Showing 183001 words to 186000 words out of 287295 words

Chapter 62 - KURA A RUMBU COMPLETE

gaya maka haka ni yarinyar nan ganinta nake kwana biyu ma kamar wacce iskoki suke ta

ɓ

awa yanzu zata birkice ta fara masifa abund

a ba halinta ba ko kuma duk zullumin auren ne ban sani ba".

[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*

*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*

*Wattpad @MaryamahMrsAm*

*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-

mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*

*Ku

ɗ

in karatu yana wakiltar mutum

ɗ

aya ne, kiji tsoron Allah karki

ɗ

auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*

*KURA A RUMBU littafin ku

ɗ

i ne, a biya na

ira 800, biya a asusun*

*1840175439*

*Access bank*

*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 42*

A yayinda muke shirin kammala wannan littafi idan har kin san kina karantawa ba tareda kin siya ba kiyi ƙoƙari ki sauke

nauyi domin babu lallai in yafe haƙƙina

🙏🏽🙏🏽

Cike da ƙaguwa da zancen ya ce

"Yanzu dai Umma wanne ake so a ciki? Lefen ko kuma ku

ɗ

in za'a bayar ko ayi mata kayan yanda tace?"

"To ai ni ba na ce ba, kaga ita Nuratu dai kayan tace tana so to ita

ya kamata ka tambaya itama kaji wanne tafi so" ta bashi amsa sai ya girgiza kai ya ce

"Ai na gaya miki yanda mukayi da ita, dama kuma ni na

ɗ

auka ma kunyi shawarane shiyasa ban tuntu

ɓ

e ki ba dan har na bayar da aikinma, kawai ki fa

ɗ

i wanda za'ayi a ciki

tunda kince tariyar Nuratu nan da sati biyu kamata yayi duka a ha

ɗ

a ai ba wai ayi daban daban ba"

"Toh inaga a bayar da ku

ɗ

in ko dan naji Nuratu nata ƙorafi kayan duk masu duhu aka aka saka mata inaga ya manta bai fa

ɗ

awa musu ha

ɗ

o kayan baƙa bace" ta fa

ɗ

a tana yar dariya, wayarsa ya zaro yana cewa

"Toh idan akwai account

ɗ

in wanda za'a turawa ku

ɗ

in a kusa a kawo idan babu kuma sai ta tura mun in fara saka mata wani abu kafin ƙarshen sati na cika dan na rigada na bayar da ku

ɗ

in kayan Wallahi yanzu kuma k

o nace musu na fasa ba zasu dawowa mun da ku

ɗ

in ba sai dai na nemi wani ya siya tunda kamfani ne"

"Ai ka tura mata a Opay

ɗ

in ta kawai tunda tareda Habiba ƙanwata zasuje kasuwar dama" cewar Umman, sai yayi murmushi yace

"Ai ku

ɗ

in da yaww Umma idan aka

saka mata a opay rufewa zasuyi account

ɗ

in nata ba zai

ɗ

auki ku

ɗ

i da yawa ba"

"Ai kuwa yana

ɗ

auka kwanaki can naji tace anyi bu

ɗ

a mata shi har maliyoyi ma za'a iya sakawa a ciki yanzu amma bari dai tazo muji kar ayi gwari" Umman ta sake fa

ɗ

a kafin ta shig

a ƙwalawa Zulaiha dake la

ɓ

e tsakar gida duk tana sauraronsu kira. Sum sum ta shigo ta tsugunna daga bakin ƙofa, Umman ta ce

"Wai akawun

ɗ

inki nace kamar naji kwanaki kince an bu

ɗ

a miki shi zai iya

ɗ

aukar ku

ɗ

i da yawa?" Da kai ta amsa ganin Bilal

ɗ

in yan

a kallonta, danne danne yayi a waya ya

ɗ

ago ya cewa Umman

"Na tura da miliyan biyu, idan na samu yanda nake so zuwa ƙarshen sati zan ƙara mata miliyan

ɗ

aya idan kuma bata samu ba zan saka

ɗ

ari biyar amma fa duka da ku

ɗ

in lefe dana sallamar amarya". Yanda

kasan Umman zata kwanta tsabar murna ne ko meye oho haka ta baza hijabi ta shiga masa godiya ƙarshe ta fashe da kuka tana jera masa addu'a. Sai da ya sake ajiye mata cash na dubu ashirin daya ruƙo dama zai mata ihisani kafin suka fita tareda Zulaiha zata r

akashi.

Rungumeta yayi da suka isa soro ta janye tana wani

ɓ

ata fuska, bai haƙura ba ya sake kamota yana dariya ta kuma janyewa tana cewa

"Ni dai bana so ni da kacewa yar iska daga gwada abinda aka ce idan ina maka zaka ƙara so na"

Ya ruƙo hannunta

ya ce

"Banda sharri mana baby a yaushe nace miki haka? Kuma ai gaskiya aka fa

ɗ

a idan kina mun hakan zan ƙara sonki kawai na jiye miki tsoro ne kar na kasa riƙe kaina na ha

ɗ

a Umma da gashin amarya" ya ƙarasa yana kashe mata ido

ɗ

aya, rufe fuska tayi da hij

abinta cikin jin kunya tana dariya ya saketa yayi waje tabi bayansa, sai da suka isa gurin mota ta sake ha

ɗ

e fuska. Da mamaki yace

"Wai menene haka kuma? Minti ka

ɗ

an kina fara'a anjima ki ha

ɗ

e rai ko dai dagaske ne da Umma tace tana zargin iskoki suna t

a

ɓ

a ki?"

Baki ta tunzura tace

"Ni ba wasu iskoki kaine kayi mun laifi" sai ya tattara hankalinsa kanta ya ce

"Ni kuma? Yaushe?"

Bubbuga ƙafa ta shigayi kamar yarinya tana cewa

"Ba kaine kawai ka tashi ka ha

ɗ

a ku

ɗ

in kayan lefe da na sallamar amarya

ba? Yanzu wlh sai iya abinda suka ga sama suka bani ni dai da kayi shawara dani Allah ba haka za'ayi ba".

Ajiyar zuciya ya sauke dan ji yayi hankalinsa ya tashi da tace wai ya mat laifi, shi fa baya son

ɓ

acin ranta Allah ma ya sani. Hannayenta ya kamo c

ikin kwantar da murya ya ce

"Shikenan kuma sai ki

ɗ

aga mun hankali kice wai nayi miki laifi akan

ɗ

an wannan maganar?"

"Oh yar magana ce ma a gurinka kenan?" Ta fa

ɗ

a tana ta

ɓ

e baki kamar me Shirin yin kuka. Zagaywa yayi da ita ya bu

ɗ

e mata sit

ɗ

in mai zam

an banza kafin ya dawo ya shiga driver sit ya tayar da motar suka fita daga layin. Gadon ƙaya sukaje ya siyo mata shawarmar daya san tana so a hanya suka sasanta bayan da suka daddale akan sai dai fa ya bayar da 3M

ɗ

in nan idan ya so ta

ɗ

auki 500k na hidim

arta dan ta san duk kashe ku

ɗ

in zasuyi ba za'a bata komai ba. Sauketa yayi ya juya yana tafe a ransa yana mamakin dama Zulaiha ta san ku

ɗ

i haka?

A sanin sa da ita ko kyautar 20k ya mata a dunƙule sai tace sunyi yawa ya rage shiyasa idan ya tashi kawai y

ake siya mata duk wani abu da yasan zata siya da ku

ɗ

i idan ya bata idan ta kama zai bata ku

ɗ

in kuma baya wuce 5k tunda tun tana 200L ya samar mata mai Adaidaita da yake kaita makaranta ya kuma

ɗ

akko kuma yana saka mata Airtime da Data kusan duk sati dan ha

ka ba wani abu zatayi da ku

ɗ

i ba amma ita ce yau suke ja'inja har tana cewa 500k

ɗ

in ma manaji zatayi dan ba isarta zatayi ba. Kamar ya biya gidan Hajja sai kuma ya fasa dan

ɗ

azu da safe da yaje ko arziƙin amsa sallamar sa ba tayi ba daga ƙarshe ma

ɗ

aki ta

shige ta barshi fushi take bilhaƙƙi dashi amma ya san zata sakko nan ba da da

ɗ

ewa ba dan Hajjan bata iya dogon fushi dashi.

Halima ta fa

ɗ

o masa a rai yayi ƙaramin tsaki a fili, idan so samu ne ta dawo kafin Zulaiha ta tare amma kuma yaga tana nema ta

kawo masa wasa itama sannan ga Hajja yanda take akan tsini yanzu bata huce daga wannan fushin ba amma kuma gara tayi lokaci

ɗ

aya ta gama a wuce gurin tunda dai gaskiya a wannan karon sai dai tayi haƙuri amma ba zai iya sakin Halima ba ya san kuma har a gur

in Allah baiyi laifi ba tunda dai Haliman nan babu abinda tayi mata. Shi yanzu duk kewar yaransa ce ma take addabarsa dan tun ranar daya kaisu gidan bai sake ganinsu ba, Al'amin ma a bakin malamin makarantarsu yaji wai anzo an kar

ɓ

ar masa transfer sai ƙary

a ya gilla masa ya ce eh ya koma can gidan kakanninsa ne da zama.

Daya isa gida falon Halima ya shiga, gurin tsaf tamkar tana ciki dan duk bayan kwana biyu sai ya share ya goge ko ina ya kuma kunna turaren wuta dake winduna a rufe suke kuma babu zurga z

urga sai turaren ya sake kama gurin sosai. Ɗakinsa na nan ya shiga ya cire bedsheet

ɗ

in kan Gadon ya canza wani dan yau

ɗ

in kawai yaji a nan yake son kwanciya, wanka ya shiga yana Allah Allah ya fito ya kirata yana wankan yana shirya maganganun da zai fa

ɗ

a

mata a ransa, yana jiyo wayarsa na ƙara ya san ba zai wuce Zulaiha ce take kira ba, sai da ya gama shiryawa kafin ya

ɗ

auki wayar ya tarar da missed calls uku na Zulaiha

ɗ

aya sai na Jalilah guda biyu.

Murmushi yayi yabi bayan kiran Jalilan, dole ce kaw

ai zata raba shi da ita ba dan yana so ba amma Jalilan hannunsa ce ta kowanne

ɓ

angare kuma da ce yana da tabbacin shi ka

ɗ

ai take kulawa da zai iya danne zuciyarsa ya aureta dukda ya san ba zai ta

ɓ

a samun nutsuwa ba saboda kullum zuciyarsa zata ringa saƙa m

asa ko da auren nasa zata iya bin wani a waje amma kuma wasu

ɓ

angarorin da yake morarta ya saka yake jin kamar zai iya haƙuri ya zauna da ita a hakan.

Muryar da take masa magana ka

ɗ

ai a yan sakanni take hargitsa masa lissafi balle aje ga sauran lamura

daga Haliman balle Zulaiha da take nan bagidajiya (a ganinsa

🤣🤣🤣

) babu wacce ta kamo ƙafarta a iya kyau, iya kwalliya, gayu uwa uba kuma iya kula da namiji ta wannan fannin kam dole ma a karya mata

ɗ

an kwali. Yana can zancen zuci ta

ɗ

aga wayar tana ta H

ello Hello harta gaji ta kashe ta kira ya zare wayar da sauri daga kunnensa saboda ƙara.

"Ina ka shige duk yau baka kirani ba" ta fa

ɗ

a bayan daya amsa wayar. Kwanciya yayi akan gado ya kashe murya shima ya ce

"Kema baki kira ni ba"

"Yaushe muka fara

haka? Idan ban kiraka ba kenan ba zaka kirani ba kake nufi?" Ta fa

ɗ

a sai ya tashi zaune dan yaji sautin muryarta ba yanda ya zata ba ya kuma san halin kayarsa idan tana sama abu ka

ɗ

an zai tuzurata shi da yake so ya kar

ɓ

i ku

ɗ

a

ɗ

e a hannunta kuma ina zai bari

suyi fa

ɗ

a?

Cikin kwantar da murya ya ce

"Ba haka nake nufi ba honey tsokanarki naso nayi ban san kuma baki cikin yanayi me da

ɗ

i ba, yanzu dai mai ya samu baby na?" Ya ƙarasa cikin sautin da ya san zai iya samun kanta. Tayi ƙaramin tsaki ta ce

"Ban sa

n me yake damunka kwana biyu ba Bee kawai shiru nakeyi amma gaba

ɗ

aya ka canza, kayi cancelling tafiyarka a die minute sannan kana sane yau ya kamata na tafi amma baka ko kirani ba balle kaji yaya nake ciki anya kuwa babu wani abu da kake

ɓ

oye mun?"

Sa

i da yaji hanjin cikin sa ya ka

ɗ

a, duk ƙoƙarin da yakeyi na kada ya kuskure har ya bada ƙofar da zata zargi wani shiri ashe ya bar baya ba zani, da sauri ya ce

"Kiyi haƙuri Honey pot kin san na gaya miki yanda nake ciki da gurin aiki na gaba

ɗ

aya sun taso

ni a gaba gashi gida ma duk sai a hankali na gaya miki Halima ta tayar da rigima tunda taga chat

ɗ

in mu yanzu haka ma kusan 1 week fa tana gidansu kin san mutanen mu kuma family kowa ya

ɗ

ora mun laifi ana ta cewa na fara wulaƙantata saboda zan kawo wata".

Tsaki ta sakeyi kafin tace

"Ta hutar da kanta ai sai ka aika mata da takardarta kawai dan dama ko bata tafi yanzu ba zata tafi idan na zo dan ka san dai ba zan zauna da kishiya ba"

"Amma Babe munyi maganar nan kin ce kin haƙura ke da ba gidan ku

ɗ

a

ya ba dan Allah menene damuwar ki da ita kuma?" Ya fa

ɗ

a kamar zai yi kuka, daga can tace

"Babu dole fa Bee, idan ita ka za

ɓ

a sai kuyi zamanku ai ba cewa nayi ka saki matarka dole ka aureni ba. Ni dan Allah duk ba wannan ba kazo ka

ɗ

auke ni, kawai sai yau

Salis ya sake tura mun da flight ticket

ɗ

in wai ashe ta Kano ya mun booking na zo kuma anyi shifting flight

ɗ

in sai 8 na safe, duk raina a

ɓ

ace yake wlh kazo ka

ɗ

auke ni na samu nayi wanka ko zan

ɗ

an samu nutsuwa".

Idan da ya san dalilin kiran kenan da

ba abinda zai zaka yabi bayan kiranta kai da kashe wayarsa ma zaiyi gaba

ɗ

aya. A hankali ya ce

"Ayya sorry Babe shine baki kirani tun

ɗ

azu ba kuma?"

"Ai gashi yanzu na kiraka dan Allah idan ba zaka zo ba na nemi taxi zaka cikani da surutunka da baya ƙare

wa" ta fa

ɗ

a a hasale. Kamar ya ce ta nemi taxi

ɗ

in sai dai ya ce

"Toh mai zai hana ki kama lodge mana anan kawai tunda da safe ne kar kuma kiyi nisa sosai"

"Tun yaushe ka fara shirya mun abinda ya kamata nayi da wanda ba zanyi ba Bilal?" Ta fa

ɗ

a kamar

wata uwarsa, da sauri ya ce

"Kiyi haƙuri gani nan zuwa" tayi tsaki ta kashe wayar.

Tashi yayi ransa duk ba da

ɗ

i, kamar ya kirata yace ta hau taxi kawai sai dai kuma baya so ya

ɓ

ata rawarsa da tsalla gara dai su rabu lafiya idan buƙatarsa ta gama cika

daga nan shima zai bu

ɗ

e mata shafin nasa rashin mutunchin. Haka nan badan ya so ba ya kama hanyar Airport

ɗ

in sha

ɗ

aya harta gota bai yi nisa ba sai ga kiran Hafiz, sai da ya gangare gefen titi ya kashe motar kafin ya amsa cikin muryar bacci.

"Afuwan na

tashe ka daga bacci" Hafiz

ɗ

in ya fa

ɗ

a, ya sake maƙale murya ya ce

"Ina zaune ne banma san baccin ya

ɗ

auke ni ba". Daga can Hafiz

ɗ

in ya ce

"Dama Jalilah ce ta shigo Kano, ka santa da hayyata ta kirani wai anyi shifting flight

ɗ

in ta zuwa safiya in samo

mata mai Taxi da na sani dare yayi tana jin tsoro ita bata san Kano sosai ba shine na kiraka ko zaka ma Abokinka me Uber

ɗ

in nan magana idan bai tashi ba dan Allah yaje ya

ɗ

auke ta ya sama mata hotel nan kusa da Airport

ɗ

in".

"Wai Ammar? Ai ya samu aik

i Lagos yana can kusan wata shida kenan ya dena Uber, amma bari akwai wani da ya

ɗ

auke ni kwanaki nay saving number sa kuma

ɗ

an nan kusa damu ne bari naji idan bai tashi ba ka tura mun number ta" cewar Bilal

ɗ

in, yana aje wayar kuwa Hafiz

ɗ

in ya turo masa

number ya wani ta

ɓ

e baki bayan daya kunna motar ya cigaba da tafiya. Rai

ɓ

ace ta zauna a motar bayan daya isa, ha

ɗ

e fuska yayi shima yana kallonta ya ce

"Na ce miki ina hanya shine kuma kika wani kira Hafiz ya nemo miki Taxi ko?"

Harara ta balla masa t

ace

"Ai naga alamar wuyanka ya fara kauri ne har in ce kazo ka

ɗ

auke ni ka ce wani na kwana a nan shiyasa na kirashi dan nasan ƙarshe kai

ɗ

in dai zai turo ka

ɗ

auke ni". Kallonta kawai yayi kafin ya

ɗ

auke kai gefe yayi ƙwafa sannan ya ce

"Yanzu ina zan

kaiki?"

"Gida na" ta bashi amsa tana danna kiran layin Hafiz. Fuzge wayar yayi da sauri ya katse kafin ya ce

"Me zaki gaya masa kuma?"

"Zan gaya masa kazo ne mana" ta bashi amsa tana kar

ɓ

ar wayar, ya zare ido ya ce

"Kinyi hauka amma? Karfe sha biyun za

ki ce masa nazo

ɗ

aukar ki me kike so yayi tunani?"

"Oho" ta bashi amsa kafin ya sake magana yaji muryar Hafiz

ɗ

in a speaker yana cewa

"Jalilah sa'arki

ɗ

aya matata bata gari amma ko dan gaba kada ki sake mun irin haka ya zaki ringa kirana tsakiyar dare?

"

"Allah ya baka haƙuri dama ce maka zanyi me Taxi

ɗ

in ya zo"

"Shikenan mu kwana lafiya ki kula da kanki" ya bata amsa bai jira tace wani abu ba ya katse kiran.

Bilal dake kallonta ya sauke ajiyar zuciya jin bata ambaci sunansa ba can cikin ransa kum

a kishi ne ya taso masa jin yanda take yiwa Hafiz

ɗ

in magana a nutse cikin ladabi kamar me tsoron sa shi kuma yana wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login