Showing 276001 words to 279000 words out of 287295 words
/>
"Ni dai kayi haƙuri ka rabu dani babu wata sauran alaƙa tsakanina da kai" ta fa
ɗ
a kafin ta ra
ɓ
e shi ta bar gurin. Murmushi mai kama da dariya yayi yana binta da wani kallo ya ce
"Baki
isa ba yarinya, Ahlan bai ta
ɓ
a neman wani abu ya rasa ba tunda kuma aka fara sai an cigaba har sai idan ni na daina yayinki tukunna".
Mota ya hau ya bar Asibitin ba tareda Fadila ba.
*KURA A RUMBU*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Wha
tsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*KURA A RUMBU ya kammala, a biya naira 1k domin karanta shi complete*
*A tuntu
ɓ
e ni kai tsaye akan 07061838488*
*GODIYA TA MUSAMMAN*
*Dukkan godiya ta tabbata ga Allah (SWT) daya hore mun lafiya da tsayin kwana har na kammala rubuta wannan littafi. Salati da aminci su tabbatar ga fiyayyen halitta, katimul anbiya'i, Nabiyyina Muhammad (SAW). Ya Ubangiji ka sake cika zukatanmu da imani ta
reda soyayyar mafi soyuwar halittarka Annabi Muhammad (SAW).*
*Ina roƙo Ubangiji ya ha
ɗ
a mu a ladan abinda na rubuta na alkhairi ina kuma roƙonsa da ya shafe zunubin kura-kuren da na aikata a cikin rubutuna. Allah Alhamdulillah nagode da ni'imar da kayi m
un*
*Godiya musamman gareku makaranta da kuka bada lokacinku cikin wannan doguwar tafiya ta littfain KURA A RUMBU. Idan nace zan lissafo sunaye toh tabbas littafi mai shafi dubu yayi mun ka
ɗ
an. Littafin nan bai zama cikakke ba sai da gudunmawar ku, da k
almomin ƙarfafawa, shawara da goyon bayan da kuka bayar, Nagode ƙwarai da karamci ha
ɗ
i da soyayya ina fatan ubangiji ya fini yabawa. Ina roƙon Allah Ya saka da alheri ga kowane
ɗ
aya daga cikin ku. Allah Ya sanya wannan rubutu ya kasance hanyar tunani, gyar
a, da fa
ɗ
akarwa ga duk wanda ya karanta shi.*
*Idan littafin KURA A RUMBU ya ta
ɓ
a zuciyarku ko ya ƙara muku hangen nesa game da rayuwa da soyayya, to lallai burina ya cika, ina fatan zakuyi amfani da saƙon da yake ciki ku watsar da duk wani abu daya ci
karo da tunani ko rayuwa ta zahiri*
*Allah Ya sa mu dace a dukkan al'amuranmu. Amin.*
*LUBNA SUFYAN yau Allah ya nufa kwana uku ta cika
🤣🤣🤣🤣
na gode ƙwarai da karamchi da ƙarfafa guiwa. Allah ya raya miki Yusra*
*MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*
*LAST PAGE*
Ranar da Bilal ya kwana bakwai a Asibiti aka sallame shi sai Hajja wacce tun zuwan Fadila jikinta ya sake rikicewa sauƙin data fara samu komai yaja baya bata da aiki sai kuka da Allah ya isa ga Ahlan da tace ya yaudaresu ya auri autarta y
aje yana azabtar mata da ita.
Ganin jikin Bilal yayi sauƙi sai abinda ba za'a rasa ba ya saka aka sallameshi bayan likita ya ja masa kunne sosai akan kulawa da lafiyarsa. Sosai Zulaiha ke tsaye a kansa tana kulawa dashi, yanda Bilal yayi wani sanyi ƙala
u lokaci
ɗ
aya dole ya baka tausayi gashi tambayar duniya yaƙi fa
ɗ
awa kowa abinda yake damunsa sai dai ya samu guri ya zauna shiru wani wani lokacin har idanuwansa su tara ƙwalla da gani akwai wani abu da yake cin ransa amma ya kasa furtawa.
Ranar wata t
alata daya kama kwana hu
ɗ
u da sallamo shi daga Asibiti, suna zaune tareda Abubakar da Nasir sai Alhaji Sani Abokinsa da kuma Anty Amina suna jajanta batun motarsa da zuwa lokacin ta tabbata sacewa akayi. Ya ce musu a waje ya barta waccen ranar kuma da muƙu
llin a jiki sanda ya koma gidan. Kwana biyu kenan daya fara bu
ɗ
e baki yana magana sosai har yayi hira da masu zuwa dubashi.
Ranar da aka sallamo shi Abubakar yake tambayarsa batun motar tunda Zulaiha tace sanda ta fito itama bataga mota a gurin ba kawai
ya saddaƙar itama Azal ta fa
ɗ
a mata an sace.
Abubakar
ɗ
in ne yaje har gurin masu gadin layin ya tambayesu tunda ba yanda za'ayi ace an sace mota suna gurin suce basu lura ba suka ce masa tabbas suna zaune aka fita da motar amma basu lura bashi bane a
ciki tunda sunga shigarsa kuma dama ko horn bayi musu yakeyi ba yanzu balle sallama shiyasa suma da ya taho kawai zasu bu
ɗ
e masa get ya wuce ne ba ruwansu dashi.
"Ai kaga illar rashin zaman lafiya da mutane, banda sakarci ta yaya za'ayi ka ringa fa
ɗ
a d
a masu gadi? Yanzu da lafiya lau kuke zaune ai ko banza ka taho ka saba musu magana idan suka ji shiru zasu iya zargin wani abu ƙila da haka bata faru ba. Yanzu ai sai a kai report police station idan da rabo ƙila a dace a gano wanda ya
ɗ
auka" Alhaji Sani
ya fa
ɗ
a.
Nasir ya bu
ɗ
e baki zaiyi magana kenan Zulaiha ta shiga falon da sallama.
A bakin ƙofar ta tsaya tana kallon Abubakar tace
"Wasu mutane ne a waje suke sallama dashi".
"Su waye, ko baki sansu ba?"
"Jami'an tsaro ne" ta bashi amsa dai-dai l
okacin da baƙin su biyar suka yiwa kansu iso zuwa falon.
Ciki suka shiga, wanda yake Shugabansu ya zaro ID card daga aljihun rigarsa fuska babu wasa ya ce
"Sunana ASP Ɗanjuma Hassan, wanene Bilal Saleh a cikinku?"
Gaba
ɗ
aya suka kalli Bilal
ɗ
in daya
sunkuyar da kai ƙasa cikin yanayin na tashin hankali dan lokaci
ɗ
aya zufa ta fara keto masa tamkar wanda ya zauna akan kunama. Abubakar ne yayi ƙarfin halin cewa
"Lafiya dai ranka ya da
ɗ
e? Wani abun ne ya faru?"
Ba tareda ya bawa Abubakar
ɗ
in amsa
ba idonsa na kan Bilal yace
"Mun zo ne mu tafi da kai bisa zargin fasa shago tare da satar kayan ciki. Haka kuma, ana tuhumarka da zamba cikin aminci, da kuma damfara ta hanyar sayar da gida da takardun bogi, ga kuma laifin raina kotu ta hanyar ƙin am
sa gayyatarta.
Kana da ‘yancin yin shiru, domin duk abin da ka fa
ɗ
a yanzu zamu iya amfani da shi a matsayin hujja a gaban kotu.
Kana da ‘yancin
ɗ
aukar lauya domin kare kanka, dan haka yanzu zamu tafi da kai office domin ci gaba da bincike. Officer, saka
masa ankwa" ya ƙarasa maganar yana kallon Ɗansandan dake riƙe da ankwa yana jiran umarni. Gurin Bilal
ɗ
in da yayi mutuwar zaune ya ƙarasa ya kamoshi babu
ɓ
ata lokaci ya buga masa Ankwa.
Salati Anty Amina da Zulaiha suka shiga yi kafin suka fashe da kuka
a tare, Nasir da Alhaji Sani suka miƙe tsaye kowanne cikin tashin hankali. Cike da damuwa Abubakar ya ce
"Amma ranka ya da
ɗ
e baya cikin yanayin d zai iya fuskantar shari'a a yanzu bashida lafiya bai da
ɗ
e da fitowa daga Asibiti ba".
"Zaka koya mana ai
ki ne Malam? Ko a gadon Asibiti yake dole doka zatayi aiki akansa batun rashin lafiya ko wani abu kuma wannan bincike ne zai tabbatar duk kuma abinda ya kamata za'ayi."
"Ranka ya da
ɗ
e amma da anyi haƙuri ba sai an saka masa Ankwar ba sai a tafi a haka"
Alhaji Sani ya fa
ɗ
a ba tareda ASP ya kalleshi ba yayiwa yaransa alama da su wuce haka suka tasa Bilal da ko uffan bai iya cewa ba kuma bai kalli kowa ba suka fice daga gidan Alhaji Sani da Nasir suka bisu.i
"Kubar kukan haka Anty, bari mu bisu dan Allah k
i kira Yaya Alhaji ko Yaya Aminu sai su samemu a station babu abinda zai faru insha Allah amma dan Allah kada ki bari Hajja taji maganar nan" Abubakar ya fa
ɗ
a.
Cikin kuka tace
"Kaima ka san su Yaya ba zasu yarda su shiga maganar nan ba tuntuni irin wan
nan ranar nake guje masa amma yaƙi ji itama Hajja ta ringa goya masa baya yanzu wa gari ya waya?"
"Yanzu ba lokacin mayar da magana bane Anty bari naje" ya bata amsa yana ficewa da sauri jin tashin jiniya alamar sun wuce ko ya akayi basuji zuwansu bama
oho?
Anty Amina na matse ido tacewa Zulaiha bari taje,
"Ki kwantar da hankalinki insha Allahu komai zaizo da sauƙi bari naje muga yanda za'ayi" cewar Anty Amina Zulaiha dake kuka ta
ɗ
aga mata kai. Anty Amina na fita itama Zulaihan ta canza kaya ta b
ar gidan cikin tashin hankali, dukda rana ce amma mutane sun cika bakin layin anata mayar da magana kowa da kalar nasa narration
ɗ
in dukda babu wanda ya san mai ya faru.
Bayan fitar Anty Amina a hanya ta kira mijinta ta gaya masa abinda yake faruwa ya
tambayeta station
ɗ
in da suka tafi tace bata sani ba amma ya kira Abubakar daga nan ta wuce gidan Baba Sani dan tace ba zata iya kiran Alhaji Aminu ko Yaya Alhaji ba kamar yanda Abubakar yace ta san ma da wahala Alhaji Aminu ya saurareta har gara Yaya Alha
jin dukda shima ranar daya je duba Hajja tana kwancen haka ta ringa zaginsa tace wai dashi aka ha
ɗ
a baki aka cuci Fadila ya san ba mutumin kirki bane amma ya bari ya aureta.
Duk irin ƙoƙarin da su Nasir da Mijin Anty Amina sukayi akan a basu belin Bila
l abu bai yuwu ba kamar yanda suka ce gobe za'a turashi kotu dan haka su nemi lauyan da zai tsaya masa kawai.
Cike da damuwa Zulaiha ta kalle Alhaji Mudan, tsohon saurayinta ne kuma babban mutum ne mai fa
ɗ
a aji. Gurinsa ta tafi ta roƙe shi akan ya shig
a maganar ya fito da Bilal; kai tsaye ya kira CP kuwa yace ya bashi lokaci zai bincika ya kira shi sai bayan Magriba Alhaji Mudan
ɗ
in ya kirata yake gaya mata sai dai tayi haƙuri for babu dama amma sunce gobe za'a kai shi kotu zai ga duk abinda zai yuwu a
kotun kada ta tayar da hankalinta.
"Abinda kuka kasa ganewa kenan ku tsallakemu ku auri yaran da yawanci banda
ɓ
acin rai da damuwa babu abinda kuke tsinta a auren nasu. Duk yanda akw ciki you keep me update, dukda zanyi tafiya goben amma idan kin kira
layina baki samu ba ki kira Bashir duk abinda ake buƙata zai yi" Alhaji Mudan
ɗ
in ya fa
ɗ
a mata tayi masa godiya kafin ta kashe wayar tana sharw hawaye.
Ummansu da ta gama jin komai tayi tsaki tace
"Aikin banza aikin wofi, haka kawai kika nace sai shi
ba yanda banyi dake ba tunda mun rigada mun gama cin moriyar ganga mu yar da fata mu huta kika ce ke ba haka ba yanzu tun ba'aje ko ina ba gashi nan, na ma rasa wane munafukin ne ya kawo zancen unguwar nan
ɗ
azu kina fita Usainar Hadi ta shigo wai daga gida
n Larai take taji ana zancen an kama mijinki wai ashe
ɗ
an damfara ne. Tunda zance yaje gidan Larai kuma ai duk Kano ta
ɗ
auka dama cike take da baƙin cikin Allah ya rufa mun asiri kun tashi lokaci guda."
Zulaiha dake jan hanci tace
"Amma Umma duk duniy
a dai kin san ba zan ta
ɓ
a samun mijin da zai so ni saboda Allah ba kamar Bilal. Kina kallo duk abinda ya faru amma ya kar
ɓ
eni a hakan muna zaune sau
ɗ
aya bai ta
ɓ
a nuna rashin amincewa ko zargina ba kina zaton da ace ba shi na aura ba da yanzu ban dawo gida
n nan ba?"
"Yawon kika cigaba dayi ko me?" Umman ta tambayeta tana dafe ƙirji, tana goge fuska da hijabi ba tareda ta bata amsa ba ta shige
ɗ
aki. Da shirin wanka ta fito, ta shige ban
ɗ
aki ana idar da sallar Isha'i ta cewa Umman zataje ta kaiwa Bilal ab
inci.
"Au ke abinci ma kike shirin tafiya kai masa? Toh bari kiji, bafa zata sa
ɓ
uba wlh. Tunda akai auren nan
ɗ
an abinda yake kawowa da yanzu ya daina. Rabon daya ajiye mana buhun shinkafa a gidan nan tun watan aurenku, haka ku
ɗ
i yanzu ko ya ya zo dubu
biyar ce ko goma Allah na tuba mai zasu mun?
Ni ba haka na zata ba dan haka an yi akan ga
ɓ
a mun samu mafaka sakin ki kawai zai yi can ya ƙarata ki nemi mijin gaske ki aura."
"Idan kika ga na rabu da Bilal Umma to kice shi ya sakeni ko ya ce baya buƙa
tar cigaba da zama dani. Ina son Mijina, abinda ya sameshi kuma ba zai sa in daina son sa ba dan ya kar
ɓ
e ni da abinda ya fi nasa muni bai gujeni ba dan haka sai inda ƙarfi na ya ƙare amma ba zan ta
ɓ
a bari ya tozarta ba" tana gama fa
ɗ
ar haka ta fice daga g
idan.
Take away mai kyau tayi masa sannan na siya masa tabarma irin mai soso a ciki da pillow harda net kafin ta wuce station
ɗ
in. Ta tarar da Abubakar da Nasir a can da kuma Lawyer da aka
ɗ
aukar masa mai suna Barr Sajid, yini
ɗ
aya kacal amma sai ka
ɗ
au
ka har an kaishi gidan yari ne duk ya fita a hayyacinsa musamman da Cell
ɗ
in da aka sakashi sai a hankali, da dabaru irin nata da kuma ku
ɗ
a
ɗ
en hannunta ta saka aka canza masa cell mai
ɗ
an dama-dama. Har after ten suna gurinsa ta ringa kwantar masa da hanka
li kafin suka tafi tareda su Abubakar zasu sauketa a gida.
Washe gari ƙarfe sha
ɗ
aya aka fara shari'ar Bilal, babu jeka ka dawo ya amsa laifinsa dukda Lawyer a jiya ya fa
ɗ
a masa idan an je kotu ya musa zargin da ake yi masa, a lokacin da za'a bayar kafi
n a sake zama zaiyi duk mai yuwuwa ya wanke shi amma daya kwanta cikin dare ya aksa bacci sai tunani daga ƙarshe ya yankewa kansa shawarar kar
ɓ
ar ƙaddara a yanda tazo masa kawai.
Sati biyu Alƙali ya bayar, kotu ta watse duk kuma yanda lauyansa ya shiga
ya fita nan ma Beli bai samu ba aka kai shi kurkuku kafin zagayowar ranar da za'a sake zama.
Yana kallon Jalilah dake tareda Ahlan tana masa murmushi irin na bakaga komai ba ma tukunna a lokacin da aka fito dashi za'a sakashi a motar gidan Kurkukun. H
aka ya sauke kansa ƙasa ya kasa kallon yan uwansa da duk suka halarci zaman kotun Hajja Anty Habiba ne ka
ɗ
ai basu zo ba ita tana can tareda Hajjan. Takanas wata maƙwafciyarsu taje da daddare daƙyar ma aka barta ta shiga ashe labarin kama Bilal taje kai mat
a. Yanda maganar ta baza gari lokaci
ɗ
aya abun mamaki, lungu da saƙo dangi kowa labari ya isar masa yanda kasan an yi yekuwa.
Haka aka wuce dashi Prison tun kuma daga isarsu ya fahimci ashe jiya a Aljanna ya kwana, yana ganin bai ta
ɓ
a riskar dare mai mu
ni irin na jiya ba yana isa Kurkukun ya fahimci Alƙiyamarsa ta tsaya, lokacin fara girbar abinda ya shuka tun a duniya ya zo. Haka ya canza kaya ya rungumi sabuwar rayuwar da Son zuciya da kwa
ɗ
ayi suka jefashi a ciki.
Dare ya tsala, yana kwance kan dand
aryar ƙasa, tun yana kore sauro da wasu ƙwaruka da suke binsa da bai ko tantance wa
ɗ
anne iri bane ƙarshe ya haƙura ya zubawa taurarin da sukayiwa sama ado idanuwa tamkar mai ƙirgasu amma a zahiri yayi nisa cikin tunanin rayuwa ne.
Ya amince duk abinda ya
faru shi ya jawa kansa, kwa
ɗ
aiyi da son zuciyarsa ya kawo shi wannan matsayin. Ya ringa tariyo rayuwarsa tun daga sanda ya fara sanin kansa, shi
ɗ
in ya taso da burika da dama. Tabbas Hajja tayi ƙoƙari akansu, ko da sun rasa mahaifinsu tun suna da ƙananan s
hekaru amma bata barsu sunyi kukan maraici ba. Iya ƙarfinta ta sama musu abinda wasu masu uban a raye ma basu samu kamarsa ba, musamman shi daya kasance na daban ko a cikin sauran tana sonsa kuma bata
ɓ
oye hakan ko a cikin yanda take tafiyar da lamuransu.
Ko da bai samu ku
ɗ
i yanda yake fata ba amma ubangiji ya rufa masa asiri domin yana samun abinda zaiyi buƙatun yau da kullum ba tareda ya nemi taimakon wani ba. Sai dai ido da hange-hange da kuma burika suka saka ya raina ni'imar da Allah yayi masa, hak
an ya saka ya zama kullum yana cikin neman hanyar da zai samu ku
ɗ
i amma fa daga kwance ba tareda ya sha wahala ba domin kamar yanda yake cewa su Nasir a sanda suke yawo cikin ruwa da rana suna fafutuka ya kan ce shi ba kalar wahala bane ruwan jin da
ɗ
i aka
masa dan haka yana zaune arziƙi zai tarar dashi ba sai ya fita ya nema kamar yanda sukeyi ba.
Cikin sa'oinsa da suka gama karatu tare shi ya fara samun aikinyi, sannan ubangiji ya hore masa macen da ya sani samun kamarta a wannan zamanin sai dace. Bata
dubi abinda yake dashi ba, bata ta
ɓ
a damuwa da mai zai bata ba, ta san yana dashi amma ta
ɗ
auke kai ta wadatu da abinda take dashi sannan bata ta
ɓ
a yin ƙyashin bashi abinta