Showing 243001 words to 246000 words out of 287295 words
/>
e maka yaran ma kenan? Ita waccen
ɗ
in daka auro menene amfanin ta? Da zuwa kawai tayi ta samu guri taci arziƙi kenan ko me?"
"Ba haka nake nufi ba Hajja" ya fa
ɗ
a a hankali ta katseshi da cewa
"Ka saurareni da kyau dole ka kar
ɓ
o yaran nan saboda ta
hakane zaka ƙuntata mata da ita da iyayen nata kuma zamu samu damar jansu a ƙasa yanda muke so a dalilin yaran sannan itama wannan yar matsiyatan daka
ɗ
akko ba zaman banza zatayi ba dole tayi maka wahalar yaya".
Shiru yayi ya kasa ce mata komai, Hajjan
ce ta sake cewa
"Wai ina Hafizu ne kwana biyu?"
"Yayi tafiya ne kusan wata uku baya ƙasar" ya shata mata ƙarya, ta ta
ɓ
e baki ta ce
"Yanzu saboda mugunta da hassada ƙiri ƙiri kaƙi kayi masa maganar Fadila ko? Tunda kai kayi mana baƙin ciki Allah ya
kawo mana mai taimakonmu har gida amma ka kwa
ɓ
ar da damar shine itama kake mata baƙin ciki karta samu in da zata huta har muma mu mora"
"Amma Hajja na gaya miki maganar nan ba mai yuwuwa ba ce ba, mutumin nan da matarsa yana sonta bai ta
ɓ
a kallon Fadila
a matsayin wacce zai iya so ba kina gani saboda rashin hankalinta ta ringa shige masa har sai da ya fahimci abinda take nufi in da yana ra'ayi ai da zai amsa amma daga haka mai ta janyo? Janye jikinsa yayi ya daina zuwa gidan nan kuma shine kike so ni na
tallata masa ita gaskiya ba zan iya ba" ya bata amsa ba tareda ya kalleta ba.
Tayi ƙwafa ta ce
"Ai shikenan nan"
"Kiyi haƙuri idan na
ɓ
ata miki rai Hajja" ya sake fa
ɗ
a cikin sigar rarrashi,
"Yanzu ita yaushe zata dawo ayi maganar auren?" Ta sake so
ko masa wata maganar, ya fahimci wa take nufi amma ya waske da tambayar wacece
"Ita shai
ɗ
aniyar yarinyar nan mana" ta bashi amsa a fusace. Ya marairaice fuska ya ce
"Yanzu Hajja ko ni na dage zan aureta dan Allah sai ki barni nayi?"
"Akan mai zan
hanaka? Dama ai abinda ya kamata kenan ko kuwa kana nufin taci banza ta lalataka sannan taƙi aurenka? Toh wlh ba zai yuwu ba" ta bashi amsa. Ya bu
ɗ
e baki zai sake magana wayarsa ta shiga ƙara dan haka ya dakata ya zarota gabansa ya yanke ya fa
ɗ
i ganin int
ernational number ko ba'a fa
ɗ
a ba kuma ya san Jalilah ce.
Ji yayi zufa ta fara keto masa ya danna wayar a silent ya mayar da ita Aljihu ya miƙe yana kallon Hajja ya ce
"Bari naje Hajja sai gobe" ta amsa masa da
"Allah ya tashe mu lafiya" tana karantar
sauyin da yayi lokaci
ɗ
aya.
A falo Zulaiha ka
ɗ
ai ya tarar tana ganinsa kuwa ta miƙe yayi gaba ta bi bayansa. Sai da suka zauna a mota kafin ta ce masa tana so taci Shawarma ta fa
ɗ
a masa kuma ta inda take so. Ya kalleta da mamaki jin inda ta fa
ɗ
o
ɗ
in,
kallon daya mata ya saka ta gane ta kwafsa dan haka tayi saurin cewa
"Saurayin Zahra ne yake siyo mata ya kai mata School, na ta
ɓ
a ci sau biyu tayi mun da
ɗ
i sosai shiyasa na riƙe sunan gurin". Bai amsa mata ba suka tafi, tana ta sako masa hira dan ta ka
war masa da tunani amma da Eh ko Uhm yake amsa mata kawai. ATM
ɗ
in sa ya bata ya ce taje tayi order dukda yanda gurin yake cike da Maza amma yana buƙatar space
ɗ
in ne saboda number
ɗ
azu da ake ta sake kiransa da ita. Tana fita kuwa kiran ya sake shigowa, s
aida ya kashe motar kafin ya
ɗ
aga murya can ƙasa kamar mai bacci yayi sallama.
Muryar Jalilah ta sauka ra
ɗ
au a kunnensa
"Yau dai Allah yayi na sameka a waya" ta fa
ɗ
a, ya sake narke murya ya ce
"Nayi kewarki Babe, mai nayi miki? Kin toshe duk wata han
ya da zan iya samunki phone call, Whatsapp, IG duk kinyi blocking
ɗ
ina what have i done to deserve such punishment Jalilah?"
"Nayi blocking
ɗ
in ka ko kayi blocking
ɗ
ina?" Ta bashi amsa da sauri ya ce
"Sa
ɓ
o kikeyi kema kin san hakan ba zai ta
ɓ
a zama ga
skiya ba ya za'ayi nayi blocking
ɗ
in ki?"
"Ai shikenan dai, kwana biyu? Nayi missing
ɗ
in ka sosai" ta rage murya ta fa
ɗ
a. Ya gyara zama yana cewa
"I missed you more Lily, yaushe zaki dawo?"
"Ya kamata ace jiya zan dawo sai kuma na wuce gurin Mom
bata jin da
ɗ
i" ta bashi amsa
"Subhanallah, mai ya sameta? Amma da sauƙi ko?" Ya fa
ɗ
a a cikin rikicewar ƙarya ta amsa masa
"Da sauƙi, kaya fa har sun kamo hanya kuma ba zasu da
ɗ
e ba dan ƙila ma su rigani isowa dan haka ka saka a gyara gurin da kace za
mu mayar dashi store kafin na dawo a fara loading kamfani, sai kaga kayayyakin da muka samu abubuwa da yawa ma basu tura mana ba sai da nazo na gansu na so tare muka zo kaima na san da ka sake ganin wasu abubuwan da zamu iya ƙarawa da su".
Window aka bu
ga ya sauke Zulaiha ta ziro kai tana cewa
"Menene pin
ɗ
in?" Ya danne speaker wayar kafin ya gaya mata ta koma Jalilah ta ce
"Baka gida kenan?"
"Aa, eh mai kika ji?" Ya fa
ɗ
a a duburce. Ta ce
"Naji muryar Mace"
"Halima ce Shawarma zata siya" yayi sa
urin bata amsa sai ta ce
"Allah sarki ta dawo kenan?"
"Eh ta dawo" ya sake bata amsa. Zancen kaya ta cigaba dayi masa yana sauraronta yana kuma kallon hanya dan kar Zulaiha ta taho bai lura ba kusan minti goma kafin ya cewa Jalilan zai kirata idan sun
isa gida ya ajiye wayar ganin Zulaihan tareda wani ya ruƙo mata ledar abinda ta siya. Kallonsu ya ringayi, da farko
ɗ
auka yayi ko yaron shagon ne sai da suka matso yaga Normal kaya ne a jikinsa ba rigar ma'aikata ba kuma magana yakeyi mata dukda fuskarta b
ata nuna sauraronsa takeyi ba amma yanda suka jero kamar ma jikinsa na gugar nata ya harzuƙa shi bai san sanda ya bu
ɗ
e motar ya fita ba dai dai lokacin da suka ƙarasa ta nuna Bilal
ɗ
in tana cewa
"Ga Mijina nan tunda na fa
ɗ
a maka baka yarda ba shi sai ya
yi maka bayani" ta fizge ledar ta shige mota ta barsu a tsaye. Haƙuri mutumin ya shiga bashi kafin ya juya da sauri ya bar gurin shi kuma ya koma motar cikin fushi ya ce mata
"Akan me kika tsaya kika kula shi?"
"Ni a yaushe na kula shi? Kuma idan da
mun fita tare da kai ai babu wanda ya isa yayi mun magana amma kayi zamanka a mota ka turani tsakiyar maza saboda baka kishina" ta ƙarasa idonta na kawo hawaye. Tsaki yayi ya tayar da motar har suka isa gida bai ce mata komai ba.
Part
ɗ
in sa ya wuce ya
na fita itama ta sakawa falon muƙulli ta fitar da Shawarmarta da Smoothie ta shiga ci bayan ta kunna kallo, wayarta tayi kara, tayi murmushi ganin mai kiran ta
ɗ
aga. Mutumin da suka ha
ɗ
u
ɗ
azu ne, ba tayi niyyar kulashi ba dan daya mata magana kai tsaye tac
e masa ita matar aure ce amma bai yarda ba da zata biya ku
ɗ
in siyayyar da tayi ya ce ta barshi taƙi shine ya zuba mata cash
ɗ
in da sai da tazo gida yanzu taga dubu
ɗ
ari biyu ce a ledar. Ta san ba zai wuce a gurin Teejay
ɗ
aya daga cikin yaran gurin ya samu
number, Ahlan da ta gani a true caller kuma ya saka ta gane shi ne dan sunan da yake kan complement card
ɗ
in daya ha
ɗ
a mata da shi kenan.
Ba tsoro ko fargabar komai ta shiga yin wayarta kamar yanda ya ce aurenta ba matsalar sa bace in dai ta yarda su ƙu
lla alaƙa. Har sha biyu da wani abu kafin sukayi sallama ta wuce ta kwanta ba tareda ta bi ta kan Bilal ba wanda yake can shima yana sheƙe ayarsa da Jalilah dan daga waya ta fara hillatarsa da abinda yayi rantsuwar ba zai sake ba ya tuba sai gashi bai san
sanda yayi unblocking nata a Whatsapp ba da kansa kuma ya kirata Video call sukayi abinda bayan sun gama kuma yayi bacci dan sai lokacin yaji ya samu nutsuwa. Duk da
ɗ
ewar da yayi da Zulaiha wuya kawai ya ci amma yanzu a
ɗ
an lokaci ya samu nutsuwar da ya da
ɗ
e bai sameta ba.
Tunani ya ringayi ko dai ta Hajjan ya yarda ya auri Jalilah ne? Aurensa da ita riba biyu ne, ga ku
ɗ
i ga kuma jin da
ɗ
i domin ita
ɗ
in ta san ta kan duniya amma kuma kishi ba zai ta
ɓ
a bari ya zauna lafiya da ita ba dan zuciyarsa ba zata
samu nutsuwa ba zai yi ta zargi da hasashen tana kula wasu a bayan idonsa wannan ya saka ko yaji zuciyarsa na son kwa
ɗ
aita masa auren Jalilah da abinda zai samu a silar hakan zai kore tunanin domin dai bariki ta ha
ɗ
a su a nan kuma zasu rabu.
Washe gari
kamar yanda sukayi da Kamalu yaje ya same shi sun tafi gurin Alhaji Balarabe mamallakin plazar da Jalilah ta siyi shagunan. Alhajin ya kar
ɓ
i takaddun take kuma ya kira Lawyer da wanda aka ci sa'a yana ta gurin dan haka ba'a wani
ɗ
auki lokaci ba ya je ya sa
me su.
"Gaskiya wa
ɗ
annan takardun ba namu bane" Lawyer ya fa
ɗ
a bayan daya gama dubasu. Alhaji ya tashi ya
ɗ
akko wata folder ya ringa fitar da original takardu na sauran shagunan da ba'a siyar ba yana miƙewa Bilal da Kamalu suna dubawa, ya kwashe su ya may
ar sannan ya
ɗ
akko photocopy ya ware su ya cire masa na ainihin shagonsu ya bashi yana cewa
"Kaga photocopy
ɗ
in original
ɗ
in da muka baka nan" ba wani dogon bincike Bilal da kansa ya gane banbanci ƙarara na takardun hannunsa da photocopy wa
ɗ
anda akace s
une wanda aka bashi. Duk kansa sai ya ƙulle, ya kuma tuna tabbas irin wa
ɗ
ancan aka bashi domin bai manta stamp
ɗ
in su da yake a kai ba wanda sai yanzu ya lura babu shi a na hannun nasa.
Alhaji Balarabe ya ce ya tafi da photocopy
ɗ
in sannan a shirye suk
e domin su taimaka masa t duk inda zasu iya idan buƙatar hakan ta taso.
"Kayi tunani ko takardun sun shiga hannun wani bayan kai kar ka ce cire kowa walau ya uwa ko Amini muddin sun je hannunsa toh abin zargi ne domin babu yanda za'ayi a tashi rana
ɗ
aya a
ce takaddu sun canza daga yanda suke zuwa wani abu na daban dole wani ne ya canza su" cewar Lawyer Alhaji Balarabe.
Haka ya bar gurin cikin damuwa duk kuma yanda zaiyi ya gano abinda ya faru ya kasa, to wa ma zai zarga bayan daga shi sai Jalilah da wa
ɗ
anda suka siya a hannunsu ne ka
ɗ
ai suka san da maganar ita kuma a hoto kawai ya tura mata su bata gansu a zahiri ba. Haka yayi ta kame kame daga ƙarshe ya watsar ya kama sabgoginsa tunda lissafin sa na farko ya wargatse ya sake dawo da Jalilar rayuwarsa sa
i dai ya jira kuma ya sake shiri.
BAYAN WATA BIYU
HALIMA
Na fara Bautar ƙasa na gadan-gadan, wani Private Research Center aka kai ni, mai gurin Abokin Uncle Mudassir ne na sha mamakin lokacin da naje gurin dan ban ta
ɓ
a sanin wanzuwarsa a Kano ba. G
uri ne mai
ɗ
auke da Laboratories babu adadi ga kayayyakin aiki yyanda kasan a irin fina finan Turawan nan na Scientist haka da yawan ma'aikatan gurin duk fararen fata ne ka
ɗ
an ne baƙaƙe iri na.
Fara aiki na ya sa na yarda dagaske da aka ce zaman banza
ne yake kashe zuciya har mutum yayi ta tunane-tunanen banza da wofi mai abunyi sau tari ya kan manta da duk wata matsala idan ba wacce ta shafi aiki ko sana'arsa ba. Toh nima hakan ce ta kasance dani domin ban rufa sati ba na fara
ɗ
aukar saiti, na tattara
duk wata damuwa na watsar na kama aiki na domin gani nayi tamkar ban ta
ɓ
a zama a aji ba komai sai ya zamar mun baƙo a lab
ɗ
in da aka kaini, da yake kuma har raina a shirye nake da na mayar da hankali na koyi abin sosai sai na ware duk wani test da akayi id
an na koma gida zan zauna nayi Reserch a waya har sai na samu cikakkiyar fahimta akan abun, na ƙulla abota da ChatGPT, duk abinda ya shige mun dubu shi zan tambaya ya warware mun musamman da na gano yana jin hausa shikenan na samu abinyi ko Whatsapp sai in
wuni na kwana ban leƙa ba ina can ina kwasar romon ilimi har na fara hasaso kaina na koma makaranta nan da wani
ɗ
an lokaci nima na zama babbar Scientist tamkar mamallakin gurinmu dukda a hoto kawai na ta
ɓ
a ganinsa sai dai ya burgeni, matashi don bai kai s
hekarun Uncle Mudassir
ɗ
in ba ma idan kuma ba hoton ne ya mayar dashi yaro ba amma har mamakin irin abubuwan da yayi nayi wanda suke rubuce cikin tarihinsa da akayi bango guda a cikin reception
ɗ
in gurin.
A cikin satin daya mutu na kammala iddar Bilal,
mun rabu kenan ko in ce na cire duk wani sauran fata da nake dashi akan al'amura zasu iya canzawa ko da ace akwai sauran zama a tsakaninmu toh fa sabon lale ne, sabon nema, sabon
ɗ
aurin aure wanda na tabbatar abu ne mai matuƙar wahala ace waliyyai na su s
ake kar
ɓ
ar maganar auren Bilal, sai dai ƙaddara mai girma irin wacce ta ha
ɗ
a mu a baya wadda a yanzu ni da kaina bana fatan ta sake giftawa.
Aurensa ya zame mun darasi a rayuwa, banyi nadamar kasancewa tareda shi ba domin za
ɓ
i na ne ba dole aka mun ba
amma kuma na godewa Allah daya farkar dani a dai-dai lokacin da rayuwara take da sauran ma'anar da zan iya canza gobe na.
Tun ranar daya bani takardata ban sake ha
ɗ
uwa da shi ba ko da a hanya haka bai sake nemana ba in banda text message daya turamun sa
u biyu akan cewar zai ƙwace yaransa shikenan bai kuma waiwayata ba ya tare da amaryarsa ya manta da ni da yaran da muka haifa tare.
Ko kusa ban ta
ɓ
a kawo cewar ko da cewar baya sona na kuma yarda da hakan babu haufi amma kuma na
ɗ
auka albarkacin zaman d
a mukayi na shekaru zan samu gurbin da zai ringa tunawa da ni a zuciyarsa har ya tuntu
ɓ
e ni, kai ko bai nemeni ba ya kamata ace ya nemi yaransa, ko da yake tun kafin ya sakeni ma zaman da mukayi bai ta
ɓ
a waiwayarsu ba har gara ni a sanda ya so ya yaudareni
ya sake mayar da rayuwata cikin uƙuba ya bibiyeni amma bai ta
ɓ
a tambayar yaransa ba, bai san cin su ba, bai san shan su balle suturar su ba shi ba hatta da yan uwansa babu wanda har kawo yau yayi tunani ko karar dai dai da rana
ɗ
aya yazo ya gansu ko ya ki
ra yaji lafiyarsu sai Abubakar.
Shi ka
ɗ
ai yake tuntu
ɓ
ata duk kuma sanda ya zo Weekend sai yazo ya gansu ba kuma zai zo hannu haka ba idan ma bai kawo komai ba zai basu ku
ɗ
i ya ce a siya musu bayan shi hatta Anty Amina da nake zaton tana so na tun ranar
da suka zo biko suka tafi ban sake jin
ɗ
uriyarta ba balle kuma uwar gayyar Hajja a taƙaice dai sun barmun yaran kawai na kuma yi murna da hakan a kullum kuma ina addu'ar Allah ya raya min su suyi tsahon rai su kai lokacin moro naga yan uwan Bilal
ɗ
in zasu
zama ire iren marasa kunyar mutanen da nake samun labari da sai a lokacin da yara suka zama abin moro ne sannan zasu gwada iko akansu matsayin dangin mahaifinsu ko kuwa sun barsu har abada?
*KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji
tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 55*
Tarin