Showing 42001 words to 45000 words out of 287295 words

Chapter 15 - KURA A RUMBU COMPLETE

amsa ya sosa mun rai har naji idanuna suna neman su kawo ruwa amma na dake. Kitchen ya wuce na bishi da kallo kafin na wuce

ɗ

aki na aje masa jakar sannan na shiga ban

ɗ

aki na tara masa ruwan wanka. Ina ciro masa kaya

n da ze saka ya shigo

ɗ

akin, kamar daga sama naji yace

"Kuma kika cinye dankalin duka". Na saci kallon sa shi

ɗ

in ma ni yake kallo se nayi gefe da kai na nace

"Idan an barshi ai lalacewa zeyi". Ƙwafa naji yayi kafin ya shige ban

ɗ

akin kamar ze tashi sama

, ni se ma ya bani dariya. Abincin ma sama sama yaci ya ture ya shige kitchen, kamar

ɗ

azu da safe ya sake kwazara mun kira saura ƙiris na ƙware da abincin baki na na maida shi cikin plate

ɗ

in na tashi da sauri.

"Dan girman Allah Bilal ka dena mu irin w

annan kiran bana so" na fa

ɗ

a tamkar zan fashe masa da kuka ganin sa a tsaye jikin fridge, ya kalle ni kafin ya bu

ɗ

e fridge

ɗ

in yana nuna ciki yace

"Ina exotic

ɗ

ina?"

"Nayi baƙi sun shanye" na bashi amsa kai tsaye. Yanda ya yi mici mici da ido yana kall

ona se ka rantse iyayen sa na zaga.

"Shi lemon nawa kike gaya mun kin yi baƙi sun shanye?" Ya fa

ɗ

a yana nuna kansa, Allah ya sani na fara zuwa bango. Wane irin abu ne daga dankali se kuma lemo se kace ana fatara ko tsiya?

"Baƙi nayi suka zo da yara ni

ban ma sani ba muna falo suka shigo suka

ɗ

auka kaga kuma babu yanda za ayi nace su mayar tun da dai abin nan munfi ƙarfin sa ba fatara akeyi ba" na bashi amsa ba tare dana kalle shi ba. Seda ya kwashi sakanni yana kallo na kafin yace

"Yayi kyau" ya fice d

aga kitchen

ɗ

in ya barni a tsaye.

[5/18, 13:09] Buhainat: *KURA A RUMBU*

*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*

*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*

*Whatsapp

07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*

*Wattpad @MaryamahMrsAm*

*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*

*Ku

ɗ

in karatu yana wakiltar mutum

ɗ

aya ne, kiji tsoron Alla

h karki

ɗ

auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*

*KURA A RUMBU littafin ku

ɗ

i ne, a biya naira 800, biya a asusun*

*1840175439*

*Access bank*

*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 11*

Daƙyar na koma cikin falo

na zauna ina jin kaina yana saramun. Me yasa Bilal yake haka? Kullum ace abinci ne ze ringa ha

ɗ

a mu rigima?

Ina nan zaune ya fito daga

ɗ

aki yanayin shigar sa na gane nisa ze yi. Ko kallo na be yi ba ya fice sabbin hawaye suka

ɓ

alle mu. Zuciya ta tana

ray

a mun na barshi naga iya gudun ruwan sa amma gangar jiki na taƙi bani ha

ɗ

in kai, bazan ce ga sanda na miƙe na bi bayan sa ina kiran sunan sa ba amma ko a jikin sa ya yi ficewar sa daga gidan ya bar ni a tsaye ina hawaye. Se da nayi kuka me isa ta, har na d

anna layin Anty Labiba zan kai mata kuka na se dai nauyi da kunya suka sa na katse kiran, Ina kallo kuma ta biyo baya amma na kasa

ɗ

agawa.

Har aka kira sallar magriba be dawo ba, bayan na idar da sallah ina zaune wani tunani ya fa

ɗ

o mun. Mu'azzam na ki

ra, bayan mun gaisa na tambaye shi yana ina ne?

"Ina kusa da gidan ki, da zan shigo ma amma bani ka

ɗ

ai bane kar nayo miki gayya kuma baki san da zuwan mu ba" ya fa

ɗ

a. Se na marairaice nace

"Yawwa, dan Allah ka agaza kazo zaka taho mun da saƙo"

" Saƙon

me? Na gaya miki fa ina unguwar ba wai daga gida zan fito ba" ya fa

ɗ

a se nayi saurin cewa

"Ai a kanti zaka siyo mun abun, lemo ne ba wani abu ba ka siyo mun Exotic carton

ɗ

aya idan kazo se na baka ku

ɗ

in".

"Ke yanzu duk uban lemukan da aka kawo miki da

gara har kun shanye shi ko mutane kika yi ta rabarwa? To se dai ki aiki mijin ki babu wani lemo da zan kawo miki" ya fa

ɗ

a yana niyyar katse kiran na san halin sa tunda ya fara hakan da wuya ze kawo mun

ɗ

in amma idan yaƙi ban san kuma ta hanyar da zan bi m

u shirya da Bilal a gajeran lokaci ba dan haka nace

"Haba

ɗ

an uwana, ina da lemo kala kala shi

ɗ

in ne dai ya ƙare kuma shi nake iya sha yanzu". Shiru yayi har nayi zaton ma ya kashe wayar kafin naji yace

"Shikenan zan kawo miki wane flavor?"

Jin na

samu mafita hankali na ya kwanta se na tashi na shiga tattare kayan abincin dana aje masa na maida kitchen tun da baze ci ba. Ba'a

ɗ

auki minti ashirin ba Mu'azzam yazo, carton biyu ya siyo mun be ko zauna ba muka gaisa daga tsaye yace ana jiransa ne. Ɗaki

na tafi na

ɗ

akko masa ku

ɗ

in amma yaƙi kar

ɓ

a.

"Lallai ƙani na an fara hankali" na tsokane shi, se yayi murmushi kawai yana kallon fuska ta dana lura tunda ya zo yake kallo na yace

"Me ya same ki naga idon ki sunyi jaa kuma sun kumbura fuskar ki ma haka?"

Se naji kamar ya fama mun abin da yake damu na nan da nan ido na ya kawo ƙwalla se dai ban bari sun taru ba na ƙaƙalo murmushi nace

"Babu komai, yau na tashi duk bana jin da

ɗ

i ne shiyasa".

"Se ki gaya masa ya siyo miki maganin malaria tun da kina bar

in ƙofa a bu

ɗ

e dama dole sauro zasu shigo miki" ya fa

ɗ

a yana fita. Na bi bayansa, se da muka je get ya sake kallo na yace

"Halima fuskar ki ta nuna kina da damuwa" kawai jin

ɗ

umin hawaye nayi akan fuska ta ba tare da nasan saukar su ba. Ya gyara tsayuwa y

ana kallo na yace

"Duk da ke kika siyawa kanki amma ba zan baki shawarar ki shanye baƙin ciki a son kar ayi miki dariya ba. Idan kika ji ba zaki iya ba ki tafi tun lokaci be ƙure miki ba" daga haka ya fice ya barni tsaye a gurin ina kuka mara sauti. Se

da gabana ya fa

ɗ

i da naga kiran Mama bayan tafiyar Mu'azzam babu jimawa. Tunanin ko ya fa

ɗ

a mata wani abu na shiga yi, to amma me ze ce mata?

Se da ta mun kira biyu kafin na amsa a sanyaye muka gaisa ta tambaye ni jiki na ce da sauƙi.

"Karki kuskura ki t

asa kayan zaƙi kice zaki ringa sha, Mu'azzam ya gaya mun kin ce ya siyo miki lemo to ki tattara su ki aje in ba haka ba wuya zaki kirawa kanki tun yanzu" ta fa

ɗ

a. Se naji dariya ta kamani, wato in da lissafin ta ya tafi kenan ciki ne dani amma dan a rabu l

afiya se kawai na bita da toh. Bamu jima ba mukayi sallama tana sake jaddadamun na kiyayi kayan zaƙi ni dai da toh kawai na ringa bin ta. Maganar da mukayi da Mama tasa na danu sauƙi cikin zuciyata se kawai nayi shafa'i da wutri nayi kwanciya ta.

Ban sa

nda Bilal ya dawo gidan ba na dai farka cikin dare na ganshi a baya na. Da safe tamkar bamu samu sa

ɓ

ani jiya ba lafiya lau ya tashi yana jana kamar yanda muka saba ni ce ma nake

ɗ

ararewa. Ban yi gigin ta

ɓ

a masa dankali ba na

ɗ

umama sauran abincin da be ci

ba jiya muka karya dashi, da ze fita yace mun na shirya idan ya dawo zamu fita wannan tasa na ware nima. Gidajen yayyen sa mata muka zagaya wa

ɗ

an da suke ciki

ɗ

aya da wanda suka ha

ɗ

a uba. Har unguwar su Anty Labiba muka je amma ƙememe yaƙi yarda mu shiga w

ai takanas zamu shiryo muje ba ratse ba. Dake dai mun shirya ya sakko daga fushin ban matsala ba kar ya sake birkice mun tun da dai yayi alƙawarin zamu je da weekend na wuni shikenan.

Haka rayuwa taci gaba da miƙawa a lissafi aure na da Bilal yana ciki

n wata na biyar kenan a kuma cikin wannan lokacin nayi karatu game da zamantakewa ta dashi ta rannoni biyu. A bangare

ɗ

aya na tabbatar da cewa Bilal yana so na domin irin kulawa da tattalin da yake bani na san cewa ba duka haka maza suke ba. Yana da sauƙin

kai sosai a halayya sannan ya

ɗ

auke ni matsayin ƙawa be hakan ne yake ƙarawa zamanmu armashi.

Idan har yana gida tare muke duka ayyukan gida. Kasancewar sa me tsafta sam baya shiri da ƙazanta be kuma so jikin sa ba, da sassafe kafin ya fita aiki ze sha

re mun tsakar gida ya wanke haka da falo na nasa ze share yayi mopping ni kuma naji da gyaran

ɗ

aku na da girki idan ya wuni a gida kuwa hatta sharar

ɗ

akunan shi zeyi ya gyara ko ina tsaf ya kunna turare dan idan yayi gyaran nafi ganin gurin yayi yanda nake

so saboda babu algus, kullum ze yi shara tofa se ya

ɗ

aga kujeru ya share ƙasan su haka duk wani abu dake ajiye se ya

ɗ

aga ya goge har mamaki nake yi yanda sam abin be dame shi ba kamar ma hakan na samar masa da jin da

ɗ

i dan cike da walwala yake ayyukansa

wankin toilet dama ko na wanke na

ɗ

akin sa cewa ya keyi be fita ba ze zauna ya sake wankewa tas yanda yake so haka wankin kaya har undies yake wanke mun wani lokacin muyi tare ina masa

ɗ

auraya wani lokacin yace ban iya ba na barshi se dai na zauna daga gef

e ina masa hira wa

ɗ

annan halayyar tasa take sake ƙara mun son sa da ƙaunar sa a zuciya nake kuma ganin

ɗ

aya

ɓ

angaren na halayensa da bana jin da

ɗ

in su a matsayin ajizanci irin na

ɗ

an adam domin kuwa babu wani mutum da yake cikakke dole ka kasance da halaye

n abin so da kuma wanda ba kowa yake so ba.

Daga cikin abin da ke yawan janyo sa

ɓ

ani tsakani na Bilal shine ƙorafi. Ko dan yana yawan zama a kusa da ni ne tun da idan ya fita aiki ya dawo idan ba sallah ba ba in da yake zuwa in kuma ranakun hutu ne yan

a gida, ba ƙaramin abu bane yake fitar dashi ko ya fita ma baya jimawa ze dawo dan haka ko yaushe muna tare dan haka duk abinda zanyi akan idon sa ne

kuskure ka

ɗ

an kuma zan yi yayi ta mita yana ƙorafi kenan. Abin da be kai ya kawo ba se ya zama na magana a

gurin sa.

Sannan na lura Bilal yana da son ya zama duk wani abu da zanyi ya zama da sanin sa. Sannan mutum ne me tattali da son abin sa. Har idan ina so na ga fushin sa to fa na ta

ɓ

a abun sa ba tare da izinin sa ba tun da kuma na fahimci hakan nake ki

yayewa shikenan nayi maganin fitinarsa. A watanni biyar

ɗ

in nan bani da wata matsala idan aka cire rashin fita da Bilal baya bari na a sanda naso se kuma rashin walwala ta ku

ɗ

i a hannu na. Ina samun ku

ɗ

i dan kusan duk sanda zanje gida Abba se ya bani ko ya

tura mun a account a cewar sa kar na ringa damun miji na da bani bani, Saboda gudun fitinar Bilal ko ƙorafi akan kayan sa bana saurar komai daga gare shi duk abin da nake so cikin ku

ɗ

i na nakeyi har shima nayi masa na kuma yiwa yan uwansa.

Abin sa na s

ake lura dashi yana jin da

ɗ

in shi na hidimta masa amma baya so nayi wa wani dan har idan wani ya zo mana nayi masa kyauta a gabansa ko beyi magana ba a fuskar sa ina karantar rashin jin da

ɗ

i abun na damuna da na gaji nayi masa magana akan hakan se yace wai

abin da nakeyi ze janyo masa raini a gurin masu zuwa gidan mu shi megida ya kamata ace idan ma kyautar ce yayi ba wai ni ba, saboda a zauna lafiya se ya zama idan yana nan mukayi baƙi idan ku

ɗ

i ne zan bashi nace ya basu idan kuma wani abun amfani ne zance

gashi in ji shi shikenan na samu lafiya da wannan ma.

Tuni result

ɗ

in mu ya fito har wasu daga cikin mu sunyi nisa a service, labarin da naji akan an yi ƙarin ku

ɗ

in da ake biyan yan bautar ƙasa ya sa na himmatu nima. Hansa'u na tambaya ku

ɗ

in da ake kas

hewa na clearance kafin a kar

ɓ

i result dan tuni ta kar

ɓ

i nata harta fara service a Abuja in da tayi aure, gaba

ɗ

aya ku

ɗ

in ya kama dubu goma sha biyu da

ɗ

ari biyar. Se da na lissafa abin da nake dashi kwata kwata dubu biyar da dari bakwai yayi mun saura cik

in dubu goman da Abba ya bani shekaran jiya da mukaje. A ciki na bawa Bilal yayo mana refilling gas ina tsaka da girki jiya ya ƙare, nasan ba'ayi albashi ba da daddare kuma naji kwa

ɗ

ayin tsire nan ma na bashi ya siyo mana na dubu

ɗ

aya na dafa mana indomie

muka ci.

Mayar da ku

ɗ

in nayi ina jiran ya dawo naji yanda zamuyi tun da y

ɗ

auka wa gobe nasan zasu iya samun albashi. Se da muka ci abinci kafin na sako masa zancen an yi ƙarin allawee.

"Na zata ma na gaya miki, se naji ina ma yanzu ne zanyi service ni

ma" ya fa

ɗ

a se na yi dariya nace

"Haba kun riga kun ci rabon ku yanzu mune zamu shana. Ina ganin ranar monday se na shiga makaranta Hansa'u tace zan iya yin komai a rana

ɗ

aya kuma nan da wani satin za'a bu

ɗ

e registration na Batch B kaga dai dai kenan".

Na

ɗ

auka maganar da nayi masa zata sa ya fahimci abin da nake nufi duk da be tambaye ni nawa ne abin da za'a buƙata ba se na barshi akan se ranar tayi tukunna. Cikin daren salaryn sa ya shigo lokacin wayar tana kusa da ni shi kuma ya shiga kitchen

ɗ

auko a

bu daya fito kuma ya

ɗ

auki wayar be ce mun komai ba nima ban damu ba. Monday ta kama hutun ranar ma'aikata dan haka babu aiki se washe gari talata a daren na sake tuna masa da washe gari fa zan je makaranta yace Allah ya nuna mana. Washe garin da wuri na s

hirya, baze fita ba kamar yanda yace suna wani field work ne se

ƙ

arfe sha biyu ze fita zuwa in da yake yin research. Se da nayi masa girkin rana saboda daga makaranta gida nake so na wuce kafin na ƙarasa shiryawa. Ina saka Hijabi na ya shigo

ɗ

akin, ya kall

e ni ba yabo ba fallasa nima ina kallon sa nace

"Na gama" yau ce rana ta farko da zan fara fita ni ka

ɗ

ai a tsayin auren mu. Duk in da zanje tare muke fita ko muje tare ko kuma mu rabu a hanya amma ban ta

ɓ

a kulle gida na fita ni ka

ɗ

ai ba.

"Amma fa kar k

iyi dare, ina tunanin Hafiz abokin aiki na zasu zo da matar sa yau ki dawo da wuri saboda ki tanadi abin da zaki tarbe su dashi" ya fa

ɗ

a. Na

ɗ

aura niƙab a fuskata ina cewa

"In sha Allah bazan da

ɗ

e ba". Gefen gado ya zauna ni kuma na gyara tsayuwa jikin ch

est of drawers ina jiran ya sallemi ni ganin yana ƙoƙarin kwanciya yasa na ce masa

"Na gama fa"

"Na miki a dawo lafiya ai, ko na zo na rakaki titi ne ba sabanba zaki fita ke ka

ɗ

ai yau?" Ya fa

ɗ

a yana murmushi. Se na

ɗ

age niƙab

ɗ

in ina kallon sa nace

"E

h da ka rakani

ɗ

in ma zanji da

ɗ

i amma bana so na wahalar da kai ga rana ta fara tsayawa sallame ni kawai na tafi".

Aljihun rigar sa ya shiga lalubawa ya zaro ku

ɗ

a

ɗ

e da nake zaton zasu iya kaiwa 20k ko su fi a ciki ya zari 1k ya miƙa mun yana cewa

"Zata

ishe ki ai"

"Nagode" na fa

ɗ

a ina kar

ɓ

a. Jimm nayi a tsaye ganin ya gyara kwanciya har da jan bargo zuwa cikin sa yasa na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login