Showing 201001 words to 204000 words out of 287295 words
bayanin da yayi mun, na san bai zama lallai abinda ya fa
ɗ
a mun gaskiya bane amma ko
ma menene tone tone bashi da da
ɗ
i ayi haƙuri har idan da yuwuwar komawa kiyi haƙuri ki koma, amma idan kinga cewa da cutuwa a lamarin zamanku wlh bana goyon bayan kici gaba da haƙuri kiyi abinda kike ganin ya fi kwanta miki a zuciya" Anty Aminan ta fa
ɗ
a.
Mama na sake kallo naga ta ta
ɓ
e baki kafin ta miƙe ta bamu guri. Nayi shiru sai Anty Aminan ta sake cewa
"Na san kina haƙuri da shi harma da mu da mahaifiyarmu baki
ɗ
aya amma ki sani Halima babu wani gidan aure da bashi da nasa kalar ƙalubalen kawai na
wani ne ya fi wani da kuma yanda ma'auratan suka iya riƙe sirrin su shine banbanci amma duk inda aka zaga hakan take shiyasa zakiji hausawa suna cewa da sabon gini gara ya
ɓ
e".
Kai na girgiza hawaye ya kawo ido na na ce
"Bana zaton zan iya zake zaman a
ure da Bilal dukda ina son sa".
Kuji tsoron Allah masu fitar mun da littafi babu lallai na yafe haƙƙina wlh
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun d
a littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 46*
"Kar kice haka mana Halima. Ke da na san ki jaruma shine zaki bari daga sa
ma wata ta zo ta ƙwace miki miji kuma ki sakar mata? Haba mana dan Allah karki bani kunya.
Na san abinda ya aikata miki dole kiji zafi ba ke ba hatta Hajja dake goyon bayansa a ko da yaushe a wannan karon tana adawa da auren nan dan wlh ba dan mun taus
heta ba rantsuwa tayi akan sai ya saki yarinyar ba zata tare ba. Mu muka yi ta bata haƙuri saboda a ganina bai kamata ace a gyara
ɓ
arna da
ɓ
arna ba, ubangiji ya rigada ya ƙaddara matar sa ce sai ayi haƙuri baki
ɗ
aya a kar
ɓ
i hakan ta yuwu silar auren sai ki
ga kina zaune ubangiji ya fitar miki da haƙƙin ki ya wanke ki a idon duk mai ganin laifinki" Anty Amina ta fa
ɗ
a cikin tausasawa.
Murmushin takaici nayi ina share hawayen da suka
ɓ
alle mun, kowa
ɗ
auka yake saboda Bilal zai ƙara aure ne muka samu sa
ɓ
ani
amma nayi mamakin yanda da ta tashi tahowa bikon bai fa
ɗ
a mata gaskiya ba ta yanda zata fi sanin hanyar da zata bi gurin shawo kaina idan ma hakan mai yuwuwa ne. Ina jin ta ta cigaba da cewa
"Kiyi haƙuri Halima, kishiya da ciwo amma sau tari mace bata
sanin matsayin ta a gurin namiji idan tana ita ka
ɗ
ai sai ranar da ya kawo mata abokiyar zama a lokacin shi kansa zai banbance tsakanin aya da tsakuwa.
Balle Bilal Allah na tuba ni da ke mun san idan ba ke
ɗ
in ba babu wata mace da zata iya jure halinsa
suyi dogon zango yanda kikayi,
ni da ace kinyi shawara dani tun farko zan ce miki ki danne zuciyarki ka bashi lokaci kawai ki kuma zuba ido ki sha kallo zakiga zuwan da dawowar amma yanzun ma bata
ɓ
aci ba hakan za'a yi kiyi haƙuri ki koma
ɗ
akin ki tun
kafin amarya ta tare balle ta samu lagonki ta fahimci kina kishi da ita".
Girgiza mata kai nayi na ce
"Ko da ina son Bilal ina kuma tsananin kishin sa hakan ba zai saka na bijirewa umarnin ubangiji na so kaina ba.
Ban ce banji zafin ƙarin auren sa
ba amma wannan bai ko kama ƙafar abinda ya aikata mun da ya saka na nisance shi ba. Kuma zuwan ki da maganganunki sun sake tabbatar mun da bai yi nadama ba, ba kuma shi ya turo ki ba zuwan kanki ne kawai domin da ace yana buƙatar cigaba da zama dani ba zai
rufe miki ainihin abinda ya ha
ɗ
a mu ba ya fa
ɗ
a miki ƙarya" na ƙarasa cikin kukan da ya ƙwace mun.
Tayi shiru jiki a sanyaye tana kallona kafin tayi ƙarfin halin cewa
"Menene gaskiyar abinda ya shiga tsakanin ku Halima? Ni dama jiki na ya bani ba gask
iya ya fa
ɗ
a mun ba, na yarda da shi ne kawai saboda rantsuwar da ya mun ban kuma yi zaton lalacewar ta sa har ta kai ya ringa rantsuwa akan ƙarya ba".
Na miƙe tsaye ina goge fuskata na ce
"Kiyi haƙuri amma ba zan iya furta miki komai ba domin bai zama
lallai ki yarda da ni ba ƙarshe ma zaku iya cewa sharri nayi wa
ɗ
an uwanku". Miƙewar itama tayi ta ruƙo hannuna ta ce
"Ashe har yanzu kina kallo na kamar sauran Halima?" Na girgiza mata kai na ce
"Ko da ace kamar su kike kin mun alkhairin da ko me za
ki mun zan
ɗ
aga miki ƙafa. Maganar Bilal kuma mu barta kawai kiyi haƙuri, idan zuwan kanki ne ba zan iya sake koma masa ba, Idan ma kuma shi ya aiko ki ki fa
ɗ
a masa; ko da ƙaddara ta kasance akwai sauran zama a tsakani na da shi ba zan koma ba har sai shi
da bakinsa ya fa
ɗ
a muku abinda ya aikata mun" daga haka na wuce
ɗ
aki na barta a tsaye da alama ta rasa da kalmar da zata tsayar da ni.
Kan gado na fa
ɗ
a na fashe da kuka bayan shigata
ɗ
aki, Amirah dake shafa mai a gaban mirror ta waigo ta kalle ni ta ce
"Wai Yaya Halima ba zaki dangana ki dena wannan koke koken banzan ba?"
"Ba zan iya ba Amirah, duk yanda na so na bari tunanin dake cunkushe a ƙwaƙwalwata ba zasu barni ba. Ban ta
ɓ
a zaton Bilal zai mun haka ba na kasa yarda mutumin da na so tamkar rain
a zai maida mun da irin sakayyar nan" na fa
ɗ
a cikin kuka har raina kuma na ji wani sanyi na samun wanda zan tattauna yanda nake ji a zuciyata da shi.
Tunda Hansa'u ta fahimci ina shirin yafewa Bilal a fa
ɗ
ar ta shikenan ta fita a sabgata ta dena kirana
kuma ko da ni na kirata ba zata amsa ba kamar ma blocking
ɗ
ina tayi dan baya bayan nan idan na kira kullum user busy ake ce mun. Mama da Abba kuwa sun zame mun kamar dodanni a yanzu, banda tsawa da hantara ba abinda yake shiga tsakaninmu, Anty Labiba da ta
kasance abokiyar shawarata tun asali na ruguza alaƙar mu tunda na kafe akan auren Bilal, ita
ɗ
in kuma bata da sauƙi ta kasa haƙuri ta rungume ni tamkar yanda sauran sukayi kafin yanzu komai ya lalace.
Tasowa tayi ta dawo kusa da ni ta zauna ta ce
"Ki
n aure shi cikin rashin sanin ainihin wanene shi, a yanzu da komai ya fito miki; idan kika sake biyewa So ba kuskure bane bane abinda zakiyi ganganci ne, kin kuma san duk abinda aka aikata shi bisa ganganci, idan aka samu akasi sakamakon sa ya kan zarce na
kuskure.
Ya hanaki abinci kin
ɗ
auke ido, ya zageki kin
ɗ
auke ido, ya doke ki duka kin shanye saboda kina son sa kina kuma son kiyi zaman aure sannan bakya so wa
ɗ
anda suka ce kar ki aure shi suyi miki dariya shiyasa kika haƙura kika zauna amma Yaya Hal
ima har zuwa wane lokaci zuciyarki zata iya jurewa bayan kin san mijinki yana da wata alaƙa a waje irin wacce take tsakaninku ma'aurata?"
Da firgici ha
ɗ
i da mamaki na kalleta, ta gya
ɗ
a mun kai cikin tabbatarwa kafin na bu
ɗ
e baki ta ce
"Kar ma ki
ɓ
ata l
okaci gurin tambayata a ina na sani, kowa kallonki kawai yakeyi suga iya tsayin lokacin da zaki
ɗ
auka kina rufa masa asiri.
Ba Jalilah sunanta ba? Har gidan da ta siya masa a Kano suke zuwa suna sheƙe ayar su a ciki an sani, mota da ku
ɗ
a
ɗ
e duk da yake
facaka da su zuwa yanzu kowa ya san karuwanci yakeyi tana biyansa.
Ke ce kike ta nuƙu nuƙu da abu a rai yana neman kashe ki a zatonki kin
ɓ
oye sirrinsa bakya so mutunchinsa ya zube bayan shi tuni ya da
ɗ
e da barba
ɗ
ar da mutunchi hotel hotel a gari, dan h
aka tun wuri idan ma zaki saki ranki ki saki, idan kin ce zaki koma masa babu mai miki dole ki rabu da shi amma kiwa kanki fa
ɗ
a tun kafin duniya ta miki.
Kinga test
ɗ
in da kuka je
ɗ
azu? Toh Abba ne ya saka ya kaiki dan ina ji yana gayawa Mama idan kika
dage sai kin koma to fa duk abinda ya je ya dawo ki kuka da kanki, waya sani ko an gaya masa yarinyar da yake neman bata da lafiya ne? Ke dai kawai ki godewa Allah bai shafa miki ciwo ba kuma kiyi ta kanki in kuma kin na ce toh sai in ce miki Allah ya bada
sa'a".
Yanda kasan wata uwar mata haka Amiran ta zauna tana tsara zance, duk maganganun nata ba wani fahimtarta nayi ba hankali na ya tafi kan cewa da tayi kowa ya san abinda Bilal yake aikatawa. A hankali na ce mata
"Mu'azzam ne ya fa
ɗ
a muku ko?"
"Babu ruwan Yaya Mu'azzam, ita magana ai kamar tusa take in dai an yita a sannu zata isa ko ina. In miki mai gaba
ɗ
aya, to hatta da cewa da Abba yayi kije ki
ɗ
akko Uniform
ɗ
in ki a gidan jiya yana sane yayi haka ne saboda ki tarar da abinda idan kina da
hankali ba zaki ko sake kallon in da Bilal ya gifta ba, amma kika sake gwada masa ke
ɗ
in fa kinyi nisa bakya jin kira.
To wlh tun wuri ki wa kanki fa
ɗ
a dan Abba ya gama kaiwa bango da lamarinki, Sai kinji yanda ya yiwa yayansa tas tas duk da ya ce shi
bai san komai ba.
Ita kuma wannan Anty Aminar raina miki wayau kawai tazo tayi dan na tabbata su dai sun san komai" Amiran ta sake fa
ɗ
a daga haka ta tashi ta fara saka kayanta tana sake jaddada mun wai in wa kaina fa
ɗ
a na san inda yake mun ciwo sai kac
e wata uwata.
Jiki na yayi laƙwas da jin maganarta. Ashe ni duk bonono nake wai rufe ƙofa da
ɓ
arawo, ina nan ina fama da abu a ciki na ashe na bar baya ba zani kowa kallona kawai yakeyi. Yanzu ashe iyaye na sun ma san abinda ni ban sani ashe su har sun
san yana kai mata gida kenan.
Kuma mai ciwo na sake fashewa da shi, na rasa gane wace irin ƙaddara ce take yawo da ni haka, ina jin zuciyata tamkar zata fashe saboda ƙunci da baƙin cikin halin da na tsinci Bilal a ciki amma kuma a wani
ɓ
angare babu ko
ɗ
igo na soyayyar sa daya ragu, ji nakeyi ma tamkar ana sake rura mun wutar ƙaunar sa a zuciyata. A fili na furta
"Ko sonka zai zama ajalina na haƙura da kai Bilal in sha Allahu na barka har abadah" na sake fa
ɗ
awa kan gado na cigaba da kukan da babu abi
nda yake rage mun saik ƙarin zafin zuciya da yake saka mun. Ina tsaka da kukan Al'amin ya shigo, motsin bu
ɗ
e ƙofar ya saka na
ɗ
ago muna ha
ɗ
a ido wani sabon kukan tausayinsu ya
ɓ
alle mun. Ganin ina kuka ya saka ya taho da gudu ya fa
ɗ
a jikina yana cewa
"M
ami menene? Momy ta ce baki da lafiya dubaki muka zo yi ko naje na kirata ina ne yake miki ciwo?"
Rungume shi na yi na cigaba da kuka, abinda nake gudu ya rigada ya faru. Bilal ya cuce ni ya cuci yarana ya
ɓ
ata musu suna ya kuma bar musu abin gori har
duniya ta tashi. Sai da ya fara kukan shima kafin daƙyar na lallashi kaina nayi shiru, ina lallashin sa Anty Labiba ta shigo.
Ta zauna kan bedside drawer fuska a washe tana kallo na ta ce
"Ta Bilal bada kanki a sare ya jikin?" Ba tareda na kalleta ba n
a amsa da cewa
"Da sauƙi" na
ɗ
ora da gaisheta. Ta amsa ta ce
"Ashe kuma haka abu ya faru? Toh Allah ya kiyaye gaba ya sa ya zame miki kaffara". Na
ɗ
aga kai na kalleta dan ban fahimci mai take nufi ba, maimakon ta ƙara mun bayani sai ta ce
"Na tambay
i Mama yaushe za'a je kwaso kaya ta ce ke za'a tambaya, yaushe zamuje? Dan na ji an ce ranar asabar amarya zata tare ko kin bar musu kayan naki ne da su zata tare?"
Sai lokacin na
ɗ
aga kai na kalleta kamar mai tsoron magana na ce
"Anty ya aiko da takar
dar ne?"
"Au jiyan haka kika fito ziƙau baki musu aika aika kin kuma kar
ɓ
o tikitin yancin ki ba?" Ta maida mun da tambaya. Ƙasa na sauke kaina hawaye suka
ɓ
alle mun Anty Labiba ta ce
"Toh Allah ya rufa asiri, daga yau zuwa gobe dai ki san me kike cik
i gaskiya in za'a je kwaso kayan toh in ma ba za'a je ba dai mu sani da wuri" daga haka ta miƙe ta fita tareda Al'amin.
BILAL
Kasa zaune yayi tunda sukayi waya da Anty Amina da safe ta ce masa ta yarda zataje gidansu Halima amma tareda Yaya Aminu zas
uje. Dukda ba haka ya so ba amma babu yanda ya iya, in dai Haliman zata dawo shine muradin sa a yanzu.
Sai da ya dai dai ci lokacin ya kamata ace sun isa gidan su Halimar har sun gama abinda ya kai su kafin ya kunna wayarsa dan tun farar safiya Zulaiha
ta dira masa kira akan Kawunsu yana son ganinsa yau. Kasa gane wasu maganganu da take masa akan wai idan ya je duk abinda Kawun ya ce masa ya ce Eh ya sani, kawai ya katse wayar bayan ya ce mata bari zai kirata yanzu shikenan ya kasheta gaba
ɗ
aya dan ya s
an kira zatayi tayi ba zata ƙyale shi ba.
Shi kam tun da aka
ɗ
aura musu aure yake ganin sababbin halayenta da a baya bai san da su ba abun na
ɗ
aure masa kai yana kuma bashi mamaki amma yanayin da yake ciki a yanzu ya sa baya bari abun ya dame shi a rai
kawai yake mata uzuri koma menene ya san idan suka zauna zai dai daita.
Wayar na kunnuwa message
ɗ
in Anty Amina ya shigo ya bu
ɗ
e ya karanta 'wayarka a kashe, idan ka kunna ka sameni a gidan Hajja yanzun nan' abinda ta rubuta kenan.
Muƙullin mota y
a
ɗ
auka ya fita dukda bai so ta ce su ha
ɗ
u a gidan Hajjan ba amma kuma ita
ɗ
in dai dama ita zata gayawa Hajja zancen dawowar Haliman dan shi ba zai iya ba. Basu gama da Zulaiha ba ma balle ya sakw
ɓ
allo wata rigimar.
Motar Yaya Aminu da ya gani ya saka
ya ji tamkar ya juya amma ya makara dan suna tsaye a ƙofar gidan shi da Baba Sani suna magana, ya gama ƙunƙunin sa kafin ya fito ya shige cikin gidan ba tareda ya ko tsaya ya gaishe su ba. Yaya Aminu dake kallon sa ya yi ƙwafa ya ce
"Kana kallon yaron
nan yanda ya wuce mu wato bamu ma ishe shi kallo ba kenan"
"Haƙuri za'a yi Aminu, yayan yau sai a barsu da halin su kawai amma ban ta
ɓ
a zaton samun Bilal da irin haka ba, ni har na rasa abin cewa ma wlh gaba
ɗ
aya" cewar Baba Sani. Yaya Aminu bai tanka
ba ya juya suka shiga cikin gidan.
Daga yanda Bilal ya tarar da Anty Amina ya san cewa tafiya ba tayi yanda ake so ba. Gefe ya samu ya zauna kan kujera ya shiga gaida Hajja da tayi masa banza tamkar bata ji shigowarsa ba, ya juya kan Anty Aminan itama a
ɗ
age ta amsa tana maka masa hararar da bai san dalili ba. Yaya Aminu da Baba Sani suka shigo kowa ya samu guri ya zauna.
Tunda Yaya Aminub ya bu
ɗ
e baki ya ringa ji ina ma ƙasa ta bu
ɗ
e ya shige ciki ko kuma ya
ɓ
ace
ɓ
at daga gurin ko ya samu sauƙin tashi
n hankali, kunya da nadamar da suka masa rubdugu lokaci
ɗ
aya. Zufa ta ringa keto masa, tsabar yanda ya duƙar da kai take wuyansa ya fara ciwo amma bai ko yi yunƙurin
ɗ
agowa ya gyara zama