Showing 210001 words to 213000 words out of 287295 words
ya rigada ya ganni dole na ƙarasa na amsa masa tambayar da yake mun akan ina zanje.
Shi ya sauke a gidan Anty Labiban, kamar mai tunanin zan tafi wani gurin bai matsa ba
sai da na shige gidan nayi murmushi kawai ina cewa "ko Abba ya zata guduwa zanyi ne ya kasa ya tsare".
Ban
ɓ
oyewa Anty Labiba dalilin zuwana gidan ba, tayi shiru tana kallona kafin ta ce
"Wace shawara kika yankewa kanki Halima"
"Ban rigada na yanke
shawara ba Anty amma In sha Allahu yau zan sanar da ke matsayata". Tayi jimm kamar tana so ta ce wani abu amma kuma ta fasa sai ta ce
"Toh Allah ya sa muji alkhairi" na amsa da "Amin".
"Zaki tanadar masa wani abu ne?" Ta tambayeni, sai da nayi
ɗ
an mur
mushi kafin na ce
"Sniper kika tanada ko green leaf?"
Ta fashe da dariya ta ce
"Daga abin kirki?"
"Ai ko shi na san sai yayi shakkar cin wani abu a gidan nan yau" na bata amsa ta wuce kitchen tana cewa
"Toh ai shikenan, bari in
ɗ
orawa mijina abi
nci yana hanya". Tashi nayi na bita na kama mata aikin, hirar duniya muka ta
ɓ
a tun ina amsawa ka
ɗ
an ka
ɗ
an har na ware abinda na manta rabon da inyi doguwar magana irin haka harda dariya inaga tun ranar dana dawo daga Camp
ɗ
in NYSC.
BILAL
Tamkar zai fas
a kuka ya fa
ɗ
awa Nasir inda Halima ta ce su ha
ɗ
u,
"Tare zamuje amma" ya fa
ɗ
a Nasir ya ce
"Wa? Ni? Idan ka ganni a lahira toh kaini akayi. Ai kayi mai wuyar tunda har ta amince ku ha
ɗ
u ai akwai haske a lamarin kawai kaci gaba da addu'a shine ya rage yan
zu".
Bilal ya goge zufar da ta keto masa dukda sanyin Ac daya cika motar kafin ya ce
"Toh dan Allah zaka rakani gurin Kawun su Zulaiha, ta ce yana son ganina yau saboda ita ma na kashe wayata tun safe idan ba haka ba addabata zatayi da kira".
Dariy
a Nasir yayi ya ce
"Ita amaryar ce tun yanzu ta fara isarka? Ikon Allah. Ha
ɗ
e rai Bilal yayi ya zaro wayarsa daga aljihu ya kunnata tun bata gama saituwa ba kuwa sai ga kira ya fa
ɗ
o ko suna bai fito ba alamar contacts
ɗ
in ma basu gama booting ba amma ya g
ane number Zulaiha ce. Ya nunawa Nasir yana cewa
"Ka gani ko?" Ai kuwa Nasir ya bushe da dariya ya ce
"Bala'i, sai kace bokanya? Ta hango ka kunna wayar a madubinta. Alamar yayi shiru Bilal ya masa kafin ya amsa wayar, yanda kasan
ɗ
an da ta haifa tanaj
i ya amsa ta ce
"Wannan wane irin kut****uba ne zaka kashe waya ayi ta kiranka ba'a samu?"
Sai da ya zare wayar daga kunnensa ya duba screen
ɗ
in ga sunanta nan ya fito yanzu DUNIYATA kafin ya sake mayar da ita kunne mamaki na neman kashe shi da jin
abinda ta fa
ɗ
a, ita kuwa ko a jikinta ta balbale shi da masifa akan me y kashe waya gashi nan ya janyo Kawunta ya kira yana ta musu tijara su da Ummansu akan rashin zuwan da bai yi ba.
"Ya ce kazo ka same shi a nan gidan bayan sallar magriba idan kaga
dama karka zo na rantse da girman Allah sai ka gane baka da wayo sai na nuna maka kai ƙaramin yen yen ne" ta ƙarƙare maganar kafin ta ja dogon tsaki ta kashe wayar.
Bilal dai kasa cire tasa wayar yayi daga kunne yayi sakato kamar wani wawa tsabar mamak
i. Nasir daya gama jin komai, duk yanda ya so ya hana kansa yin dariyar data taso masa dole ya saketa jin tana nema ta shaƙe masa maƙogaro, Bilal ya kalle shi da idon sa da suka ka
ɗ
a sukayi jajir sai kawai ya
ɓ
alle murfin motar ya fita waje ya ringa sheƙa
dariya kamar wani ta
ɓ
a
ɓɓ
e.
Bilal ya sauke ajiyar zuciya bayan daya ajiye wayar maganganun Zulaihan na masa amsa kuwwa a kunne, a fili ya ce
"Ba ita bace, aljanunta ne suka motsa"
"Aljanu ko?" Nasir daya bu
ɗ
e kofar motar ya fa
ɗ
a yana sake sheƙewa d
a dariyar data fi ta farko. Sai da yayi da gaske kafin ya iya riƙe kansa ganin Bilal
ɗ
in ya cika yayi fam kamar zai fashe. Suna tafi Nasir na cewa
"Amarya, Amarya bata laifi ko ta kashe
ɗ
an masu gida" shi dai Bilal tafi ka mutu bai ce masa ba har ya sauke
shi a ƙofar gidansa.
"Dan Allah ka shirya da wuri" Bilal ya fa
ɗ
a bayan Nasir
ɗ
in ya sauka, Nasir ya danne dariyarsa kafin ya ce
"Baka da matsala mutumina sai ka zo" ya wuce ciki yana sake tuntsurewa da dariya.
"Da
ɗ
i na da gobe saurin zuwa" ya fa
ɗ
a
a fili yana shiga gida.
Bilal kuwa gida ya wuce, sai da ya shiga gidan ya tuna ashe ko breakfast bai yi ba yau
ɗ
in. Sai lokacin ya ha
ɗ
a tea ya sha da ya ringa jin sa kamar ma
ɗ
aci, yanzu Allah ka
ɗ
ai ya san mutum nawa suka san halin da yake ciki. Ƙila ha
r yan unguwar ma sun sani yanzu da ya shigo sai ya ga kamar masu gadin layin daya wuce sunyi gulmar sa gaba
ɗ
aya ya tsargu ji yake kamar duk in da ya wuce kawai kallonsa akeyi amma labari ya gama baza ko ina ga halin sa.
Zuciyarsa ta raya masa komai za
i wuce da zarar Halima ta dawo kuma Zulaiha ta tare, musamman tunda dama maganar daga
ɓ
angaren Haliman ta fita idan aka ga ta dawo gidansa hakan zai aka kokonto a zukatan mutane domin da wahala ace bayan wannan abun ya faru kuma ta sake komawa gidansa amma
idan akayi haka kuma gashi yayi aure za'a iya cewa ma saboda ƙarin auren ya saka tayi masa yarfe yanda mata suka saba yiwa mazajensu idan zasuyi aure.
Wannan tunanin da yayi ya sanyaya masa zuciya har ya
ɗ
an samu nutsuwa ya shiga kiran Agent
ɗ
in daya
bawa tallar shagunan Jalilah. Duk ma abinda zai faru a ƙalla ya tsira da abinda zai riƙe kansa surutun mutane mai wucewa ne da sunyi sun gaji zasuyi shiru. Agent
ɗ
in ya sanar masa an samu mai siyan gurin kuma da daraja sosai dan haka gobe yaje a ƙarƙare ma
gana dan dagaske suke kuma da ku
ɗ
in su a hannu.
Wannan labarin ya sake faranta masa rai, yana kashe wayar ya kira Engineer dake aikin gyaran sabon gidan da ya siya wanda Zulaiha zata zauna a ciki. Sabon gini ne bene na zamani wanda har plaster anyi mat
suwa ta saka mai shi siyarwa kuma ya same shi kwasha kwasha,
ɗ
an gyara ka
ɗ
an akayi na abinda baiyi masa ba, jiya da ya je an gama komai ƙwayayen wuya ake ƙarasa sakawa dan har yaran da zasu share gidan su wanke ya tarar an samo yana kiran Engineer kuwa ya
gaya masa ai an gama komai yanzu ya bar gidan muƙullin yana hannun maigadin gidan da yake jikin nasan dama shi ake barwa ya ma tura masa video ta WhatsApp tun
ɗ
azu.
Godiya ya masa, a ransa ya ayyana da gidan zaiyi bikon Halima. In dai ta yarda kawai ita
ta koma can idan ya so a canzawa Zulaihan penti ta shiga nan ita tunda babu abinda gidan yayi a matsayinta kuma ko wanda bai kaishi ta samu ba ai sai dai ta godewa Allah ita kuwa Halima dama gidan bene shi ya dace da ita tunda daga cikinsa ta fito.
Ƙ
a
rfe shida ya fesa wanka ya tafi gidan Nasir daga can zasu wuce gidansu Zulaiha dukda idan ya tuna abinda ta fa
ɗ
a masa
ɗ
azun sai ya ji kamar kar ya je sai kuma zuciyarsa ta tuna masa ba laifinta bane iskokin da Ummansu ta fa
ɗ
a ne suke ta
ɓ
a ta sa wannan ya t
aushi zuciyarsa ya isa gidan Nasir
ɗ
in.
"Kaga na Halima angon Zulaiha ga kuma Jalilah a gefe" Nasir ya tsokane shi bayan ya fito, ya ha
ɗ
e rai tam ya ce
"Bana so"
Nasir ya
ɗ
aga hannu biyu sama ya ce
"Na bari Allah ya baka haƙuri". Suna tafe suna
yar hira har suka isa unguwar, sai da suka tsaya sukayi sallar magriba a masallacin layin su Anty Jalilah kafin suka fara wucewa gidansu Zulaiha dan yana sallah ta turo masa text wai ga Kawun fa ya iso.
A tsakar gida suka zaune, Zulaihan da Ummansu sai
Nuratu sun sha hijabai kamar masu takaba kowacce ta ra
ɓ
e a gefe tana zare ido sai Kawun nasu dake zaune kan farar kujerar roba yana girgiza ƙafa. Tare suka isa da Mijin Nuratu wanda shima suka zo tareda wani abokinsa, suka gaisa gaba
ɗ
aya kafin akayi musu
iso suka zauna kan tabarmar da aka tanadar musu.
Cewa Kawun yayi Nasir da abokin Faruk Mijin Nuratu su
ɗ
an basu guri.
"Ai komai yana son sirri, dukda ku aminanku ne amma ai akwai abinda ba zaku so suji akan matanku ba ko?" Kawun ya fa
ɗ
a, Ummansu Z
ulaiha tayi saurin cewa
"Ai babu wani abu ma"
"Ni dai ban sako bakinki ba idan kuma ba zaki iya yin shiru ba kema ki tashi ki bamu guri" Kawun ya taso mata. Hannunta Zulaiha ta kama cikin alamar tayi shiru, Kawun ya ja tsaki ya ce
"Na san dai dukka
ninku ba yara bane tunda kuma kuka yarda har kuka
ɗ
aura aure da yaran nan toh kunji kun gani kuna son su a yanda suke ne musamman kai" ya nuna Bilal. Kallonsa Bilal
ɗ
in yayi yana jira yaji ƙarin bayani Kawu ya cigaba da cewa
"Tone tone dai babu kyau tun
da abinda ya faru ya rigada ya wuce amma dukda haka dole in ja musu kunne shiyasa na taraku gaba
ɗ
aya, babu kawo ƙara dan iya shari'ar da nayi a baya masa Allah ya bani lada na gaji. Duk wacce ta muku ba dai dai ba kuci ubanta dai dai gwargwado amma banda
dawowa gida iya gatan da zaku musu kenan dan wlh duk wacce ta kuskura aurenta ya mutu ta sani ba sake auruwa zatayi ba dan suma
ɗ
in ba ƙaramin jahadi sukayi ba da suka.... "
"Haba Shafi'u wannan wane irin abu ne?" Ummansu ta sake katse shi. Zulaiha ta
ruƙo ta ganin tana shirin miƙewa Nuratu dai na gefe kanta a ƙasa Kawun ya ce
"Mariya, ko dai rufa rufa kuka yiwa yaran nan shiyasa kike ta katseni kar in fa
ɗ
i gaskiya?"
"Rufa rufar me? Ai duk cikinsu babu wanda bai san tsanar da ka mana ba da irin sh
arrin da kake bibiyarmu da shi kullum. Kai nake so na rufawa asiri karka zubar da mutunchin ka a gabansu amma ka saki baki bayan duk wanda yake sauraronka yasan tsantsar hassada da baƙin cikin Allah yayiwa yara gata ya basu mazaje irin wanda yayanka basu s
amu ba shiyasa kake so ka
ɓ
ata su toh ta Allah ba taka ba" Umman ta fa
ɗ
a cikin masifa.
Kawun ma baiyi shiru ba ya ce
"Sai dai ki na
ɗ
e tabarmar haukarki da kunya amma ni
ɗ
an gaskiya da gaskiya ne kin sani kuma dole in tabbatar ba'ayi kitso da kwarkwata
ba".
Bilal dai kallonsu kawai yake, shi dai Umman da ya sani sama da shekara goma idan aka saka mata hannu ba zata ciza ba amma yau ita ce take tada jijiyar wuya haka tana masifa ana riƙeta kamar zata daki Kawun?
Faruk ne ya ce
"Dan Allah kuyi haƙ
uri, ni dai a
ɓ
angarena babu wata matsala dan babu abinda Nuratu ta
ɓ
oye mun kuma iyayena basu nema mun aurenta ba sai da sukayi bincike kuma da yardarsu da komai na aureta dan haka ni dai a gurina babu wata matsala In sha Allahu".
Bilal ya kalle shi,
kansa ya fara kullewa. Wai toh meye ake cewa an sani da shi bai sani ba?
Zungurinsa Faruk
ɗ
in yayi yayi diriri kafin ya ce
"Nima haka".
"Toh madallah Allah ya taya ku ruƙo sai aje ayita haƙuri. Ranar Asabar in Allah ya kaimu aka ce tariya ko? Dama
babu wani taro da za'ayi, mutum biyu sun isa daga kowanne
ɓ
angare suzo su
ɗ
auki amaren" Kawun ya sake fa
ɗ
a.
Umma ta zauna tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudun tsira, daga nan Kawu ya miƙe ya musu sallama Faruk ma ya fita bayan ya ce Nuratu ta bi
yo shi aka bar Bilal da Umma sai Zulaiha data sunkuyar da kai kamar wacce take gaban Alƙali. Yafi minti goma ya gagara ce musu komai suma haka sai da Nasir ya kira shi a waya kafin ya miƙe yana musu sallama ko motsi Zulaihan batayi ba Umman ma kamar a tsor
ace ta masa Allah ya tsare ya fita, a soro ya tarar da su Nuratu tana rungume jikin Faruk tana kuka ya giftasu yaa jin sa yana cewa
"Ki dena kuka, kowa da kalar ƙaddararsa a rayuwa kuma na gaya miki ko me kika aikata a baya ina sonki a haka tunda dai ki
n tuba kin dena kuma har kika iya fa
ɗ
a mun na tabbatar dagaske ne kin bari karki ji komai In sha Allahu daga ni har dangina ba zaki samu matsala da kowa ba".
Ya ringa juya maganar a ransa, to ko dai abun iya ita Nuratun ya shafa shiyasa Zulaiha bata gay
a masa ba? To menene ma? Ya ringa tambayar kansa a garin tunani har ya wuce gidan Anty Jalilan ma sai da Nasir ya ankarar dashi.
A falon baƙi suka zauna, ya ringa kallon Al'amin da yayi kamar bai sanshi ba dan da suka shiga yana kallon su ya juya ya wu
ce sai da Nasir ya kira shi ne ya tsaya amma yaƙi zuwa gurin Bilal
ɗ
in Nasir
ɗ
in ma daya riƙe masa hannu bai sake da shi ba Alhaji Sale na shigowa kuma ya fizge ya tafi gurin sa.
Faran faran suka gaisa da Alhaji Salen da bai da
ɗ
e da shiga gidan ba daga
tafiya, masallaci zai fita sallar isha'i dan haka suka tafi gaba
ɗ
aya. Can falon ya ce a kai musu abinci bayan sun dawo suka ci tare Nasir dai ya ware ya kashi abincin sa Bilal kuwa dukda yana jin yunwa ka
ɗ
an ya ci dan haka kawai yake ji kamar wata manaƙi
sar aka shirya masa idan ba haka ba shida yake da laifi a gurinsu shine harda bashi abinci?
Sai da aka kwashe kwanukan kafin Alhaji Salen ya wuce ciki ya turo musu Halima. Ta shiga da ƙaramar sallama kai a ƙasa kamar farin shigar maita haka Bilal ya zu
ba mata ido yana kallonta, rabon da ya sakata a ido tun ranar daya kaita gida. Ramar da tayi ta ta
ɓ
a shi dan sukda hijab ne har ƙasa a jikinta ramarta ta fito ƙarara.
A hankali ta ringa tafiya harta isa kujerar da tafi kusa da ƙofa ta zauna, murya ba a
mo ta gaida Nasir da tausayinta ya rufe shi lokaci
ɗ
aya. Halima mace yar gayu amma kalli yanda ta lalace lokaci
ɗ
aya ta zama kalar tausayi. Miƙewa yayi ya fita dan ya basu guri, yana rufo ƙofa Bilal ya tashi da sauri ya nufeta, da sauri itama ta miƙe tayi
baya ganin rungumarta yake shirinyi.
Ta galla masa hararar da ta saka gabansa fa
ɗ
uwa domin ko a mafarki bai ta
ɓ
a ganin ta da irin kallon nan ba.
HALIMA
Ganinsa nayi tamkar baƙin kumurci lokacin daya nufoni, hoton fuskarsa akan cinyar Jalilah ya gi
fta mun da sauri na miƙe na ja baya ganin yana rungumata.
"Meye haka Halims? Kin san adadin kewarki da nayi kuwa? Dan Allah ki tsaya inji
ɗ
umin ki ko zan samu nutsuwar zuciya nayi kewarki har bansan adadi ba wlh" ya fa
ɗ
a yana sake nufo ni.
Tsawa na
buga masa da dukkan ƙarfin daya rage mun, ya tsaya can a inda yake cikin mamakina, ban damu ba na nuna shi ina cewa
"Ka koma in da ka taso idan ba haka ba zan tafi ba kuma zaka sake samun damar magana dani ba har abadah"
"Haba my Halims sai kace wa
cce zata mutu?" Ya fa
ɗ
a yana ja baya bai dai koma kan kujerar daya tashi ba, nayi tsaki na ce
"Ba wasa nakeyi ba, minti goma kake dashi idan kuma ya cika baka nutsu munyi maganar data kawoka ba kada ka tsammaci zaka sake samun irin wannan damar a gaba".
Ganin da gaske nake ya saka ya koma kan kujerar ya zauna yana kallo na, nima zama nayi kaina a ƙasa dan ba ƙaramin ƙarfin hali nake ba ji nake kamar an jona mun mayen ƙarfe yana jana in je gare shi amma na dake.
"Wlh Halima duk abinda ya faru ba laifi
na bane sharrin shai
ɗ
an ne" ya fa
ɗ
a yana zamowa daga kujerar kamar zai durƙusa a ƙasa. Ban kalle shi ba ya