Showing 126001 words to 129000 words out of 287295 words
shaƙuwa da sakewa tsakanina da ita da zan iya tatt
auna maganar da mukayi da Bilal amma yanda abubuwa suke tafiya yanzu a tsakanin mu nasan wani ruwan zan
ɓ
allo duk da dai na lura dagaske kamar yanda ta fa
ɗ
a babu ruwanta da sabgata da Bilal ta zame hannun ta a ciki ba wasa take yi ba.
Ranar da zai dawo
ɗ
in da kanta tace na duba kitchen naga idan akwai abin da zan buƙata da babu a siyo, jirgin sha biyu ya ce zai biyo dan haka da wuri na fara girkin mai aikin ta ta taya ni kafin sha biyun mun gama komai. Bilal na sauka ya kira ni ya gaya mun,
"Na biyo m
u tafi ko zaki zo daga baya?" Ya fa
ɗ
a. Na rasa me zance masa sai kawai na
ɓ
ige da cewar bana jin sa na kashe wayar. Babu da
ɗ
ewa ya sake kira na akan gashi a waje, da na gaya mata ta ce ya shigo mana ko kuma gidan baƙon sa ne.
Nayi zaton yanda yake nana
ta yayi kewata idan muka ha
ɗ
u zai yi kamar ya cinyeni amma sai naga akasin haka, rungumar da ya mun ma ni ban wani ji ta ba, a gidan ya ci abinci yana ta mun hirar aikin da suka je. Anty Labiba suka fita harda Al'amin ta ce zasu je kar
ɓ
o
ɗ
inki ba jimawa za
suyi ba na yi zaton zaiyi amfani da wannan lokaci ya rage zafi kamar yanda yake ta kwakwazo a waya amma bai nuna alamar komai ba ƙarshe ya
ɓ
ige da nuna mun hotunan da ya yi a gurare cikin sabuwar wayar sa Iphone da ya siya. Sai da aka kira la'asar kafin ya
ce mun zai tafi, ya ja ni jikin sa yana murmushin da ke wanke dukkan laifukan sa a gare ni ya ce
"Tun da na zo kike fushi kuma ko dai baki so dawowa ta bane?"
Gefe na
ɗ
auke kai ba tare da na ce masa komai ba, ya juyo da fuskata ya ha
ɗ
e bakin mu guri
ɗ
aya.
Yanda kasan na rufe kaina da duka saboda takaicin yanda na kasa riƙe kaina a gaban Bilal. Da ya kira ni ma kasa amsa wayar na yi to na ce masa me bayan abin kunyar da na kusa tafkawa na je ina ta wani rawar jiki shi da yake namiji ma bai nuna min z
umu
ɗ
in sa ba sai ni.
Kwanaki ukun da suka biyo baya kullum zai zo da daddare bayan magriba muyi hira har zuwa ƙarfe tara ko goma kafin ya tafi. Satin sa
ɗ
aya da dawowa ya sake ce mun zai koma Abujan dama wai basu gama aikin ba kawai kewata ta saka ya z
o. Dama Anty Labiba ta fara ƙananan maganganu akan
ɗ
an abincin da yake ci idan ya zo abinda dama ko ya zo ko bai zo ba dole za'a dafa ba wai wani abu na daban na ke bashi ba da ta ke mita akai.
A haka muka cigaba da gungurawa har muka yi arba'in, a ranar
kuma na tattara na koma gidana dan tun ana saura kwana uku aka je aka gyara mun Bilal ma ya dawo daga Abujar da na kasa gane abinda ya samu a can da ya tattare kusan sati uku tun da ya zo ya tafi bai sake dawowa sai yanzun.
Satin farko na dawowar mu za
n saka shi a jere ranakun jin da
ɗ
i da kuma farin ciki a rayuwar aure na. Irin tarairaya da soyayyar da Bilal ya gwada mun ba ta nan kusa ba ce na kuma yarda da gasken da ya ce yayi kewata haka ne, ban san dalilin sa na
ɓ
oye hakan a wancan zuwan da yayi ba
amma dai duk wani haushin sa da nake ƙunshe da shi daga wancen lokacin sai da ya saka klin da hypo ya wanke fushin tas.
Kamar yanda aka ce yau da gobe bata bar komai ba tabbas haka ne domin kuwa yau na wayi gari babu ko ƙwayar hatsin da zan sarrafa mu
ci a safiyar Talata. Tun dawowar mu nake tsammanin Bilal tun da ya san cewar komai na mu yayi ƙasa zaiyi ƙoƙarin ya siyo, kusan miya da soyayyen naman da na taho da su daga gida ne ma suka
ɗ
an ja mu sati
ɗ
ayan ba tare da na buƙaci cefane na dole dole ba. R
uwan shayi na tafasa ma zuwa a flask nayi wanke wanke na gyara kitchen
ɗ
in, indomie guda
ɗ
aya da ta rage na tafasa na ci dan yunwa nake ji dagaske ba zan iya jira har sai ya tashi daga bacci kafin ya ƙaro wata na dafa mana ba dan dama na
ɗ
auka guda biyu ce
shiyasa ko da ya dawo jiya da dare bai shigo da komai ba ban wani damu ba.
Ina cikin shirya Al'amin Bilal ya shigo
ɗ
akin yana hamma ha
ɗ
i da shafa cikin sa, yanda yake yi ko bai yi magana ba na san yunwa nake ji, ya jefe ni da harar da ban tantance ta
wasa ba ce ko ta gaske kafin ya ce
"Dariya ma kike yi mun ko?"
"Ni na isa? Ba dariya nake yi ba ka san dai haka fuska ta take dama" na fa
ɗ
a ina miƙa masa Al'amin da na gama shiryawa. Ya kar
ɓ
e shi ya zauna tare da shi a gefen gado ni kuma na wuce gaban w
ardrobe dan ciro kayan da zan saka.
"Badai baki
ɗ
ora abin karyawa ba?" Ya fa
ɗ
a yana bi na da kallo. Sai da na ware doguwar rigar atamfar da na ciro kafin na kalle shi na ce
"Na dafa ruwan tea kai nake jira ka tashi ka siyo Madara da Milo tun da da sau
ran cake
ɗ
in can sai a sha da shi dan na san babu lallai a samu burodi tun da rana ta fara yi goma yanzu".
"Ban gane na siyo Madara da Milo ba, kina nufin babu kayan shayi a gidan ko me?" Ya fa
ɗ
a kusan cikin
ɓ
acin rai, na dakata daga zuge zip
ɗ
in rigar
da nakeyi na ce
"Amma dai kai ne ƙarshen amfani da su jiya da dare tun kuma da zaka sha shayin sai da na gaya maka sauran kenan na juye a container baka kula ni ba".
"Kada ki gaya mun maganar banza Malama, kina nufin saboda na sha shayi da dare dan hak
a na sha rabo na ma safe ko me?" Ya fa
ɗ
a yana miƙewa tsaye. Hannu biyu na
ɗ
aga na ce
"Mai da wuƙar ni ba haka nake nufi ba amma dai kayan tea sun ƙare, ni da wannan sutun ma da taimakawa kayi ka siyo dan yunwa nake ji sosai Indomin da na ci babu in da ta
je mun".
Fita yayi ba tare da ya sake cewa komai ba, na cigaba da shiri na ina mitar yanzu kuma kayan shayi ne zasu ha
ɗ
a husuma da safiyar Allah, shi dai baya raina abin magana dama.
Madara biyu Milo biyu ya siyo na sachet sai burodi babba guda
ɗ
ay
a, na ringa kallon kayan sai dai gudun jan fitina ya sa ban ce komai ba na
ɗ
ora komai a try, sai da na
ɗ
akko container sugar na ga shima ashe ya ƙare burbu
ɗ
i ne a ciki na tattara na kai masa falo in da yake zaune yana jira. Har muka gama karyawa babu wanda
ya ce ƙala, yana gamawa ya wuce can part
ɗ
in sa, ƙamshin turaren sa da na jiyo har cikin falo na ya sa na gane wanka ya yi zai fita, ina nan ina sauraren ya shigo na ji yanda za'ayi da girkin rana sai jin ƙarar rufe get na yi. Na tashi na fita da sauri am
ma ko ƙurarsa ban tarar ba sai ƙamshin sa da ya baza tsakar gidan.
Komawa na yi na
ɗ
auki waya ta na shiga kiran sa, kira uku bai amsa ba haka na haƙura na ƙyale shi. Shiru shiru har sha biyu bai biyo kiran ba ga yunwa ta fara kawomun farmako dan Al'ami
n tsotso ne da shi ba na wasa ba, sha
ɗ
aya idan ya yi sai na samu wani abun na cike gurbi. A can gidan Anty Labiba da yake ba na aikin komai sai dai na ci abinci na kwanta shi ya sa na cika na yi dam kamar ba jego nake yi ba yanzu kuwa daga dawowar mu sati
guda har na fara jin ƙashin wuya na ya bayyana.
Ganin tunanin da tsammanin dawowar Bilal ba zasu kaini ko ina ba ya sa na zura Hijabi na na fita neman yaron da zan aika. Babu kowa a layin kasancewar rana ta take haka ta taka har bakin titi na yo cefan
e na da kaina. Sai bayan la'asar ya dawo na ringa kallon sa kawai yanda ya shigo babu ko tsinke a hannun sa sai fuska da ya ha
ɗ
e kamar hadari amma da ya shiga kitchen ya fito sai naga ya
ɗ
an saki fuskar ba kamar sanda ya shigo ba. Sai a lokacin ya ke ce mu
n wai ya ga missed calls
ɗ
ina me ya faru?
Takaici yanda ka san na rufe shi da duka kuma kamar wadda aka kullewa baki na kasa amayar masa da abinda ke cikin zuciya ta. Ban jinjinawa rashin ta idon sa na sai da ya tambaye ni ina abinci, haka na wuce na h
a
ɗ
a na kawo masa ya zauna ya hau ci na ringa kallon sa kawai har sai da ya gaji ya ce mun
"Wai kallon me kike mun haka ne ko so kike yi ki saka na ƙware?"
"Babu komai" na fa
ɗ
a ina cigaba da kallon sa. Ya bata rai ya cigaba da cin abincin. Wayar sa d
a ya ajiye akan dining lokacin da zai shiga kitchen ta
ɗ
auki ƙara, ban motsa na har sai da ya ce na miƙo masa ita kafin na tashi. Na ringa kallon sunan da ke yawo akan screen
ɗ
in 'JALILA ABJ'.
A iya sani na Bilal ba shi da wata yar uwa ta kusa ko ta ne
sa mai irin wannan sunan, amma ko wanda baya son sa in har zai bayar da shaida akan sa kowa ya sani Bilal bashi da kule kulen yammata kuma nima zan shaidi hakan domin wayar sa ko password babu akai tun ina
ɗ
auka na masa bincike ba tare da ya sani ba har na
saki zuciya ta na yarda ni ka
ɗ
ai nake da dashi dan haka ko yanzun abinda na bawa zuciya tabbaci akai shi ne Abokiyar aikin sa ce ba wata Mace daban ba.
[5/19, 22:05] Buhainat: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice
up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata
ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Ku
ɗ
in karatu yana wakiltar mutum
ɗ
aya ne, kiji tsoron Allah karki
ɗ
auki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin ku
ɗ
i ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*A
ccess bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 29*
Kafin na kai masa wayar ta yanke dan haka da na bashi ajiye ta ya yi ya cigaba da cin abincin ba tare da ya duba wanene ya kira ba. Duk yanda na so na mayar da h
ankali na kan Al'amin dake ƙananun rigima sai na kasa ƙarshe kawai na goya shi na yi tsaye ina kallon Bilal da ke cin abinci wayar sa na ƙara alamar shigowar wani kiran amma be amsa ba. Kamar me tsoron magana na ce masa
"Ana kiran ka a waya fa" ya
ɗ
ago ya
kalle ni kafin ya
ɗ
aga wayar ya karata a kunnen sa lokaci
ɗ
aya yana miƙewa tsaye.
"Ranki ya da
ɗ
e Hajjaju na" ya furta kalmar da naji ta dirar mun a ƙwaƙwalwa tamkar saukar aradu, ya gota ni ya shige kitchen yana murmushi ko na ce dariya ƙasa ƙasa. Ina
nan tsaye kamar mutum mutumi ya fito fuskar nan kamar an masa bushara ya sake wuce ni ya koma kan kujera ua zauna ya cigaba da amsa wayar sa.
Gashi dai ina gurin kuma kallon sa nake yi amma ba zan iya cewa ga abinda yake fa
ɗ
a ba dukda ba wai a hankali
yake wayar ta yanda ba zan ji me yake cewa
ɗ
in ba, Aa, gaba
ɗ
aya kunnuwa nane suka toshe ko kuma ƙwaƙwalwa ta ce ta dena fassara saƙon murya oho, kiran suna na da ya yi da ƙarfi ya maido da ni hayyaci na. Na sauke ajiyar zuciya kafin a hankali na matsa ku
sa da shi ganin ya miƙo mun wayar sa.
Screen
ɗ
in na fara kallo Jalila
ɗ
in ce dai suke magana kuma har tsayin minti goma kenan minti na goma da yin mutuwar tsaye.
"Ina wuni Maman Al'amin" ta fa
ɗ
a bayan da na yi sallama cikin muryar da banyi zaton ta j
i ni ba. Na amsa da "lafiya lau". Da "Eh, A'a " na ringa amsa mata tambayoyin da ban ma san me take cewa ba har ta gaji ta mun sallama ta kashe wayar ba tare da na maidawa Bilal ba.
"A can head quarter ta ke tare muka yi workshop
ɗ
in da na je da ita, ta d
amu kullum muka yi waya sai ta tambaye ni ke yau dai kun gaisa na huta" ya fa
ɗ
a bayan da na miƙa masa wayar.
Na sauke numfashin da ban san dalilin yin sa ba ha
ɗ
i da yin gajeran murmushin da iyakacin sa baki. Fita yayi ya barni. Ban san tsahon lokacin d
a na
ɗ
auka a zaune ba ban kuma san tunanin me nake yi ba har aka kira sallar magriba kafin na iya tashi daga gurin da nake. Me ya sa ban tambaye shi matar aure ba ce ko budurwa ko ba komai na samu cikakkiyar nutsuwa daga tunane tunanen da zuciya ta take ta
raya mun? Haka nan na yi sallah ina jiran ya dawo na ji cikakken bayani akan wacece JALILA? Daga muryar ta zan iya fasaltata a shekaru talatin zuwa sama daga kuma maganar ta na tabbatar yar gayu ce, har na fasaltata a idanuwa na irin matan Abuja jiki duk
madarar nan. Wannan tunanin ya saka mun ƙunci da rashin nutsuwa a zuciya ta amma kuma duk yanda ma zaƙu ya dawo na yi masa tambayar sai na kasa lokacin da ya dawo.
Sai da aka yi isha'i ya sake shigowa falon lokacin ina cin sauran abincin da ya rage, ya
zauna a kusa da ni fuska a sake ya
ɗ
auki Al'amin ya fara masa wasa ni dai kallo
ɗ
aya na masa na mayar da kai na cigaba da cin abincin da nake yi ina kokawa da zuciya ta dake azalzalata akan na tambaye shi wacece JALILA amma na kasa.
"Akwai sauran abincin
ne?" Ya tambaye ni, ba tare da na yi magana ba na girgiza masa kai kawai, ya sake cewa
"Ba har dare kika yi girkin gaba
ɗ
aya ba ko me?"
"Iya abin da na siyo kenan na dafa" na bashi amsa ba tare da na kalle shi ba, sai na ji ya ce
"Au, dama ba Gara a
ka kawi miki ba?". Na yi tsam kafin na waiwaya na kalle shi dan ban fahimci in da maganar sa ta dosa ba, wace Gara kuma yake magana akai?
"Wace irin Gara kuma?" Na tambaye shi ganin ya tsare ni da ido, ya ha
ɗ
e girar sama ya ce
"Gara kala nawa kika san
i?" Nima ha
ɗ
e tawa girar na yi na ce
"Nasan dai ana Garar aure ta al'ada, idan ita kake magana kuma an yi mun" na bashi amsa ina cigaba da cin abincin gabana. Sai ji na yi ya d
Sake cewa
"Kawai ki ce saboda mugun hali ku a gidan ku bakwa yin Garar hai
huwa ko kuma kece ba za'a yi wa ba tun da ba'a sona?"
Mamaki, takaici da haushi duk suka kamani lokaci
ɗ
aya. Bilal dai ba zai canza hali ba, sam bakin sa ba zai ta
ɓ
a koyon tauna kalami kafin ya furta su ba. Gyara zama na yi na kalle shi da kyau na ce
"Muguntar ce ta saka aka baka aure na, duk a cikin muguntar aka cika maka gida da kayan
ɗ
aki aka kuma ha
ɗ
o ni da kayan abincin da har yau shekara biyu auren mu babu wata uku kake ci a cikin su ba. Shara
ɗ
in ciyarwa akan Namiji ya ke ba Mace ba, haƙƙin ka n
e da ka kawo mun abin da zan ci a cikin gidan nan ba wai ka zauna kana jiran a kawo daga gidan mu ba, baka ga duk ƙoƙarin da aka yi maka a baya ba ashe kai nan jira ma kake yi bayan Garar aure a sake lodo ta haihuwa a sake