ba ya wuce
ɗ
aki abin sa se na tashi na bishi. Ganin ya shiga wanka se na koma na ha
ɗ
a masa abinc
i, shinkafa da wake da mai da yaji dan bani da ko ƙwayar attaruhu balle nayi miya ko jallof nasan kuma yanda yake fushin nan ba siyowa zeyi ba. Har ya zauna na manta ban aje masa ruwa ba na koma na
ɗ
akko da sauran zo
ɓ
o roba
ɗ
aya daya rage Fadila bata shany
e ba.
Yana ci ina satar kallon sa yanda kasan me cin guba, na tabba harda yunwa tasa shi ci ba tare da yayi ƙorafi ba. Se da ya kammala ya dawo cikin falon kafin na matsa kusa dashi ina cewa
"Kuma
ɗ
azu daka dawo se baka tashe ni ba"
Kallon rashin fa
himta ya mun, ban damu ba naci gaba da cewa
"Yanzu saboda Allah duk yanda nayi maka magana baka haƙura ba se da kace ta tafi? Haba Bilal, a zato na ko can wata bare ce tazo gidan nan cin arziƙi ai beci ka koreta ba balle ƙanwar ka uwa
ɗ
aya uba
ɗ
aya ashe m
a duk fa
ɗ
ar da kake tana da matsayi a gurin ka duk surutu ne
gaskiya baka kyauta ba kuma ban ji da
ɗ
i ba gashi na kira wayar ta ma bata amsa ba nasan fushi tayi".
Kanzil bece mun ba, abu da me ciki abu ka
ɗ
an ke hasala ni u duk hidimomin su shara mopp
ing yayi shirin aiki ya fita. Se da ya tafi na tuna ban tambayeshi zan fita ba, a waya na kira shi nace masa zanje gida na duba Amirah dan tayi zazza
ɓ
i se yace na bari idan ya dawo se muje tare. Na sake gwada kiran Fadila ta bu
ɗ
e wayar amma haka ta ƙaraci
ringing bata amsa ba se na kira Abubakar dan hankali na ya kasa kwanciya ina so na tabbatar da lafiyarta tunda ko babu komai daga gida na ta tafi. Abubakar yace mun ta koma can gidan su taje tana kuka ya tambaye ta meya faru taƙi gaya masa sanin da zeyi ba
ze wuce ita da Bilal bane shi yasa ma be biyo kadin dawowar tata ba kuma yau da safen ta tafi gidan Anty Amina babbar yayar su. Ni dai tunda naji tana lafiya shikenan can su ƙarata da
ɗ
an uwanta shi ya kore ta ba ni ba.
Kwana uku tsakani Hajja ta dawo,
ita da aka ce zatayi sati biyu. Tun ana gobe zata dawo
ɗ
in Bilal ya gaya mun dake naje gida na samo yan ku
ɗ
i se nayi amfani dasu nayo cafane nayi mata girki yan da naga Anty Labiba tana yi idan surukar ta tayi tafiya ta dawo zata mata girke girke ta kai m
ata. Da wuri suka iso dan asubanci suka yo kamar sanda zasu tafi, da la'asar bayan ya dawo aiki yayi wanka na kwashi kwanuka ya goya ni a mashin muka tafi gidan, rabon ayi. Da ace nasan abin da yake jira na a gidan da ban yi giggiwar zuwa mata sannu da zuw
an ba. Da Yaya Uwani wadda Bilal yake bi muka fara cin karo a soro zata fita mu kuma zamu shiga, da fara'a na shiga gaishe ta, irin kallon banzan data watsa mun ha
ɗ
i da tsaki yasa jiki na yayi sanyi laƙwas nabi bayan Bilal da dama be tsaya ba.
"Yanzu ke
har kina da kunyar da zaki sake tako ƙafar ki cikin gidan uban Fadila?" Kalaman da Hajja tayi mun maraba dasu kenan. Nayi zuku
ɗ
i ina ƙoƙarin tantance in da maganganun ta suka dosa amma na kasa se kawai na zura mata ido ina jin irin fisaji da cin mutunchin
data ke mun a maganganun nata nayi nasarar gano akan Fadila takeyi. Bani ka
ɗ
ai ba hatta iyaye na dake can gida basu san wainar da ake toyawa ba se da suka amsa rabon cin mutunchi a gurin Hajjan,
"Da
ɗ
in abun tun kafin uban ki yasan zeyi arziƙi a duniya ub
an Fadila yayi da har zaki mata gorin gida gidan ma na
ɗ
an uwanta da idan ya fa
ɗ
i ya mutu yanzu tana da gadon sa. Ko da yake ba laifin ki bane, laifin sa ne daya barki kika bararraje har kike tunanin kin ci gida se wanda kika ga dama ze shiga ya zauna" ta
fa
ɗ
a tana kumfar baki.
Sautin kukan da na keyi ƙasa ƙasa ya ƙaru, a duniya ka mun komai karka zagi iyaye na ko kaci mutunchin su.
"Haba Hajja ki bari mana ya isa haka" naji muryar Bilal, se na
ɗ
aga kai na kalle shi dan ban ta
ɓ
a zaton yana
ɗ
akin a tsa
ye Hajjan take mun wannan tijarar kuma yayi shiru ba.
"Yanzu kana tsaye kana ji ana tuhumata da laifin daka aikata?" Na fa
ɗ
a cikin kuka, ya kalle ni yace
"Ban gane ba?"
Kan Hajja na juya ina kukan nace
"Allah shine shaida ta ban kori Fadila ba, idan
kuma zata fa
ɗ
i gaskiya ni ko kallon banza be ha
ɗ
a ni da ita ba balle nace ta bar gida. Ina ruwa na da zaman ta? Shi me gidan ai gashi nan shi yace baya buƙatar zaman ta kuma Allah shaida sanda ya kore ta ma bana gurin kuma kana tsaye kana kallo ana tuhumat
a ba zaka fa
ɗ
i gaskiyar abinda ya faru ba" na ƙarasa ina kallon Bilal daya tsuke fuska yana muzurai.
Hajja ta rafka salati ta shiga tafa hannu tana cewa
"Ba shakka yau naga in da ake bariki, kai Bilal uwarka Halima na magana se ka rufe ni da duka sabod
a ma mata ƙazafi". Maimakon ya kare ni se gani nayi ya juya ya fice daga
ɗ
akin gaba
ɗ
aya ita ko kamar an iza wuta taci gaba da maganganu tana fa
ɗ
ar duk abin da yazo bakin ta. Daƙyar ina ganin dishi dishi na miƙe jin tijarar bame ƙarewa bace, Allah ya taima
ke ni ina fita daga gidan na samu Napep kai tsaye na wuce gidan mu. Ina rusa kuka na shiga gidan ba tare da na ko sallami me Napep
ɗ
in ba ya biyo ni yana tambayar ku
ɗ
in sa.
A ƙasa na zube ina cigaba da rusa kuka Mama dake kitchen ta fito kusan a guje t
ana tambayar waye? Gani na yasa ta ƙaraso da sauri ta
ɗ
ago ni cikin tashin hankali tana cewa
"Meya samu Bilal
ɗ
in?". Se da naji numfashi na na neman
ɗ
aukewa kafin na haƙura na dena kukan amma naƙi cewa komai tun Mama na tambayata harta tashi ta barni ta k
ira Abba a waya tace masa gani nazo ina kuka naƙi cewa komai yace mata karta kira kowa gashi nan zuwa. Ina kwance ina jan rai, wani irin azababben ciwon kai ya dirar mun lokaci
ɗ
aya. Ina kwance riƙe da kai Abba ya dawo, tiryan tiryan na kora musu yanda aka
yi tun daga zuwan Fadila har zuwa yau
ɗ
in. Mama ta zabga tsaki tace
"Tun wuri ki nemi yafiya ta dan wlh kin
ɗ
auki alhaki na gaba
ɗ
aya kin tada mun da hankali na
ɗ
auka ma wani tashin hankalin ne ya afku" Abba ma miƙewa yayi yace
"Allah ya rufa asiri" da
ga haka ya fice daga
ɗ
akin. Mama ta dira mitar
ɗ
aga mata hankalin da kuka na yayi kafin ita ma ta fita ta bani guri. Se naga su abun ma be dame su ba kenan, ba ma wanda ya sake bi ta kai na se da akayi magriba Mama ta leƙo ni lokacin har baccin wahala ya f
ara fizgata kai na na ciwo sosai. Se da naci abinci nasha magani nayi wanka kafin na kwanta. Bilal be kira ni ba har kuma bacci me nauyi ya kawashe ni be zo ba se da safe Mama take cemun wai miji na yazo tayi ta tashi na ban farka ba shine yace a barni kaw
ai.
"Se ki maza ki gama abin da zakiyi Mu'azzam ya kai ki gida dan jiya har gurin sha
ɗ
aya yana nan se kace wanda aka ce za'a cinye ki" Mama ta fa
ɗ
a. Nayi rau da ido nace
"Da yazo kin masa maganar abun da Hajjan su ta mun?"
"Ni kuma a wane hurumi? Wa
nnan ai tsakanin ku ne kun fi kusa shikenan kuma saboda kinyi ba daidai ba maman mijin ki ta miki fa
ɗ
a se na shiga na
rama miki kike nufi ko me?" Mama ta fa
ɗ
a. Se ko hawaye suka
ɓ
alle mun ta miƙe tana cewa
"Kin so dai ki ƙarawa kanki wata damuwar banda ha
ka wanda ya siyi rariya ai dole dama yasan zata zub da ruwa. Duk mutumin da Allah ya ha
ɗ
a ka zama dashi se dai haƙuri da taka tsantsan kawai abinda ya rigada ya faru kuma ai ya faru se dai ayi rigakafin wanda be zo ba" ta fa
ɗ
a tana ficewa daga
ɗ
akin.
B
a dan raina ya so ba se dan rasa goyon bayan Mama na tattara Mu'azzam ya kaini gida da yamma na ringa share hawaye a hanya, an mun wulaƙanci na tafi gidan mu akan su shiga su ƙwatar mun yanci ba daraja sun koro ni yanda gobe ma za'a ji da
ɗ
in sake ƙala mun
abin da ban aikata ba aci mun mutunchi da gangan. Yau na ga ranar Anty Labiba, ita ka
ɗ
ai ce zata tsaya mun amma da nauyi abun da
ɗ
i be kaini gidan